Chapter 12 Reading SAFIYYAH Sirrin Tsakaninmu By Maman Maama HN Novels

SAFIYYAH Sirrin Tsakaninmu By Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   12 / 21

33K to 36K   out of 62.6K words

ai kika wuce ni baki ganni ba. Amma Fiyya mai zai kai ki fada da Daddy a halin da yake ciki? A halin da kike ciki? Me ya haɗa ku" ya fada yana miko min hanky. Na karba tare da kokarin tsayar da kuka na. Ya sake cewa "talk to me.... At least let it out of your chest " na girgiza kaina "ba zaka gane ba Abdul" ya gyara zaman sa "Try me. Wata kila zan gane har ma in baki shawara. And just so you know, Mama ta faɗa min komai a kanki. She told me about your situation. She said she wants me to marry you" na juyo ina kallon sa na fahimci da gaske yake abinda ya fada, but I still noticed the sadness in his eyes.

Na danyi murmushin tausayin rayuwata nace "Allah sarki Aunty Hajjo. Lallai ta cika kawai kwarai. Ammi would be very proud of her" yayi ajjiyar zuciya "yeah. I guess so" nace "but I will not marry you Abdul" ya jiyo da mamaki, nace "na riga na yanke shawara, Mukhtar zan aura. Hakan shine sanadin fadan mu da Daddy. And I am not changing my mind. Tunda ai shi ya bani options ɗin kuma na zaba" ya danyi shiru yana tunani sannan yace "but why him? Me yasa kika zabe shi? Why not me?" Nace "I am not sure why. Kawai dai nayi addu'a and naji a raina shi ya kamata in dauka. And personally, na farko I believe yana so na da gaske. Cos ya jima yana ta bina da maganar soyayya ina ƙi, nacin da yake yi min da kuma goyan bayan sa da uncle Ahmad ya fara yi shi ya saka na bar gidan su da zama a Abuja na koma hostel. Shi kuma Daddy ya goya min baya yace ba za'a yi min dole ba. Wannan shine silar fara rikici tsakanin Daddy da uncle. And secondly, ina ganin auren mu zai gyara tsakanin Daddy da dan uwansa. He needs him a yanzu. Su biyu iyayensu suka haifa, bashi da kowa sama da shi" Abdul ya gyada kai cikin fahimta "at least in yana son ki auren will be much easier on you" na ce "yes. And kai kuma abinda yasa ban zabe ka ba shine, akwai wani wanda nake so, shine dalili na biyu da yasa muka yi faɗa da Daddy. I love him so much shima haka. So ina imagining yadda muke dashi idan da ace wannan kaddarar bata fado min ba, ace kawai a gidan su a yanke shawarar cewa ba zai aure ni ba wata yar abokin babansa wadda tayi cikin shege zai aura. It would have destroyed him and me. I don't want destroy you and your girlfriend"

Yayi murmushi, I can see his love for her a idonsa, yace "thank you. I really appreciate what you did. Kin yiwa soyayya halacci. And ina ganin zabin ki shine dai dai. Amma pardon me for asking, ya labarin wancan guy din da kike so ɗin? What happened to him? Ya san halin da kike ciki?" Na yi shiru ina kallon yatsun hannuna, ban so nayi mishi magana akan Muhammad ba dan ko tunawa da Muhammad bana son zuciya ta tayi saboda irin damuwar da nake shiga idan na tuno shi, nace "I can't even imagine halin da yake ciki. Soyayya ta bata yi masa halacci ba. It destroyed him".

Waya ta tayi kara. Na dauko ta daga cikin jaka ga mamaki na sai naga number ɗin Mukhtar. Na kife ta akan cinyata tare da rufe fuskata da hannayena. Na fahimci Daddy ya hakura kenan saboda fushin da yaga nayi, har ya kira uncle Ahmad ya gaya masa zabina shi kuma har ya gaya wa dan na sa. Or not.

Ni na zaba da kaina amma yanzu a raina bana jin zuciya ta zata karbi zabin nawa, da zata so Mukhtar da tini ta so shi. "Ana kiran wayarki" Abdul ya fada yana kallo na. Na bude fuskata tare da daukan wayar na amsa kiran "hello?" Daga daya bangaren aka amsa "Hello Habibty"


*Him👳🏻*


Bai tsaya ba har saida ya shiga dakinsa sannan ya rufe kofa ya jingina bayan sa da jikin kofar tare da rufe idonsa yana jera numfashi kamar wanda yayi gudu. Sai kuma ya bude idon ya fara magana da kansa. "Yes. Wannan shawarar tayi. I will get married and I will forget about her, and fall in love with my wife and have kids like every other person. Babu wani abun da zai chanja. There is nothing special about her. She is just like every other girl".

Ya kwanta akan gado ƙafafuwan sa a kasa yana kallon ceiling, a ran sa yana jera yadda zai cigaba da tsara rayuwar sa step by step. Farko, da farkon fari kafin ya fara komai zai fara da cire Safiyya daga ransa dan in dai har tana yawo a cikin zuciyarsa babu abinda zai iya aikatawa. And to forget about her sai ya fara raba kansa da duk wani abu da yake tuna masa da ita. Ya mike zaune yana karewa dakin kallo, bata taba shiga dakin na sa ba amma kusan a kowanne angle na dakin akwai memory dinta, ko dai wani abu da ta bashi ko kuma abinda suka yi maganar sa ko ta saka ya siya da kansa. Yayi tsaki tare da yanke shawarar cewa dakin zai bari gabaki daya ya koma wani. Nan da two months ma gidan zai bari gabaki daya ya koma nasa gidan shi da matarsa. Sai dai kuma shima wancan gida babu abinda babu memories din Safiyya a ciki.

Ya sake yin wani tsakin. One step at a time. Dole zai manta da ita amma one step at a time, tunda dama ai ba lokaci daya ta shiga rayuwar sa tayi zurfi haka ba. Ya dauko wayarsa ya fara da step din farko. Numbers dinta ya nemo duk yayi blocking sannan yayi deleting. Sai kuma ya nemo dukkan messages dinsu da chats dinsu duk ya haɗa kansu ya goge.

Ya ajiye wayar tare da rufe fuskarsa da hannayensa, a ransa yana jinjinawa kansa. "You can do it" ya fada wa kansa. Ya bude fuskar tare da sake daukan wayar yana jujjuya ta. Tare ya siya musu wayar iri daya shi da ita. Too many memories. Ko dai ya ajiye wayar kawai ya chanja wata? Amma in ya ajiye ma zuciyarsa zata iya rinjayar sa wata rana ya dauko ya kunna ya duba pictures da videos dinta da suke fal a ciki. To completely forget about her dole sai ya goge wadannan ma. Ya bude wayar da sauri ya fara nemo pictures da videos din da duk take ciki yana marking, yayi marking da yawa har yazo kan wani video da bai tabbatar nata be ko ba nata bane ba sai ya bude shi dan ya tabbatar. And then he saw her face, as clear as a lokacin ne yake daukan ta video ɗin. Kuka take yi shabe shabe da hawaye a cikin video ɗin tana bubbuga kafa a kasa irin yadda shagwababbun yara suke yi. Yana jin muryarsa a ciki yana dariya

"wai da gaske kukan kike yi? La ila! Mutane fa suna kallon ki" ta turo baki tare da tabe shi, sak yar yaye, "ni wallahi ba zan daina kukan ba sai ka siya min ice cream".

Ya kife screen din wayar akan gadon tare da kife fuskarsa akan wayar yana jin zuciyarsa kamar zata fado kan gadon. Ya tuna ranar da ya dauki video din. Ranar sun haɗu a school da safe tace masa mura take yi, daya tambaye ta abinda ya saka ta murar sai ta bashi labarin cewa ruwan sama aka yi da assuba ita kuma ta shiga ciki tayi wanka. A ranar da ya kira ta da dare sai yaji muryarta har ta dashe saboda mugun kamu da murar tayi mata. Babu shiri ya dauki mota ya tafi hostel ɗin su ya dauke ta da niyyar kai ta pharmacy ya siya mata maganin mura.


****. ****. ****. ****. ****. ****.


A hanya ya lura da yadda take ta takurewa a cikin hijab dinta. Ya kalle ta yana lura da yadda idonta yayi ja. Yayi tsaki "pharmacy din nan ba zai yi ba Piya, asibiti zamu tafi, naga alamar ma harda zazzaɓi a jikin ki" ta bude ido tare da saurin sakin jikinta. "babu zazzaɓi fa. Allah babu. Mura ce kawai ita ma yar kadan" ta karasa maganar tare da yin atishawa. Ya harare ta "yar kadan? Wannan murar ce yar kaɗan ɗin? Asibiti zan kaiki. Let me call our doctor inji in da yake. Ya kamata a duba ki sosai" ya fada yana daukan wayarsa. Tayi saurin karbe wayar daga hannunsa. "Please kar ka kira shi. Ni na warke ma" yayi slowing down yana kare mata kallo, sai kuma yayi dariya "yanzu na gane matsalar ki. Tsoron allura kike yi" ta tura baki "babu wani tsoron allura, kawai ni lafiya ta kalau ne shi yasa" yayi kokarin juya steering motar "okay tunda ba kya tsoron allura muje asibitin kawai" ta saki wayar tare da saurin rike hannunsa "na shiga uku. Dan Allah kar ka kai ni asibiti" ya cigaba da yi mata dariya yana kallon yadda take zazzare ido kamar wadda za'a yanka "wannan tsoron asibitin naki Piya, duk ranar da zaki haihu bansan yadda za'a yi ba". Sai kuma taji kunyar sa ta rufe ido.

Sun jima suna rigima a mota, daga karshe pharmacy ɗin ma cewa tayi ba zata je ba sai da kyar sannan ta yarda amma da sharadin cewa ba zata shiga ba shi kadai zai shiga ya karbo mata magani ya fito. Haka da suka je ya barta a mota ya shiga shi kadai, sai dai ga mamakin sa ya na tsaye a gurin cashier sai ganin ta yayi ta shigo gurin ta shiga bangaren da suke siyar da kayan ciye ciye, jimawa kadan sai gata da manyan robobin ice cream guda biyu, ta ajiye a gaban cashier tana kallon sa tace "one for you and one for me" ya girgiza kansa "no, no, no. Babu yadda za'a yi kina wannan murar ki sha ice cream. I won't allow it ".

Ta kwabe fuska "ni Allah sai na sha. Ai naji wani doctor yace ba shan abu mai sanyi ne yake kawo mura ba, mura viral infection ce, kuma ......" Yace "oh! Viral infection? Shi yasa naga kin shiga ruwan sama kin fara mura? Ko virus ɗin a cikin ruwan saman yake?" Ya karasa maganar yana daukan robobin da niyyar mayarwa. Ta bishi da sauri "ni dai kazo ka siya min. Allah in baka siya ba ba zan fita daga shagon nan ba zama zan yi in yi ta kuka" ya juyo yana kallon ta da mamaki. "kuka? Really? To kiyi ɗin mu gani. Ni kuma I will record you and show our kids"

Ai kuwa ranar yaga rigima. Tun da ya hadu da ita dama ya fahimci shagwababbiya ce amma bai san irin girman shagwabar tata ba sai ranar. A dole sai da ya sai ice cream din nan har da karin chocolates, mai shagon yana ta yi musu dariya. Suna shiga mota ta darko roba daya ta buɗe ta fara sha. Ya zauna kawai yana binta da kallo. Tayi atishawa ta kara diban wani ice cream din ta sha. Ta juyo tayi masa gwalo. Yayi ajjiyar zuciya. "This has to change. My no has to mean no and my yes yes. Dole ki ringa jin magana ta in nayi miki ita" ta juyo tare da saluting dinsa irin yadda sojoji suke yi tace "Yes Sir!".


****. ****. ****. ****. ****. ***


"Hamma. Hamma Gidado. Yaya Gidado".

Kamar cikin mafarki yaji muryar Mufida tana kiran sunan sa, duk kuwa da yasan cewa ba bacci yake yi ba sai dai yayi matukar nisa a cikin tunanin sa. Ya dago fuskarsa ya sauke jajayen idanun sa akan Mufida da take tsaye a bakin kofar dakinsa da waya a hannun ta. Ta dan tsorata kadan sai kuma yaga tayi sauri ta rufe mic din wayar hannunta da daya hannun, tace "uhm dama waya ce aka ce in kawo maka. Amma bara in ce mata kawai you are busy zaka kira ta an jima" ya tashi ya zauna sosai ya a shafa goshin sa yace "who is it?" Tace "yarinyar da muka yi maganar ta dazu ce. Mama tace in kira ta dan a samu information ɗin ta. Shine na kira ta ita kuma tace in kawo maka" ya sauke ajiyar zuciya, with all his heart yana son yayi rejecting kiran ya fadi wani excuse ɗin amma kuma yasan bashi da wani excuse ɗin fadi. Ya san shi yayi choosing wannan option ɗin amma accepting ɗin choice din nasa yana kokarin ya zamar masa nightmare.

Ya mika mata hannu. "Give me the phone " ta bude mic din sannan ta mika masa. Yana karba ta juya ta fita. Ya zauna yana kallon timer din kiran tana cigaba da reading, sai da yayi ajjiyar zuciya sannan ya saka ta a kunnen sa, "Assalamu alaikum " yace, daga daya barin yaji ance "Ameen wa alaikumus salam Habibi" yayi shiru bai ce komai ba, sai ta sake cewa "Mufida ce ta kira ni. She told me the most wonderful news ever. Ina so ka sani cewa tunda nake a rayuwata ba'a taba gaya min labari mai daɗin wannan ba" ya sake yin shiru sai kuma ya fahimci shi take jira yayi magana sai yace "okay. I am glad you feel that way. But uhmm, this is just a procedure, I don't want to give you any false hope. Maganar aure ce and dole sai an gudanar da bincike. Am sure she told you abin yazo ne lokaci daya. I have been giving two months in fito da mata. So I am going to need some information from you and if the background check comes back okay then that's when we will celebrate" ta dan yi dariya kadan "it is going to come out okay. Everything will insha Allah be okay. And I am going to make you the happiest insha Allah. And ." Ya katse ta "Okay. Uhmm. First, menene sunan ki? Ni sunana Muhammad Lawan Muhammad. Ana ce min Gidado" tace "I know. I know a lot about you. Ni sunana Safina. Safina Ibrahim"

To gain access to the book contact

👇

0704 203 0419

Ta manhajar telegram

*❤‍🩹 Safiyya*❤‍🩹


*Episode Nine: Safina*


*Him 👳🏻*

"Safina?" Ya maimaita da mamaki a muryarsa, ta ɗan yi shiru sannan tace "eh. Uhmm, ko ka san wata Safina Ibrahim ne?" Sai daya ɗan ajiye wayar akan cinyar sa ya yi tsakin jin haushin kansa, why must he relate everything to Safiyya ne wai? Kawai daga jin Safina sai ya dangantata da yar uwar Safiyya?

Ya sake daukan wayar yace "uhm. Sorry Please. Akwai wata Safina da na sani ne, in fact ita ce the only Safina dana sani. Though ita ma sunan ta kawai na sani. Yar uwarta ce wacce na sani" ya kuma ajiye wayar tare da dafe kansa "damn it. Must I talk about her?"

Ya sake daukan wayar sai kuma yayi shiru gudun kar ya cigaba da maganar Safiyya. Tace "hello? Ina jin ka. I guess you know the sister very well ko? I want to know. Tell me" yace "there is nothing to tell. Just tell me about your self, like, yar wanbe gari ce ke? Kano?" Sai kuma ya sake jin haushin kansa.

Tace "noo, not Kano. Ni yar Katsina ce" yace "really? But hausarki doesn't sound like hausar yan Katsina" ta danyi dariya "I get that a lot from people that don't know me. Bana son dialect ɗin so ina kokarin cire shi, musamman saboda duk makarantu na ba anan na yi su ba" yace "okay. Uhmm, I think that's all I need from you now. Please ki bawa Mufida number ɗin wani haka da za'a yi magana da shi, like your uncle or something. My family will contact them and do all the necessary stuff. That's all for now"

Tace "all? I thought zaka ce zaka zo muga juna ko?" Ya girgiza kai "no. My family will meet yours and do all the necessary things. I will see you idan komai ya daidaita. But now I am very busy" ya ji bacin rai a muryar ta "amma idan da zaka zo ɗin zanji dadi sosai, you have no idea how much I waiting and prayed for this. And ko suma su Abba zasu fi bawa abin muhimmanci idan suka ga kazo gurina" yace "no, zasu fi bada muhimmanci idan suka ga elders dina sun zo gurin so. I am sorry but I cannot come" tace "okay. Then how are we suppose to know and understand each other?" Yace "I will call you when I need more informations" tace "how can you call me bayan baka da number ta?" Yace "ki karbi tawa a hannun Mufida ki kira ni" tace "how can I call you bayan kayi blocking number ta " ya rufe idonsa yana jin kansa yana sarawa yace "okay. I will collect your number and unblock you. Shikenan?" Tayi murmushin da yaji sautinsa a cikin wayar "shikenan, naji dadi sosai. You have......"

Ya katse kiran ya jefar da wayar akan gadon tare da dafe goshin sa da hannu biyu. Zuciyar sa tafasa take yi, kokari take sai ta lissafo masa aibun yarinyar da suka gama waya da ita. Safina she said. But why? Upon all the names na mata a duniya why did she have to be Safina, bayan kuma Safinan ba wani suna ne irin wanda ya cika gari sosai ba. Yana ta so ya goge duk wani abinda zai ke tuna masa da Safiyya and then all of a sudden yarinyar da yace zai aura tana da sunan step sister din Safiyya. Safiyya used to talked a lot about her, ta kan

12 / 21