SEXY BOOS BOOK 1 ROMANTIC NOVEL BY MAMAN TEDDY.pdf

Author :  Aisha Maman Teddy Category :  Taskar Novels

Chapter   9 / 10

24K to 27K   out of 28K words


Cikin gwasalawa da wawantar wa Yaya Hadiza tace " Au iskancin naki har ya kai ga Nan? Kin
san waye Sir Umair kuwa da har zaki masa wannan sharrin , don an kawo ki gidan mijin ki a
ragowar ƙattai . Kinje wani ƙato ya gama buga maki iska sai Kizo mawa ƙaninmu a matsayin
ragowa . To hattara kar ki ƙara faɗin munin abu akan Sir Umair , don kaf dangin ku zai ƙarar
Bakya kaɗai ba ,mubafaka muguwa kinci mana mutunci tsakanin mu dake ALLAH ya isa.!

Wani irin fashewa da kuka Umaima tayi tana ɗaura hannun ta aka ,sam ta rasa me ma zata ce
fadi take wayyo Ni Umaima ,Ni naja wa kaina ..! Kai Da ALLAH sake ta yanzu ka fito ,iyayen ta
da suka kawo mana Ragowa gindu a fafake su taho su dauke ta ,don har da ajiyar ƙwarto.'
girgiza kai Ashiru yayi kana yace " Ina son ta a haka , ku barta zan Zauna da Umaima , har ta
haifi ɗan ta ko ƴar ta zan riƙe su mu cigaba da zama har Abada...sakarcin banza ,au Dama Kai
shashasha ne nasani . Idan soyayya ya rufe maka ido ,mu namu idon a bude yake ,yanzu
wannan shedaniyar a yau sai ta bar gidan nan.!

***

Umair lafiya me yake damunka haka?. Ammie ke Tambayar sa cike da mamaki ,Daddy ne yake
furta Umair kana lafiya kuwa? Kasan me kake sha a tsakiyar falo? A gaban ma'aikata ,idan
baka ji kunyar mu ba ,ai kaji tsoron Abun da mutum zai je ya faɗa. Wannan fa giya ce.! Cewan
Daddy Yana pointing ɗin Ƙwalbar barasan da hannun sa . Meye Daddy ,Ammie wannan ce
kaɗai zai ɗabemin kewar rashin ta kusa dani. Ina Son Umaima ,Ina son ta , but she Go and live
me aside. Why she do that to me???. Daddy Bana da kyau ne ,ko kuwa bana da matsayin da
wata ɗiya kaman Umaima zata soni ne??. Dad you now what??? Yayi maganan cike da murya
ta maye ,kana yace akan ta na fara jin daɗin Sex ,I need her." Kamin ya rufe baki ne yaji mari
tassssss". Cikin wani irin huci Daddy Ke kallon Umair kamin yace" Tashi ka fucemun daga falo
mara kunyan wofi . Umair kai naka giyar kudin da ƙuruciyar da haka yazo maka?. Miƙewa yayi
ya na tangadi. Nigeria is urs'. Bana wa bane ba, since before now na tsani Nigeria , a yau zan
ɗauki visa na zan koma ƙasar Momy na nayi rayuwa ta . Yana gama faɗin haka ya juya yana
tangadi ya nufi hanyar fita daga falon. Umair .!! Ammie ta ƙwada kirar sa idon ta na zubda
Hawaye . Bai bi takan ta ba ya sa kai yana ficewa daga falon. Cikin sauri Ammie ta juya tana
bin bayan sa tare da kirar sa.


Kar ki taka ko nan da can.! Taji Muryar Daddy Yayi maganan a fusace . Cak taja ta tsaya tana
kallon sa hawaye na bin kumcinta . Daddy ya Zamu yi mu sa Umair farin ciki. Ammie magana
kika tsaya yi , Ya Umair fa ya fita ,kuma ba a hayyacin sa ba , nasan ma da kansa zaice zaiyi
driving lemme go and escort him . Cewan Surayya da duk abun da ya faru tana daga bayan su
tana jin su. Ammie ki daina kuka zan sa yaya Ya fasa tafiyar nan duk yanda zanyi zanyi naga
bai koma can ƙasar ba. Don Allah Surayya kiyi kokari wallahi mukayi kuskure Umair ya bar
Nigeria to ganin sa sai yayi mana wuya. Ammie na sani . Da gudu Surayya ta bar falon tare da
nufar farfajiyar gidan tana ƙawsa kirar Ya Umair.!!!!





*AUNTY AISHA MMN TEDDY*
*Q*

*Littafin THE SEXY BOSS na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun ba tare da kin biyani haƙƙi na
ba... Regular group ₦300...Vip group₦500... Special ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha
keystone bank ko kuma ki tura katin MTN ta wannan number 08081202932 Idan VTU transfer
zakiyi ki tura kai tsaye ta wannan number 09061466409*

Da wani irin gudu Surayya ke bin bayar Umair wanda tuni ya isa ga moton sa yana kai hannun
sa tare da buɗe murfin moton , jin Kirar sunan sa Da Surayya keyi yasa shi dakatawa daga
shiga cikin moton yana juyowa tare da bin ta da kallo a miskilance. Isowa Surayya tayi tana haki
don gudun da tayi kana tace " Pls Yaya Umair Kar kayi driving da kan ka , idan kayi a wannan
halin da kake ciki komai ka iya faruwa da kai . Bari Ni na kai ka. Duk maganan da take bai bata
amsa ba har ta dire ayar ta , baya yayi yana Matsawa ita tare da juyawa yana nufar side ɗin mai
zaman banza , ita kuma ta shiga daga ciki tana fara driving ɗin moton , tare da barin farfajiyar
cikin gidan.! A hankali take tafiya tamkar ƴar koyo domin jikin ta yayi sanyi , Shiru tayi tana
tunanin kalaman Yayan nata akan UMAIMA ,wannan wacce irin marar rabo ce da har ya Umair
zai ce yana Son ta ,ta zaɓi Aurar talaka akan Yaya na.? Wacece ita? Niko zan so naga ita ɗin
wacece??? Mai ta taka Ƙyau ko dukiya..? Abun da Surayya ke faɗi kenan a zuciyar ta tana
driving tare da kallon Umair ta gyefen ido. Addu'a Surayya keyi ALLAH yasa Umair yayi barci
,wanda juyowa n da zatayi taga tuni barci yayi gaba dashi. Murmushi tayi tana furta Alhmdllh .
Gidan sa na Abuja ta wuce da shi kai tsaye , bin gidan na tsaya yi da kallo , ina mmkin
ƙayatuwar shi , wato shi ko a ina sojoji yake sakawa suna masa gadi kenan. ,don anan ɗin ma
sojojin ne securities nasa . Horn Surayya tayi nan take aka buɗe mata Gate ɗin tana kutsa
moton izuwa cikin farfajiyar gidan . Shiru Tayi tana cikin moton kusan mintuna Biyar tana
tunanin ya kuma zata yi da Umair shi da yace " Airport kuma ta kawo sa cikin gidan sa .

Juyawa tayi tana bin securities masu fararen kaya na gidan ,da kowa ke aikin gaban sa. A
hankali ta fice daga moton tana nufo side din da Umair yake kana tasa hannun ta a saman
nashi tana ɗan girgiza shi da faɗin " Yah Umair .! Yaya Umair.!! Tana ƙara girgiza hannun sa .
Buɗe lulun idon sa yayi yana sauke su akan fuskar Surayya da ta sakin masa murmushi kamin
tayi magana ya fito da kafarsa waje yana fitowa daga moton . Kama shi tayi tana rungumo shi
wai ala dole ga mai iya Bada kula ,hannun ta ta zagoyo dashi ta bayan sa . Murmushi yayi a
haka suka isa har falo. Ni ma dai kaina nayi dariya ganin. Surayya ce zata iya rike yayan nata
wai gudun kar ya faɗi a maye . Gata can ƙasan kafaɗan sa . Ko da suka shiga daga ciki direct
Bedroom ɗin sa ta wuce da shi ,tana ƙwantar dashi a saman lafiyayyen Bed ɗin sa mai shegen
ƙyau. Lumshe idanun sa yayi Surayya na rufe sa da Blanket tare da cewa " Ya Umair barci mai
daɗi". Bata jira jin mai zai fito daga bakin sa ba ta juya tare da barin Bedroom ɗin tana nufar
falo. Bin falon ta tsaya yi da kallo , sai taji wayar ta ta fara ruri . A hankali tasa hannu tana
picking call ɗin kana ta kara A kunne tana furta" Hello Ammie". Yana lafiya ko?. Abun da
Ammie ta tambaya kenan . Eh Ammie y samu barci ne yanzu haka , zan zauna da Yaya anan
Har zuwa lokacin da zai manta da wannan yarinyar a zuciyar sa da rayuwar sa . Kuma zanyi
kokarin ganin ya amince ya zauna a nan Nigeria bai bar ƙasar nan ba.

Hummmm Ajiyar zuciya Ammie ta sauke kana tace " Ohk to ba damuwa , Allah ya taimake mu ,
ka sanyaya zuciyar wannan bawa naka". Amin Ammie cewan Surayya tana ƙare cewa " Sai
munyi waya .Ohk Ammie tace tana datse kirar . A hankali Surayya ta nufi under ground don
anan ɗakin da duk tazo gidan anan ɗakin ta yake . Nufar Bedroom din ta tayi wanda anan ta
tadda komai tsaf kaman tana nan a koda yaushe,don rabon ta da Bedroom ɗin tafi shekara
guda . Fitowa tayi kai tsaye ta nufi Kitchen don haɗa mawa Ya Umair dishes sanin kan ta ne ya
farka daga barcin sa zai iya buƙatar abun da zaici ,wannan yasata nufar Kitchen ɗin don fara
shirya masa Abun da zai taɓa .!

***


Ɓangaren Umaima kuwa bala'i yanzu take don Yayan Ashiru wato Yaya Uwauwa fita tayi daga
ɗakin nata wanda yake falle ne ɗaya , babu abun da aka sanya sai gado da durowa , da kujerar
mai cin mutum biyu guda ɗaya komai nata na ɗan talaka ne . Fitar da yaya Uwauwa tayi gidan
ta bari baki ɗaya ,kowa ta gani a hanya sai ta furta gashi can Umaima daga kawo ta ɗaki ta fara
amai ,ta taho masu da cikin shege , wallahi Ashiru ba zai shiga ɗakin ba yanzu iyayen ta sai sun
zo sun ɗauke ta . Haka take sambatu na masifa kowa ta gani a layi sai ta fallasa , kamin
magana ya iso gidan su Umaima kunsan ƙaramar unguwa tuni magana ya gama karade layin
da ko'ina . Koda ta isa gidan su Umaima cikin dandazon dangi da ƴan uwa da abokanan arziki a
wannan lokaci ta kama ƙugu tana faɗin su taho su dauki yar su ,dama sun san yar su
watsatstsiya ce suka liƙa mawa ƙanin su , to su zo gashi ta kunso ɗan zina , maza su taho su
tattara koman su ,su fitar da ita daga gidan su . Kallon ta Kowa keyi yayin da Yaya Hannatu ta
nufo Yaya Uwauwa tana cewa " Kaman ya ban gane ba.? Umaima yarinya ƙarama kuma kuka
taho mana da wannan sharrin akan ta?. Sharri ai mu bamu saba sharri ba ,gashi can ta kilaya
Amai kaman zata fidda yan hanjin ta kuce sharri . Hummmm ko wacce burga zakuyi kuyi dai
,dama kun san yarinyar nan watsatstsiya ce , to mu gidan mu duka ba shegu bane . Hannu
yaya Hannatu ta ɗaga tana shirin Wanke fuskar Yaya Uwauwa da mari Nan Umma tayi saurin
riƙewa tare da faɗin " A'a dakata Hannatu Rabu da ita maza yanzu kuje ku dawo mun da
Umaima .!

Wani irin zafi zuciyar yaya Hannatu keyi kana tace " Wallahi kinci Albarkacin Umma ,da badon
haka ba,sai kin yaba ma aya zaki ,meye a dangin naku ban da tsiya da tijara,kuma gashi kunzo
kun nuna mana hali ai . Kuma kusani Wallahi Umaima ta bar Ashiru har Abada . Juyawa yaya
Hannatu tayi bata jira jin na bakin Uwauwa ba ,ita da su Lawisa kusan su huɗu suka ɗauki
mayafi suna nufar gidan su Ashiru don dawowa da Umaima . Yayin da Yaya Uwauwa take wani
zambaɗa sauri don tuni tayi gaba ta isa gidan basu zo ba . Da isan ta ne ta shiga ɗakin da har
yanzu Ashiru bai fito daga ɗakin matan gidanab fiye da goma sha sun cika dakin kowa na Allah
wadai . Itako Umaima sai kuka . Ji tayi Yaya Uwauwa ta fizgota tana yo waje da ita zuwa tsakar
gidan. Dai dai su Yaya Hannatu na isowa . Ke baiwar ALLAH iskan cin ki ya fara yawa fa.!

*Zamu kammala book 2 don haka idan mun kammala book 2 masu saye ₦300 ne complete ,
Idan kuma duka muka kammala masu sayen complete 2 and 3 ₦600 ne .*


*AUNTY MMN TEDDY*
*R*


*Littafin THE SEXY BOSS na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun ba tare da kin biyani haƙƙi na
ba... Regular group ₦300...Vip group₦500... Special ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha
keystone bank ko kuma ki tura katin MTN ta wannan number 08081202932 Idan VTU transfer
zakiyi ki tura kai tsaye ta wannan number 09061466409*
_Happy New year to u and all ur near dear ones wish you all only the best..great health and
happiness, peace, sucess and learning in Al u Do...#Welcome 2023️_

*END OF BOOK 2*

Yaya Hannatu ne yi ɗammara da mayafin ta tana kallon Yaya uwauwa da take daɗa surfa
masifa. Ke baiwar Allah na rantse da ALLAH kika kuma taɓa Umaima sai kusa zubar maki da
jini ,kawai daga yarinya tayi amai shikenan sai kuce ciki , wato ba'a amai haka kurum kenan. To
bari gargaɗeki mu mun karbi Umaima , kuma kisani daga yau mun rabata da ke da ahalinki
dashi kan shi Ashirun rabawa ta har Abada .don haka kuja kunnen ɗanko. Idan kuma yayi
kuskuren kawo ƙafarsa ko bakin sa to duk Abun da yabiya baya shiyasa Ni . Yaya Hanne tana
gama maganan taja hannun Umaima dake kuka kaman ranta zai fita. Yaya Hannatu don ALLAH
kuyi haƙuri kuskure ne da rashin fahimta ,amma ina son Umaima ,ficewa yaya Hanne tayi ,kana
Lawisa ta tsaya tana kama ƙugu tare da bin gidan da matan Gidan da Kallon uku saura ƙwata .
Humm shiyasa aka talaka bai ya samun wuri ba. Ku kalla gidan da Umaima ta fito ba kaman
wannan gida da aka jefota Aure ba. Me kike nufi kenan? Cewan Yaya Uwauwa tana matsowa
kusa da Lawisa da ta cigaba da cewa " Eh mana ai gaskiya na faɗa . Kalli da Ashirun wani
zagalo dashi ,ai wallahi Umaima ta wuce mawa Ajin Wannan da gidan nan baki ɗaya ,dama
karamci aka maku amma kun nuna baku san hakan ba.

Kamin taji wani magana da zai fusata ta ta juya tare da barin gidan Su Ashiru da ƴan biki cike
da dangi da yan uwa .

***

Da sanyin safiya ne Surayya ta miƙe cikin sauri ganin yanda rana ya fito har 8:35am bata farka
ba sai yanzu . Saurin fitowa tayi izuwa falo , wanda dai Umair yana bamawa wani mai aikin
gidan nasa , jakarsa irin babban nan na matafiya wanda sojoji ke tafiya dashi. Saurin saukowa
Surayya tayi tana hugging din Umair tare da cewa " morning Yah Umair. Shafa kan ta yayi yana

cewa " Kin tashi.? Gyada masa kai tayi alamun eh. Ohk yanzu ki shiga ciki ki kimtsa , ga
breafast ɗin ki a dining area , Ni zan wuce Germany yanzu zanbi jirgin 9:00am ,nayi magana da
Julayb zai zo ya ɗauke ki ya mayar dake gida. Ƙwallah ne ya ciko idon ta ,kana a shagwaɓe
tace " Ya Umair me yasa ba zaka zauna anan ba Pls ya Umair ka zauna damu. Ammie zata
nemo maka mata mai kyaun gaske fa fiye da Umaima.!

Ba zaku sami kamar Umaima ba ita ɗin ta daban ce , Zaman can zaifi mun fiye dana zauna
anan a kowacce rana tunanin ta nake yi bana iya hasala komai Surry , matso kiji . Yayi
maganan yana kallon Surayya da idon ta ke fidda ƙwallah. Baki ji komai ba?.


Kallon sa Surayya tayi cike da rashin fahimta kana tace "Yah Umair banji komai ba. Hummmm
nisawa yayi yana sauke ajiyar zuciya kana yace " Har yanxu jiki na ƙamshin turaren ta yake yi .
Bazan taɓa iya mantawa da Umaima ba. Je ki shirya . Yana faɗa mata haka ya fara takawa
yana barin falon . Bin sa da kallo tayi kawai sai ta fashe da kuka tana fadawa saman kujerar
falon , Tabbas da gaske ne ya Umair ya kamu da So.! So zazzafa ,wanda zai iya saka shi ko
wani hali . Cikin sauri ta nufi gidan ƙasa don ɗaukar wayar ta ta sanar mawa Ammie don ta
dakatar dashi daga wannan tafiyar .

***

Bayan tafiyar Hajiya Mulayka ne Hajiya Turai ta fara faɗawa Duniyar tunani , wanda sam ta
gaza fiddo mawa kan ta da mafita . A hankali ta fara tunano mawa kan ta mafita daban daban
,kana Tana wannan kaiwa da dawowa ta furta' Mai jidda". Shiru tayi tana tunani kamin tace "
Anya wannan yarinyar nata tana da Raye kuwa?? . Rabona da wannan a halin Kusan shekara
goma sha takwas tun da ta haihu ta rasu ,ban kara komawa wannan dangin ba ,dole na fara
kira na tambaya , a yanzu ba sharri nake son kulla masa ba ,neman wanda zai tarkata mun kaf
dukiyar sa nake yi. Wanda dole babu wacce zata iya sai jini na.! Dole a satin nan na leƙa
ƙanwar mahaifiyata wato Hajiya Balki.


Wai shin wacece Hajiya Turai.??? . Hajiya Turai ta kasance macace wayayyar gaskiya , tun
tana yammatan cin ta haka take , mahaifin su shine Ƙani Wurin Hajiya Balki , wato kakan
Umaima . Su biyu Allah ya basa , daga ita Sai ƙanwar ta wato Umman Umaima da ta rasu
Sunan ta bilkisu . Tun tasowar Hajiya Turai ta nuna ta fi ƙarfin a nuna wannan dangin ace yan
uwan ta . Idan ka ganta a to mutuwa ne wanda ya zaman mata dole sai tazo ko tarar biki bata
zuwa bare kuma ta ɗauki jiki ha ka kurum ta taho. Tun da Umaima take sau ɗaya ta taɓa ganin
wanda a yanzu ko ta ganta zata wuce itama ta wuce basu san juna ba. Iyayen Hajiya Turai da
Balkisu duka basu yi tsawon rai ba ,don mahaifin su ya rasu ita Hajiya Turai tana da shekara 15
a duniya yayin da Umman Umaima keda shekara sha ɗaya . Ba kuma ayi shekara ba
Mahaifiyar su ta rasu . Wannan yasa Hajiya Balki cewa a dawo mata dasu gaban ta da zama. A
lokacin da Hajiya Turai ta fara yammatan cin ta ne , ta gummaci da zaman gidan Hajiya Balki
gwara taje G.R.A aikatau daganan tasan

9 / 10