Author : MAMAN MAAMA Category : KDP NOVELS
na farka sai inga ba haka bane ba.
Lokacin dama Daddy ya kawo ni Abuja da niyyar uncle Ahmad ya nema min jami'a a cikin manyan jami'o'in Abuja saboda in samu in zauna a guri daya in daina binsa ƙasa ƙasa, uncle Ahmad ɗin kuma yayi kokarin samar min admission ɗin, jira kawai yake a fara registration ya kaini inyi, a lokacin ne wata dabara tazo min.
Ina tunawa a cikin maganganun da muka yi da Muhammad ya fada min family dinsa sun bude sabuwar jami'a in honor of his late grandfather. Ya kuma shaida min yana son yin aiki a can. Duk da dai lokacin da muka yi maganar bai fara aikin ba. Sai na yanke shawarar why not in saka a nema min admission a makarantar, maybe mu sake haduwa a can. Maybe ma in ganshi a aji a matsayin malami na. Na tuna sunan makarantar "MD University". Naje na samu uncle Ahmad da maganar "uncle wata sabuwar jami'a da aka bude kwanan nan, MD University, can nake so a nema min" ya bata rai "ban gane ba. Ita kuma wannan da aka nemar miki menene matsalar ta?" Nace "babu komai uncle, kawai dai ni nafi son waccan ne, akwai kawayena da suka ce min can zasu je, kaga zan samu abokan karatu". Haka nayi ta bugawa amma uncle Ahmad yaki yarda, ranar nan ma cewa yayi in na sake yi masa maganar sai ya kwada min mari. Mukhtar yana ta yi min dariya. Ni kuma naki hakura dan gani nake makarantar ita kadai ce chance ɗina na haduwa da Muhammad again.
A haka Allah ya kawo savior dina kasar, Daddy, ai kuwa ranar da yazo da maganar na tare shi, "Daddy ni MD University nake son a nema min, ni bana son wannan da aka samu" ya juya yana kallon uncle Ahmad "wacce ce kuma MD?" Uncle Ahmad yace "kar ka biye mata yaya, wata sabuwar jami'a ce da ko kafuwa bata yi ba ballantana musan kyanta ko akasin haka. Wannan shekarar fa suka fara daukan daliban su na farko" na zamo daga kan kujera na fara kuka "ni wallahi Daddy ita nake so. Dan Allah ni dai a kaini can. Allah in ba'a kai ni ba ba zanyi karatun ba" Daddy ya fara fada "ba za'a kai ki ba ɗin. Wannan da aka samo ɗin ita zaki je".
Amma daga ni har duk wanda yake gurin mun san cewa kamar an kai ni ne an gama.
Wata guda bayan nan har na gama registration na fara zuwa lectures.
Tun daga nan kuma sai na fara abinda ya kai ni makarantar, neman Muhammad. Farko na fara neman sa a cikin malaman department din mu, amma ban same shi ba, sai na fara nema a na sauran departments amma na rasa a ina zanyi concentration neman tunda ni ban ma san me ya karanta ba ballantana in san me zai koyar. Sai na fara shiga cikin yan wani department din da ba nawa ba, in ana hira sai ince something like "ai naji labarin wannan malamin naku Muhammad Lawan, ance bashi da kirki" and they will be like "mu bamu da malami Muhammad Lawan" and I will be like "Okay ba department din ku bane ba ashe".
A haka har sai da na fara fitar da rai, thinking ko ya chanza shawara bai karbi aikin ba. Amma kuma na kasa hakura. A haka har semester ta kare aka fara shirye-shiryen exams. A lokacin ne kuma naje zanyi submitting wani assignment ɗina a office ɗin wani malamin mu. A lokacin ne kuma na ganshi.
Building din hawa biyu ne, duk offices din lecturers ne, office ɗin wanda zan kaiwa yana sama, ina hawa hawa saman idona ya sauka akan Muhammad a kofar wani office yana budewa. Sai dai bai ganni ba ya bude ya shiga ciki sannan ya mayar ya rufe. Na karasa da sauri ina jin wani irin excitement amma kuma zuciya ta tai yarda da cewa shi din ne. Naje kofar office din da ya shiga na tsaya na karanta sunan jikin office din "Muhammad Lawan Muhammad" naji wani dadi ya rufe ni kamar in taka rawa a gurin. Amma kuma what next? Gani dai gashi, katanga ce kawai a tsakanin mu amma me zanyi kenan? Shin zanyi knocking ne in ya buɗe ince hi? Ko kuma shiga kawai zanyi inyi pretending kamar batan kai nayi ba nan zan shigo ba, in yaso sai in nuna mamakin ganin sa a office ɗin. To amma kuma ai ga sunan sa nan baro baro a jikin kofar, in na shiga dole zai gane neman sa nake yi. Na dafe kaina, ga koshi ga kwanan yunwa.
A karshe haka ina ji ina gani na wuce office din ban shiga ba naje nayi submitting assignment dina na sake wucewa na koma gida. Amma hankali na ya kwanta tunda na ganshi na tabbatar yana makarantar, sai na kudiri aniyar zan san yadda zanyi ya ganni kuma ya fara yi min magana.
Daga nan na fara monitoring dinsa, na lura da sanda yake shigowa makarantar da kuma sanda yake fita. Sai na shirya plan dina. Sai da na daidaici lokacin da yake fita sannan na kwashi littattafai da takardu na tafi kan stairs din offices din nasu na baje wai ni lallai karatu nake yi. Ina zaune da uban takardu a gaba amma hankali na yana kan duk motsin da za'a yi a sama. A haka har na ji taku, na dan duba ta gefen ido na ga shine sai na dauke kai na cigaba da bude littafin gaba na amma ina jin zuciya ta tana ta bugawa da karfi. Ban ankara ba sai gani nayi yazo ya wuce ni ba tare da ko kallon inda nake yayi ba, yaje ya shiga motar sa ya tayar ya fice daga makarantar. Naji takaici ya kama ni. Amma na gaya wa zuciya ta cewa bai gane ni ba musamman saboda bayana zai gani sanda yaje saukowa.
Sai na chanja shawara.
Washegari takanas na samo kujeru guda biyu da dan karamin table na dasa a direct opposite stairs din su. Na baza takardu sannan na sawa kofar office ɗin sa ido, a haka har naga ya fito ya rufe kofa sannan ya fara saukowa, sai da naga ya kusa gama saukowa sannan nayi dabara na zubar da takardun gaba na, kamar irin iska ce ta zubar da su ɗin nan, ko bai ganni ba na san hasken takardun zai dauki hankalin sa.
Naji takunsa ya doso inda nake, ina jin kamar a cikin zuciya ta yake taka kafafunsa, sai kuma ya tsaya a dai dai sai ti na. A lokacin na tabbatar cewa ya ganni kuma ya gane ni amma ban kalle shi ba sai na cigaba da bude pages din littafin da yake gaba na. Naji Muryar sa "oh my God" still ban daga kai ba. Ya kara matsowa "oh my goodness. Piya? It is really you" na dago kai ina bata fuska, sannan na bishi da kallo tun daga kan takalmin kafarsa zuwa fuskarsa da take reflecting wani irin annuri da farin cikin da zuciyar sa take ciki.
Na bayyana mamaki a tawa fuskar "wow. Malam Muhammadu dan fillo. What are you doing here?" Ya ja kujerar da dama dan shi na ajiye ya zauna "ke zan tambaya Piya, what are you doing here? How comes? Taya kika zo nan? Shin ko mafarki nake yi ne?" Nayi murmushi ina nuna masa takardun gaba na "karatu nake yi. Anan makarantar nake. Kai fa?" Yace "I work here. Ga office dina can. I can't believe this. You have no idea yadda na sha wahalar neman ki a garin Abuja" a raina nace "taka wahalar ka sani ba ka san tawa ba".
Yace "ranar nan was the best and the worst day of my life. I can't believe I let you go ba tare da na karbi number ɗin ki ba. I went back to your car na zauna jiran mechanic dinki yazo daukan mota in karbi number ɗin ki a hannunsa, amma that good for nothing mechanic bai zo ba, anan nayi sallar la'asar da magrib" na rufe bakina ina dariya, shima yayi dariyar "stop laughing at me. Nasha wahala fa. Har dare bai zo. Da sassafe kuma dana koma gurin already har ya dauke motar".
Nace "to ai Allah ya yi yanzu, gashi mun sake haduwa" bai ce komai ba sai ya dauko wayar sa ya ajiye min a gaba na "i won't repeat the same mistake. Dauki ki saka min number ɗin ki" na dauka na saka, na mika masa amma sai yaki karba yace "save it" nace "okay, me zan saka maka yadda zaka gane. Safiyya Adam Muhammad kamar yayi tsaho, ko in saka maka Fiyya?" Ya girgiza kai "Piya. You will always be Piya to me" nayi murmushi ina jin zuciya ta fari kal. Nayi saving da Piya💝 na mika masa still sai yaki karba yace in kira, sai dana kira ya tabbatar ta shiga sannan ya karbi wayarsa. Na dauko tawa wayar a jaka nayi saving tasa number ɗin, farko na saka Muhammad, sai kuma na goge na saka "Pyar💝"
To gain access to the book contact
👇
0704 203 0419
Telegram Only...
❤🩹 *Safiyya*❤🩹
*By*
*Maman Maama*
*Episode Eleven: The First Visit*
Free Episode
Assalamu alaikum
Mun kusa gama free episodes insha Allah. And the paid episodes will insha Allah come on telegram. Na gaji da replying cewa ba'a fara payment ba 😅, so zanke including payment details a kasan episodes daga nan har zuwa sanda za'a gama free episodes ɗin.
Nagode sosai da kaunar da kuka nuna mini kullum, Allah ya bar mu har gaban abadan. Safiyya will be worth your money and time, that I promise you 💕.
Nayi sauri na mayar da wayar cikin jaka ta dan kar ya ga abinda nayi saving number ɗin sa da shi. Ya fara yi min tambaya game da department din da nake da kuma yana yin da nake ciki, ni kuma nayi masa duk bayanin da nake ganin ya dace sannan na sanar masa da cewa ina gidan uncle ɗina ne, zuwa nake yi kullum. Muna haka aka fara kiran sallar magrib dama yamma tayi sosai, muka tashi ya taya ni tattara takarduna da ba katantawa nayi ba na zuba su a cikin jaka sannan yace "let me take you home" na bude ido ina kallon sa "ya hade hannayen sa "Please" na girgiza kai da sauri "no. In dai ba so kake yau in kwana a gadon asibiti uncle Ahmad ya balla min kafa ba" yace "saboda me?" Nace "in yaga wani ya kai ni gida, ai karshen karatu na kenan. Besides, nazo da mota" yayi ajjiyar zuciya "Finally an baki motar kenan" muka fara tafiya inda nayi packing nace "da kyar. Farko ai bai yarda a bani motar ba tunda na lalata waccan, sai yace sai dai Mukhtar yake kawo ni school kullum kuma yana zuwa yana daukana, ni kuma....." ya bata rai "waye Mukhtar" nace "cousin dina ne, a gidan su nake zaune" yace "ohh, that guy that picked you up the other day?" Nace "yes, shi" ya girgiza kansa "I don't like that" na tsaya ina kallon sa da mamaki "why not. Menene matsalar?" Ya daga kafada "kawai dai. But tunda kinyi mota ai shikenan ko? Yanzu ke kike zuwa da kanki ko?" Nace "yes" and then I saw relief a fuskarsa.
Muka karasa na tsaya a gaban motar ina kokarin dauko key. Yabi motar da kallo, noticing cewa daga ledar ta aka bare ta "wow. Rich kid" nayi murmushi "zaka fara ko?" yace "na daina. But it is a good one. Really. Congratulations" na shiga na zauna nace "thanks". Ya rufo min kofar yace "I will call you, for real yanzu dai" nayi murmushi "i will be glad if you do".
A lokacin duk mu biyun tunani muke munyi hitting jackpot, bamu san cewa kaddarar mu a chakude take da several heartbreaks ba, heartbreaks ɗin da zasu barmu with nothing but bitter sweet memories.
****. ****. ****. ****. ****. ****
Nayi ajjiyar zuciya na ajiye wayar a gefe, da ace a lokacin na san kaddarar da take bi na da ban neme shi ba, da ko ya neme ni ba zan bari ya same ni ba ballantana har in tarwatsa rayuwarsa kamar yadda nayi a yanzun. Na mike na dauko kaya na na saka, doguwar riga mai fadi sosai da hula, ba zan iya tuna rabon da in saka comb in taje kai na ba, na tabbatar yanzu ko na saka comb din ba zai wuce ba, ban kuma san ranar da zan taje shi ba and I do not care.
Na fita na tarar da Daddy suna yin physiotherapy da nurse dinsa, an siyo masa wani machine da zai taimaka masa wajen motsa hannunsa automatically ko da yana bacci ne dan a dan karawa muscles din hannun karfi. Na zauna ina kallon su ina jin yadda zuciya ta take cigaba da karyewa, a duk abinda ya same ni babu abinda yafi dukan zuciya ta kamar rashin lafiyar mahaifina, zan iya sake going through duk abinda nayi going through and more idan da ace in nayi haka zai samu lafiya. Na tashi na koma kitchen na kira Hassan ina son inji ko sun samu wani sabon labarin, a lokacin ne yake gaya min uncle Ahmad ya kawo musu motocin da nace ya siya musu tun kafin in taho, ni na manta ma da maganar dan na dauka ba zai siya ɗin ba, yanzu ma nafi tunanin ya siya ne kawai saboda yaji daɗi na zabi auren Mukhtar akan Mustapha, na tabbatar da Mustapha na zaba da ba zai sayi motocin nan ba sai dai ni insan yadda zanyi in siya musu, suna ta murna, ya bawa Hussein shima yayi ta min godiya, sai na tambaye su labarin su Mommy "ya maganar auren Safina? Any development?" Yace "ana ta shirye-shirye, kamar dai a Katsina za'a yi daurin aure, I don't know ko za'a yi wani event din again a can. Amma naji Mommy tace za'a yi dinner anan Abuja sannan zata yi yini a gidan Hajiya, kuma kamar a Abujan zasu zauna" nace "okay. That's nice. Angon fa? Kun haɗu da shi?" Yace "chafdi. Ni wannan mijin nata already ma bai yi min ba tun kafin in ganshi. Can you believe har yau bai je ya gaishe da Mommy ba? To katsinan ma Mommy tace sun ce bai je ya gaishe su ba. Kin taba jin irin haka?" Nayi dariya "kai Hassan kar ka zama mai yaɗa kananan maganganu mana kamar mace, tunda dai ita tana son kayanta shima kuma yana sonta ba shikenan ba, na tabbatar ai yan katsinan sunyi binciken su kafin su ce sun bashi ita". Sai kuma yayi min maganar abinda yake raina tun tafiyar Mommy "dazu da nayi maganar Hajiya sai na tuna da sakon ta, munje gaishe ta ranar nan tace mu gaya miki ki kirata. Kamar fa itama tana fushi ne akan batun yaya Mustapha. Ki kirata kinji yaya?" Nayi ajjiyar zuciya nace masa zan kirata ɗin, sai dai a raina nasan bani da karfin zuciyar yin hakan, I already have enough problems on my plate.
A haka muka gama wayar mu na zauna ina ta jujjuya wayar a hannu, wani irin uneasiness nake ji a raina duk sanda aka yi maganar auren Safina, haka kawai na kasa cire maganar da ga raina duk kuwa da cewa ina da abubuwan da suka fi maganar muhimmanci a gurina.
*Him 👳🏻*
Duk abinda ake yi na shirye shiryen bikinsa yana sane, sai dai sam baya shiga cikin maganar, in an tambaye shi abu sai yace ayi ko menene ma. Abba da Mama suna sane da hakan kuma dama sun saka ran cewa hakan ce zata kasance amma su a lokacin a ganin su babu abinda zai dawo musu da hankalin dan nasu zuwa gare shi sai idan ya manta da Safiyya, babu kuma abinda zai mantar da shi Safiyya sai wata macen, musamman da Mama taga hotunan Safina kuma ta ga cewa tana da dukkan abinda ake bukata a gurin mace idan za'a kira ta da mai kyau, sun kuma samu nasabar ta mai kyau ce kuma a iyakacin binciken su basu tarar da wani halin ta marar kyau ba. A ganin su idan suka hada auren, musamman yadda suka fahimci Safina tana mugun son Gidadon nasu, to tabbas zata yi duk abinda zata yi dan ta mantar da shi Safiyya, dan ta dawo dashi cikin hankalinsa.
Yana ji yana kallo aka dauki kayan lefen da aka haɗa da sunan Safiyya, aka chanja sizes din wasu abubuwan musamman undies saboda sizes din Safina yafi na Safiyya, aka kai Katsina. Da kyar dai ya samu Abba ya amince aka chanja masa gidan da zai zauna, wancan da ya gina da sunan Safiyya ya ajiye shi aka siya masa wani. A bangaren abokansa kuma suna jin an fara maganar auren sa suka fara murna, sai dai kuma da suka fahimci ba da Safiyya bane ba duk sai suka dame shi da tambaya "guy, what happened? Ina Safiyya kuma? Ban taba dauka zaka auri wata ba Safiyya ba musanman saboda yadda ka susuce a kanta. Ina take?" "Ta mutu" ya amsa musu direct "Allah yayi wa Safiyya rasuwa".
Duk suka dauki salati "innalillahi wa inna ilaihir rajiun! Yaushe? Kuma ba ka fada mana ba? Ko gaisuwa ba muyi maka ba ballantana muje gidan su?" yayi shiru sannan yace "sometimes it is hard to admit something. Fadar a baki yana kara zafi a zuciya" duk sai suka ji tausayin sa ya kama su, dan babu wanda ya san Gidado bai san cewa akwai yarinyar da yake so mai suna Safiyya ba.
Daga nan kuma duk jikin su yayi sanyi, sun kuma yarda da maganar sa musamman ganin yadda kwana biyu duk ya zama wani iri ya rame ya lalace spirit dinsa duk ya bar jikin sa. Wannan ya sa da yace babu abinda zaiyi na wannan bikin nasa sai suka goya masa baya, sun fahimci cewa auren hadi ne komai