Author : Sumayya Abdulkadir Category : Taskar Novels
karatunsa “Sakeeinah” ‘yar asalin kasar
Libya a garin Tripoli. Kusan duk abin da ya mallaka ya narkar ya auri Sakieenah sabida
aurensu babu sauki, suka yi aurensu a Tripoli, ban da kanin shi Tasi’u da Baffanshi Malam Sule
babu wanda ya sani, sai da suka kammala karatunsu tsaf suka tattaro suka dawo, Sakinah
dauke da guzurin ciki na watanni biyu.
Lami ba ta zata ba, ba ta tsammana ba sai ganin Abba ta yi da sankaceciyar Balarabiya wai a
matsayin matarsa. Hauka ne kawai ba ta yi ba, tayi bala’in tayi masifar ta yi kuka ta yi kuka
kamar ranta zai fita, tana murnar sabon gida katoton gaske ita kadai ranta, amma ashe abin da
Abban zai yi mata ke nan.
Don haka a washegari ta goya diyarta ta yi yaji ta koma Bidda gidan wan mahaifiyarta. Abba ya
yi sintirin biko har ya gaji amma ta ce ba za ta dawo ba. Inda amarya Sakeeinah ta yi zamanta a
Dutse tana rainon cikinta hankali kwance, har zuwa sanda ta haifeni.
Saboda son da Abba ke yiwa Sakeinah ya sanya yasa mini sunanta. Kamana daya da
Mamana, ko a farce ban yi kama da Abba ba. Sakienah ta kama dangin Abba ta rike cike da
alheri, mutuntawa da kyautatawa.
****
A can Bidda Lami ta fara shiga halin ni ‘yasu, a dalilin Baffan nata ba wani mai hali
bane(Herbalist) ne wato mai bada magungunan gargajiya, ga shi dama ba ta san babanta ba
balle danginsa, haka ta tashi ta ganta tare da mahaifiyarta, ba ta kuma taba tambayarta cewa
wane ne babana ba balle danginsa. Ita ma kuma ba ta taba budar baki ta yi mata zancen ba. Hatta abin da za su sanya a bakinsu ita da diyarta ya soma gagararsu, sannan ga rashin arzikin
da matan kawun nata ke mata, don sun gaji da zamanta tare dasu, babu gaira babu dalili ga shi
ta ce mijin bai saketa ba balle su yi tunanin watarana za ta yi aure su huta.
Babban tashin hankalinta yadda yaran gidan suke cin zalin Safina, ba ta isa ta rarrafo tsakar
gida ba za ta jiyota ta tsandara kuka, dole kullum kuma ko yaushe ta goya ta don sama mata
lafiya.
Naira biyar wannan ta fi karfinta, tunda ita ba karatu ba balle ta yi aiki, ita ba jari ba balle ta yi
kasuwanci. Gaba daya sun fige sun lalace ita da diyarta, yadda wanda ya sansu a Dutse da
‘Yan Leman ya kuma gansu a lokacin da kyar zai gane su.
Ga Abban tuni ya yi watsi da al’amarinta ya kama Balarabiyar matarshi ya kulle a kofar
zuciyarshi. Don haka ta soma bin soron malaman tsibbu wai a kado mata hankalinshi ya dawo
da kanshi ya mai da ita.
Sunyi iya yinsu har sun gaji, duk ‘yan gwala-gwalanta sun kare amma babu M.T Liman babu
dalilinshi.
Mahaifin Abbanmu mai rasuwa shi ne babban limamin garin ‘Yan Leman, don haka gidan
kakanninmu ba boyayye bane a ‘Yan Leman. Babba da yaro kowa ya san gidan Liman Tukur.
Sakinah ta bi duk kannen Abba mata dake gidan aure ta jari mai tsoka, kowacce ta kama
sana’a. Dija na kiwon kaji (Poultry). Zainaba na dinki, Kubra na gashin gurasa. Sannan ta tsaya tsayin daka wajen ganin M.T Liman ya kula da karatun Tasi’u wanda ke karatu
a jami’ar Maiduguri mataki na biyu, fannin aikin jarida. Don haka suma suka kamata suka
rungume abin da basu samu daga Lami ba, sai bakin qyashi da rowa, sannan da rashin son
kowa ya rabi mijinta. Wannan halinta ne tun M.T ba shi da komai.
Watanni biyar ke nan da tafiyarta, a lokacin cikin Sakina ya shiga watanni bakwai, ta goyo ‘yarta
babu ko biko ta dawo ‘Yan Leman gidan Baffa Sule ta ce gata ta dawo dakinta, ya bai wa M.T
hakuri ya maidata.
Baffa Sule bai yi la’akari da halayen Lami ba da kowa nasu ke kokawa ya sa M.T ya mai da ita
dakinta, ba tare da wata tashin-tashina ko bin ba’asi ba.
Ya ce, ai shi dama ba korarta ya yi ba ita ce ta kori kanta, amma idan ta san ba za ta zauna
lafiya da matarshi ba, to ta koma inda ta fito.
Tana kuka da al’ajabi ta ce, “Ta yarda za ta zauna da Sakienah”. Don haka ta bude dakinta ta
share ta zauna, sai dai kuma ko maganar arziki wannan babu ita tsakaninta da Sakeinah, duk
da yadda Sakina take ba ta girma.
Zuwa lokacin Sakina ta zama ‘yar gari ta iya Hausa, sannan M.T ya samu promotion suka
tattara suka koma jihar Lagos. A can ne Mami ta hadu da Adama take mata aikace-aikace tana
biyanta, tana zaune tare da su har suka koma jihar Kaduna inda aka haifeni.
Aminci mai tsanani ne tsakanin Mami da mai aikinta Adama. Bayan haihuwata ba da dadewa
ba mahaifiyata ta koma kasarsu, bayan ta ajiyewa Abba ni ko yaye ni ba ta yi ba.
Na girma na ganni a gidan mahaifina cikin wata irin rayuwa mai wuyar fassaruwa ta kunci da
zalinci, har ma da rashin tsoron Allah cikin al’amarinsu.
Sai kuma Allah ya sanyawa Adama tausayina, duk da kiyayyar da Mami ke min, take taimaka
min a boye tun ina kankanuwa. Ta sha kwatata in Mami na jibgata, haka nan tana bani abinci a
boye, a duk lokacin da muguntar Mami ta motsa ta hanani.
A tasowata na ga Abbanmu ya yi aure har sau hudu bayan mahaifiyata, kowacce kuma ta fita
ba tare da wani kwakkwaran dalili ba. Kamar yadda na fada a baya. Don haka ne Abba ya
hakura da aure, sai Mami ita kadai ranta.
Shekaru biyu ne tsakanina da Nadiya wadda Mami ta haifa a Kano, muna Porthearcourt aka
haifi Ilyas, sai Abba (Muktar) sannan Nazir wanda aka haifa a nan Abuja.
Mami gogaggiyar ‘yar duniya ce ta a buga a jarida, ta yi kawaye da yawa matan manya iri-iri a
nan Abuja, masu ra’ayi da akida irin tata ta rashin hada mijinsu da kowacce mace ta hanyar
asire-asire da tsaface-tsaface, musamman Hajiya Laila, uwargidan Justice Ribadu mataimakin
Abbanmu, halinsu daya, akidarsu daya, sannan turbarsu daya na sun fi karfin zama da kishiya. Da dukkan alamu kuma suna cin nasara cikin al’amuransu, tunda dai an ce tsafi gaskiyar mai
shi ne.
Domin ita Hajiya Laila duk kishiyar da a kai mata sai ta rasa wani bangare na jikinta sannan ta
fita, kamar ido, kunne ko kafafu. Wannan ne yake tsorata mata da auran masu mazaje.
Don haka Mami (Lami) ta zamo BABBAR MACE a katafaren gidanta. BABBAR MACEN da
mijinta ke shayinta. BABBAR MACEN da ta takurawa rayuwar mijinta, ta hana shi dandana
kwanciyar hankalin aure da ni’imar da Allah ya yiwa sauran mata.
Sannan BABBAR MACEN da ta yi sa’ar raba shi da farin cikin rayuwarsa (Sakeeinah), ya koma
waina a tanda, sai yadda Lami ta juya shi.
Don haka ne duk wani wanda ya san irin rayuwar da M.T Liman ke yi a gidansa, ya kuma
ganshi a waje, cike da haiba da kamala, dole ya tausaya masa, har in yana da imani, to ya taya
shi da addu’a ya kuma zubar masa da hawaye.
****
[9/14, 9:59 PM] Asmau: To haka abin yake a gareni, kullum na yi sallah ina yiwa Abba addu’a,
ko da nike yarinya karama, na san Abbana ba ya jin dadin zama da Mami. Sau tari idan ina son
ganin shi, na leka ta tagar falonshi, na kan ganshi ya yi tagumi, kuma kullum cikin rama yake,
abin da ya haifar mishi da cutar hauhawar jini, yake yawan ganin likita akai-akai, wanda yake
zuwa har gida yana duba shi duk sati.
M.T Liman mutumin kirki ne, kowa ya san haka. Wanda abin hannunshi bai rufe mai ido ba,
wanda Allah ya halitta da yawan kyauta da alheri.
Sai dai kuma duk yadda ya so da ya dinga tallafawa ‘yan’uwansa hakan ya ci tura, Mami ta bi ta
kankane komi, komai zai yi sai ya yi shawara da ita, ta tabbatar masa ta amince.
Tuni su Kubra suka dauke kafafunsu daga gidan dan’uwansu saboda wulakancin da Mami ke
musu, duk dumbin arzikin Abba basa cin kwandalarsa sai dai su Nadiya. Dadinta da ya kasance
Kawu Tasi’u ya kare karatunshi ya yi hidimar kasa ya samu aiki a can Dutse, shi yake tallafa
musu.
A da Daddy baya watanni uku bai je ‘Yan Leman ba gai da Baffanshi Sule da sauran danginsa,
amma tun sanda muka dawo Abuja Mami ta san kissar da ta yi ta hana shi, don a cewarta Baffa
Sule baya kaunarta, tunda a kanta ya ki auran ‘yarsa, wadda kuma mijinta ya rasu a wannan
lokacin tana zaune gida. A cewarta so yake ya sake kakaba mishi. Har ga Allah Abba na son ya auri Suwaiba ko don Baffa Sule ya ji dadi, amma yana tsoron kara
yunqurin yin auren, don ya san ba da dadewa ba wani mummunan abin zai faru ya saketa. Don
haka ya yankewa zuciyarshi da muguwar rawa…... gwamma kin tashi.
****
Yau ranar ta kasance asabar, don haka duka yaran gidan suna nan basu je makaranta ba.
Abbama yana gida bai je ko ina ba.
Ina bayan gida ina wanke-wanke, yayin da Adama ke gefena tana yankan salad. A can wani
gefe daban Abba ne ke wasa shi da dan makotanmu Salim a kan kekunansu suna wasan tsere.
A cikin gida kuma dakin su Safina ita da Nadiya suna kwance kowacce a gadonta suna cin
biskit din digestive suna kallon film din Indiya a tashar tauraron dan Adam.
Safina ta kau da idonta daga talabijin din cikin damuwa, ta ce,
“Yanzu abin da Mami ke yi tana jin tsoron gamuwarta da Allah kuwa Nadiya? Tun asuba ta
tashi Sakeeinah, diba har zuwa yanzu tana bayan gida tana aiki ba ci ba sha”.
Nadiya ta ce, “To laifin wa? Laifin Abba da ya saki babarta. Da tana nan ai ba za ta yi mata haka
ba, ya aura ya saki kamar na mamajo”.
Mami ta shigo duk suka yi muqus! Ta dauki abin da za ta dauka a dakin ta fita. To haka ne, hatta
‘ya’yanta shayinta suke balle Abbanmu. Amma a zahiri akwai boyayyar kaunata ta ‘yan
uwantaka a zuciyoyinsu wadda ba ta da tasiri tunda basu da karfin gwiwar da za su bayyanata
a fili.
Safinah na aji hudu na sakandire, ya yin da nake a J.S 2, sai Nadiya tana J.S 1, Ilyas da Abba
duk ‘yan firamare ne.
Abba ya zo wucewa ya ganni, takaicin duniya ya kama shi, wai kamar shi da arzikinsa da komi,
wai amman a ce ‘yarsa ce ke wanke-wanken gidansa.
Ya ce,
“Sakinah!”
Cikin wata murya mai rauni da rashin amo. Na dago kumburarrun idanuna wadanda ke cike da
barci da gajiya na dube shi. Ya ce,
“Tashi ki tafi daki”.
Cike da tsoron abin da hakan zai haifar na tsame hannuna na dauraye na mike na nufi hanyar
cikin gida, ina jinshi yana ce da Adama ta karasa wanke-wanken.
Dakin da Mami ta ware min a gidan kusa da dakin su Safinah ne, da babu komi sai fallen
tabarma da kayana cikin (Ghana must go), amma shi Abba bai san hakan ba, ya dauka daki
daya muke kwana da su Safinah, don bai cika kwakkwafi ba.
Daga nan inda dakina yake ina jiyo muryar Abba a dakin Mami, ya ce cikin tattausar murya,
“Yanzu saboda Allah Lami ina kudin da nake biyan masu aiki suke yi miki aiki? Da za ki dinga
sanya Sakinah cikin ayyukan gidanki masu tsauri? Naki ‘ya’yan kin killace su a daki suna kallon
talbijin?”
Mami sai ta fashe da kuka, cikin kuka take cewa,
“Dadin ta dai ba za a yi min gorin haihuwa ba, har da bakinka za ka fada min cewa Sakina ba
‘yata ba ce don kawai ina yi mata horo na ‘ya mace. Uwar tata tana sonta ta ajiye min ita tun a
bakin nono? Na yi rainonta har Allah ya rayata, don na dan sa ta aikin da bai taka kara ya karya
ba shi ne za ta kashe min aure?” Mamaki ya hana Abba cewa komai, ya juya ya fita. Fakam-fakam! Ta yo dakina ta soma buga
kaina da bango, na yi kara na sa kukan da ya jawo hankalin su Safinah, sai dai babu wacce ta
yi gigin zuwa. Shi ma Abba yana ji amma bai kara juyowa ba.
Yana isa daki ya kwanta numfashinsa yana hawa yana sauka da sauri da sauri, ya mike a three
seater ya dafe kirjinsa da hannun dama.
Kafin zuwan Dr. Saddiq ya galabaita matuka. Ya shigo da sauri ya bude lokar magungunanshi
ya diba ya dora masa da gorar ruwan eva mara sanyi. Sannan ya yi masa B.P yasa abin
awonshi kan kirjinsa ya girgiza kai cikin damuwa ya ce.
“Justice I’m sorry to say, jininka ya kara hawa har ma fiye da yadda ba a so. Nayi-nayi in ji
damuwarka a matsayina na likitanka ka ki gaya mini. Idan babu aminci da amana a tsakanin
likita da patient dinsa sai mene ne?”
Abba ya yi murmushi cikin karfin hali, ba tare da ya kawar da murmushin ba ya ce,
“Ka yi hakuri Saddiq, ina iyaka kokarina wajen yakice damuwar nan amma na kasa. Ko na yi
kokarin yin hakan bana cin nasara.
Sannan baka da maganin da za ka maganta min damuwata, sai dai ka bani maganin da zan ji
sauki a cikin gangar jikina, amma ban da a zuciyata”.
Dr. Saddiq ya ce,
“Yadda muke da maganin kowane ciwo dake cikin gangar jiki, haka muke da maganin kowacce
damuwa ta hanyar counselling. Ta hanyar amfani da hankali da tunani wajen magance ita
wannan damuwa. Ka yi hakuri Justice ka gaya min damuwarka cikin amana, insha Allah zanyi
iya kokarina in ga cewa na taimaka wajen gushewar damuwarka”.
Abba ya yi shiru yana dan tunani, ya yin da Dr. Saddiq ya ci gaba da kwantar mai da hankali ta
hanyar gaya mishi tausasan kalamai masu sanyaya zuciya, har dai ya amince Dr. Saddiq mai
kaunarsa ne, don haka ya yanke shawarar kwaye mishi bargon damuwarshi.
“Saddiq matsala ce ta cikin gida, yarinyata Sakinah ke fuskantar matsin rayuwa a cikin gidan
nan, saboda mahaifiyarta ba ta nan, mun rabu tun Sakinah na jaririya, don haka Sakinah ba ta
san dadin uwarta ba.
Na auro uwarta a kasar Libya, na kuma koma na neme ta a adireshinta ban tarar dasu ba, an
ce sun dade da barin Tripoli sun koma wani gari daban.
Ina so in samawa Sakinah kyakkyawar rayuwa, ban san ya zan yi ba, domin mai dakina ba za
ta bari ba”.
Dr. Saddiq ya ce, “Wannan har matsala ce da za ka dinga wasa da ranka a kanta Justice?
Shawarata a nan shi ne, ka dauki Sakinah ka kaita makarantar kwana”.
Abba ya ce, “Saddiq mai dakina ba za ta bari ba”.
Dr. Saddiq ya maimaita kalmar, “Mai dakina ba za ta bari ba”. Da Abba yake yawan ambata.
Which means yana shayinta, a matsayinsa na Alkalin-alkalai na kasa bakidaya, zai iya zartar da
hukunci kan diyarshi ba tare da amincewarta ba.
Abba ya ci gaba da cewa, “Ka ga ana zuwa hutu, dole Sakinah za ta zo hutu bayan kuma ni so
nake kwata-kwata in nesanta ta da gidan nan. In kaita inda za ta samu hutu dauwamamme ba
na wucin gadi ba.
Don haka ne na so na sadata da mahaifiyarta, in roketa alfarmar ta rike min ita zuwa sanda za
ta isa aure in aurar da ita, in yaso in dauki dawainiyarta.
To ka ji yadda al’amarin ya kasance, wato sun bar garin da na sansu a nan sun koma wani garin
daban wanda ban sani ba”.
Dr. Saddiq ya ce,
“To ka yi mata AURE!”
Abba ya zaro ido cikin tsorata, kafin yace, “Wanene zai auri wannan ‘yar kankanuwar yarinyar
da ko kirgen dangi ba ta fara ba?”
Daga can bakin kofa aka ce dasu;
“…..ARCH. ABDULHAKEEM RIBADU”.
Cikin nutsattsiyar murya irin ta dattijantaka, kuma kamilalliya mai kwantar da hankalin mai
sauraro.
Abba da Dr. Saddiq suka juya a razane kuma a lokaci daya. Justice Ibrahim Khalil Ribadu ne
tsaye a bakin kofar, aminin Abba kuma Alkalin da ke bin bayan M.T Liman a Najeriya gaba
daya.
Ya karasa shigo da gangar jikinsa gaba daya cikin falon yana murmushi, ya mikawa Dr. Saddiq
hannu suka yi musabiha, ya mikawa Abban ma.
Ya zauna a kusa da shi yan ninsa da ido cikin yannayi na tausayawa, ya ce,
“Yanzu Ba don kunnuwana sun jiye min ba M.T Liman da haka za ka hallaka kanka a banza ka
cucemu, ka cuci al’ummar Najeriya, ka cuci kotun koli a kan al’amarin da bai kai ya kawo ba!
Duk hirar da kuke ina tsaye ina jinku, al’amari irin wannan M.T Liman ka kasa furta shi gareni
sai ka barshi yai ta cinka a zuci?
To za ni ce ta tadda muje mu, nima nan zuwa na yi idan kana da diya ka bani in baiwa
Abdulhakim, jiya an yi min tozarcin da ban taba zata ba a kan auren Abdulhakim.
Abdulhakim ya kai kayan aure da izinin yarinya iyayenta sun ce ta fi karfin ta auri dan Alkali, me
na sama ya ci balle ya baiwa na kasa? A takaice dai an dawo mai da gayyar tsiyar shi
(kayanshi).
Yana nan kwance a daki ciwon so zai illata shi. Na ce da shi ya kwantar da hankalinsa cikin
satin nan zan yi mishi aure a inda na ga ya dace, ba diyar masu kwadayi ba”.
Abba ya girgiza kai ya ce,
“Sai dai ko Safinah, ita ce mai shekaru sha hudu, tana shirin shiga sha biyar. Amma Sakinah
shekarunta