Chapter 2 Reading LELEWAL by Farin Wata HN Novels

LELEWAL by Farin Wata

Author :  Farin Wata Category :  KDP NOVELS

Chapter   2 / 5

3K to 6K   out of 12.3K words

πŸŒ•πŸŒ•



STORY AND WRITTEN BY:- Fatima Muhammad Gurin.



MARUBUCIYAR:-

ZUHRAA

HAMRAH

IGIYAR RAYUWA

NOOR IMAAN and

RUWAN SAMA.



FOLLOW ME ON WATTPAD @Gureenjoh6763



SADAUKARWA:- wannan littafin gabad'ayanta sadaukarwace gareku @68Billygaladanchi wato Anty billy
and my dearest sister haneefah Muhammad Gurin thanks for your Advices and support Allah ya bar
kauna.



JAN HANKALI:- Toh masoya na ga ni da sabon labari kaman yadda kuka dad'e kuna tsumayi, am not
perfect but I promise to give you all my best on this, akwai tufka da warwara masu matukar sarkakiya a
wannan labari. Kaara d'aya zuwa biyu nake bukata daga gareku please ku Nuna min jin daad'inku ta
hanyar comments and share ta yadda ze karad'e ko ina, wannan littafi kyauta ne domin jin daad'inku
masoyana. Na godeπŸ₯°πŸ™.




EXQUISITES WRITERS FORUM πŸ“
(Home of exquisite writers')



Godiya ta tabbata ga Allah me kowa me komai.

β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”



2
.........
2️⃣ 2



Dafa kafad'unta baaba tayi dukda kuwa tsawo da bilkees ta fita cike da tausayawa tace "Daga ranar da
na fara ganinki bilkeesu na san akwai murd'dd'iyar abu cikin rayuwarki, kwarai na kasance me matukar
tausaya miki Allah ya kawo miki mafita" rungume baaba kawai tayi tana me ci gaba da hawaye cikin
rawar murya tace "kwarai kuwa baaba rayuwata bata da wani abu face duhu me matukar sarkakiya
tabbas a Baya nayi farin ciki sede ya wanzu a rayuwata ne na lokaci kankani, na gode kwarai da
kulawarki watarana zan baki labarin bilkees.." tana kai nan ta d'ago ta share hawayenta tare da sakin
murmushi tace "baaba bara na karasa wankin nan kar dare ya min".



Da mamaki baaba ke kallonta kaman ba itace ke kuka yanzu ba, ta jinjinawa matukar dauriya da shanye
damuwa irin na bilkisu, ita ma murmushi tayi kan ta wuce, bata kai ga kulewa ba indo ta dawo kallonta
bilkees tayi tace "se yanzu? Ko wani aikin aka saki?" Girgiza kai tayi tace "na tsaya kallon dramar ya Aadil
da yayanshi ne" bilkees na me cigaba da wankinta tace "ya zo ne?" Indo tace "har ma yayi zuciya ya fice
kuma fah da 'yarshi yazo baki ga kyaunta ba" d'an kallonta bilkees tayi tace "zuciya kuma?" Indo na
tsoma hannunta cikin wankin Don tayata tace "eh kin san ya tsani halin Aadil na bin mata so yana
kokarin shigowane yaga wata karuwa da ta fita daga gidan nan shine fah yazo ya haushi da fad'a hajiya
kuma ta shiga ta kareshi Toh ko zama be yi ba ya fice".



Girgiza kai bilkees tayi tana cewa a zuciyarta 'ashe ba ni kad'ai bace na kyamaci wannan hali na ya Aadil'
a fili kuwa cewa tayi "oh watana uku a gidan nan amma Allah be yi na ga wannan yayan nasu ba" waro
ido indo tayi tana cewa "ashe fah baki ta'ba ganinshi ba duk ya fi su kyau da hankali har Anty Sumayya
da Anty Rufaida kuwa ga 'yarshi Masha Allah In kin ganta" murmushi bilkees tayi tana cewa "wata rana
zan ganshi Ai tunda Ina gidan".



Daga nan ta kauda hiran en gidan suka koma na kauyen su indo se labari take bata tana dariya, kusan
8pm suka gama wankin, bilkees na da tattare parlorn kasa inda anan suke cin abinci hakan ya sa indo
d'auka musu dinner d'insu ta wuce shiyarsu na masu aiki da ya kasance da d'akuna manya biyu kowanne
da kewaye an zagayeshi Sannan tsakiyar ya kasance kaman zaure da aka sa mishi tiles.



'Daki d'aya ya kasance su su uku indo, bilkees da baaba kowacce da katifanta kuma su ne masu share
share na cikin gida, se baaba lami dake girkin abincin gargajiya a duk sadda suke marmari ko Alhajinsu ya
dawo, d'ayar d'akin kuma na grace da blessing sune masu aikin duk wani abincin da ya shafi turawa.



Da sallama ta shiga parlorn Allah ya taimaketa sun haura Don chan take jin muryoyinsu suna hira, a
tsanake ta tattare parlorn tsab duk wasu kwanuka dake dining wadda suka ci abinci suka wargazar ta kai
kitchen ta goge dining d'in tare da share parlorn, a gajiye ta mike da ta gama aikin sbd bayanta da ya
kama lumshe ido tayi ta kuma bud'e komai normal se ta ja kofa ba tare da ta kashe wuta ba sbd su
Fahad da zasu sauko zuwa d'akinsu dake parlorn kasan In sun gama hira.



Seda tayi Alwala a tab kan ta wuce d'akinsu hira ta samu baaba nayi da indo yayinda abincinsu ke zaune
suna jiranta ba tare da tayi sallar da tayi Niyya ba tayi joining d'insu suka ci abincin, dake a ka'idarta In
tana cin abinci In ba ya kama dole ba bata ta'ba iya magana hakan ya sa sede ido take binsu dashi tana
gamawa kuwa ta mike ta kurkuro baki tazo tayi sallah tare da gabatar da shafa'i, kasancewar tana tashin
dare yasa batayi wutiri ba kan ta idar indo ta tattare inda suka ci abincin kwanukan se gobe in sun tashi
fita zasu fita dashi sbd tsoron sharrin mutan gidan.



Hamma ta saki tana kallon indo dake son fara janta da hira tace "ke wallahi bacci nake ji kaman me
bazan iya biyewa surutun kin nan ba" kwanciya tayi tana jin yadda indon ke mita bayan ta gama
adu'o'inta na bacci ta shafa tace "baaba se da safe" baaba da ita ma ta kwanta tace "Allah ya tashe mu
lafiya d'iyar albarka" sossai bilkees taji daad'in sunan se ta lumshe ido kawai tana tuno mahaifiyarta, a
lokaci d'aya tana dariyar indo sbd ganin ta kashe wuta itama ta kwanta sbd ba me biye mata ayi surutu
har da hawayenta, kan kace me bacci ya sureta sbd wahalan da ta sha na aiki.



~~~~~~~~



Abinda ya faru kuwa ta 'bangaren Aayan yana danna horn na shigowa gidan nasu yaga wata ta fito da
wani irin shiga na Allah wadai cikin takaici da jin haushi yake kallonta har ta fice, gaba yayo da motarshi
ya sauke glass yana kallon baba lawalli dake gaisheshi sama sama ya amsa ya d'aura da "wan chan
bakuwar hajiya ce?" Girgiza kai yayi yace "a'a Alhaji karami wurin Me gida Aadil ta zo" had'e rai yayi yace
"tun yaushe?" Me gadin yace "tun bayan la'asar ranka ya dad'e" lip d'inshi ya taune yana me lumshe ido
yace "shikenan baba" ya ja motar ya karasa shigowa cikin gidan.



Sossai ranshi ke 'baci In ya tuna wai a gidansu cikin gidansu kaninshi ke masha'a ba tare da Ummie ta
tsawatar mishi ba, In basa tsoron idon alumma Ai ya kamata su ji na Allah da ya ara musu rai da lafiya da
kuma kud'i suke yadda suka so bare kuma mahaifinsu da ba mazauni bane in ya ji wannan labari ze iya
yanke jiki ya fad'i sbd matsananciyar hawan jinin da yake dashi, me yasa basu da tausayi haka?.



Hannunshi rike da na samha ya tura kofar babban parlorn Aadil dake tsaye daga gefen kofan yana
magana da ummie da ta hakimce tana kallon tv yayi arba da dama shi yake nema Ai kuwa be yi wata
wata ba ya tsinka mishi mari wadda ya sa yasmin dake danna waya mikewa tare da kama baki tana zaro
ido, sahla dake saukowa ai da sauri ta koma yayinda ummie ta kafa mishi ido cikin 'bacin rai.



A zafafe yace "Aadil kai kam wani irin dabba ne? Me ke damunka? Ko shaye shayen da kakeyi ya fara
ta'ba maka kwakwalwane ban sani ba? How many times did I warned you in zaka bi matanka kasan inda
zaka je kabi ba cikin gidan nan ba?" Huci kawai Aadil ke yi idanunshi sun kad'a sunyi jajir ba Don yana
tsoron wan nashi ba ba abinda ze hanashi rama marinshi.



Ummie ne cikin masifa tace "me haka Aayan? Akan wani dalili zaka gaura mishi irin marin nan? Na sha
fad'a maka hakuri zaka na yi da Kanin kan nan har yanzu fah yaro ne yaushe ya gama mallakan hankalin
kanshi da ya san abinda yake me kyau ko marar kyau? Toh ka fita idanuna In rufe akan wannan shine last
da zan ga ka d'aga hannu ka mareshi In ba haka ba zan iya sa'ba maka akanshi" cike da takaici yake
kallon ummien a sanyaye yace "me yasa a ko yaushe kike goya mishi Baya ne ummie? Baki ganin irin
Girman zunubin da yake aikatawa? Idan Allah ya tashi tambayanki amanar da ya baki me zaki ce mishi
ummie?".



Ajiyar zuciya ta sauke tana tahowa gareshi tace "Son ka fahimceni ba fa wai ki nake ka ma kaninka fad'a
ba sede ka duba....." katseta yayi da "shikenan ummie he should do what ever he felt like doing" ya
kausasa murya yana kallon Aadil "but ba a gidan nan ba sbd baza ka 'bata future d'in kannenmu dake
tasowa In zuba maka ido Ina kallo ba useless boy" yana kai nan ya juya rike da hannun ershi ya fice
ummie na kiranshi ko tsayawa be yi sbd ranshi dake tsananin suya.



Mota kawai ya ja ya fice direct mafiyas ya nufa dake cikin yola, a tsanake ya danna horn har sau biyu kan
me gadin ya leko ya koma kuma ya bud'e gate d'in sbd gane shi da yayi, a mutunce suka gaisa ya karasa
kutsawa ciki tare da samun wuri yayi parking, part babba dake tsakiyar flat house d'in ya nufa ya
kwankwasa, ba 'bata lokaci aka bud'e "oyoyo uncle Aayan" yarinyar da ta bud'e ta fad'a tare da
rungumanshi sede ganin samha yasa tayi ihu tana kwala kiran sunan kanwarta da kaninta "mu'azzam,
Salma guess who is here?" Da gudu suka karaso suna me tureta ganin Sahar yasa suka fara murna.



Aayan dake murmushi yace "a matsamin to kan yanzu na juya da ita mu koma inda muka fito" cikin
harshen fulatanci suma duk da fulatancin suke magana da sauri suka matsa ya shiga, Aisha ta tsaya
gaidashi kawai ta ga Salma ta d'auke sahar dake ta dariyar ganinsu tayi d'aki da gudu mu'azzam ya bita
Ai itama da gudu ta bisu tana kwala kiran ta rigasu da d'aukanta.



Murmushi kawai Aayan ke yi yaji rabi da kwatar damuwar da ya kwaso ya kau, "A'a Barrister lafiya kuwa
da irin wannan ajiyar zuciyar?" Kallonta yayi sanye take da khimar alamun sallah ta idar cewa yayi "Adda
wallahi ba lafiya ba I'm tired of zaheera and Aadil" Tace "zo zauna" zama yayi ta wuce kitchen d'inta ta
had'o mishi abinci a tray da ruwa da kuma drinks tazo ta ajiye gabanshi akan center table, ba tare da
'bata lokaci ba ya d'iba a plate ya fara ci rabonshi da kwakwaran abinci tun jiya.



Cike da tausayawa take kallonshi har ya gama ci ya ajiye plate d'in, "ka ci gaba da hakuri barrister komai
me wucewa ne" yace "magananku kenan maman Aisha daga ke har ummie kullum hakuri hakuri ni kam
zaheera ce kad'ai mace a duniya? I'm very tired of her habit Ina kuma ganin lokacin d'aukan mataki na
yayi dama chan she wasn't my choice sbd ummie kawai na aureta but look..." ajiyar zuciya ta sauke tace
"A kullum Ina tayaka da adu'a Allah ya shige maka gaba a duk lamuranka barrister ya kara maka jumriya
da hali irin na zaheera but abinda baka sani ba shine akwai fah sharad'in da aka gindaya tsakanin ummie
da First Lady kan a aura maka zaheera wadda kai baka da masaniya......"



Bata karasa ba yace "to hell with their sharad'i, I don't care abinda kawai na sani shine duk hukuncin da
na gama yankewa idan time yayi zan aiwatar" saninshi da kafiya yasa ta ajiye maganan gefe tace "d'azu
naji ka ambaci Aadil wani abin kuma yayi?" Seda ya tauni lip sossai ita dae ta zuba ido tana kallonshi sbd
hakan da yayi ya nuna Aadil ya kaishi makura sossai, "could you imagine yaron nan mata yake kaiwa har
cikin gida yake abinda yaga daama ba tare da ummie ta tsawatar mishi ba?" Salati ta saki tana me gyara
zama a lokaci d'aya tana al'ajabin irin son da ummie ke wa aadil Anya kuwa wannan soyayyace me
d'aurewa? A sanyaye hawaye na gangaro mata tace "since when baka ta'ba fad'amin ba?" Yace "last
three weeks naje gidan na ga wata na shiga side d'inshi I followed her sbd sanin ba family bace ko one of
masu aiki ganin shigar dake jikinta but to my biggest surprise Ina shiga na gansu rungume da juna yana
shafata yayinda d'ayan hanunshi rike da wine yana sha nayi musu fata fata na koreta inda nan na samu
ummie da maganan se ta nuna min ta sani Ai Aadil yaro ne be girma ba, saurayi me almost 25 years take
cewa yaro fah"
Dafe goshi yayi na mintuna yana jin yadda yayar tashi ke kuka ci gaba yayi "and also today zan shiga
naga fitan karuwar, I even slapped him but maimakon ummie taga gyara nake kokarin yi kasancewana
babba na miji se cewa tayi zata sa'ba min na kuma ta'bashi" salati Adda sumayya take ta nanatawa wace
irin uwa ce wannan? Muskutawa Aayan yayi yace "ba kuka zaki mishi ba adu'a zaki mishi In Shaa Allahu
kan Abba ya san da maganan nan zan san yadda zanyi da Aadil" share hawayenta tayi tace "Allah
ubangiji ya shirya mana zuri'ah" ya amsa da "Ameen" tace "Toh barrister ka d'auki me aiki mana ko don
sbd sahar tana cutuwa fah sossai" yace "I know play class zan sa ta, you know I hate maids d'innan
wallahi" Tace "but akwai fah masu hankali" seda ya ta'be baki kan yace "what ever, kira yaran nan please
ki ba sahar abinci mu tafi almost 10" yayi maganan yana duba had'add'iyar wrist watch d'inshi.



Kiransu tayi dukkansu suka fito sahar tazo da gudu ta rungumeta itama rungumeta tayi tana cewa
"oyoyo my baby" ta d'auketa zuwa kan cinyarta, kallon Aisha tayi tace "sa min abinci kad'an a plate in
bata" sakawa tayi tana dariya hirar da mu'azzam ke ma uncle Aayan na zane Salma da akayi yau a school
sbd fad'a a class shi kam da ake ba labari murmushi kawai yake yana rike da hannun salma Dake son
kaiwa mu'azzam duka, Adda dake kokarin bawa layla abinci tace "Ai ke kam salamatu ko borkono nayi
taci da cikinki albarka" wadda hakan ya sa en uwanta kwashewa da dariya se ta hau kuka.



Aayan dake murmushi yace "uhm uhm ku dena sa salmahta kuka Ai abu aka miki kika rama ko?" Kai ta
gyad'a tace "ba ita bace ta ce min wai salamatu" dariya suka kuma kwashewa dashi aiko mu'azzam
bud'an bakinshi yace "hajiya salamatu" ya kwasa da gudu ta kuwa bishi, girgiza kai Aayan yayi yana
murmushi dramar yaran nan se su, sahar da ake ba abinci se kokarin zillewa ta bi su take.



Bayan Adda ta gama bata abinci ta dubeshi "yaushe ne EDDn zaheeran?" Yace "In next three weeks tace
min she was even saying ita bazata iya wannan haihuwa haihuwan ba sbd a gidansu bata ga ana haka ba
so tana haifan na cikinta zata juya mahaifa" zaro ido Adda tayi tace "and kayi shiru kai kuma?" Kafad'a ya
d'age yace "damuwanta" tare da mikewa ya rike hannun sahar, yace "bari mu wuce, gud night" mikewa
tayi ita da Aisha suka rakosu bakin mota seda suka shiga kan Addan tace "Allah ya tashemu lafiya" ya
amsa da Ameen ya ja motan ya fice.



A sanyaye ta bi shi da kallo har me gadi ya rufe gate d'in ta san shi da son yara dukda be fiye surutu irin
nasu ba but yana son yara, aiko idan har zaheera ta kuskura ta juya mahaifannan she will definitely push
him inda ba wadda ze so a familyn, ajiyar zuciya ta sauke tana furta "I most stop her".
~~~~~~~~~~



Juyi take cikin bacci tana fidda wani irin numfashi da sautin kuka kad'an kad'an wadda duk alamu suka
nuna cikin bacci ne hakan ke faruwa sanadiyar mafarki da take, sossai tayi jigib da zufa a hankali sautin
kukanta ya cigaba da karuwa kaman an mitsineta tayi wani irin zabura ta mike zaune tana ambaton
sunan Allah, shafa fuskan ta tayi tana goge hawayen da ya gama jike mata kumatu ko bata duba time ba
ta san karfe biyu ce daidai sbd wannan ba shine karon farkon mafarkinta da tashinta hakan ba.



Kusan zata ce ta saba sbd tunda tayi turning 12 take irin wannan mafarki tun bata saba mikewa tayi
nafila ba har ta fara a ko da yaushe idan hakan ya faru se ta mike ta kaiwa Allah kukanta sbd ta kasance
me matukar damuwa da se Allah ne kad'ai ze iya fiddata, mikewa tayi a sanyaye tana gyara d'aurin d'an
kwalin kanta, da lalu'be ta fad'a toilet ta d'auro alwala ta fito ta kuma lalu'bawa ta shimfid'a sallaya ta sa
khimar ta tada sallah raka'a biyu tayi a na karshe ta jima cikin sujjada tana zub da hawaye tare da yiwa
Allah kirari ya kawo mata haske cikin rayuwarta ya bayyana mata yayanta a duk inda yake.



~~~~~~~~~



A daidai wannan lokaci Aadil ke wani had'add'en bar wurin wani partyn friend d'inshi gabad'aya wurin
duhu ne hasken er kad'ance sbd fitila marar haske da suka saka kowanne saurayi a wurin rungume yake
da buduruwa Suna rawa da shafe shafe, sossai Aadil ke enjoying moment d'in sbd a rayuwarshi yana
matukar son party mussaman irin wannan cikin dare ga harka ko ta Ina.



Dukda en mata biyu da suke rungume dashi tunaninshi da hankalinshi gabad'aya na ga Bilkees ne, yana
mamakin irin kyaun fuskanta wadda ze so ganin cikin ya yake amma munafuka kullum cikin hijab take
tana mishi bakin ciki, ya ayyana hakan a ranshi, be san me yasa komin daad'in mace se yake ji a jikinshi
kaman bazata kai bilkees ba, he has one and only wish yaga ya samu yarinyar nan yayi yadda yake so da
ita wadda soon yake saka ran hakarshi zata cimma ruwa, wani mugun murmushi ya sake wadda yayi
mugun kara mishi kyau sbd shi d'in kyakyawa ne na sossai, Sannan ga dala abinda ke jan en mata gareshi
kenan, wadda ya mayar kamar rigar sawa a rana ze kwanta da mace har uku ko a kwalar riganshi gobe
wasu ze nema.



~~~~~~~~
A daidai wannan lokacin barrister Aayan ya gama duba case da ze fara gabatarwa jibi wadda hakan ya
nuna mishi dole gobe ya ziyarci familyn yarinyar ya kara fuskantan abinda ya shige mishi duhu, rufe
system d'in gabanshi yayi ya mike ya shige toilet alwala ya d'auro yazo ya wuce inda ya kebance don
sallah a cikin d'akin nashi bayan ya saka jallabiya ya tada sallah, raka'a biyu ya gabatar bayan ya sallame
ya had'e kai da gwiwa yana adu'a hawaye na zuba mishi, cikin sanyin murya da zub da hawaye ya furta
'maami...' da sauri ya share hawayen ya mike ya cire jallabiyar ya koma gadonshi bayan ya sa hannu yayi
switching light ya janyo sahar jikinshi tare da rintse ido hawayen shi na cigaba da gangara duk kuwa da
yadda yake son dannewa.



Mutuniyarshi

2 / 5