Zuciyar Mutum Book Complete By Sumayya Abdulkadir Takori .pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Taskar Novels

Chapter   1 / 7

1 to 3K   out of 19.8K words

[9/14, 9:59 PM] Asmau: ZUCIYAR MUTUM…….
…….BIRNIN SA
1
Sunkuye nake a gindin famfon bayan gida ina wanke kayan kashin qanina Nazir. Safiya ce mai
tsananin hazo, wanda matsanancin sanyin watan Fabrairu ya haifar.Ina sanye da ruwan bular
siket mai fadi da farar suwaita mai dogon hannu. Kaina nade cikin hular sanyi mai fuska irin ta
yaran-goye. Sanyin dake kadawa na karfe shidan safiya da sanyin ruwan da nake wankin da
shi, shi ya hadu ya haifar min da toshewar hanci. Can anjima sai kaduwar hakora qaf-qaf-qaf!
Kamar ana kada cokali a tsakaninsu, don haka na mike a galabaice na juya hagu da dama,
kana na mai da raunannun idanuna da suka kankance cikin dan lokaci zuwa hanyar cikin gida.
Na tabbatar babu kowa ba mai kallona, babu motsin su Ilyas ‘yan rahoton Mami, wadanda nake
da tabbacin yanzu suka yi juyin farko a barcin su.
Sai na tsame hannuna na koma karkashin bishiyar guava dake nan bayan gidanmu na kwanta,
na cure na dunkule wuri guda kamar curin alkaki, jikina na kaduwa, hannayena biyu na hade na
tura cikin rigata, hawaye na bilbila. Wani bangare na zuciyata ya ce,
“Bai kamata ki yi kuka ba SAKINAH! Inda sabo ya kamata a ce kin saba........” To ana saboda
wahala ne???

Rai dangin goro ne yana bukatar hutu, ko da kuwa a ce jikin na karfe ne. Balle jiki na jijiya da
tsoka, wanda jinni ke zagayawa a cikinsa. Na tambayi kaina shin haka sauran yara tsararrakina
da nake gani a makaranta suke rayuwa a gidan ubansu? Shin da gaske ne Abbanmu ne ya
haife ni ko ko “Walagigi” ce kamar yadda Mami ke cewa? To idan ba Abbanmu ne ya haifeni ba, mai ya sa ake kirana da sunanshi a makaranta? Idan shi
ya haife ni, mai yasa ake banbanta ni da sauran kanne na?
Kwakwalwata ta cunkushe, tunanina ya yi zurfi, haka kukana ya tsananta. Hawaye ya hade da
majina, har sautin kukan ba ya fita sosai. Watakila hakan ne ya yi sanadiyar da ban ji tahowar
Mami ba, sai tsawarta da azababben rankwashinta mai shiga har cikin kwakwalwata, ya dusar
mini da ji da gani na wucin gadi.
Ta kama hannayena duka biyun ta murde tana ci gaba da rankwashina, na yi kara don azaba.
Cikin kuka na ce,
“Ki yi hakuri Mami ba zan sake ba.....”!.
Ta ce, “Ko ubanki bai isa yau ya bani hakuri ba. Ashe gaskiyar Ilyas ne idan na saki aiki barci
kike yi a gindin bishiya. A yi magana ki ce ayi hakuri. Da bana hakuri dake da tuni na kada ki
duniya kamar yadda na kada uwarki. To dadin ta kina yi min amfani, don haka ya zame min dole
in yi hakuri dake, amma ba zan dauki wannan sakarcin ba”. Ta sakar min kunnen ta hankadani iya karfinta, na bugu da bishiyar da nake jingine da goshina,
kafin ki ce meye wannan goshi ya haye ya yi suntum. Na kai hannuna duka biyun na dafe
goshin ina kuka mai ban tausayi.

Kwalar rigata Mami ta ja keeeey……! Har jikin famfon, kana ta jawo kwandon kayan wanki ta
karo, duk rabi na Nadiya da Ilyas ne, sai ‘yan kadan na Abba.
Ta ce, “Mintuna talatin na baki ki wanke su fes! Ki dauraye ki shanya ki yi ta firfita su har sai sun

bushe. Ga doya can a kicin ki feraye ki dora, idan ta dahu ki kirba mana sakwara a turmi kafin
Adama ta zo ta yi miya, kina ji na ko ba kya ji?”
Na daga kai da sauri, kamar in ce,
“Mami makaranta fa? Yau ba za ni ba?”
Na jiwa kaina tsoron al’amarin da hakan zai jawo, da rankwashin dake azabta ni, wanda ban
san lahanin da yake yi min cikin kwakwalwa ba.

Na dukufa wanki ba ji ba gani, na nemi sanyin da nake ji na rasa, zuciyata ta kekashe. Ina cikin
shanya na jiyo hayaniyar su Nadiya suna fita don tafiya makaranta.
Na zo bayan bishiyar goba na rabe ina lekensu, kaunata da makaranta na cigaba da ruruwa,
hawayena na ci gaba da kwarara. Na kai bayan hannuna ina share idona.
Daga inda nake rabe na jiyo Nadiya na cewa da Safinatu,
“Yau su Walagigi an gamu da fushin Mami........”. Safina ba ta ce komai ba suka fita.
Har suka gama ficewa ban gama dawowa hayyacina ba daga azabar zugin, rankwashin wadda
take a matsayin Mamana.

Na fara kirbar sakwara kenan Adama mai aikin Mami ta iso. ‘Yar kabilar ‘Itsekiri’, ba tun yau ba
nake jin tsoron Adama. Ba don komi ba sai don munin halittar ta.
Baqa ce wuluk! Guntuwa, amma ba (wada) ba. Mai nanannen hanci, idanunta miri-miri kuma
jajaye. Ban san me ya kai Mami daukar Adama a matsayin mai aiki ba. Sai dai ga yadda na
fahimta wani boyayyen aminci ne a tsakanin su, ba aiki kadai Adama ke yiwa Mami ba.
Adama tana nemo mata asirai a tsibirin su da tsubbace-tsubbace kala-kala a garinsu Bayelsa.
Wadanda ake dirkawa Abbanmu yana ci ina ji ina gani don ba tsorona suke ji ba, balle su boye
wai don ganin idanuna.

Ganin irin rikon sakainar kashin da wulakancin da Mami ke min, ya sa Adama jin tausayina, da
son jana a jiki, wanda ban ga dalili ba a matsayinta dai na aminiyar Mami. A kullum in tana aiki
na kan ganta da wani tsumma kunshe da wani abu wanda take shaka lokaci-lokaci. Idan kuma
ta shaka za ta yi ta aiki da kuzari babu gazawa. Daga karshe in ta gama aikin, zubewa take a
corridor din kicin ta yi ta barci har sai Mami ta tashe ta, ta ce ta tafi Baskwata.

Ina tsoron Adama, ita kuma tana sona, ba don komi ba sai don ba ta yi min kama da mutane
masu dauke da ALHERI ba.
To yau ma kamar kullum, tana shigowa muka hada ido, ta yankwane fuska kamar zakanya wai
ita a nufin ta murmushi ta yi min. Na yi saurin kau da kai.
Ta ce,
“Sakina, Sakinatun Abba”.
Ban amsa ba. Ta soma kiciniyar dora sanwa tana cewa;
“Yau muguntar Mami ko makaranta ba ta barki kin je ba?”
Ni dai ban amsa ba, sai jibgar doya nake tun karfina kamar Allah ya aiko ni, har da hadawa da
tsalle, wai don dai in samu sakwarar ta hada jikinta, amma yawan doyar ya sanya kamar ba
jibgarta nake ba.
Ta juyo ta dube ni ta yi dariya cike da tausayi, ta soma taku tana matsowa inda nake. Ta ja

kujera ‘yar tsugune ta zauna, ta sassauta murya ta ce.

“Da za ki bi shawarata da kin gudu wurin Mahaifiyarki kin huta. Dubi irin kyawun da Allah ya yi
miki, wanda bai yiwa kowa cikin gidan nan ba, ki zauna matar uba tana azabtar dake a banza.
Ai yanzu an daina wannan zamanin. Abu ne da ake yi a can wani karni a baya da ya shude,
amma ba a wannan karnin na ‘yancin kai da muke ciki ba”.
Na bi ta da kallo galala! Ina tunanin ko ba ta da hankali ne? Matar da ta tsige ni a nono, ta
dankafar dani hannun matar uba, bata taba waiwayena ba koda da ziyara itace wacce zan bi?,
Da dadi ba dadi na rayu da ita, har na kawo wannan munzalin. Shekaru goma sha biyu ba ta
waiwaye ni ba, ita ce wacce zan bi? Alhalin ba ta kaunata? Tunda ta iya ta barni tun ina bakin
nono, ba ta kara waiwayata ba! Nima zan ci gaba da hakuri, in ci gaba da rayuwata a haka.
Tunda dai wuya ba ta kisa, da tana kisa da tuni ta kashe ni tun ina mitsitsiyata.

Tukunna ma, ina na ga kudin jirgin da zan je Libya in nemo (Sakinah)? Libya a ina? A wane
bangare? Wadda ta tafi ta barni tun ina shekara daya, yanzu haka ma ta manta da kamannina.
Nima ban santa ba, ban san kamanninta ba. Sunanta kawai na sani a bakin Abbanmu, inda ya
ce sunanta ne aka sa mini. Magana nake a zuci ni kadai kamar zararriya. Ban san cewa a fili nake yi ba. Adama ta kafe ni
da jajayen miri-mirin idanunta, ta ce, “Zuwa Libya, da neman Mamanki ba wahala bane.
Abbanki yana da adireshinta. Kudin jirgi kuwa sai in baki so ba. Ni din nan ba wani sirrin Mami
da ban sani ba, idan kin lura duk ni nake kawo mata magungunan da take wa Abbanku amfani
dasu tana biyana.
To amma ai ba haka kawai nake mata wahalar ba, abin dari nake maidawa dari biyar. Ke baki
san Mami kurciya ta yi mata ba ta koma kasarsu ta kuma dawowa da Abbanku sadakinshi???”
Na saki baki ina kallon ta. Maganganunta sun girmi kunnuwa da tunani na, na bude baki da kyar
na ce,
“Ke wa ya gaya miki?”
Ta yi dariya sosai ta kai hannunta ta bugi kirjinta, “Ni din nan ni na binne asirin da hannuna a
makabarta. Sakina ki yi hakuri, Allah ne ya sanya min kaunarki, shi yasa nake gaya miki sirrin
Mami.
Ki yarda ina kaunar ki, ki tserar da rayuwarki ki tafi inda za ki huta. In ba haka ba Mami za ta
lalata miki kuruciya, babu birbishin imani a tare da ita. Idan ba ta lalata ki ta hanyar azaba da
wahala ba, za ta sabautaki da asire-asirenta kamar yadda ta sabauta duk wani da ya shafi
Abbanku. Ta sha gaya min ba ta kaunarki....... Ke kadai kika rage mata, ba ta son ki samu
gadon Abbanku. ‘Ya’yanta ne kadai ke da shi.
Sakina ki nemawa kanki gata, ki tserar da rayuwarki. Zan ranta miki kudin jirgin zuwa Libya, in
kin je sai ki aiko min......”.
Cikin tashin hankali da tsorata, gami da tsanarta gaba daya ita da Mamin na ce,
“Babu inda za ni, duk abin da ya faru da bawa da sanin Allah! Nan ne gidan ubana, don haka
bani da wani gata da ya fi nan. Dabarata ko taki ba ita za ta fissheni daga abin da Allah ya
hukunta a kaina ba.
Kuma idan da rai watarana za ni ganta. Ki daina gaya min wani al’amarinku ke da Mami, babu

ruwana, bana son ji. Can a tsakanin ku, bana neman taimakon kowa sai na Allah. Don haka rike
kudinki, babu inda zani. Nan ne gidanmu, banida inda ya fishi. Don haka ki daina jin tausayina,
ba akan qaya nake ba”.

Ta yi murmushi ta mike ta karbi tabaryar daga hannuna,
“Kawo sakwarar in karasa miki, ba zan daina tausaya miki ba Sakina, bari na karasa miki kafin
ta zo ta kama kwarzabarki”.

Ba musu na sakar mata, jikin cabinet na koma na jingina, na runtse idanuna. Tunanin
abubuwan da na fahimta game dani kaina, ke dawo min filla-filla. Na fahimci ni SAKINAH ‘I am
leading an incomplete life.’ Duk da ina tare da mahaifina yana kaunata sama da komi a duniya,
to amma kaunar ba ta amfana ni da komi ba, tunda ba ta da power din da za ta fitar dani daga
halin kuncin da nake ciki a gidanmu.
Kaunar uba ba ta da tasiri musamman in babu uwa a tare da Da.

Ita ce ta san ciwonka, ita ce za ta tsaya ta san me kake ciki. Ita ce kadai za ka iya gane your
inner feelings, meye matsalarka, me ke damun ka? Ita ce za ta tsaya a kan tarbiyyarka da
rayuwar ka wanda ni duk ban samu wannan ba. Ita ce kadai za ta yi maka soyayya mara algus,
sai ko uban da ya haife ka. Ta yi aiki da karfi da lafiyarta. domin amfanin ka. Kenan ni Sakinah
na rasa wani bigire ko-ko bango, kuma majingini mai muhimmanci ga dan adam, musamman
diya mace........

***​​ ***
[9/14, 9:59 PM] Asmau: ZUCIYAR MUTUM....
Sunana Sakinatu, wadda mutane da dama ke taqaitawa da Sakinah.

M.T Liman shi ne mahaifinmu, wato Chief JusticeMukhtari Tukur Liman (Alkalin alkalai na kasa
baki daya).
Sakinah M.T Liman, shi ne sunan da nake amfani da shi, kuma kowa ya sanni da shi a
makaranta. Abbanmu dan asalin garin ‘Yan Leman ne ta jihar Jigawa, ya yi zuzzurfan ilimi a kan
alqalanci, tun daga kuruciyarsa a gida da waje da taimakon gwamnati, har zuwa matakin da
yake kai a yau. Tsohon Alkali ne fitacce, kuma shahararre wanda ya shahara kwarai a kan aikinsa, wanda ya
sha gwagwarmayar rayuwa a kuruciyarsa, ya samu kudi da suna a shekarun girmansa.

Abbanmu dan dangi ne gaba da baya, amma bamu sansu ba, domin babu mai kaimu, suma
basa zuwa. Duk ba don komai ba sai don Mami da izayarta, duk wani talakan da ya san ciwon
kansa ba zai kawo kafarshi gidan M.T Liman ba, ko da kuwa a ce a ciki guda suka fito. Mami
(Lami) ta hana wannan, Abba nata ne ita kadai da ‘ya’yanta. ‘Ya’yan Mami guda biyar ne, idan ka hada dani ‘ya’yan gidan mun zama mu shida ke nan.
Safina ita ce babba ‘yar kimanin shekaru goma sha hudu, sai Ilyas sannan Nadiya, Abba ke bin
Nadiya, yayin da Nazir ya kasance autanmu, wanda Mami take goyo a halin yanzu.

Mun zauna a garuruwa daban-daban, kusan duk manyan biranen Najeriya babu inda bamu
zauna ba, kamin daga karshe mu dawo nan Abuja inda Abba ke aiki da (federal high court)
matsayin Alkali na qololuwa da kasa ke tinqaho da shi, domin babu wani Alkali da ya sha gaban
M.T Liman a Najeriya gaba daya.
Zan iya cewa ban san dadin arzikin babana ba, tunda ba ci nake ba. Sitturuna kwata-kwata zan
iya kirga su; goma. Wadanda Mami ke bani kala dai-dai da kowacce sallah da takutaha. Don
haka mafi yawa sunyi min kadan haka nake sanya su a matse, suttura da kayan qawa na mata
sai dai in gani a jikin su Safinah. A tasowata na ga Abba ya auri mata daban-daban har guda biyar, in ka cire mahaifiyata. Sai dai
kowacce ba ta shekara take sa takalmanta ta fice. Ta karshen ce ma ta yi ciki har ta zo haihuwa
ta haifi qadangare ya yi kanta ya shaqe har ta mutu. Tun daga nan Abba bai kara marmarin
kara yin aure ba, Mami dai ita ce har yau babu wadda ta kama kafarta a zuciyarsa. Ita kadai ke
mulkin wannan tangamemen gida namu.

Mami ‘yar garin Bidda ce, sun hadu da Abba tun lokacin da yake karatu a jami’ar Legas
(UNILAG). Ita da Mamanta suna sayar da abinci da lemo cikin jami’ar, kullum a ‘kiosk’ dinsu
yake cin abinci har suka saba da Maman-Lami da Lamin kanta. Daga baya Maman Lami Allah
ya ji qanta ta daina karbar kudin sa, a kyauta yake ci kullum safe da rana, saboda son da ta lura
Lami na masa.
Bai taba tsammanin zai so Lami ba, sabida kwatakwata ajin rayuwarsu ba daya bane, ko
firamare bata yi ba, gata ba kyau ba ba fasali ba, ba’a zancen tarbiyya, gata girman Legas, a
yayinda shi ya kasance dan Limami jikan Limamai, amma farat Daya ya ji ta shiga zuciyarsa,
saboda ladabin da take mishi da yadda take nuna mishi kauna. Shikuma Allah yayi shi mutum mai girmama duk mai kaunarshi. Don haka ne da Mamanta ta
bijiro da batun aure tun kamin ya kare karatu bai yi musu ba.

Ya zo gida ‘Yan Leman ya kawowa mahaifinshi Liman bukatar shi na aje masa neman auren
Lami a Bidda, ya manta da diyar wan mahaifinshi Suwaiba da aka yi musu baiko shekaru uku
da suka wuce, an hanata kula kowa tana zaman jiransa ya kare karatu kamar yadda ya bukata,
a lokacin yana kokarin hada (LLB) dinsa. Wannan shi ne abin da ya fara janyo masa sabani da iyayenshi, domin kafewa suka yi kan
sam-sam basu amince ya auri Lami ba. Kai ko su biyu basu amince ya hada ya aura ba, don
basu yarda da asalinta da tarbiyyar ta ba.

Wannan ne ya sa ya tsallake ya bar gida ‘Yan Leman. Suka je garin su Lami Bidda suka yi
aurensu, suka dawo Legas inda Mamanta ta kama musu haya a Surulere har ya karasa karatu.

A lokacin ne Maman Lami ta rasu, wadda ita ce taqamarsu mai tallafa musu, tunda ba aikin
komi yake ba. Dole suka tattaro suka dawo gida ‘Yan Leman.
Abba ya ce min wannan shi ne babban kuskuren da ya tafka a rayuwarshi, wanda har gobe
yake nadamar shi. Domin fata-fata mahaifinshi da mahaifiyarshi suka yi masa, suka ce ya tafi
sun sallama shi sun barwa Lami da uwarta.

Malam Sule mahaifin Suwaiba da ya ki aure kuma Baffansa, shi ne ya tsaya tsayin daka ya
sasanta tsakanin shi da iyayenshi suka hakura suka karbi Lami a matsayin surukarsu kan ba
yadda za su yi.
Aka ware musu sassa guda a nan gidan mahaifinshi suka zauna. Nan ya bar Lami ya koma
Lagos ya ci gaba da karatun shi. Bayan watanni uku-uku yake zuwa.
Don haka Suwaiba ta hakura da shi ta auri wani malamin firamare a nan ‘Yan Leman.
Allah bai bawa Lami haihuwa da wuri ba sai da Abba ya kammala karatun shi ya tafi (Law
School) ya kare ya samu aiki da babbar kotun jihar Jigawa, aka dauki shekaru uku da fara
aikinsa har ya samu ya kammala ginin da yake yi a cikin garin Dutse suka koma shi da Lami.
A lokacin Allah ya karbi ran Liman Tukur wato mahaifinsa, sai mahaifiyarshi Inna Abu da
qaninshi Tasi’u da sauran kannen shi mata Kubra, Dijah da Zainaba, wadanda duk an musu
aure sun haihu a gidan mazajensu.

Sun dade a garin Dutse kamin Abba ya samu damar fita qaro karatun Alqalanci a kasar Libya
da taimakon Gwamnatin jihar Jigawa. Ya bar Lami da yaron ciki. Bayan watanni tara ta haifi
Safina mai kama da Abbanmu sak, ashe rabon haihuwata ya kai Abbanmu kasar Libya.

Inda ya fada a matsananciyar soyayyar wata abokiyar

1 / 7