Chapter 8 Reading SAFIYYAH Sirrin Tsakaninmu By Maman Maama HN Novels

SAFIYYAH Sirrin Tsakaninmu By Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   8 / 21

21K to 24K   out of 62.6K words



Al'ameen ya karbi wayar yana kallon hoton jiki yana girgiza kai, a ransa yana matukar tausayin dan uwan nasa saboda yasan zafi da kuma zakin so, ya kuma fahimci soyayyar tayi wa Gidado mugun kamu, sai dai bai yi dace ba. So baiyi masa adalci ba.

Ya mika masa wayarsa yace "Muhammadu...... You should stop thinking about how to see or talk to her. You should start thinking about how to forget about her. Mama da Abba are very worried. She is not worth that. Nothing is worth that". Gidado yace "I can't. Ba zaka gane ba Ya Ameen. Ko da zan manta da ita ɗin ina bukatar in san gaskiya. Ina bukatar in ganta mu zauna muyi magana ta fahimtar juna ni da ita. In san ko akwai wani abu da yake damunta.."

Al'ameen ya mike tsaye, baya son yaji haushin Gidado amma kuma ya kasa hana kansa. Yace "okay taso muje gidan su sai mu tambaya" Gidado ya kalle shi bai ce komai ba dan ya fahimci bakar magana yake gaya masa, ya sake cewa "ko kuma ka kira wani a cikin yan gidan su kaji abinda yake faruwa. Ko babbar kawarta haka, ai nasan ita ma zata sani". Gidado ya jingina kansa a jikin bango yana jin kamar ya tashi ya shake Al'ameen. Al'ameen yace "ohh haka ne fa. Na manta. Baka san ko daya a cikin wadannan ba. How are you going to know the answers to those questions kuma?".

Sai kuma ya dawo ya tsuguna a gaban Gidado yace "look Muhammad, there is no way da budurwar da take son saurayi, so na gaskiya kuma na aure, zata ki kaishi gidan su, zata kuma hana shi sanin kowa nata, for over two years. A cikin biyu dole akwai daya. Ko dai rage dare kawai take yi da shi ba sonsa take ba, ko kuma kamar yadda ta gaya maka, matar aure ce take cin amanar mijinta da kai. I know it is hard Muhammad, but you must see reasons. You must be strong and accept the truth. You must let go ko ba dan kan ka ba ko dan mahaifanka" Gidado ya gyada kai, ba tare da ya bude idonsa ba yace "thank you " Al'ameen ya mike zai fita, har ya kai kofa Gidado yace "Muhammad. Kar ka gaya musu please. Kar ka gaya wa Mama".

Sai da yaji alamar ya bar dakin sannan ya bude idonsa yana kallon kofar da Al'ameen din ya fita ta cikinta, amma ba kofar yake kallo ba dan hankalin sa yana can wani gurin daban. Ya dauki wayarsa a gurin da Al'ameen ya bar ta ya kalli hoton kan screen din zuciyarsa taki amince masa da first maganar Al'ameen cewa Safiyya bata son sa tun farko, ba ya jin kuma zai taba yarda da hakan.

Ya tuna da rana ta biyu daya sake ganinta a rayuwar sa bayan haduwarsu ta farko a jirgi. Haduwar su ta biyu ta kasance ne shekara bakwai bayan ta farkon. Bayan ya gama first and second degree dinsa ya dawo yayi service. Shekaru bakwai sun wuce amma bai manta da yarinyar da ya taɓa haduwa da ita a jirgi ba. Kuma can a kasan zuciyarsa yana fatan zai kuma haduwa da ita.

****.     ****.    ****.    ****.    ****.     ****

A hankali yake tafiya a motar sa, yana juya stirring cikin nutsuwa zuciyarsa cike fal da farin cikin da bai san dalilin sa ba, amma yana tunanin akan maganar da suka yi da Abba ne dazu. Ya kunna kida kadan kadan yana tashi yana kara masa nishadi, a ransa yana lissafa rayuwarsa and how successful everything has been going for him. 

Yayi dialing number ɗin abokinsa da ya fito nema "kai ya? Gani fa a junction ɗin, ina zan juya" abokin yayi dariya yace "kai fa matsala ta da kai baka san gari ba. Abeg I can't direct you, ask Google map" ya katse wayar. Gidado yayi dan karamin tsaki "karamin dan is, sai in fasa zuwa ma" ya cigaba da driving a hankali da hannu daya dayan hannun kuma yana kokarin nemo direction din inda zai je. Ya dago kai dan tabbatar da inda yake. A lokacin ne ya ganta.

Tana tsaye a gaban mota hannunta daya rike da key din mota dayan kuma rike da jakarta. Fuskar ta a murtuke da alamar bacin rai. Ga uwar ranar da ake kwallawa a ranar. Kallo daya yayi mata ya dauke kai ya cigaba da abinda yake yi, har motar sa ta gota inda take sai kuma ya dago kai da sauri ya sake kallon ta ta mirror din motar. Gabansa ya fadi yana ganin kamar yasan fuskar. Yayi slowing down ya sake gyara mirror dinsa dan yana kare mata kallo. Yaji wani excitement ya shige shi. Komai na features din fuskarta suna nan kamar yadda yake tuna wa da su but more matured, no longer child like but lady like. More feminine. More beautiful. More beautiful than he had ever imagined she would be.

Ya tuno da ranar da suka hadu a cikin jirgi. Surutun da ta ringa yi masa, tsokanar sa da ta ringa yi, da kuma yadda suka rabu. Ita ta riga shi fita daga jirgin a ranar dan air hostess ce ta dauko mata jakarta daga inda ta barta ta taho gurinsa, ta kuma zo suka fita tare. A arrival yayi ta baza idon ko zai sake ganin ta amma bai ganta ba. He then wondered ko paths dinsu zasu sake crossing later in life.

And it did ...

Sai dai kuma bashi da tabbas din zata ma tuna da shi ballantana har ta gane shi.

Yayi reversing motar a hankali still yana kare mata kallo dan ya tabbatar da cewa ita din ce dan kar yaje yayi wa wata magana. Sai dai yana zuwa saitin ta sai ta kara yin gaba kamar bata san mota ta tsaya a gaban ta ba. Ya bude kofar motar ya fito still idonsa a kanta. Yana jin zuciyarsa wani iri dan shi dai bai taba ganin macen da ta yi masa kyau kamar ta ba, bai kuma taba tsayar da mace a hanya yayi mata magana ba.

Ta ƙara bata rai tare da juya fuskarta daya side ɗin, daga alama kallon da yake yi mata ya dame ta. Ya tako zuwa gabanta, sai ta zaro wayar ta ta fara dannawa kamar bata san dashi a gurin ba. Yayi mata sallama. "Assalamu alaikum" ta amsa, amma shi kansa da yake kusa da ita motsawar bakinta kawai ya gani amma baiji muryar ta ba. Ya danyi shiru yana tsoron kar ta wulakanta shi amma kuma yana son gwada sa'ar sa, ya dan leka fuskarta a hankali yace "Piya?"

Ta dakata da danna wayar da takeyi ta dago kai tana kallon sa da alamar tunani a fuskarta, lokaci daya kuma sai yaga recognition a fuskarta, and farin cikin da yaji a ransa was more than he thought.

"Malam Muhammadu dan fillo?"

Yayi dariya, dariyar da yaji ts wanke dukkan tsoronsa. Ta nuna shi da dogon yatsan ta "Washington DC" ya girgiza kai "no. Manchester" tace "yeah. Right. Manchester. What are you doing here? How are you here?" Yace "ke zan tambaya. Never thought I will ever see you again" tace "me too. It has been five years?" Yace "seven" tace "wow. How time flies. Kayi girma sosai" ta fada tana kallon sa tun daga kan takalmin kafarsa har zuwa yalwatacciyar sumar kansa da bai rufe da hula ba. Ya shafa kansa "ke ma haka".

Suka yi shiru duk su biyun, kowanne su trying not to look at the other. Sai kuma suka kalla a tare, suka hada ido, and then they smiled together.

"uhmm ...... Trouble with the car?" Ya tambaya yana nuna motar da take tsaye a gabanta. Ta bata fuska "wallahi... Ta mutu.... I don't know why. Ina tafiya kawai ta mutu. Na kira kuma an hada ni da mechanic har yanzu kuma bai zo ba" yace "why not leave the car here in yazo ba sai ya dauka ba. You shouldn't be here standing under the sun" ta daga mishi key din motar "sai yazo zai karbi key ai" ya girgiza kai "still sai yaje gida ya karba. You shouldn't be here alone" tayi ajiyar zuciya bata ce komai ba. A hankali yace "can I take you home?" Ta juya ta kalli motar ta, sannan ta kalle shi fuskarta kamar zata yi kuka, yace "sai in dawo wa da mechanic ɗin key din, in bai zo ba kuma I can get another one for you" ta girgiza kai "ba wannan ne damuwa ta ba. Uncle Ahmad will kill me today. Yace kar in fita da mota. Yace ban iya mota ba. Baya son a bani mota ni kuma so nayi in nuna masa na iya" Gidado ya mika mata hannu yace "mu ga key din" ta bashi, hoping motar lafiyar ta kalau itace dai bata iya din ba.

Ya bude ya shiga yayi ƙoƙarin tayar da ita amma sai yaji yana murda key din tayi wata irin kara. Ya fito yana kallon Safiyya yace "key starter din ta ta lalace. Maybe kinyi ta murda key din ne" ta fara bubbuga kafa a kasa "to ba ita ce taki tashi ba" yayi dariya "tuba take yi. Now call the mechanic and tell him key starter issues ne, tell him kuma zaki tafi gida yazo gida ya karbi key ɗin".

Tayi abinda yace sannan ya bude mata passenger's seat din motarsa ta shiga ta zauna shi kuma ya zagaya ya shiga seat din driver. Suna kama hanya ya lura duk ta zama uncomfortable, sai yayi kokarin yi mata hira "you look good. You look really good" ta danji kunya "thank you. You too" yace "so... how have the 7 years been going?" Tayi ajjiyar zuciya "like the blink of an eye" yace "na dauka ba zaki gane ni ba fa, I was praying kar ki yarfa ni" tace "nayi niyyar yin hakan fa. But sai kuma ya kasance kai ne. Ni ma nayi mamaki dana gane ka. Amma kai ya akayi ka gane ni?" Ya daga kafada "ina da saurin gane mutane. Besides, I have thought about you a lot within these years. Ke fa" tace "ina tuno da kai ne kawai idan na shiga jirgi na hadu da me aerophobia" suka yi dariya a tare.

Wayarta tayi kara, ta dauka. Shi kuma ya samu damar cigaba da kare mata kallo "Yaya Mukhtar na bar gurin fa. Na kira shi nace ya same ni a gida. Alright. Don't tell Uncle please. Thank you". Ta ajiye wayar tare da ajjiyar zuciya yace "I like the way you talk" ta juyo tana kallon sa tace "what?..." Ya maimaita "I like the way you talk. I am not sure if it is the way your lips moves or the sound of your voice or the body language, ban sani ba. I just like it. It is therapeutic" ta sunkuyar da idonta kasa tana murmushi, ya kara da cewa "and the way you smile too". Sai ta ja mayafin ta ta rufe fuskarta. Ya tsaya yana kallon dogayen yatsun hannunta.

Aka kira wayar sa, ya dauka direct yace "kai na fasa zuwa fa. And don't call me again". Ta bude fuskar ta tana murmushi tace "babu kyau karya alkawari fa" yace "ba alkawari nayi ba  fa. Besides, there is no where I would rather be then here".

Motarsa ce tayi wata yar kara sannan ta mutu. Suka juya suka kalli juna. Yayi kokarin sake tayar da ita amma taki tashi. Safiyya ta rufe fuskarta tana dariya yayin da shi kuma ransa in yayi dubu ya baci. Ta bude fuska tace "it is official. Yau da rashin sa'a na tashi" ya juyo yana kallon ta yace "ni kuma yau sa'ar dana tashi da ita bata ma misaltuwa". Tace "I am not sure. Maybe this is a sign that we are not meant to be together" ya bude kofa ya fita yana girgiza kai da sauri. "No. This is a sign that we will walk the path of Destiny together" ta fito itama tace "walking? Not driving" yace "I am ready to do it if you are" ta saka hannu tana kare rana tace "under the sun?" Ya zagayo gaban ta ya tsaya, jikinsa yayi blocking mata hasken rana yace "I will shield you".

Suka fara tafiya a hankali, side by side, enjoying each other's company, breathing in each other's scent, suna kuma updating juna akan abubuwan da suke faruwa a rayuwar su. A lokacin ne ya gaya mata karatu dama yaje yi Manchester, kuma ya gama degree dinsa na daya dana biyu, ya kuma yi service. Ya kuma sanar mata da bukatar mahaifinsa akan yaje yayi aiki a ƙarƙashin sa, da kuma shi burinsa na yayi aiki a sabuwar jami'ar da baban masa da siblings dinsa suka bude in memory of mahaifinsu ambassador Muhammad Dikko, M.D University Abuja "ina so nima in bayar da tawa gudummawar wajan kafa jami'ar".

Ta fahimta, sannan itama ta bashi nata labarin. Family dinta mazauna garin Kano ne. Ta gama Sec school dinta three years back, amma kuma sai babanta ya fara rashin lafiya. Jinyar sa ya saka bata fara jami'a ba saboda basa zama a kasar ko da yaushe suna yawon kasashe neman magani, sai yanzu ne yayi insisting dole ta dawo Nigeria ta zauna a gidan Uncle din ta anan Abuja ya nema mata admission a daya daga cikin manyan private universities ɗin da suke garin. Last week ta zo garin. Kuma already ta gaji da garin.

A lokacin suka kai karshen junction ɗin suka hau kan babban titi. Suka tsaya suna kallon juna yace "we did it. The path was rough, tiring and very sunny. But we arrived at the destination, together"

Kafin tayi magana mota ta tsaya a gabansu. Aka sauke glass din wani ya leko "Fiyya. There you are. Na kasa hakura shine na biyo bayan ki. Let's go home kafin ya dawo ya ga bakyanan" tayi ajjiyar zuciya, daga alama ranta bai so haka ba. Ta so su ci gaba da tafiya a kafa ita da shi. Duk da dai cewa a kwai wahala, but with him by her side, zata jure.

Ta juya tana kallon Muhammad tace "cousin dina ne. Gidan su na sauka. Kafin kazo dazu shi na kira na gaya masa inda nake" Ya gyada mata kai "go" tace "okay. Zamu yi magana" yace "yes. I will call you" ta danyi shiru tana kallonsa. Ya sake ce mata "go... Rana tana dukan ki. It is not good for your skin" tayi murmushi. Ya bude mata kofar motar. Har zata shiga ta kuma juyowa tana kallon sa tace "are you not forgetting something?" Yayi shiru yana tunani sannan yace "no. Me na manta?" Tayi murmushi tace "I don't know. Kawai ji nayi kamar kayi wata mantuwa" na motar ya leko. "common. Let's go sauri nake yi fa" ta shiga reluctantly ta zauna, Gidado ya ja baya tare da yi mata alamar I will call you. Ta yi murmushi.

Sai da motar tasu ta ja sannan hankalin sa ya dawo jikinsa. Sannan ya fahimci abinda take cewa ya manta. "God damnit" ya fada da dan karfi. "Damnit" Ya maimaita yana saka yatsun hannunsa duk goman a cikin gashin kansa yana jin kamar ya fincike gashin ya zubar.

Bai karbi number wayar ta ba.


To gain access to the book contact

👇

0704 203 0419

Ta manhajar telegram


****.    ****.    ****.     ****.    ****.    ****.   
❤‍🩹*SAFIYYAH*❤‍🩹
*By*
*Maman Maama*


*Episode Six (6): Mother*

Knocking kofa ne ya dawo dashi daga tunanin da yake yi. Ya mike ya koma kan kujera ya zauna yace "yes". Mama ce ta turo kofar amma sai ta tsaya daga bakin kofa tana karewa dakin kallo tace "ina Al'ameen ɗin? Ko ya fita bai yi min sallama ba" Gidado yace "ya fita, maybe ba kya kusa" ta karasa shigowa da bacin rai a fuskarta tace "ko bana kusa ai sai ya neme ni, saurin me yake yi? Ni fa na kira shi kuma sai ya tafi ba tare da na sallame shi ba" Gidado bai ce komai ba amma ya san shi ya jawowa Al'ameen wannan fadan tunda shi yace kar ya gaya mata maganar da suka yi, ya san kuma Al'ameen ya gudu ne dan baya so ta tambaye shi ya suka yi.

Ta shigo ta zauna akan gado tana kallon sa tace "ya jikin?" Ya ajiye carbin hannunsa tare da safa addu'a a fuskarsa yace "da sauki Mama, kar ki damu da ni. Zan je asibiti anjima" ta bata rai "in kaje asibitin me zaka ce musu? Ji nake dazu da na tambaye ka abinda yake damunka cewa kayi kwakwalwar ka ce take ciwo, haka zaka ce musu a asibitin? ta yaya zaka ce kar in damu? ji yadda ka koma cikin kwana biyu, me yasa ba zan damu ba? Akan ka aka fara faɗa da budurwa ne wai?"

Gidado ya dago kai yana kallon ta, ya bude baki sai kuma ya mayar ya rufe. Shi bai san me zai ce mata ba. Baya son ya gaya mata abinda ya faru tsakanin sa da Safiyya saboda baya son ta tsani Safiyyan, duk kuwa da cewa bata san ta ba. Wannan shine zurfin soyayyar da yake yi mata.

Yin shiru sa ya saka ranta ya kara baci. "Kai ba zaka gaya min ba kuma shima dana turo ya tambaye ka ya tafi bai gaya min ba. Wani abu ne mai muni ya faru? Ko wani laifin ka aikata kake boye min?" Yayi saurin girgiza kai tare da bude ido "no, Mama babu abinda nayi fa. Babu abinda ya faru, kawai bana jin dadi ne. Kuma zanje asibiti in an jima".

Ta dauki wayarsa daga kasa ta mika masa tace "idan har babu wani abu da ya faru kira Safiyya ka bani ita mu gaisa" ya rike wayar yana jujjuya ta. "Bata kasar, kiran ba zai shiga ba" tace "WhatsApp call nko? Shima ba zai shiga ba? Ko kuma da ta tafi wata kasar a matsayin ka na mai neman aurenta

8 / 21