BACCIN SO BY M SHAKUR

Author :  M SHAKUR Category :  African Stories & Novels

Chapter   27 / 51

78K to 81K   out of 151.6K words

Daddy yacemai yana zuwa zasuyi magana bayan an gama daurin auren nan, Baffa yace dai toh yashiga masallaci yazauna.

Abba dayayi shigan alfarma kiran Saleem yake baiga Saleem ko abokan sa ba kodaya masallaci sai su iyaye, ga liman ya tambayi wakilin Amarya Dady yace gashi, still ba Saleem dasauri yace ina zuwa dan Allah Liman, yafita waje dasauri kirjinsa sai bugawa yake yashiga kiran Saleem ba amsa, watsapp message yagani daga Saleem yabude dasauri video yagani saiya danna download yashiga, Saleem yagani tsirara yanashan giya yanacin mace baitaba ganin al auran kaninsa ba sai yau, dasauri yafita daga video yana istigifarai da karfin gaske kaman mahaukaci.  Astagafurullah Astagafurullah!


 Saleem, Saleem, Saleem Precious tai tapping fuskansa Saleem da idanunsa sukai jajir sun kada sun juya yasaki nononta yace  uhn Precious tace  zan kira Yayanka nabaka wayan, kacemai kafasa auren ya aurama wani yarinyar, kai Precious kakeso ita zaka aura, okay? Gyadamata kai yayi yace  okay Abba nacikin dilemma kawai yaga video call from Saleem cikin fushi yadaga wayan iya fuskan Saleem yagani ga nono abakinsa woh wlh Abba saiya kasa magana yakai hannunsa yadaura kan kirjinsa dake neman bugawa, Saleem da baya hayyacinsa yace  Kai Yays! Nafasa auren! Ka aurama wani ita! Ni Precious nakeso! Yawani ja nipples Precious ta katse wayan, baya Abba yayi zai fadi dasauri Babba Amininsa daya biyosa waje jinsa shiru jama a sun taru ana jiransa da ango ya taresa& & .
EPISODE 4?? 3??




Dasauri Babban aminin Abba Alhaji Bashiru yace  subhanallahi, lafiyan ka kalau ? Abba yace  Sa& sal& &  yakasa magana yana wani haki bana wasaba, yanada BP sosai dakemai barazanan ciwon zuciya, Alhaji Basharu yace  kaga dan girman Allah calm down put yourself together ga jama a anan, babu abinda yafi karfin Allah, kace Innalillahi wa innailaihi raji un! breathing out Abba yayi da kyar yace  Innalillahi Wa Innailaihi Raji un! La ilaha illallahu Muhammadu Rasulullahi SAW! Alhaji Bashiru yani bakinsa suka karasa tare yace  to gayamin menene? Abba daya sami natsuwa da kiran sunayen Allah dayayi cikin murya mai raunin gaske yace  Saleem ne yakirani video call yace yafasa auren, karuwai yakebi, wai karuwan sa yakeso ita zai aura, nama mance sunan daya fadi ni Abba yama kasa boye zancen karuwan, yabawa Alhaji Basharu tausayi sosai bana wasaba, ahankali yace  ya isa you don t have to beat yourself up like this, Matar mutum kabarinsa, dama chan Allah yayi ba matarsa bace, yanzu yazamuyi? Mesamu cewa duka mutanen nan eh? Abba idanunsa sukai jajir yace  ni Saleem zai tozarta yasa nazama karamin mutum anan? I will become laughing stock ai, ince musu an fasa aure ko yazanyi? This is so embarrassing Alhaji Basharu da shima Sam baiji dadin abin ba dan duk manyan manyan gari na wajen yace  babba dakai ai sai darajan ka yazuba wlh da kimarka kaje kace ango wanda duk an dauki Saleem a matsayin danka yace yafasa auren, think of something kan Abba yakulle baya tunanin komi yayi shiru kawai, Alhaji Basharu yace  Marwan fa?! Dasauri Abba ya kallesa kirjinsa na bugawa, Alhaji Bashiru yace  naga Dr Marwan shi ya dauke ka a matsayin mahaifinsa tunda maraya ne yataso a hannunka, we just have to do something and get out of this mess Abba yadade yana kallon Alhaji Basharu daya ambato sunan Marwan take wani natsuwa yashigesa sabida wlh yasan kukansa ya kare indai Marwan ne zai sharemai hawaye, anatse yace  nasan d ana, nasan cewa Marwan bazai tabaso na tozarta nazama abin kunya da abun dariya aduniya ba, Marwan yaro ne mai Imani da amana, da dattaku, da hakuri Abba yayi shiru kafin cikeda karfin guiwa dawani sabon confident yace  muje Marwan zan aurama Amirah Abba yayi gaba Alhaji biyedashi abaya suka wuce ciki, yana shiga duk aka bisa da kallo harda Baffa dan yasan Abba sosai a TV baitaba sannin zaiga mai kudi haka da idanunsa ba, karban speaker yayi yace  dan Allah ayakuri, ango yayi hatsari yanzu haka yana asibiti masallaci akadau salati, Abba yayi murmushi yace  let s go ahead adaura auren Ya Liman sunan d ana Dr Marwan! Yaba Liman speaker, alot of people basuma lurada difference dinba, dan a IV is Saleem, yanzu yace Dr Marwan, Daddy dai mamanki yakamasa cus yasan Saleem yasan likitan mahaukatan kuma Marwan, what happened? Saleem yacema yayansa shi bazai auri mahaukaciya bane yagudu tunda gashi yaki zuwa shine uban zai aurama Dr? Lallai mutanen nan rikakkun matsafa ne Daddy yafadi yana murmushi abinsa.

Daddy, Baffa, Abba, jama a da abokar arziki, suka sheda daurin aure tsakanin Dr Marwan da Ameenatu Amirah akan sadaki naira miliyan daya da Abba yabiya take yanke wajen Daddy ya amsa amatsayinsa na uba dakuma waliyi na Amirah aka shafa Fatiha! Aure ya dauru damdam!

Marwan na asibiti, Saleem na gindin mace, Amirah na gida dukansu babu wanda yasan meke faruwa banda Baffa dayaji an kira sunan Ameenatu Amirah wanda yasan cewa diyar kanwarsa ce Haleematu, sai Daddy da Abba!!!!!

Jama a yakuke ganin zata kaya ne=??
EPISODE 4?? 4??



Gaban Baffa bugawa kawai yakeyi trying to understand what is happening, me yakeji, ko banda Ameenatu Amirah shima Daddy yanada diya da Maman Baby mai suna Aminatu dasuke kira da Amirah ne? Sai gaishe gaishe ake ana rabe raben abinci lafiyayyu, mabukata na rububi ana amsa, Daddy yazo inda Baffa yake a tsaye jiki asanyaye yawashe baki yana gyara Babban rigan giznan dake jikinsa yace  Bismilah Baffa Baffa yabisa suka zaga waje inda Daddy yayi parking Range Rover dakeda rai tana numfashi Baffa yabi motan da kallo, Daddy yabude masa yace  shiga bismillah shiga Baffa yayi yazauna Daddy ma yashigo yajawo kofan yarufe yawani kunna AC yace  yauwaa sanyi yadan dake ka, ahhhhm Malam Sani yajira sunan Baffa yana zaro miliyan dayan daga aljihunsa saiya rabata biyu tsabagen maitan kudi yace  ga wannan miliyan dayan sadakin Amirah ce, ga dubu dari biyar ka kaiwa Uwarta a matsayina na ubanta dana aurar da ita narike wannan Baffa dake wani irin kallonsa batare daya karbi kudin ba yace  Amirah ka aurar Yusufa! ? Daddy yace  to laifi nayi dan na aurar da ita uban waye ubanta inba niba? Nine yayan mahaifinta uwa daya uba daya, a hannuna ta girma mahaifinta ya rasu, dudda kan ba dadi amman Allah yayi ta sami miji da Saleem zata aurar Babban amman kaman yayi tunani yace yafasa auren, uban ya aurama dansa karamin likitan ta Dr Marwanu, to me aciki bakin ciki kake mata? Zuciyan Baffa yayi zafi shine ke gayama Ammi kullum tayakuri idan tana kawomai karan Abba amman yau ransa ya munnana badan komi saidai tayaya zai kama yarinya ya aurar bai sanar da mahaifiyanta ba eh, Baffa yace  mesa zaka yanke wannan Babban hukuncin akan rayuwan Amirah batare daka sanar da mahaifiyarta ba Yusuf? Cikeda gadara Daddy yace  sabida na isa ne uba keda yarinya ba mahaifiya ba, ni ba kiranka nayi muyi musayan yawun baki ba dan banda lokacin nan sauri nake nakoma gidana dake GRA da Range Rover dita, ga sadakin ta nan ka kaimata zan basu address na gidan ka suzo su amshi matarsu atoh! Wuce kafitarmin daga mota karka samin dauda nidai Daddy ya shiga kakkabe kakkabe dan ko abu daya baiso yagani a motan, Baffa yadade yana kallonsa kafin yayi wata murmushi yasa hannu yadauki 500k da Daddy ya ijiyemai a jiki yajuya kudin ya kalla saiya kalli Daddy dake kallonsa yace  nayarda da abu daya daka fadi wanda babu amfanin musayar yawun baki nima bazanyi dakai ba amman dai kasani cewa akwai Allah Yusuf, sannan Allah yana kallon komi, ga kudinka niba dan sakonka bane, kaje ka kaiwa mahaifiyar yarinyar kudin da kanka ya ijiyemai kudin yabude kofa yafita Daddy ya sauke glass kasa yana ihu yace  oho dai kuma idan an isa Kuki Kai yarinya gidan mijinta kuga wlh ko k?t? kuka kaini nafiku gaskiya dan nine uban yarinya saidai ku mutu Daddy yahau zage zage.

Machine Baffa yahau bazaima iya tantance ga abinda yakeji ba aurar da Amirah? Yarinyar nan is a total sick girl, meta sani kan aure? He see sometimes Mamanta kemata wanka ma wlh, yana ganin yanda Amirah ke shirme, me Amirah tasani? Meta iya? Idan aka cutar da ita agidan auren fa mijinfa? Menene manufan su na auren yarinyar da ana gani andan cewa at this junction Amirah ba abar da za a aura bace dan babu kan,& Sosai Baffa ke lissafi haryakai gida, azaure yayi parking da sallama yashiga gidan Amirah da Ammi yagani a tsakar gida Lami da Miemie na kitchen, Ammi na tsefema Amirah kalaban kanta Amirah kuma na rike da bowl da naman Kazan kayan matan Miemie ke ciki tanaci tayi wani irin kyau da fresh tayi bulbul takara haske dan ana musu gyaran jiki, sallaman sa yasa Ammi yadago kai lami ma tafito tace  harka dawo Malam gyadamusu kai yayi Ammi ta tsaresa da idanu ganin yanayinsa daman yagaya musu ina zaije daki yashiga yace  zo Maman Amirah da Lami dasauri Lami tabi Baffa ciki Ammi takalli Amirah dakecin kaza abinta tace  Miemie karki bari taje wajen rijiya Miemie tace  toh Ammi tafito tazo zata cigaba da mata tsifan Amirah ta make mai cikin tar kannauwan murya tace  naki zafi
Uwardaka Baffa yashiga Lami tabiyosa dasauri tace  meya faru Babansu? Mesa kai wani iri haka? Daidai Ammi tai sallama Lami tace  shigo shigo Maman Amirah labule Ammi tadaga tashigo tana kallon Baffa daya zauna bakin gado saitaja kujeran dake gaban dressing mirror ta zauna takalli Baffa tace  Baffa meya faru? Karka wani damu kanka indai mutumin nanne, meya faru? Ammi ta kallesa sosai tana jira yayi magana, ijiyan zuciya Baffa yasauke ahankali yace  Haleematu ammm yasake shiru sai gaban Ammi tashiga bugawa sosai, ahankali Baffa yace  mutumin nan ya aurar da Amirah! Wani kalan zabura Ammi tayi tamike tsaye Lami ma haka ta dafe kirji tace  Innalillahi wa innailaihi raji un, Amirah ya aurar Baffa yadan sauke ijiyan zuciya yace  kodanakai masallacin naga mutane yace na zauna zamuyi magana bayan an daura auren nan kawai jinayi ana daurama Amirah aure, aka gama yakirani zuwa motansa yabani dubu dari biyar cikin miliyan daya na sadakinta wai nakawo miki, nabar masa kudin awajen yace zai bada address namu azo daukan Amarya kirjin Ammi bugawa yake sosai ba wasaba, saita koma ta zauna ahankali takai hannu tadaura hannunta saman fuskanta brain dinta was blocked for a moment saita kalli Baffa da murya wanda bazaka iya tantance wani yanayi take cikiba tace  kasan wanda ya aura mata Yaya? Ahankali Abba yace  that is where it gets complicated sabida Yusuf cewa yayi wai yayan yakamata ya aureta sai kuma aka aurama kanin Dr Marwan! Dawani kalan sauri Ammi takalli Baffa, Baffa yace  kuma mahaifin ya sanar a masallaci cewan yayi hatsari yana asibiti iyakan abinda nasani kenan Ammi tai shiru tai mutuwan zaune yaya yakamata ya auri Amirah sai aka bama kani wanda ke asibiti in all this thing the only person data sani is Marwan, da Yaushe har sukaje neman auren Amirah ita tana mahaifiyar Amirah batasan komiba, Dr Marwan bata taba ganin alamun yana son diyarta ba, wayan nan mutanen dasauri Ammi tace  yaya zaka iyamin kwatancen uban angon? Baffa yace yanada jiki da katon ciki haka yanasa glasses a idanu gemunsa fari tabbas sune wayanda yagani rannan da sukaje inda Marwan yake does that mean wanda yaduka ya gaidata dinnan shine Saleem din sai yafasa aurenta maybe sabida mahaifin najin kunya sai aka bawa Dr ita, wani abu taji a wuyanta, saitaji zafi aranta badan komiba saidan cewa Dr Marwan datake ganinsa mai amana yasan da anason diyarta bai sanar da itaba, ahankali Baffa yace  dakata Haleematu yawanci akaga diya anaso uba ake nema ama magana ba uwa ba kada ki fushi dashi wannan itace gaskiya! Ammi bamatasan maganan zucin datayi awaje tayisa ba, mikewa tayi azuciye dasauri Baffa yace  ina zaki? Batare da Ammi tajuyoba tace  zanje naga mutumin nan nanne fuu zata fice a falo Baffa yaci mata yarike mata hannu yace  Haleematou! Dasauri Ammi tajuyo tace  Yaya me kakeso nayi look at her kalleta! Tanuna Amirah dake compound kan tabarma Miemie namata tsifa saura guda daya hannuwanta biyu duka abaki tace  Yaya kai karan kanka zaka yarda a aurar da yarinya mai kalan wannan laluran me aure zai amfaneta dashi eh? Ka kalleta Yaya
Baffa yace  nasani Haleematu but fushi baya maganin komi ki tsaya ayi magana Asan yanda zamubi abim nan cikeda hikima dan aure fa ya dauru unless mijinta ne ya saketa kokuma kotu taraba aure amman dai Amirah kam ta auru MATAR wani ce yanzu hawaye masu zafi Ammi suka fito daga idanunta, Baffa yace  I know what you re feeling amatsayina na babba abu daya zan gayamiki tashin hankali baida amfani karki manta abinda aka gayamiki game da Amirah bata kaynar ganinki cikin tashin hankali ko damuwa dan warke wan nan da muka samu tayi zata koma gidan jiyane, da Dane kin isa kibar Amirah kizo nan bata biyoki ba? Ammi ta girgizamai kai Ammi tace  to kingani, shi mutumin chan so yake ki biyosa kuyuta bala i kuma bazaki bisa ba, kome yayi yaje shida Allah, aure fa ta auru yabada iko yanada hurumin aurar da Amirah da Miemie dan haka kibar wannan I think ni atunanina tunda kunsan likitan nan amatsayinmu na manya mu nemesa da iyayensa mu sanar dasu laluran Amirah mu nemi yasaketa kawai
Ahankali Ammi tace  babu abinda bai sani kan Amirah ba anatse Baffa yace  shine mutumin da Amirah tagayamin tanaso? Shiru Ammi tayi saita gyadamai kai, zatai magana sai Lami dasauri tace  tsaya Maman Miemie, zuwa asibitin sa ya_a Amirah taji sauki haka kinyi tunanin cewa tunda tana sonshi aurensa yasa kuma ta warke gabaki daya fa ? Ammi dasauri tace  to shi yanasonta ne Lami? Shirme kawai Amirah takeyi? Yana likita akan wani dalili zai auri mai matsalan kai eh anatse Baffa yace  banson ki nemi mutumin chan, ni zan nemi gidansu ko asibitin inda yake zaki gayamin naje nai magana dashi Ammi tadade tana kallon Baffa batai magana ba, Baffa yace  I know you re hurting kiyakuri kinji hawaye ne masu zafi suka zubo daga idanun Ammi batasan metama Daddy ya tsaneta da yaranta hakaba amman dai tabarsa da Allah.
EPISODE 4?? 5??





Daga wajen daurin auren nan bayan ya gaggaisa da mutane driver ne yatuka Abba bai tsaya ko ina ba sai asibiti, Mami na zaune kan gadon kusada Marwan data ke basa oath da kanta da yau shiya tambayi oat din, yarame Mami tayi kuka fin adad1 bata taba sanin soyaya zata iyasa Marwan yafice hayyacin sa ba, wayanta ne yahau ringing hannu daya tasa zata dauka sai Marwan yasa hannunsa ahankali ya karbi bowl din yana magana kasa kasa yace  take your call Mami Mami tadan kallesa taga yacigaba dashan Oats din ahankali, takai wayan kunne batamaso ta tambayesa an daura aure lafiya cus she s afraid she will hurt Marwan more sai kawai tai shiru, ahankali Abba yace  fito parking space akwai maganan dazamuyi yanayinsa taji saitace  okay tom saita kalli Marwan dayayi kaman baimasan da Abba take magana ba, tace  Abban ka na kirana, ina zuwa Gyadamata kai kawai yayi baice komiba Mami tawuce tafita daga dakin tana gyara mayafinta tafito direct zuwa motan Abba daga ciki yabude mata baya tana zuwa saita shiga tana kallonsa baya farin ciki yana cikin damuwa tace  baka da lafiya ne meya sameka? Takai hannunta zata taba jikinsa saiya kama hannunta tareda sauke ijiyan zuciya yace  Zainab yau namiki laifi Abba yayi shiru Mami takasa magana gabanta sai faduwa yake
Ahankali yace  I know Marwan kanni ki ne, kece matsayin mahaifiya garesa amman yau amatsayina na wanda ya dauki Marwan dan cikinsa na dauki wani babban hukunci kanaa batare dana tambayi shawaran ki ba Abba yayi shiru saiyace  babu abinda zan iya boye miki aduniya saiya bude wayansa yashiga chats na Saleem yace  watch this video da zuciya daya Mami ta amsa tana danna video tai wani ihu ta yarda wayan kasa ta kulle idanunta tana salati Abba ma haka dukansu sunajin karan muryan Saleem da karan yanda yake sex dan Mami bata danna purse ba ta yarda wayan Abba ne yaduka yadauki wayan saiya tsaye da video yakalli Mami yace  nasan bai dace na nuna mikiba but inaso kiga abinda ya tunzurani nayi abinda nayi ne yayi shiru yace  bayan Saleem yaturomin video nan yakirani video call yana kan aikata alfashan sa idona idanun Saleem ya sanar dani shi bazai auri Amirah ba karuwansa yakeso ina miko magana lokacin biyu tawuce jama a birjik masallaci manyan mutane da fada aure bama aa ango ba zai zama abin kunya gareni da iyalaina dana sana ata, the only solution to the problem danagani is yaron daya daukeni tamkar mahaifi wanda bazai taba saba umarnina ba and bakowa bane wannan ba illa Marwan! Abba yayi shiru yana kallon Mami kaman yanda take kallonsa, saiya kama hannunta asanyaye yace  I don t know idan zaki dauki abinda nayi kaman na cutar da kaninki ne na aura masa wacce bawai lafiya kaman kowa gareta ba, zaki iyamin kowani hukunci kikaga dama amman na aurama Marwan Amirah Sweetheart!
Mami tadade tana kallonsa she s extremely happy dan yau takara yarda cewan Allah baya bacci kuma inhar mutum matarka ce ko anika kake sai tazama matarka,

27 / 51