Chapter 3 Reading LELEWAL by Farin Wata HN Novels

LELEWAL by Farin Wata

Author :  Farin Wata Category :  KDP NOVELS

Chapter   3 / 5

6K to 9K   out of 12.3K words

kuwa na chan tana aikin dannan wayanta bama ta san halin da yake ciki ba, ko da ya dawo
dama ba magana ta mishi ba shima kuma be neme ta ba se samanshi da ya hauro ya shiga harkokin
gabanshi......




πŸ–€GureenjohπŸ–€

[15/07, 6:26 pm] Diddi Walida: πŸŒ•πŸŒ•



πŸŒ•LELEWALπŸŒ•

πŸ¦‹FARIN WATAπŸ¦‹



πŸŒ•πŸŒ•



STORY AND WRITTEN BY:- Fatima Muhammad Gurin.



MARUBUCIYAR:-

ZUHRAA
HAMRAH

IGIYAR RAYUWA

NOOR IMAAN and

RUWAN SAMA.



FOLLOW ME ON WATTPAD @Gureenjoh6763



SADAUKARWA:- wannan littafin gabad'ayanta sadaukarwace gareku @68Billygaladanchi wato Anty billy
and my dearest sister haneefah Muhammad Gurin thanks for your Advices and support Allah ya bar
kauna.



JAN HANKALI:- Toh masoya na ga ni da sabon labari kaman yadda kuka dad'e kuna tsumayi, am not
perfect but I promise to give you all my best on this, akwai tufka da warwara masu matukar sarkakiya a
wannan labari. Kaara d'aya zuwa biyu nake bukata daga gareku please ku Nuna min jin daad'inku ta
hanyar comments and share ta yadda ze karad'e ko ina, wannan littafi kyauta ne domin jin daad'inku
masoyana. Na godeπŸ₯°πŸ™.




EXQUISITES WRITERS FORUM πŸ“

(Home of exquisite writers')



Godiya ta tabbata ga Allah me kowa me komai.

β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”



..........3



Cikin baccin da ya kuma d'aukanta kan sallayar take jin kiran sallah sama sama, a hankali ta bud'e
idanunta tana me mikewa zaune, ta d'an jima kan ta mike zuwa toilet ta kuma yin alwala tazo ta tashi
ba-ba lami da indo se da taga tashinsu kan ta tada raka'atainil fajr, a natse take komanta yadda daga
gani zaka fahimci ilimin addini ya ratsata, bayan sun idar da sallahn asuba kowa ya fice Don fara
Ayyukansa.



Indo Zata haura sama bilkees tayi saurin riketa tana furta "Da karambanin kin nan bazan barki hawa
sama ba kije ki tashesu ni In shiga uku, gyara kasan bara na haura" harararta indo ke yi ko kulata batayi
ba ta haura ta share saman tas ta kuma yi moping.

cikin lokaci kankani wurin ya d'auki kamshi da haske, a natse ta leka d'akin sahla ganin bacci take
yasa ta wuce toilet d'inta ta fara shirin wankewa.



Tab ta kunna tare da tura bucket don tarar ruwan da zata sa omo don wankewa, a yayinda ruwan ke
zuba idanunta kuma suna kanshi hankalinta gabad'aya ya tafi ga tunanin hasken rayuwarta da har yau
bata san inda yake ba, kaman an kunna mata kaset haka mafarkinta ya ci gaba da dawo mata.



Kasurgumin daaji ne me cike da duhu ba abinda kake ji se kukan tsuntsaye daban daban........



kafafune guda biyu na namiji da mace suna gudu cikin zafin nama namijin ke jan hannunta yana kuma
waiwayen baya, cike da tsoro da fargaba, tuntu'be taci ta fad'i hawaye na zuba cikin tsantsar gajiya da
kishirwa ga wani bala'in yunwa dake azalzalanta ta kalleshi ta furta.;



"yaya na gaji..." Baya ya kuma kalla Jin alamun motsi yasa ya duka cikin haki yace "oya hau bayana
Bilkees yi sauri karsu taddamu" hawa tayi ya mike ya cigaba da gudun da dukkan alamu gudun na ceton
rai ne ba shi ya tsaya ba se bakin wani rafi..



Ya ajiyeta yana duba kafanshi da ya fashe duk kayoyi sun shiga, kallonta yayi yayi murmushi wadda har
kumatunshi na dama ya lo'ba, cikin tausayawa ta rike kafarshi tana kuka;



hannayenta ya kama ya mikar da ita yana furta "hey me na kukan? I'm fine" zatayi magana suka ji gudu
ta bayansu da sauri ya janyota bayan wani bishiya da ganyayyaki suka rufeshi tare da danna mata baki.



d'aga kan da ze yi me ze gani!! maciji ne daidai wuyanta yana shirin sarinta cikin zafin nama ya juyata ta
dawo kirjinshi macijin yayi azamar sakin dafinshi a daidai kafad'unshi, idanunshi ya runtse da karfi sbd
azabar zafi wadda se lokacin ta lura a take ya fara had'a gumi kan kace kobo ya yanke ya fad'i wani irin
ihu ta kwala tana kiran "yaayaaa"........



A firgice ta dawo daga tunaninta jin zuban sassanyar ruwan sanyi a fuskanta a rud'e take jan numfashi
sbd shid'ewar da ta so yi sbd ruwan a bazata ya zo mata, sahla dake tsaye rike da bowl tace "iskancin
banza iskancin wofi, wato tsabar salon wulakanci Ina cikin bacci kika kunna ruwa da gangan yake ta zuba
har yayi sanadiyar tashina wadda kin san ba komawa zanyi ba sbd ke bazaki samu daman baccin ba shine
kike bakin ciki?".



Zata yi magana sahla tace "shut up bloody fool wuce fitar min daga toilet kuma wallahi bashi kika ci se
naci ubanki yau" fita tayi jikinta a sanyaye runtse idanu tayi ta kuma bud'e sun kad'a sossai sbd a
rayuwanta ta tsani ruwan sanyi tunda tayi wani ciwo sanadiyar azabar ruwan sanyin Mama take tsoron
sanyi, kallon kayan jikinta tayi In ta zauna dashi to tabbas se bala'e'iyar mura ta kamata kasa ta nufa Don
chanza kaya, Tana gama sauka parlorn taji an fisgota zuwa lungun stairs an danne bakinta.........



A firgice ta zare idanu a lokaci d'aya tana shirin kwacewa sbd warin giya da ya kusa sumar da ita, ba
tantama Aadil ne, cike da 'bacin rai ta sa hannu biyu ta hankad'ashi da iya karfin da Allah ya bata;



aiko ya tafi luuuu ya buga keyarshi da tsinin ginin stairs abinka da tsautsayi ga kuma jiki luwai luwai na
en hutu abu kam ya hud'a mishi keya se jini, cikin azaban zafi ya sa hannu ya ta'ba wurin tare da dawo
da hannun zuwa ganinshi waro ido yayi yana kallonta ita kuwa ta daskare a tsorace.



A take ya fara gani bibbiyu, ga dama chan a shaye yake tatul, luuu ya tafi ya zube kasa dukda haka be
fasa yi mata kallon 'you are dead' ba .



Sahla da ta biyo sahunta Don ganin In ta barta taci bulus ne ta kwala kara tana kiran sunan yayan nata,
zuwa lokacin ba karamin rawa jikin bilkees yake ba ta san yau ta gama kad'ewa har ganyenta hawayen
idanunta ne suka gangara a sadda Sahla take kwala kiran sunan "ummie! ummie!!" Cikin karaji



Ummien da tun ihun sahla na farko ta fara kokarin fitowa ce ta amsa tana gangarowa daga stairs, kallo
d'aya zaka mata ka san bata wani samu baccin kirki ba, ko me yasa? Allah masani.
Da sauri ta karasa gangarowa cikin tashin hankali tace "sahla me ya sameshi??? Maza maza Kira
shu'aibu da lawwali a kama min shi a sa mota mu tafi asibiti, Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun".



Da gudu sahla ta fita ba tare da ta damu da kayan bacci ne jikinta ba, sbd a lokacin bacci ya kwashe Aadil
wadda su a zatonsu suma yayi sede basu san giya ce ta fara aikinta ba.



Sanin bala'in mutan gidan yasa driver da me gadin baro abinda sukeyi da wuri suka shiga parlorn, a take
suka d'auke shi da kyar zuwa motan ummie, sahla ta haura ta d'auko mata key da khimar ta fice cikin
sauri a lokacin kusan 6:30am.



Dukar da kanta tayi ganin irin kallon da sahla ke jefanta dashi a hankali ta matso gabanta tare da sa
hannu ta rike kunnenta.



"Dan ubanki me kika mishi??" Shiru bilkees tayi kanta kasa ta san yau ta kad'e har ganyenta tunanin
abinda zata ce takeyi bata hankara ba se jin saukan mari tayi akan kuncinta, a razane ta d'ago ta zuba
mata idanu hannunta dafe da kunci.



karfa kuyi mamaki In nace muku bilkees ta girme ma sahla da almost year, idanunta ya kad'a sossai
ranta wani irin kuna da tafarfasa yake "me mutanen gidan nan suka d'auki kansu ne?" Tayi maganan ne
a zuciya ba tare da sanin a fili tayi shi ba se jin wani saukan marin tayi.



"Har se kin tambaya?" Tayi wani irin dariya kan tace "dan ubanki har kin isa ki ce min me muka d'auki
kanmu? Bayan ji ma wa na ciwo da kikayi? Wallahi bilkeesu In har Ina da rai kuma kina gidan nan se na
kaskantaki kaskancin da baki ta'ba tunani ba, wawiya jaka, yau se kin yabawa aya zakinta a hannuna kan
mommy ta dawo, shegiya me kama da mayu wuce muje."



A Baya ta bita har waje ta kirawo me bawa flowers ruwa, ta kuma kira baaba lami da indo cikin fisge kai
da nuna isa tace "yau gabad'aya na hanaku aiki, duk wani aikin da kukeyi ku tabbatar kun bar wa er iskar
yarinyar nan yau ita zatayi, kuma na rantse In kama wani na tayata ku ga..." tana kai nan ta juya ta fice.
Lumshe manyan idanunta tayi na mintuna ta kuma bud'e hawayenta suka gangaro da sauri ta sa hannu
ta share tare da sakarwa su baaba laami dake aika mata kallon tausayi murmushi, juyawa tayi ta koma
parlorn kasan ta shige d'akinsu fahad.




~~~~~~~~



Tunda ya dawo sallahn asuba be kwanta ba se cigaba da duba wannan case d'in yake yana mamakin
maza marasa Imani masu yiwa mata fyad'e, Me yasa bazasu nemi mata karuwai da suka kai kansu ba se
waenda suka killace kansu? Tabbas shi kuwa se ya d'aukawa yarinyar nan fansa Don se inda karfinshi ya
kare kan wannan shari'ah.



Bayan ya gama d'an abinda ze yi ya shiga wanka cikin mintuna da basu wuce 40 ba yayi ya fito a
shiryenshi tsab cikin blue suit da er ciki fara tare da blue black tie, blazer d'in na rike a hannunshi ya
d'auko brief case d'inshi ya fito har seda ya fito ya tuna sahar kallon time yayi a tsadaddiyar wrist watch
d'inshi ze makara In yace se ya tsaya mata wanka da nemar mata abinda zata ci dukda shi cikakken
lawyer ne me zaman kanshi.

"sahar" ya kira sunanta da sauri ta kalleshi dama ita ba me baccin safe bace duk inda 6 yayi ta farka.



Yace "ina ummanki?" Tace cikin fullancinta da maganarta da ba fita yake sossai ba "tana bacci, Abbie zan
bika" tayi maganan cikin turo baki irin na shagwa'ba'bbun yara, yace "Toh mamana zo muje".

Da gudu ta mike ya rike hannunta suka shiga d'akin zaheera se 'bata fuska yake sbd zarnin fitsarin
toilet d'inta da ya tabbata ya kai sati be ga wanki ba, karamar drawer d'in sahar ya nufa ya d'aukar mata
kaya suka fito zuwa mota ba tare da ya kalli ko ta 'bangaren da zaheera take tana kwasar baccinta ba;



Sbd ya san ko tashin duniya ze mata ba tashi zatayi ba bare har su saka ran samun breakfast, gidansu ya
nufa da ita daga bakin gate ya sauka tare da d'aukanta da kayanta zuwa bakin gate ya sa hannu ya
kwankwasa lawwali ya leko ganinshi yasa ya washe baki "aaa Alhaji karami barka da safiya" yace "Yauwa
baba Barka dae, dan Allah taimaka ka mika min ita cikin gida na so in makara ne, kar In shiga kuma In
zauna".
"A'a to to ba damuwa Allah ya tsare" yayi maganan yana kar'banta kasancewar bata da kyewya yasa ta
je, har tana yi ma babanta bye bye, shima byee ya mata bayan yayi pecking d'in kumatunta ya juya ya
fice, rufe gate d'in baba yayi ya nufi cikin gidan.



~~~~~~~~~



Da d'akinsu fahad ta fara, d'aki ne me d'an yalwan fad'i da gado na katako irin na yara, gadon farkon an
saka zanin gado blue me zanen spider man yayinda d'ayar ya kasance me red zanin gado da zanen Ben
10, a gefe kuma kwabar kaya ne guda biyu shima d'aya red da fari d'ayar ma blue da fari, se kafet me
kalolin nan uku da aka kawata d'akin dashi se karami na takawa da aka saka daga chan daidai kofar
toilet.



Standing fans guda biyu da Ac ne kawai a d'akin bayan kayan gadajensu ba karamin kawatuwa d'akin
yayi ba, fahad dake kan na farkon ta fara tashi suka shiga toilet ta had'a mishi Ruwan wanka ta fito da
kanshi yayi sbd baya yarda a mishi kan ya fito ta fidda mishi uniform d'inshi wando three quarter blue da
milk shirt me guntun hannu, da karamar tie haka ma na khalil yana fitowa ta d'aga khalil shi kam ita ta ta
mishi suka fito se ma surutu yake mata sbd yanayin da take ciki yasa sama sama kawai take amsa shi, ta
shafa mishi mai ta saka mishi uniform bayan shorts da ta sa mishi.



White Socks da black boots d'inshi ta d'auko ta sanya mishi dama tuntuni fahad ya saka nashi,
kowannensu ta d'auko mishi school bag d'inshi ta mika mishi "ya fahad aje a ci abinci a tafi school kar a
makara".

dayake shegen son girma ne da fahad hakan yasa take tsokanarshi da yaya sbd ba yadda be yi
khalil ya dinga ce mishi yaya ba yaki, suna fita ta hau gyaran d'akin seda ta share ta shiga toilet d'insu ta
wanke ta kunna musu Ac ta sa fan d'insu a chargy tana shirin fitowa se ga khalil rike da hannun sahar.



Kallonta bilkees ta tsaya yi da murmushi sbd yarinyar ba karamin sha'awa ta bata ba kyakyawa sossai ga
gashi Masha Allah, maida kallonta kan khalil da ya fara magana tayi.

"Bilki ga Baby sahar nan itama wai se an mata wanka an sa mata uniform" rike hannun layla tayi
dake hangala mata baki ta dubi khalil ba tare da ta damu da kiranta bilki da yayi kai tsaye ba sbd ta san
yayyunsu sun hanasu ce mata wani Aunty, tace "toh je ka karka makara" kallon sahar tayi da ke cewa
"Anty nima zan je ki min wanka In bisu".
Shafa kanta tayi tace "right away baby, sede fah In nayi miki wanka kika tafi school a haka zane ki Antyn
school zatayi kinaso ta zane ki?" Shagwa'be fuska tayi tana make kafad'a tace "uhm uhm" Tace "yauwa
baby girl muje muyi wanka mu wanke kai kanki yayi datti" turo baki tayi bilkees ta d'auke ta zuwa toilet
tayi mata wanka ta nad'o ta towel se surutu take zuba mata nan da nan bilkees ta sake tana jin son
yarinyar a ranta.



~~~~~~~~~~



A asibiti kuwa seda doctor ya aske daidai inda ya ji raunin kan ya d'inke aka bashi gado ya fito ya samu
ummie dake safa da marwa yace "hajiya ciwon nan ba wani ciwo bane na har chan an ma mishi d'inki
yanzu dae matsalar itace shaye-shayen da yakeyi In har baku mishi fad'a ya kiyaye ba nan gaba Ina jiye
muku tsoron halin da ze fad'a na tabbatar Alhaji sadiq chubado ba sanin hakan yayi ba da kila ya d'auki
mataki".



Cikin masifa tace "Ina ruwanka? Nace Ina ruwanka da saninshi da rashin saninshi, aikinka shine ka
dubamu ka rubuta magani ba'a sa da saka ido ba" ta kama tafiya tana mitar "In ba ma nigeria ba mutum
na aiki a karkashinka yana ci gaba dakai amma ya nemi ci ma fuska".

girgiza kai yayi ba Don yana ganin girman Alhaji sadiq chubado da Barr. Aayan Sadiq chubado ba da
ya jima da dena yiwa familynsu aiki sbd sauran yaranshi amma ba komai aje zuwa ya juya ya fice cike da
kunan rai.



~~~~~~~~~~~~



Zaune yake a wani karamin tsakar gida kan kujeran tsuguno inda mutanen gidan ke zaune kan taburma
uwar da yayar mace se kuka suke yayinda uban ya zabga tagumi tare da zubawa yarinyar da bata wuce
12 years ba ido, idanunta a kafe wuri d'aya ko juyasu batayi.

cike da tausayawa yace "kuyi hakuri inna haka Allah ya kaddaro mata tata rayuwar, In Shaa Allahu
se inda karfina ya kare wurin kwatar mata en cinta bana bukatar ko naira biyar d'inku akan wannan aiki
burina kawai ku yarda a kaita asibiti a duba ta, kunga rashin sake maganan nan babban abu ne ba'a sani
ba ko ya bita har abada".



Ajiyar zuciya baba ya sauki yace "d'an nan me yasa kake son taimakonmu haka?" Aayan yace "Saboda
Allah" baban yace "yaro ka gama magana, Allah ya saka maka da alkhairi ya biyaka yaji kan iyaye, Allah
ya baka masu Jin kanka haka, bara na shirya muje" Da Ameen Aayan ya amsa yana murmushi, zaro
wayanshi yayi ya shiga kiran Dr. Basheer Abdulbasid, ringing biyu ya d'auka cikin zolaya yace..



"Kaga barrister dodon en iska" murmushi kad'an Aayan yayi yace "likita bokan turai, ya aiki?" Yace "Da
godiya ka Kira jin ya jikin kaninka ne? Cikin rashin fahimta Aayan yace "kanina kuma?".

Dr. Basheer yace "au baka sani ba? Brother d'inka na nan ban san taya ya ji rauni a kanshi ba, he
was drunk sanda suka zo har d'inki na mai".

Aayan yace "subhanallah was it that bad?" Dr. Yace "da sauki dae, ya ne to kiran me aka min? I
know you baka kira seda dalili" Aayan yace "gani nan zuwa patient zan kawo, raping d'inta akayi wadda
tun daga ranar bata iya magana se de ta kurawa wuri d'aya ido I think shock ne zan kawota ka taimaka
pls gobe akwai shiga court".

Dr. Basheer yace "subhanallah!! To Ina jiranku se kun karaso" suka ajiye wayan kan nan innan ta
sa khimar ta sanyawa yarinyar me suna Aisha, baban ne ya kamata suka fito suna ba yayar amanar
gidan, da kanshi ya bud'e musu Baya suka shiga ya zagaya ya shiga ya ja se asibitin.

Direct office d'in Dr. basheer sukayi inda shi kuma ya kamata suka fita bayan yayiwa iyayen jaje,
Aayan ma ya mike yana cewa "Ina zuwa baba" ya fice, d'akin da Dr. basheer ya fad'a mishi su ummie
suka ya nufa, yana shirin tura kofar yaji Aadil na furta.



"Na rantse randa na kama yarinyar nan se na mata fata fata, ummie daga na rungumeta shikenan se taji
min wannan rauni? Ba ma wannan ba kin kuwa san yadda nake valuing hair styling na? Yanzu kwalkwal
zata sa nayi?".

Ummie tace cikin fad'a "nace maka ba ruwanka da yarinyar nan Aadil, In zakayi neman matanka ka
nema waje gasu birjik me had'inka da wata banza me aiki? Ka kiyayeni na gayama Sannan na rantse In
baka rage shaye shayen kan nan ba duk randa mahaifinku ya sani ba ruwana".

Girgiza kai Aayan yayi wace yarinyace kuma Aadil ke kokarin wulakantawa? Kwafa yayi tare da
knocking kofan ba tare da ya jira izini ba ya tura ya shiga, ummie ne ta kalleshi da mamakin wadda ya
gayamishi, Ita Allah ya gani tana takaicin ganin duk wani ci gaba 'ya'yan zara'u ke samu amma nata
babban da ya kamata ya yi abin kirkin se shegen shaye shaye da bin mata kaman wacce akayiwa baki.



Ajiyar zuciya ta sauke tare da sake murmushi tace "Son wa ya Fad'amaka muna nan? Kila sahla ko? Ta
d'aga maka

3 / 5