BACCIN SO BY M SHAKUR

Author :  M SHAKUR Category :  African Stories & Novels

Chapter   31 / 51

90K to 93K   out of 151.6K words

ma agansa atasahi gaba.
**



Wuraren 11 aka gama yima amare makeup wanda da kyar Amirah ta yarda dan she was feeling uncomfortable, makeup is something da bata taba yiba, Ya Rabbi ita karan kanta Ammi saida takara kallon Amirah cus yaune rana na farko datake ganin Amirah tazaman mata yar budurwa a ido dan she always sees Amirahnta as a baby, Amirah tayi kyau cikin black and gold lace data saka ana gama makeup din tazo wajen Ammi adaki ta zauna taboye abayan Ammi, batason yanda mutane keta kallonta da yanda taga mutane dayawa agidan acike ana hayaniya dudda babu kida ko DJ but she doesn t like it.
Kallonta Ammi tayi tace  tashi muje ahankali ta tashi Ammi tariketa, saita kaita dakin Baffa wanda babu kowa ciki tazuba mata abinci karba tayi tafara ci ahankali, Ammi na kallonta taci sosai sannan ta kalli Ammi tace  Ammi anjima zamu tafi gidan Ya Marwan? Gydamata kai Ammi tayi, murmushi tayi tacigaba da cin abincin sosai taci tana gamawa sai bacci, gyaramata kwanciya Ammi tayi tafito daga dakin tana kallon Miemie dake tareda kawayenta Miemie tayi kyau sosai, tadade tana bacci sai bayan asir ta farka Miemie tagani kusada ita tana kuka tana goge hawaye tashi Amirah tayi zaune ta tsareta da idanu saita matso ahankali tazo kusada ita murya chan kasa like a baby tace  menene? Cikin kuka Miemie tace  Amirah banson narabu da Ammi dake, banso saita rungume Amirah tana kukan wani iri Amirah tashigaji sai hawaye yashiga cikowa a idanunta, ahankali tadago Miemie saitakai hannunta kan fuskanta ta girgiza mata kai alamun tadena kuka, Miemie tadade tana kallon Amirah saita gyadamata kai, daidai Ammi tabude dakin tashigo takalli Miemie da idanunta sukai jajir anatse tace  kuzo ku shirya anzo tafiya daku daidai nan Lami na shigowa dakin tace  ina suke muje muje ga motoci sunyi layi a waje ana magrib zaku wuce, muje muje tai wajen Miemie tadagata suka fice, Ammi takalli Amirah tace  zomuje tasowa Amirah tayi saitazo dab da Ammi tana kallon fuskan Ammi sosai cikin yar karaman muryan nan tace  Ammi ai tare zamuje gidan Yaya Marwan ko ? Tsareta da idanu Ammi tayi saita gyadamata kai kawai, murmushi Amirah tayi ta rungume Ammi suka fito tare tana mammannewa jikin Ammi tana boye fuskanta wanka Ammi takaita tayi dawani ruwan turare sannan tafito da ita sukaje daki Ammi da kanta tashiga shiryata cikin wani lafaya black and red tasata tai salla Ammi bata mata wani kwalliya ba tasa mata kwalli saita zauna gaban Amirah tana kallonta hawaye Ammi taji zasu zubo daga idanunta dasauri tadauke kai dakin aka bude dasauri Amirah ta tashi taboye bayan Ammi tai lamo kaman yar yarinya, Lami dasauran manyan matan wajen suka shigo da Miemie dake kuka sosai an lullubeta sukace  ammm Ammi ga Miemie za a tafi da ita tsareta da idanu Ammi tayi saita lumshe idanu bata taba sanin this is how a mother feels when she s saying goodbye to her children ba sai yau, she s feeling kaman ta taya Miemie suyita kuka tare sabida yanda takeji amman saita dake anatse tace  Maryama I know daidai gwargwado nabaki tarbiya mai kyau, ke yarinya ce mai hankali da bazaki taba bani kunya ba, baki taba kuntata min ko batamin raiba, I pray Allah yabaki farin ciki irin wanda baki taba tunanin zaki samu ba gidan mijinki Allah ya albarkaci aurenku, go start your new life kinji My Babygirl Miemie rungume Ammi Maryam tayi tama kasa magana sai kuka da kyar tace  Ammi banso narabu dake dariya akahau yi adakin itama Ammi tai murmushi tace  ai duk diya mace saita rabu da iyayenta mumanan duk hakane maza dena kukan nan Ammi ta dagota, bakin mayafinta Ammi takama ta share mata fuskan tasss saita manna mata kiss a goshi tace  go to your home Maryam wasu sababbin hawaye ne suka shiga zubo mata.
EPISODE 5?? 4??




Lami tace  muje toh ahankali Miemie ta tashi saita zagayo bayan Ammi tai takalli Amirah dataga idanunta sun ciko da hawaye duk tayi wani irin kaman tasoma gane abin is getting real, ahankali Miemie tace  kin haddace number na dana Ya Umar ko? Gyadamata kai Amirah tayi ahankali, Miemie tace  toki kirani idan kika sami waya kinji bazan iya rayuwa babu ke ba Ya Amirah, you re my best Sister kuma in sha Allah zaki warke Ya Marwan zai kula dake kinji gyadamata kai Amirah tayi tana kallon yanda Miemie ke kuka saita rungume Miemie ahankali tace  kuka bari tadagota tana share mata fuska murmushi Miemie tayi tace  tom nadena, Bye Ya Amirah na Lami tazo takama Miemie suka fita da ita daga dakin Amirah tabisu da kallo sai kawai tafado jikin Ammi tana kuka sukaje waje.

Ammi tariga tagayama Lami itace zatabi Amirah cus Amirah bata yarda da kowa hakan yasa sai Harira kanwar Lami itane jagoran kai Miemie gidanta, saida Lami ta tabbatar an shiga mota sannan aka tafi yarage saura motocin su Tawagan Marwan, friends nasa guda biyu that are Drs yasanar sai Abba yabada motoci da drivers guda uku, dawowa dakin Lami tayi da kawayen Ammi dakuma makota har lokacin Amirah kuka take, da idanu Lami tama Ammi alamun it s time, dagota Ammi tayi tace  dena kukan yanzu tashi kibi Mama Lami kutafi gidan Mijinki Marwan anjima kadan ni sainazo idan na sallami baki na makema Ammi kafada tayi cikeda rigima alamun a a, Ammi tadan hada fuska tace  kinason nayi fushi dake ? Ahankali ta girgizama Ammi kai, Ammi tace  yauwa yarinyar kirki tashi to kuje, muje nasaki a mota da kaina kasa ma tashi tayi daga jikin Ammi da kanta Ammi tadagata daga jikinta saita gyaramata mayafin saita bata wani flat shoe black na Gucci ya Allah kafafunta sunyi kyau a takalmin tasaka Ammi tai jimmm tana kallonta itama Amirah haka sai kawai Ammi ta rungumeta Amirah ta kankame Ammi kaman jira take tafashe da kuka, Lami ta girgizama Ammi kai alamun kartai kuka da kyar Ammi ta daure saita dago tace  ke yarinya ne kike kuka haka, wuce muje Ammi takama hannunta da kanta Ammi tafitar da ita har waje jama a na binsu abaya wata roll Royce Dr Hassan yabude yace  motan Amarya ne wannan Ammi da kanta tasa Amirah aciki Lami tashiga ta dayan side din, su biyu kawai zasu zauna a motan sabida yanzu tana ganin jama a saita rikice, Ammi ta dake tai murmushi tana kallon Amirah data rirriketa that looks so scared tace  Ammi mutafi Ammi tace  eh bari kutafi zan taho uhn yarinyana tayi kyau, Lami bari nai sauri ganinan zuwa Lami tace  yauwa kiyi sauri Maman Amirah Ammi tace  to cikani sabida nai sauri na biyoku ahankali tasaki Ammi tana kallon fuskan Ammi sosai, Ammi tamata murmushi tace  good girl bari naje toh da sauri Ammi tai maza tamaida kofan tarufe tawuce zaure Amirah tabuta da kallo aka kunna mita akaja Ammi na labe azaure tana kallon ana tafiya da Amirah ta gidan miji kawai sai Ammi tafashe da kuka duk yanda zatai bayani bazata iya ba, but she s feeling too many things at a time, her only two daughters leaving her in the same day to start a new life, cikin those 2 imagine the sick one, that s helpless, weak, have zero idea how the world is itama ta tafi gidan miji, Amirah should be by her side, she should be protecting her not ta aurar da ita me Amirah tasani what if Marwan is not a good man ya cutar mata da yarinya eh? Babu abinda Ammi bataji kaman tafita tace adawo mata da yarta tafasa aurar da ita she s feeling so lonely Wayyoo Allah na, idanun Ammi har saida suka kumbura sabida kuka sannan ta lallaba ta tashi tashiga ciki.


 He s calling again Dr Hassan dake tuka motan yafadi yana daukan wayan,  Hey Dr ka kirani yafi sau miliyan yau, yes mun daukota she s here we are on our way dan juyowa yayi saiya ba Lami wayan yace  mijinta wants to talk to her Lami murmushi tayi ta karbi wayan saitace  Amirah ga Mijin naki tabata wayan karban wayan Amirah tayi garin karba tasa a speaker, murya chan kasa Marwan yace  Ameenah& .!
Kaman yabude abinda ke rike mata kuka kawai saita fashe da kuka sosai harda wani rerawa Marwan yayi shiruuuu yana sauraronta chan saiyace  so kike ki kasheni! Dan zaro idanu Lami tayi dasauri ta juyarda kai Dr Hassan yayi murmushi, Amirah da baruwanta da wayan na speaker ta girgizamai kai alamun noo, asanyaye cikin lallashi da tsantsan kauna yace  stop crying kinji gyadamai kai tayi asanyaye yace  wat do you want me to buy for you ? Ahankali ashagwabe tace  wayaaaa ahankali yace  mezakiyi da waya?  Miemie murya chan kasa yace  okay zan sayama matana waya wanda yafi na kowa kyau dazata dinga kiran Miemie, da Ammi, da Ya Mustapa da Baffa aciki ko ? Shiru tayi tana sauraronsa hankalinta nawani kalan kwanciya mamaki yakashe Lami daman Marwan din na magana haka, ahankali Amirah tace  uhn dan shiru Marwan yayi duk yanda yaso yadaure yakasa murya chan kasa yace  I m so happy you ve become my wife Ameenatu, and I m ready to give you not just this world but my entire life, I Love you! Wani bugawa kirjin Amirah yahauyi Dr Hassan ganin kar abokinsa yawuce gona da iri ga iyaye a mota yasa yace  yoh Docs you re on speaker wani kunya Marwan yaji dasauri ya katse wayan.


Amirah ta ijiye wayan jikin Lami tai shiru kanta sai maimaita mata I love you I love you yake, daga wajensu zuwa bangaren su Marwan it s soo far is like daga area yaku bayi zuwa area masu kudi almost an hour drive sukakai family house nasu Mami inda akai decorating sosai za ayi kamu parking akayi a dankareren compound din ganin mutane a compund din sai Amirah tarike Lami dasauri tana shirin fashewa da kuka ta tsorace tace  Ammiiii cikeda hikima Lami tace  Ammi na wajen nan muje ki ganta daidai lokacin Mami datasha shigan alfarma dasauran yayin Marwan sunzo wajen ana guda harda su Faiza da Farida da sun kosa suga wacece matan Ya Doc, dudda kan Amirah a lullube but tana ganin kowa ganin fuskokin dabata saniba sai kallonta suke suna murmushi suna guda saita wani koma baya dasauri tashige jikin Lami taja gyalen lami tarufe fuskanta duka tana sakin kuka ahankali kaman zata koma cikinta dan jimmm Mami tayi saita kalli su Ya Ammah tace  ku wuce ku tafi babu wanda yayi musu duk suka wuce, ahankali Mami tamika mata hannu calmly tace  Amirahhhhh! Dan dago kanta daga jikin Lami tayi Lami tace  je mamanki na kiranki hannunwanta Amirah tasa taja mayafin baya ta kalli Mami dake kallonta tanama Mami kallon tsoro idanunta na fitar da hawaye, sosai Mami ke kallon Amirah Ya Subhanallah Allah yayi halitta mai kyau awajen nan yarinya kaman ita tai kanta, and shes so adorable yanda take kukan ashagwabe, anatse Mami tace  taho muje bazan bari su kalleki ba kinaso kiga Marwan ? Tsare Mami tayi da idanu kaman bazatai magana ba saita gyadama Mami kai ashagwabe, Mami tace  yauwa toh zomuje tadade tana kallon Mami batasan mesa ba kawai saitaji zuciyanta yadan kwanta da Mami saita taho ahankali tasaka hannunta acikin na Mami, ita kanta Mami saida ta jinjina kalan taushin da Allah yama tafin hannun yarinyar tanajin kamshin datakeyi saukowa tayi ta tsaya gaban Mami, Mami tai murmushi sosai tasa hannu taja mayafin ta rufe mata fuska kawai she feels very happy yanda Amirah ta yarda da ita itama Lami taji dadin hakan Mami tace  sannunku da zuwa Bismillah ku Mami da Amirah na gaba tawagan kawo Amarya na baya, sai kallon Amirah da ba a ganin fuskanta ake but lallenta takalmin kafanta kayan jikinta kadai abin kallo ne yanayin fatanta kadai zaisa kasan tanada kyau, before sunso adanyi rawa but yanayin Amirah da Mami tagani kawai saita wuce da ita falo ta zaunar da ita kan kujera itama ta zauna kan kujeran tawagan kawo Amarya aka zazzauna su Ya Ammah dasu Farida suka shishigo sun kosa suga Amaryan ya Marwan, gaishe gaishe aka fara aka shiga kawo abinci da abubuwan ciye ciye dangin Amarya sukace Abiya kudin bude fuskan Amarya aiko su Mami da su Ya Ammah akai barin kudi sai Lami ya tashi tazo gaban kujeran ahankali ta yaye gyalen daga fuskan Amirah da rinanun idanunta, Amirah takalli kowa yanda ake kallonta dan har su wayanda suka kawota kallonta suke sai da sauri kawai tai hugging Mami taboye fuskanta abayan Mami, Farida tace  wowwwww Faiza this is Matar Ya Marwan she s dead pretty Ya Fadila tadan sosa kai tana kallon Ya Maryam tace  no be lie my brother sabi choose wife, he no disappoint duk cikin whispering suke maganan Maryam tace  but she s nuts Fadila tace  that s his specialty give her a month I doubt idan yarinyar nan bazata ji sauki ba takashe mata idanu sukahau dariya, wlh Mami doesn t know why but saitaji tana wani irin son Amirah kaman yanda takeson Faiza da Fadila somehow morethan yanda ma takeson Faiza da Fadilan cus this is a sick girl da batasan anything ba and kaninta hopelessly loves, she hopes and pray Allah yabata lafiya albarkacin auren nan da aka mata, Mami tadan juyo takalleta tace  nakaiki dakina inda babu wanda zai ganki? Gyadamata kai Amirah tayi ahankali, murya chan kasa tace  Mami ruwaaaa da kanta Mami ta tashi zata wuce tadauki ruwa dasauri Amirah ta tashi sai Mami ta tsaya tace  bani ruwa Faiza dasauri Faiza tadauki bottle water tazo wajen Amirah taboye bayan Mami Faiza ta leka bayan Mami suka hada idanu da Amirah tace  Hi tsareta da idanu Amirah tayi batare datayi magana ba, Mami tace  stop scaring her Faiza she will all get use to you guys give her some time Mami tabude ruwan sai tabata takarba kadan tasha taba Mami tasha sai Mami tacema Lami bari kuje gidan nata ita tana nan zuwa Mijin nata yazo saisu tafi tare, Lami tai murmushi tace tom wucewa gidan Amirah sukayi Mami ta tafi da Amirah sama zuwa dakinta.


Mami takaita har gaban gadon ta zaunar da ita tace  kinajin yunwa? Girgiza mata kai Amirah tayi cikin yar karaman tiny voice nata tace  Ammi na gatanan zuwa tsareta da idanu Mami tayi saitai murmushi tace  eh nan bada jimawa ba zatazo, yi zaman ki nan bari nakawo miki abinci kunnenta Amirah tashiga tabawa dan manyan dankunnen da aka samata na damunta bata saba saka irinsu ba, Mami tace  mesuke miki ? Ahankali Amirah tace  ciwooo da kanta Mami takai hannunta kunnuwanta tace  tsaya to acire saita shiga cire mata ta ijiye dan kunnen kan side drawer, Amirah ta kwanta tai lamo Mami tajuya tana bude kofa taga Faiza da Farida da Ya Fadila gaban dakin Mami tarufo kofan tana kallon Fadila tace  da girmanki Fadila ? Dariya tayi tace  Yaya that day ban kalli yarinyar sosai a hospital ba wlh she s so pretty wai bantaba sanin Marwan nada idanu dudda glasses yake sawa ba sai yau danaga matarsa su Faiza suka kwashe da dariya Mami tace  karki batamin yara Fadila dasauri Ya Fadila tace  Au wai dama agabansu nake magana kutashi daganan Yaya Fadila tabisu da gudu suka sauka suna dariya Mami tai murmushi tawuce da kanta tazuba mata dirty rice dayaji namomi baja baja da zobo mai sanyi da ruwa tahayo sama tabude dakin ahankali Amirah ta tashi zaune, Mami takawo abincin ta ijiye gabanta Amirah tasa hannu tadauka tafara ci ahankali tanayi tanashan zobo, Mami sai kallonta take she s very very innocent saitakeji kaman tarike ta anan ma kartaba Marwan, kawai saitakega kaman idan Marwan yanemi yarinya zai kara birkitamata kai ne cus tayaya kanta zai dauki wani tarayya da miji, how will she know yanda ake kula da miji, gida, girki da sauransu? This girl needs parents she needs to be under someone that will watch her not ita kadai tai zaman gidan miji, Mami dai sai lissafe lissafe take.

JAMA A MAMI TARIKE AMIRAH AWAJENTA A HANA MARWAN????


KO ABA MARWAN MATARSA???

BUT TAYAYA AMIRAH ZATA IYA RAYUWAN ZAMAN G0DAN MIJI BABU IYAYE KO WANDA WILL WATCH HER???

KUNA GANIN DA CONDITIONS DINTA ZAI YU???


DONT BE SELFISH OR SENTIMENTAL KUNA GANIN ZAMAN G0DAN MIJI JUST SHE KO ZAMAN GABAN IYAYE GIDAN MAMI WHICH ONE WILL HELP HER BETTER????
EPISODE 5?? 5??



Family house dinsu Umar aka fara kai Miemie. Babban gidane sosai anma irin na da dinnan, jama a cike gidan dan sunada dangi, ga makota duk anzo welcoming Amarya.
Anyi wake, anyi wake, anyi rawa kafin daga baya suka biya dubu 100k aka bude Amarya, zokaga ihu anata cewa wai balarabiya Ya Umar ya auro, Umman Ya Umar taba Miemie atampa da lace masu kyau da tsada tukuici Miemie sai kunya takeji tana sunnar dakai, daganan aka komar da ita mota aka wuce da ita gidanta dake nan chan wani sabon layi, area Masha Allah, Umar yayi bala in kokari a gina gidan, gidan flat guda da compound dakeda wajen parking mota guda daya, ya sassaka flowers agidan, aka shiga da ita bayan ansa tai alwala, Ammi tayi kokari anmata furnitures masu kyau na yayi na zamani, sosai Ammi spends her last dime on her kids especially Miemie kayan dakinta sukafi cin

31 / 51