Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
iyayen da suka hada su suke shirya abin su.
Babu wanda ya san gaskiya sai Al'ameen, shi kuma Gidado avoiding dinsa yake yi dan sam baya son su hadu ballantana har yace zaiyi masa maganar Safiyya ko ya nemi bashi hakuri akan abinda ya faru. Ya fi son kawai a barshi shi kadai with his thoughts.
Sai da ya rage three weeks biki sannan Mama da kanta ta nemi Mufida ta karbar mata number ɗin maman Safina dan su samu suyi maganganun yadda abubuwa zasu kasance, tunda a gurin angon ya kamata su samu duk information din da ya kamata shi kuma baya basu haɗin kai. Sai da ta kira ta ne sannan suka tsara duk yadda bikin zai kasance. Za'a yi kamun amarya Thursday a Katsina, shima ango za'a yi nashi kamun Thursday a Abuja. Friday za'a yi daurin aure a Katsina, sannan a taho da amarya Abuja, Saturday Mommy zata yi yinin ta anan Abuja ita ma kuma Mama zata yi nata, a Saturday din ne kuma za'a yi daurin auren Mufida anan Abuja, Sunday za'a yi dinner, a sunday din kuma za'a kai amare.
Sai bayan da suka gama maganganun su ne sannan Mommy ta yi wa Mama korafi. "shi dan namu ne nace har yanzu bamu ganshi ba, ya kamata yaje katsina ya gaishe da iyayen yarinyar nan su ganshi ido da ido, wasu ji dadi sosai su ga cewa an girmama su" Mama taji babu dadi a ranta, tabbas tasan Gidado baya kyauta wa, tace "insha Allah a cikin wannan satin zai je. Shi din ne sabgogi sunyi masa yawa amma insha Allah zanyi masa magana. Tabbas ya kamata yaje" Mommy tace "yauwa. In yayi hakan ya kyauta. In ya dawo daga katsinan kuma sai yazo muma nan ya gaida Hajiya, Hajiya yayata ce a gurin ta na girma anan Abuja, kamar uwa take a gare ni. Zata ji dadi idan yazo" shima nan Mama ta sake alkawarin zai je.
Sai dai suna gama maganar ta ajiye wayar ta dafe kai, bata san ta yadda zata lallaba Gidado yayi wannan ba. Ta san in ta matsa masa dole zai yi, amma kuma ba zaiyi cikin son zuciyar sa ba. Abinda kuma yake damunta kenan, she wants him to be happy, but he is getting sadder every day.
Sai da suka shigo gidan tare da Abba bayan sallar magrib sannan tayi mishi maganar zuwa Katsina. "Yaushe zaka je ka gaishe da iyayen yarinyar nan ne? Ya kamata kaje su ganka. Zasu ji dadi sosai. Shi tuwon girma hausawa sunce miyarsa nama". Ta ga yanayin sa ya chanja lokaci daya. Amma bata hakura ba ta cigaba "ita kanta yarinyar har yau ba kaje ka ganta ba Gidado. Ya kuke ciki ne wai?" Ya nuna wayarsa "muna waya Mama, ina kuma ganin ta a waya. She understands cewa akwai nisa. Kuma kwana nawa ya rage" tace "minti nawa ce katsinar a jirgi? Ko ce maka akayi ka dauki mota ka tafi?".
Yayi shiru sai kuma tayi ajjiyar zuciya "Gidado, kulawa ma ai yabawa ce. Ina laifin wanda yace yana sonka? Wanda yake hakuri da duk abinda kake masa saboda yana son ka? Ko a haka ai yarinyar nan tayi kokari. Ka daure kaje kaji babana?" Yace "to Mama, zanje insha Allah" tace "yauwa, Allah ya yi maka albarka" yaji dadi a ransa yace "Ameen Mama" Abba yace "sai ka nemi friends dinka ko mutum biyu sai su raka ka. Yaushe zaka je?" Gidado yayi shiru yana shafa fuskarsa data cika da gashi sannan yace "zanyi magana da Ya Ameen inji sanda yake free, sai muje tare da shi".
Ya zaɓi tafiya da Al'ameen ne shi kadai saboda shi kadai ne a friends dinsa ya san gaskiyar halin da ake ciki, shima kuma dan Mama ta saka shine a ciki tun farko. A waya suka yanke sanda zasu je. Suka saka next weekend. A take Al'ameen yayi musu booking flight ɗin safe da kuma return na yamma.
Bayan sun gama wayar Gidado ya zauna yana jujjuya wayar a hannunsa. Tun kiran wayar da yayi wa Safina na farko bai kuma kiranta ba, in ta kira shi kuma daga ya dauka sai yace mata yana busy ne zai kira ta. Daga baya ma sai ya saka layin shi da take da shi a DND (do not disturb), yayi excluding mahaifansa da siblings dinsa. Wannan yasa babu wanda yake kiran shi a layin ma gabaki daya sai su, sai ya cigaba da using dayan layin nasa for his friends and relatives. Yayi tsammanin zata yi korafi gurin su Mama cewa bata samun sa a waya amma sai yaji shiru Mama bata yi masa faɗa akan hakan ba. Ta kan turo masa messages, shima kuma ya kan bata amsa akan abinda ya ga ya chanchanci amsar.
Amma yanzu yasan dole ya kira ta, tunda in sunje katsinan bai san inda zasu dosa ba. Kuma shi bai isa ya samu iyayen sa yace su bashi address ba. Ya nemo number ɗin ta ya kira. Ta dauka sallama "Assalamu alaikum Habibi" yaji kamar ya ajiye wayar amma sai ya amsa sallamar, ta gaishe shi ya amsa, sai ya tsaya yana jiran tayi masa korafin rashin kiranta da kuma rashin samun sa da bata yi. Amma sai yaji bata yi ba. Yace "dama ina so ne ki samarwa da su......ki sanar a gida, zamu zo ranar Saturday insha Allah mu gaishe su" yaji yana feeling awkward, remembering sanda yake ta yiwa Safiyya nacin yana son zuwa ya gaishe da Daddy.
Tace "alhamdulillah. Zan gaya musu. Nasan zasu ji dadin hakan sosai. Nima kuma zanji daɗi. Amma in saka ran ganin ka ko kuma zuwan nasu Baba ne su kaɗai?" Ya shafa fuskarsa yana jin babu daɗi, kamar yadda Mama ta fada, ina laifin wanda yace yana son ka? Yace "zamu haɗu, insha Allah" tace "masha Allah. I can't wait" yana jiyo farin cikin ta daga cikin wayar. Sai kuma ya tambaye ta abinda ya kira ta saboda shi "sai ki turo min address ɗin" tace "babu matsala, kawai ka gaya min sanda zaku sauka, I will pick you up from the airport".
Ranar Saturday ɗin kuwa suka tafi. Mama ta haɗa musu kayan ciye ciye exotics ta basu ta ce su kaiwa yar tata. Sai da suka zauna a jirgi sannan suka samu damar yin magana. Al'ameen ne ya fara ce masa "so? Anything new?" Ya juyo yana kallon sa yace "concerning what?" Al'ameen yace "you know what. I don't believe ka bar maganar waccan yarinyar ka karbi wannan. And I don't want any surprises. So if you are planning something now is the right time to tell me so that I can talk you out of it" Gidado ya danyi dariya kadan yana girgiza kansa yace "I wish. I wish cewa akwai abinda nake planning, something that can get me out of this mess, amma babu komai, my brain is no longer working. Ban san me nake yi ba ban kuma san me zanyi ba next. I just want all of these to be over so that at least su Mama su san cewa I obeyed them and did my best" Al'ameen ya rage ido yace "and you are sure baka searching for that girl under ground?" Gidado yana kallon sa yace "there is no need. Ba zan neme ta ba. I have given up on her. All what I want to do now with all my heart is to forget about her. But the mission is impossible".
Sai da suka sauka sannan ya kira number ɗin Safina ya gaya mata sun iso, sai ta ce masa Baba ya hana ta zuwa daukan su yace ba dai dai bane ba, amma ya turo yayanta ya dauko su. Suna fita wanda yazo daukan su ya gane su. Ya karaso tare da mika musu hannu suka gaisa "kaine Muhammad ɗin" ya fada yana kallon Al'ameen. Al'ameen yayi masa murmushi yace "eh nima Muhammad ne. Amma ga Muhammad ɗin da kaje nema nan" mutumin yasake mikawa Gidado hannu yana fadada murmushin sa yace "Muhammad Gidado, barka da zuwa katsinan dikko gidan kara da mutuntawa. Sunana Mustapha.
Saura kadan mu gama free episodes 😅. Get your 500 naira ready and subscribe to an amazing journey with Safiyya and Gidado. I can't wait to share all of the story with you. Har hango yadda fuskokin ku zasu kasance nake yi when the drama really began to unfold. 🤣
Ga masu son kama seat ɗin su da wuri, send your *500* naira to the following account
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
And send your evidence to the following number via telegram
0704 203 0419
Posting of paid episodes is going to be strictly on telegram.
Please no phone calls. Just send the evidence and I will reply you.
Thank you.
One love 💕
*❤🩹 Safiyya ❤🩹*
*By*
*Maman Maama*
*Episode Twelve: Twisted*
💕
Gidado yayi taku biyu baya yana kallon hannun da mutumin ya miko masa, sai kuma ya kalli fuskarsa kamar mai kokarin gane wani abu "Mustapha? Mustapha kace" mutumin ya sauke hannun sa ganin gidadon bai yi shaking ba, Al'ameen yace "eh Mustapha yace, ka san shi ne?" Wani murmushi Gidado yayi, a zuciyarsa yana jin kamar an dauke masa wani babban dutse, yace "no. Ban san shi ba. At least not yet" mutumin ya mayar masa da murmushin sa yace "Yes. I believe we will soon know each other a matsayin in laws".
Yayi gaba su Gidado suka bishi a baya zuwa mota, sai a lokacin suka lura da cewa su biyu ne suka zo. Suka gaisa da dayan shima sannan suka shiga bayan motar su kuma suka shiga gaba, wanda ya kira kansa da suna Mustapha yana driving. Gidado ya juya kansa yana kallon waje yana jin daɗin iskar da take dukan fuskar ta sa, iskar yanci. Yanzu tabbas yana da tudun dafawa. Safiyya tana yawan ambaton Mustapha a maganganun ta kamar yadda take ambaton Safina. Ya kuma san cewa shi Mustapha ɗin yayan Safina ne uwa daya uba daya. It cannot be a coincidence ace wannan yarinyar sunan ta Safina sannan kuma tana da yaya Mustapha.
Ya san idan ya tabbatar wa da Mama cewa Safina yar uwar Safiyya ce to tabbas zasu yarda a fasa auren, ko ba dan komai ba ya san yanzu babu halittar da suka tsana irin Safiyya. Ya juyo da kansa, fuskarsa still dauke da murmushi, Al'ameen da yake ta kallon sa ya yi masa alamar tambaya "what?" Dan ya san ba da irin wannan fuskar suka taho ba. Amma Gidado bai kula shi ba so yake yi suje gidan ayi maganar a gaban Safina a gaban kuma Al'ameen yadda Al'ameen din zai zamo masa shaida a gurin iyayensa. Dan yanzu duk wani abun da ya shafi Safiyya ba yarda suke yi da maganar sa ba.
Basu yi nisa sosai ba suka sauka daga kan titi suka shiga wani layi sannan suka shiga wani gida. Gidado ya bude ya fito yana kallon gidan, gida ne na masu rufin asiri, not luxuriously rich but middle class rich. Daga gani kuma gida ne mai mutane da yawa a cikin sa. Wadanda suka kawo su suka yi musu jagora zuwa bayan gidan, sannan suka shigar da su wani ƙaramin parlor. Suna fita Al'ameen ya tambayi Gidado "what? Menene kake ta fara'a haka? Don't tell me daga ganin yayanta har ka matsu da ka ganta" ya karasa cikin tsokana "Gidado ya zauna ya dora kafa daya akan dayar yana jujjuya ta yace "yes, in a way zaka iya kiran abinda nake ji a raina haka. Kai dai ka jira. You will be surprised with the outcome of this visit" Al'ameen ya zauna, trying as much as he can to be comfortable akan kujerar yace "to Allah ya sa muji alkhairi".
Basu dade da zama ba wasu samari suka shigo su biyu suka fara jera musu kayan ciye ciye bayan sun gaishe su. Gidado ya yi tilting kansa yana kallon yaran kokari yake lallai sai yaga kamannin Safiyya a tare da su, sai da suka gama sannan yace "are you guys twins?" Suka juyo suna kallon sa sannan suka kalli junan su suka yi dariya. "no" daya yace dayan kuma yace "a'a. Abokina ne wannan. Dan makotan mu ne". Gidado ya koma ya jingina kansa a jikin kujera tare da rufe idonsa, yana jin al'ameen ya bawa yaran wani abu suka yi masa godiya suka fita. Sai da suka fita Al'ameen yace "kannen ta ne twins din da kake nema?" Bai bude idon ba yace "kannen Safiyya ne" Al'ameen yayi ajiyar zuciya yace "Gidado, gidan su Safina muka zo nan ba Safiyya ba. What is wrong with you" gidado ya gyara zama yace "na sani, akwai abinda nake tunani. You will understand idan ta fito.
Ba'a jima ba kuwa ta fito ɗin. Kamshin turaren ta ne ya fara iso musu kafin ta karaso. Kyakkyawace son kowa kin wanda ya rasa. Fara tas mai cikar jiki da shape mai kyau wanda ta tabbatar ya fito a cikin doguwar rigar lace ɗin da ta saka, ba irin fitowar da za'a kira da tsiraici ba amma irin fitowar da zai dauki hankalin duk wanda ya kalle ta. Fuskarta da kwalliya dai dai gwardado. Tayi daurin dankwalin da ya zauna ɗas a kanta ya kuma bayyanar da yalwataccen gashin kanta ta baya. Ta yafa mayafi a side daya ya rufe rabin kirjinta.
Ta tsaya a bakin kofa tayi sallama. Suka amsa mata a tare sannan ta shigo kanta a kasa ta zauna a kujera ta gaishe su "sannun ku da zuwa. Da fatan hanya bata gajiyar da ku sosai ba" duk suka yi shiru babu wanda ya amsa. Kowa yana saka ran dayan zai amsa. Sai kuma suka kalli juna a tare suka amsa "lafiya lau" "yauwa".
Suka sake yin shiru gabaki daya. Ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da fingers dinta, Gidado kuma ya tsare ta da ido a ransa yana son ya ga ko zai iya tuno kamannin Safinar Safiyya, maybe ko ya taba ganin ta a hoto amma ya manta, yayin da shi kuma Al'ameen yake kallon Gidado da mamakin kallon da yaga yana yiwa Safina. Al'ameen ne ya katse shirun ta hanyar yin gyaran murya tare da cewa "malama Safina ya shirye shirye?" Ya fada already feeling awkward, dan shi ba gwanin magana bane ba musamman ga wadanda bai sani ba. Ta dago ido suka hada ido da Gidado, tayi murmushi tare da sake mayar da idonta kasa sannan tace "alhamdulillah. Ya naku?" Kafin ya amsa mata Gidado yace "ina twins?" Ta sake dago ido tana kallon shi, shi kuma yayi kokarin studying fuskarta yana neman yanayin mamaki amma sai yaga confusion. "Twins kuma? Wadanne twins?" Yace "naga Mustapha shi ya dauko mu dazu, na dauka tare da twins suka zo" ta sake bata fuska tare da girgiza kai "still ban gane abinda kake nufi ba. Mustapha daga ina yazo? Ai dama yana nan. But ka san shine wai?" Yace "shi Mustaphan ba yayan ki bane ba?" Ta gyada kai still cikin nuna rashin fahimta tace "eh yaya na ne, dan kanin baban mu ne. Ka san shi ne?"
Gidado ya mayar da kansa baya tare da rufe idonsa, yana jin dutsen da ya daga daga kan zuciyarsa dazu yana komawa yana cigaba da danne ta. Al'ameen yayi saurin cewa "kamar naga kin kawo mana snacks, ɗan zuba min" ta mike da sauri ta dauki dan karamin plate ta na zuba masa samosa amma hankalin ta yana kan Gidado, ta durkusa ta mika wa Al'ameen still tana kallon Gidado tace "is he okay? Ko baya jin dadi?" Al'ameen yace "fine, he is fine, akwai serviette ne?" Ta dudduba gefe sai ta mike tace "bara in kawo".
Tana fita Al'ameen ya ajiye plate din da ta bashi ya taba kafadar Gidado yace "kai lafiyar ka kuwa? What are you doing. What is with wani Mustapha and twins" Gidado ya bude idonsa, duk annurin da ya sauka a fuskarsa dazu ya kauce yanzu, yace "Piya tana da step sister mai suna Safina, and a step brother mai suna Mustapha. When I saw that guy yace min shi yayan wannan Safinar ne kuma sunan sa Mustapha, I thought......" Al'ameen yace "Muhammad! Must you relate everything to her? Komai na rayuwa sai ka jingina da ita sannan zai baka ma'ana. Are You telling me kazo gurin yarinyar da zaka aura and the first thing da kake kokarin tambayar ta shine ko ta san dangin tsohuwar budurwar ka? Does that even makes sense to you?"
Gidado ya dauki robar ruwa ya bude ya daga ya shanye gabaki daya sannan ya ajiye robar. Yayi murmushin takaici yace "maybe I am loosing my mind. But yes. To me everything relates to her. Nothing makes sense to me in dai ba'a haɗa da ita a ciki ba" Al'ameen yace "then I don't think you are fit to marry " Gidado yace "ha! Finally someone ya fahimta. Go and tell that to Abba and Mama watakila su ma su fahimta"
A dai dai nan Safina ta dawo hannunta rike da sabuwar serviette. Ta ajiye a gaban Al'ameen amma shi kuma sai ya mike. Tace "ba ka ci samosar ba" ya kalli samosar, shi ya manta ma ta ajiye masa, yace "thank you, zan dan je waje ne inyi waya" yana fita ta zauna akan kujerar da ya tashi daga kai tana kallon Gidado cike da damuwa tace "Habibi, kamar ba ka jin dadi ko? Ko tafiyar ce ta gajiyar da kai?" Ya dan juyo ya kalle ta "am fine. Kar ki damu. Yanzu zamu ga su baban? Gwara mu gama mu zo mu tafi"
Ta dan bata rai "tafiya fa ka ambata, yanzu fa kuka zo and ko gaisawa bamu yi ba sosai musamman tunda yau muka fara haduwa. Ya kamata mu danyi hira ai ko?" Ta karasa tana langwabe kai gefe. Ya gyara zamasa yana kallon ta yace "hira? Okay what do you want us to talk about?" Tace "at least ka fada min ya ka ganni? Tunda yau ka fara ganina. Gwara in san cewa nayi maka ko ban yi maka ba. And maybe tell me abinda yake