Author : Farin Wata Category : KDP NOVELS
hankali a banza gashi har ka baro aikinka".
Yana zama yace "No wani aiki ne ya kawoni asibitin se kuma basheer yake gayamin kuna nan se nayi
branching, ya jikin?"
Wani kululun bakin ciki ne ya tsaya mata wuya wai wani branching se kace shara suke, Aadil da tun
shigowarshi ya lumshe ido kaman me bacci ne yayi juyi kaman cikin bacci ya fuskanci gini tare da bud'e
ido wani irin haushi da tsanar Aayan ke taso mishi.
Ummie ce ta daure tace "da sauki" mikewa yayi yace "Toh ummien mu In ya tashi a mishi sannu da jiki
kuma a ja mishi kunne kar ya kuskura ya fara abinda ze yi da na sani sbd ba ruwana da shi waye...." yana
kai nan ya fice.
Taune lip ummie tayi tana hararar iska, Allah kasa yana shiga motan ta kife dashi.
~~~~~~~~~~~
Yana komawa ya samu Dr. basheer ya ko gama duba ta ya rubuta wasu magunguna inda ya tabbatar
mishi ko yaushe zata iya fara magana kaman yadda yayi tunani she was shocked ne beyond extent, ta de
ci gaba da shan maganin anytime zatayi magana.
Godiya sossai ya mishi suka mike suka fito seda ya saya maganin ya maida su gida, suna ta shi mishi
albarka kan ya wuce police station inda yaron yake sede duk yadda ya so yaron yayi magana kiyawa yayi
se kawai ya kyaleshi ya wuce office.
π€Gureenjohπ€
[15/07, 6:26 pm] Diddi Walida: ππ
πLELEWALπ
π¦FARIN WATAπ¦
ππ
STORY AND WRITTEN BY:- Fatima Muhammad Gurin.
MARUBUCIYAR:-
ZUHRAA
HAMRAH
IGIYAR RAYUWA
NOOR IMAAN and
RUWAN SAMA.
FOLLOW ME ON WATTPAD @Gureenjoh6763
SADAUKARWA:- wannan littafin gabad'ayanta sadaukarwace gareku @68Billygaladanchi wato Anty billy
and my dearest sister haneefah Muhammad Gurin thanks for your Advices and support Allah ya bar
kauna.
JAN HANKALI:- Toh masoya na ga ni da sabon labari kaman yadda kuka dad'e kuna tsumayi, am not
perfect but I promise to give you all my best on this, akwai tufka da warwara masu matukar sarkakiya a
wannan labari. Kaara d'aya zuwa biyu nake bukata daga gareku please ku Nuna min jin daad'inku ta
hanyar comments and share ta yadda ze karad'e ko ina, wannan littafi kyauta ne domin jin daad'inku
masoyana. Na godeπ₯°π.
EXQUISITES WRITERS FORUM π
(Home of exquisite writers')
Godiya ta tabbata ga Allah me kowa me komai.
βββββββββββββββββββββββββ
..........4
Duk inda tayi se Sahar ta bi ta a baya kaman jela, sossai ta debe mata kewa har ta samu ta gama duk
ayyukan gidan cikin sauri, duk d'akunan gidan seda ta gyara banda na Aadil da Alhaji, bawa flowers ruwa
shine na karshe wadda zatayi zuwa lokacin 11 da wani abu, ai tana d'auko tiyo sahar ta fara tsalle cikin
murnan za'ayi wasan ruwa sede ganin bilkees ta dukufa bawa flowers d'in ruwa tana baya baya dasu a
wahalce yasa ta turo baki gaba tana kallonta.
Nan da nan ta fara jero atishawa hawaye na zuba a idanunta a takaice kan ta gama bawa flowers nan
ruwa wasu kananun kuraje sun fito jajir a fuskanta, da kyar ta daddafa ta zauna tana lumshe idanu, cike
da tausayawa sahar ta dafa ta "Anty baki da Lafiya?".
Bilkees tace "eh sahar amma nayi sauki" sahar tace "a'a Anty Daddy fah ya hana karya yace Allah na
hukunta me karya gashi har yanzu kina kuka..."
Share fuskanta tayi tace "Toh baby sahar na dena, zo muje" kama hannunta tayi suka wuce kitchen
don d'aukan breakfast d'inta sede ga mamakinta kitchen d'in ba wani sauran kwano da ya nuna akwai
abu ciki an wanke su tas an maida komai muhallinshi, kallon blessing dake 'bare garlic kan bowl tayi tace
"blessing Ina abincina?" Ba tare da ta kalleta ba tace.
"Anty sahala tace kar a ajiye miki" da mamaki take kallon blessing bayan duk wahalan ayyukan nan da
ta sha yau kuma a ce mata ba abinci!! A sanyaye ta juya sahar ta bi bayanta d'akinsu ta nufa tana zuwa
ta kifu kan katifarta tare da fashewa da kuka, kuka sossai takeyi har jikinta na rawa ita kam rayuwar nan
ta isheta haka, duniyar da ba iyayenta ba yayanta da ta tabbatar zuwa yanzu ta mance sunan shi, ba
wani jin daad'in rayuwa se gallazawar waennan family biyu to ina zataje taji sanyi?.
In ta koma gidan mahaifinta azabanshi yafi nan, bata san wasu en uwansu ba bayan su uncle Mukhtar
da iyalanshi bare tace zata gudu wurinsu, ba karatun kirki ke gareta ba bare tace zata dogara dashi ta
gina kanta, dafata da taji anyi ne yasa ta tsagaita kukan tana me d'agowa a lokaci d'aya tana share
hawayen fuskanta tare da jan majina, idanunta sossai ya sauya kala ya kankance.
Ba-ba laami ce cikin tausayawa tace "kiyi ta hakuri bilkisu komai na duniya me wucewa ne, ki mikawa
Allah lamuranki sbd komai kika gani daga gareshi ne watarana se kiga kaman komai be faru ba, nan gaba
zakiji daad'in rayuwa in Shaa Allahu, kalli kiga yadda yarinyar nan ke kuka sbd ke".
Da sauri ta juya shap ta mance da sahar ganin yadda fuskanta yayi jage jage da hawaye yasa ta
janyota jikinta ta rungume, hawayenta na kuma zuba, indo tace cikin hawaye itama sbd saurin kuka da
take dashi tace "ga abincinmu ni da ba-ba mun rage miki".
Murmushin karfin hali ta saki tana kar'ban kwanon da indo ke mika mata tace "na gode ba-ba dake da
indo bazan ta'ba mancewa da ku ba har abada" ba-ba da se yanzu ta lura da kurajen fuskanta tace
"subhanallah me ya sami fuskanki haka?".
Bilkees tace "ba-ba jinina ne be son flowers, I'm allergic to them" indo tace "wayyo sannu Akwai ciwo
ko?" Girgiza kai tayi tana kuma murmushi tace "ai na bar inda suke shikenan kuma a hankali kurajen
zasu tafi" d'ago sahar tayi tace "tashi ki ci abinci sahar na san kina jin yunwa kema" da sahar suka ci
abincin suna er hira tsakaninsu.
Bayan sun gama ci ta d'auko comb da kifiya da kuma man kitso dayake ta iya kitso, tsefewa sahar kai tayi
da wayo da dabara sbd lura da tayi sahar na tsoron kai, cike da kwarewa ta yi mata kalabanta
madaidaita wadda yayi kyau sossai, kan ma su gama sahar tayi bacci hakan yasa ta gyara mata kwanciya
ta shige toilet ta watso ruwa cikin en kayanta da suka fara kod'ewa ta za'bo wani doguwar bakin riga
wadda ummu hadiya ta bata ya d'an d'ingile mata haka ta sa tare da d'aura gyalen a kanta.
Tana sa khimar aka banko kofan a tsorace ta d'ago sbd indo da ba-ba lami duk sun fice Don kama
wasu ayyukan tuntuni, hajiyace ta shigo a masifance ta nufi Bilkees ta kwasheta da mari ta kuma kara
mata cikin fad'a tace.
"Ke har kin isa? Kina kaskantacciya me aiki ki jima d'an gida ciwo? Bilkisu don't you dare try me baki
san da wadda kike tare ba, daga randa kika sake cutar min da d'a na rantse se na lahira ya fiki jin daad'i,
zan kira ita uwar taki inji In ita ta aikoki yin hakan don ban cike da halin iskanci In bazakiyi aikin ba ki
kama gabanki".
Kallon sahar dake kan gadonta tayi har zatayi magana se kuma ta watsa mata harara tayi gaba, a
hankali bilkisu ta sulale kan katifar ta zauna dabas zuciyarta na wani irin kuna, cin kashin nan har Ina?
~~~~~~~~~~~
Tsaye yake jikin windown office d'inshi da ya yaye hannunshi zube cikin aljihun wandonshi yayinda
idanunshi da suka d'an kad'a ke kafe wuri d'aya, kallo d'aya zaka mishi ka san yayi nisa ba kad'an ba cikin
tunani me zurfi, dafa kafad'anshi yaji anyi wadda hakan ya saka shi juyowa a matukar harzuke se suka
had'a ido da shaheed.
Ajiyar zuciya ya sauke yana cewa "yaushe ka shigo?" Shaheed yace "taya zaka san sadda na shigo
bayan kayi zurfi cikin tunanin da bashi da anfani? Allah abokina wannan tunanin ba shine mafita ba dubi
idanunka" lumshe zara zaran idanunshi masu tafiya da natsuwar en mata yayi ya kuma waresu kan
shaheed a lokaci d'aya ya kama lip d'inshi na kasa da yake red sbd yawan sawa da yake a baki ya hau
tauna a hankali.
Se da ya mula don kanshi zuwa lokacin har shaheed ya je karamin fridge dake office d'in ya d'auki
maltina ya bud'e ya fara sha yace "Toh shaheed ya zanyi? Wacce irin mata ni kuma Allah ya bani? Duk
wani irin hukuncin da Allah ya tanadar tsakanin miji da mata na mata, first of all na mata fad'a ba sau
d'aya ba ba sau biyu ba, shaheed na kaurace mata amma ta kasa fahimta sbd kanta ba na mutane bane,
na kai karanta wurin iyayen mu mata amma ba wani sauyi, yanzu haka zan iya ce maka na kai sati rabon
da magana me karfi ya had'amu amma a banza bata sauya ba, ya take son inyi da ita ne?"
Ya karashe a raunane, shaheed yace "Toh barrister kayi auren mana kawai ko ka samu natsuwar
zuciya" tsaki yayi yana dafe kanshi dake sarawa yace "ba auren bane matsala matar ne, banga macen da
ta min ba shaheed har yau Sannan Ina tsoron sake za'ben tumun dare kaga garin neman gira se a zo a
rasa ido".
Shaheed yace "ka cigaba da adu'a Allah ya za'ba maka abinda yafi alkhairi In auren ne se kaga ka zo
kayi amma a gaskiya kana kokari zama da kazamar mace a wurin irinka me tsantsar tsabta kaman azaba
ne" ya karashe yana sake kurawa Aayan d'in ido, "Aayan alamu sun nuna baka jin daad'i me kuma ke
damunka bayan matsalar zaheera?".
Yace "nothing just headache" shaheed yace "maybe stress ka kuma zo ka sawa kanka tunani, sorry
why not kaje gida ka huta kaga gobe kana da case" ba tare da ya musawa shawaran shaheed ba ya fara
tattare abubuwanshi dukda har kasan ranshi ya san in yaje gidan ma wani Karin 'bacin ran ne, sallama
sukayi da shaheed bayan ya sallami sakatariyarshi da masinjanshi ya ja motar ya bar harabar wurin zuwa
gida.
A tsaye a tsakiyar parlorn kasa ya sameta hannunta d'aya dafe da kwankwaso d'ayar kuma ta dafe kai
dashi, ta'be baki yayi a zuciyarshi yace yau kuma Ina wayan? Kallon jikinta yayi tayi wanka ta sauya kaya
zuwa doguwar riga me guntun hannu cikinta ya bayyana sossai, ba laifi kyakyawa ce ajin farko ga gashi
Masha Allah, tana ganinshi tace;
"Barrister!!" Chak ya tsaya da niyyar hawa sama da yake ya juyo ya kalleta fisha ya d'auke ido wadda
hakan ba karamin rud'ata yayi ba har ta kasa furta wani kalman seda yace "ya akayi? Kina bukatar wani
abu ne?" In ina ta fara "am uhmm wai nace kai ne ka fita da Sahar tun safe?" Ya san ta san ba me fita da
ita tun sassafe haka se shi amma se yace "yeah tana chan gida".
"Allah sarki" tana fad'an haka ya juya ya fara haurawa se ji yayi tace "am sorry" ba tare da ya juyo ba
yace "wani abin kikayi ne?" Be jira amsanta ba ya haura abin shi, dafe kanta tayi tace "Anya kuwa zan iya
Adda ramla?" Ta karashe da turo baki;
Wuraren 9am yayarta Ramlah tazo kasancewar da tazara sossai tsakaninsu Sannan tana da matukar
zafi wadda hakan yasa zaheerar ke shakkarta, a sadda ta zo d'inma tana haurawa d'akin zaheerar ta
d'aka mata mari a cinya wadda ya sata zabura ta tashi a firgice tana kallonta, ganin itace yasa ta natsu ta
kuma had'iye masifar da ta tashi dashi tare da yin kasa da kai tace "Adda Yaushe kika zo?".
Cikin azalzala tace "ban sani ba! Nace ban sani ba!! Wai ke zaheera yaushe zakiyi hankali ne? Wani irin
banzan d'abiya ne wannan? Baki kunyar a ganki a haka a ga gidanki a haka ace kuma ke d'iyar gomnan
Adamawa ne? Ji fa zarnin da toilet d'inki ke fitarwa... na rantse kin yi dacen miji me hakuri amma fah Ina
jiye miki randa zaki kaishi bango, tashi ki wanke toilet d'innan Ina nan Ina jiranki kuma ki tabbatar kin fito
a wanke tsab kin kuma wanke kankin nan, wawiya kawai shashasha".
Sumsum ta mike ta shige toilet, tsabar masifa Irin na Adda ramla har zaheera ta fito daga toilet bata
zauna ba se diri take tana karkad'a kafa, kaman sabuwar munafuka haka ta karasa wardrobe d'inta ta
d'auko riga doguwa turare kawai ta shafa ta sanya rigar tare da drying kanta da ya fita sossai wadda se
yanzu na lura ashe tana da gashin, bayan ta gama ta tsaya tana kallon Adda ramla.
Dakuwa ta mata tana furta "d'akin kuma uban wa ze gyara miki?" Har da hawayenta wurin gyaran
d'akin Adda ramla na nan tsaye har ta gama, seda ta gama ta tattara kayan wankinta jibgi ta fitarwa me
masu kan Adda ramla ta zauna bakin gado bayan ta bayar ta shigo, Adda ramla ta mika mata hannu
"bani wayarki".
Rau Rau tayi da ido seda ta daka mata tsawa kan ta mike ta d'auko ta mika mata tana rike bayanta da
take ji kaman ze fita sbd ba saba motsa jikin tayi ba, Adda ramla cikin takaici tace "zaheera yaushe zaki
zauna wai kiyawa kanki fad'a? Ashe kunnenki na kashi ne bazaki ta'ba jin magana ba? Allah ya baki miji
nitsatse marar son tashin hankali amma ke gaki kazama fitsararriya, Toh karki yarda ki kaishi bango
kaman yadda na gayamiki Don bazaki ji daad'i ba kuma da na sani ko... keya ce, wayanki na kar'ba se jibi
zan kawoshi na rantse da Allah in shigo gidan nan jibi In ga d'igon datti kuma ban samu abinci akan
dining ba se na fasfaskeki ba ruwana da cikin jikinki Sannan inji labarin kin saya wata wayar wallahi
watan cin ubanki ya kama, wawiya ana nuna miki annabi ya faku kina runtse ido".
Tana kai nan ta mike ta fice ko sauraran hakurinta batayi ba kan ta gama sauka ta juyo tace "Sannan ki
tabbatar kin shirya da mijinki zan kirashi inji abinda ba haka Allah da Abba zan had'aki kin san halinshi",
tana kai nan tayi gaba abinta.
Shinefa abinda ya d'aga mata hankali ta gangaro take safa da marwa cikin tafkeken parlorn kasan
cikin tunanin Anya zata iya rayuwa na kwana uku ba waya? Allah ya gani bazata iya rayuwa ba In ba
Instagram, Twitter da Snapchat ba......
**
Yana haurawa ya samu magaani ya sha tare da fad'awa kan gado ya jima sossai kwance har be san
sadda bacci ya kwashe shi ba, kiran sallahn azahar ya tasheshi ya mike ya karasa cire kayan jikinshi ya
fad'a toilet, wanka ya tsala ya fito yana zabga kamshi d'aure da towel kugunshi wardrobe ya nufa ya
fidda kayan da ze sa tare da gyara hair style d'inshi ya tashe had'add'iyar kasumbarshi tare da feshe
jikinshi da body's pray ya saka kayanshi ya kuma feshe jikinshi da perfumes.
Cikin azama ya fito yana d'aura had'addiyar agogon fatanshi a tsintsiyar hannunshi kafafunshi sanye
da normal takalmi na maza, yana shirin fita yaji muryanta tana cewa "amm barrister ga abinci fa" kallon
mamaki ya mata irin tooh yaushe rabo!! Ta'be baki yayi yace "Ohk se na dawo" yana kai nan ya fice
abinshi da mota ya fita sbd ba dawowa ze yi ba se ya gama abinda ze yi.
Seda yayi sallah kan ya wuce AUN nursery section inda ya samu baturen headmaster d'insu ya mishi
bayanin yarinyarshi abunku da harkar kud'i a take aka mata komai da komai aka bada uniform d'inta
zata fara zuwa monday, daga nan se da ya tsaya gidan Adda sumayya sbd suna kusa da Aptin sama sama
suka gaisa ya wuto jimeta inda direct GRA ya nufa wato Dougirei, horn ya danna sau biyu lawalli ya zo ya
bud'e mishi ya kutsa kan motanshi ciki.
Ganin motan ummie yasa ya d'an ta'be baki a fili yace "kenan an sallamesu" fitowa yayi ya nufi cikin
gidan kan ya karasa yaji wayanshi na ringing zarowa yayi tare da kai idanunshi kai, d'an wara zara zaran
idanunshi yayi ganin sunan dake rubuce baro baro a kan screen d'in wayan, a ladabce ya d'aga cikin
sanyi yace.
"Abba tuba nake" murmushi Abba yayi daga d'ayan 'bangaren yace "barrister nawa, ka san kayi laifi
kenan?" D'an zagayawa yayi yana tafiya a hankali yace "Abba aiki ne fa yake sha min kai" Abba yace
"wadda har yake sa kake manta Abbanka a wani kasa ko? Da maaminka ne na tabbatar baza ka iya
kwana ka yini baka kirata ba, amma ni yaushe rabon da muyi waya?".
Idanunshi ne suka rine a take sbd maaminshi da ya ambata wadda har Abban ya gane baran baramar da
yayi se waskewa yayi yace "Barrister ya ayyukan hope kana kan ganiyar nasararka kaman yadda na
sanka?" Murmushi yayi yace "Abba ai nasara tana nan ne bayan me gaskiya a duk sadda wannan nasara
ta kau to fa me gasakiyan ne ya sauya zuwa marar gaskiya".
Abba yace "Toh Allah ya taimaka sede a dinga kula please Alhj Umar mubi ya kirani yana min
barazanar In ja wa d'ana kunne, me ya had'aku?" Taune lip d'inshi yayi yace "Abba ba wani abu bane
case ne ya had'a da building d'inshi da Yayi collapsing da talakawa dayawa sbd rashin Ingancin gini da
saninshi kuma akayi hakan, Abba Allah bazan rabu dashi ba se an bi ma talakawan nan hakkinsu" ajiyar
zuciya Abba ya sauke yace "Allah ya baka nasara ya taimakeka a kan duk abinda ka sa a gaba"
***
Rike da hannun Sahar suka fito ta mata wanka ta sauya mata kaya zuwa wadda mahaifinta ya kawo ta
dashi riga doguwa fara iya kaurinta Don bata kai kasa ba an kawata rigar da adon manyan blue fulawowi.
Sam bata kula dashi ba seda ta kusa iso inda yake daddad'ar kamshi da kuma zazzakar muryar da ta
tsinta a wajen ya katse mata tunanin da take ciki, a natse ta d'ago kanta ta dubi me ita.
Tsaye yake ya zura hannunsa na hagu cikin aljihu wandonsa, hannun damansa kuma ya kasance
wayace da ya kafa a kunnensa, farin bafulatani ne, kansa cike da suma, saje a saman fuskan sa yayi
lufluf, yana da tsawo ba laifi hakanan yana da fad'in fuska kad'an, idanunsa zara zara masu matsakaicin
girma farare sol, hakanan tsiririn hancinsa da tsukakken lebbansa ruwan hoda ya kara taimakawa wurin
fiddo da tsantsar kyaun da Allah ubangiji ya mishi.
Sanye yake da shadda ruwan toka kansa babu hula