Chapter 5 Reading LELEWAL by Farin Wata HN Novels

LELEWAL by Farin Wata

Author :  Farin Wata Category :  KDP NOVELS

Chapter   5 / 5

12K to 12.3K   out of 12.3K words

agogon da ya d'aura a hannun hagunsa ya kara
fiddo da kyaun hannunsa wadda ke cike da ke cike da gargasa.

A tsanake yake fidda kalmominsa cikin hausa da turanci, a daidai lokacin da yake sallaman wadda suke
wayan suka had'a idanu, Ai babu shiri tayi gaggawar janye idanunta daga gareshi, waye wannan me
matukar kama da Aadil sede ya d'ara Aadil nesa ba kusa ba kyau? Bata gama tunaninta ba taji Sahar ta
fisge hannunta tare da kwala kiran "daddyyyy".

Dukawa yayi fuskanshi cike da annuri ya warewa d'iyar tashi hannu taje da gudu ta fad'a tace "I miss
you daddy" yace "miss you too babynah" d'agota yayi yana kallon gashin kanta yace "eyyeh wa ya miki
kitso?" Juyawa tayi tana kallon bilkees tace "Antyn chan" shima kallonta yayi se suka kuma had'a idanu
da sauri ta matso tace "Ina yini" bata jira amsanshi ba ta wuce da sauri.

Dage kafad'a yayi yace "albishir!!" Tace "goro" tana dariya yace "zaki fara zuwa school monday" tsalle
da ihu tayi ta dire tare da bashi hannu suka tafa yana sakan murmushin ganin farin cikinta Ai da gudu ta
wuce tana cewa bari taje tayiwa Anty Albishir da su uncle fahad.

Girgiza kai yayi tare da gimtse fuskanshi yabi bayanta cikin yanayin cin magani ya shiga parlorn da
azama Yasmin da ta sauke hannunta kan fuskan Bilkees tayi saurin daka tsalle zuwa Baya tana zazzare
ido, Sahar ce ta tsala ihu tana fashewa da kuka ita da ba ita aka mara ba, cikin kuka tace "daddy ba kaga
Anty yasmin ta duki Anty me kirki ba, kuma ba abinda ta mata" zaro manyan idanunta tayi tana kallon
daddyn da ake kai kaara a zuciyarta take furta na shiga uku zata kasheni da bala'in yasmin, kallonta yayi
cike da son tabbatar da abinda idanunshi suka gane mishi se suka kuma had'a idanu....
🖤Gureenjo🖤

5 / 5