Author : Aisha Maman Teddy Category : Taskar Novels
zai bari ayi wannan Auren ba .!
Kuyi manage wannan Pls ba yawa
*N*
*Littafin THE SEXY BOSS na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun ba tare da kin biyani haƙƙi na
ba... Regular group ₦300...Vip group₦500... Special ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha
keystone bank ko kuma ki tura katin MTN ta wannan number 08081202932 Idan VTU transfer
zakiyi ki tura kai tsaye ta wannan number 09061466409*
*Night Update*
Hankalin Umair sosai ya tashi da jin maganan Alh Iblo , wanda bai shawara da kowa ba ya
yanke hukuncin dawowa Gida Nigeria . A kusa can Abuja Daddy ne ke sanar mawa Ammie
abun da iyayen Umaima suka faɗa mawa Alh Iblo na An riga an mata miji sai dai Umair yayi
haƙuri . Shiru Ammie tayi tana faɗawa Duniyar tunanin ya Umair zai amshi wannan zance?
Anya zai iya haƙuri kuwa? Don a ƙwayar idon Umair take ganin mahaukacin Soyayyar Umaima
, wannan yasa yana ɗaya daga dalilin da ta amince da maganan nasa bata ɗauke shi a shirme
ba. Sauke Ajiyar zuciya Ammie tayi tana kallon Daddy kana tace " To Allah yayi mana zabi mafi
alheri . Amin ya Allah Daddy yace , kana Ammie ta muskuta tana fitowa daga Part ɗin Daddy ,
Direct Bedroom ɗin ta ta nufa . Bedside Drower ta Kai hannun ta ,tare da ɗaukar Wayar ta ,don
ta kira Umair ta rarrashe shi ,ta kuma basa haƙurin matar mutum bata taɓa Auren mijin da bana
ta ba . Abu kaman Wasa ta kira layin sa yafi sau biyar amma switch up .wannan yakuma ɗaga
Hankalin Ammie ƙwarai . A wannan ranan dai barcin ta rabi da rabi ne.
Ɓangaren Umair kuwa ƙwana yayi zaune yana jin wani irin zafi a zuciyar sa , a cewan sa shi
sam bai taba niman abu ya rasa ba . Bai kuma taɓa ƙwalla fa rai a abu bai samu ba. A kan ta
baza'a fara ba. Ƙwana yayi yana shan sigari baya duba koda lafiyar sa . Cikin matsanancin
ɓacin Rai yake furta " duk wanda yayi kuskuren Auren matar shi sai yasa shi ya ƙare Rayuwar
sa A gidan Kaso na har ƙarshen rayuwar sa. A washe gari ne Umair ya taso daga jirgin
Oustralia zuwa gida Nigeria .
***
Wani irin dariya Hajiya Turai tasa kamin ta juya tana kallon Aminiyar tugun ta wato Hajiya
mulaika . Masha'allah Allah mun gode maka , da wannan Aure ba'a bashi ba , don tamkar
shigar sauri yayi mana ,ya kauce mawa tugun mu. Don haka yanzu wasan zai fara . Kyacewa
da dariya Hajiya mulaika tayi tana miƙamawa Hajiya Turai hannu suka tafa . Ƙwarai Turai
wannan gaskiya ne , kinga sai mu zabo masa ko wacece muce zamu yi masa Auren Huce
takaici. Eh kuma da Hjy mulaika kin kawo mafita kwarai , to mai zai hana Musa Ru'aifa?. Wani
irin Kallon Hajiya mulaika take mawa Hajiya Turai kana tace " A'a wanda zaki saka ,sai kin
tabbatar jikin ki ne , saboda kin san fa komai ba don Allah zamuyi shi ba. Na farko asirin sa
zamu tona a duniya ,ko ta hanyar sharri ne ,dole gwamnati ta ɗauki mataki . Daganan ne zamu
fara cin dukiyar sa ,muyi facaka da ita . Shiru Hajiya Turai tayi sai kuma tace " To yanzu wazan
hada shi da ita ta kuma iya mun wannan Aiki ,cikin sirri?. Gyara zama Hjy mulaika tayi kana
tace " Baga ƴata Nusaiba ba.! Sauke numfashi Turai tayi cike da farin ciki tace " Ƙwarai kuwa
,yanzu idan kin koma sai ki mata bayani , Ni kuma zan samu mahaifin sa da maganan ,nasan
dole zasu amince ,tun da babu wata mafita bayan hakan.!
****
A hankali suke tafiya kusan su Biyar hannun su duka kowa yasha lallin fulawa mai ƙyau ciki
harda Amarya Umaima , wanda a yau biki saura Ƙwana biyu. Yaran layin kunsan Amarya da
farin jini haka kowa kebin ta irrrrrr.
A zaure ne sudai su Fatima sun ga Umaima ta saki wayar hannun ta yayi ƙasa tana furta '
Innalilahi wa'inna ilaihir rajiun . Kallon kallo suka tsaya suna yi ita da Umair .wanda ganin ta
yasa duk wannan raɗadin da yake ji ya ƙwaranye. Umaima Yaudara ta zakiyi? Wani zaki Aura
bani ba? Anya kina Son shi kuwa? Hummmm Bakya son Umaima da kina Son shi ba zaki taɓa
fitar dashi a matsayin mata miji ba ,bayan kin san nine Mijin ki.! Zaki jefa rayuwar sa cikin haɗari
maslaha ɗaya ki hakura da wannan Auren idan ba haka ba ,kin fi kowa sanin ko Ni waye .! Na
baki Daga yau zuwa gobe Duk shawarar da kika yanke , ga card ɗina ki Kirani. Ya ƙare magana
yana wurga mata card tare da ficewa . Nisawa Ummalo tayi ƙawar Umaima kana tace " Wannan
me baƙar tabarau ɗin Waye kuma ? Umaima kin san shi ne.??. Shiru UMAIMA tayi tabbas
maganan Umair ya firgita ta ƙwarai . Duƙawa tayi a hankali tana share hawayen fuskar ta ,tare
da sa hannun ta tana ɗaukar katin....!
*MMN TEDDY*
*O*
*Littafin THE SEXY BOSS na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun ba tare da kin biyani haƙƙi na
ba... Regular group ₦300...Vip group₦500... Special ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha
keystone bank ko kuma ki tura katin MTN ta wannan number 08081202932 Idan VTU transfer
zakiyi ki tura kai tsaye ta wannan number 09061466409*
*Morning update*
Miƙewa Umaima tayi jiki a sanyaye tana kallon Su Ummalo da Fatima , kana tace "kumu tafi !.
Bin bayan ta suka yi yayin da Fatima ke faɗin mun shiga uku.!! Ɗakin Hajiya Balki suka shiga
don tun da bikin ya ƙara so kusa ta tattaro ta dawo gidan da zama ,a cewan ta ba zata koma ba
sai anyi biki an watse . Tun da suka shiga ɗakin Ƙawaye da Son jin gulma sukayi ta baza idanu
wai ko zasuji Umaima tayi magana Umair , amma kuma shiru , a haka da ɗaya da biyu kowa ya
watse ,don Umaima katin Hajiya ta ɗare tana juya masu baya kamar mai barci ,amma nan
kuwa sam ba haka bane , damuwa ne ya taru ya lulluɓeta . Rintse ido tayi tana saurun buɗe su
,hango fuskar Umair tayi tana sakar mata wannan murmushin nasa , hushiryar sa da ya raba
tsakanin fararen haƙoran sa na bayyana. Ɗan tsaki ta jah kana ta furta mugu kawai . Jin
wannan magana nata yasa Fatima da ita kaɗai tayi saura cewa " Umaima wai ya ake ciki ne? .
Juyowa Umaima tayi tana muskutowa daga ƙwance bata tare da ta miƙe ba tace " Kaman ya
kenan Fati.." hummmm sauke numfashi Fatima tayi kana tace" Umair ,Ni anawa ganin mai zai
hana ki Auri Umair kaman zai fi mana , kiyi duba fa , da gaske yake a yanzu . Wani irin
murmushi Umaima ta saki ,kana tace " Baki san waye shi bane,Amma ina da yaƙinin Umair ya
Aure Ni to ba zaman daɗi zamuyi ba ,mugu ne macijin sari ka noƙe ,azabtar dani kawai zaiyi
,don duk izayar nN da yayi mun bai ishesa bane shiyasa yake son Aure na ta rabani da duk
wani farin ciki na. Kar fa ki manta da baki nayi masa kan Allah yasa ayi mawa ya'yan sa haka
shine yace " Zai Aure Ni don dole.
Shiru Fatima tayi kamin kaman wanda aka tsikara tace " Amma dai kin san kunfi dacewa dashi
ba Ashiru ba. Dacewa.? Umaima ta maimaita maganan kamin ta taɓa baki tana faɗin , idan na
Aure sa da wannan ƙanƙantan shekarun nawa ,kashe mun Rayuwa zaiyi ,matar shi kan ta abun
ki tausaya mata ne ,mugu kawai ". Umaima tayi maganan tana tuno da maganan sa da yake
cewa " Ni bana barci da kaya , haka kuma nake son Matar da zan Aura ta kasance. Hummmm
to ai shikenan Umaima kin fini sanin waye shi ,tun da ke kika zauna dashi . Cewan Fatima tana
murmushi .
***
Bayan Umair ya fita ne yana shirin fita layin ya haɗu da Baba Sule , Wanda kallo ɗaya yayi
mawa Umair ya gane sa . Cikin matsanancin Fara'a ya kalli Umair da shima shi yake kallo "
Cikin mutuntawa Umair ya gaishe da Baba Sule ,kana Baba Sule ya amsa yana faɗin Saukar
yaushe ? Ko kun zo ɗaurin Auren ne?. Wani irin bugawa ƙirjin Umair yayi sai ya ɗan yi
murmushin yaƙe yana cewa " Ina Baba.? Au Baku haɗu ba kenan da Malam Ibrahim ?. Eh
Bamu haɗu ba. To muje Na kaika shagon shi. Shiru Umair yayi yana bin bayan Baba Sule , a
zuciyar shi yana cewa " Dama Baba Kasuwanci yake yi?. Gani yayi sun fito bakin hanya Baba
Sule na shirin tare Abun hawa .! Cikin sauri Umair ya ce dashi" Ah Baba baga mota na can mun
barota ta a layi, mai zai hana muje mu shiga sai muje Ai ban kawo shagon da nisa ba.
Murmushn su ta manya Baba Sule Tayi kana yace " Ai shagon a kasuwa take . Juyawa sukayi
tare da nufar Moton da Umair yazo da shi kirar wane yaro . Suna shiga Umair ya fara driving
basu ɗau mintuna goma ba suka isa kasuwa . Bin shagon Umair yayi da kallo ,shago ne ɗan
madaidaici , ga yaran shagon suna ta sallamar customers . Ɗaga kansa sama Umair yayi yana
duban Shagon ,anan ya fahimta shagon siminti ake sayarwa . Ba Bismillah Umairu shigo daga
ciki ,cewan Baba Sule yana shiga Umair ya biyo bayan sa. Masu saye da sayarwa wurin duk
idanun su ya dawo kan Umair , kowa na tunanin ne ya kawo wannan matashin attajirin nan cikin
kwacalcalin Kasuwar ? Wai kuma ya rasa inda zai zo sai shagon sayar da siminti .
Zaune Baba yake akan Sallaya yana zikiri don rana yana gab da faɗuwa. Shafa addu'a yayi
yana kallon Baba Sule da Umair da suka zauna a gyefe suna jirar kammalawan sa .aaa Umairu
kune da yammaci?. Murmushi Umair yayi yana sunkuyawa cike da ladabi yana gaida Baba
,kana ya baba ya amsa yana tambayar sa kowa da kowa. Ba tare da Umair ya basa Amsa bane
ya kalli Baba Sule kana ya juya yana kallon Baba tare da cewa " Baba Wai Shin gaskiya ne an
mawa Umaima miji bani ba?. Kallon sa Baba Yayi kana yayi shiru sai kuma ya ɗago a yana
girgiza kai tare da cewa "Ƙwarai Umairu , yau saura kwana biyu kenan. Sai daga baya Aka zo
da maganan ka , haƙuri xakayi Allah ya baka wata wacce tafi Umaima.
Ina Baba bazan samu ba. Yayi maganan idon sa na kaɗawa daga fari zuwa ja. Umaima ba
matar kowa bace ,matata ce.! Baba don Allah ku warware wannan Sa ranan A maida akaina. A
jibin a bani ita . Ƙara ware ido Baba yayi cike da mmki , kamin yayi magana Baba Sule yafara
ba Umair haƙuri ,tare da masa bayanin idan suka raba wannan Aure sunyi ƙaranta ,kuma
sannan Mutan unguwa zasu ce sunyi Auren kudi ne , kuma kar ka manta Umaima ba tsarar
Auren ka bace ,ka fita komai . Cewan Baba yana kallon Umair wanda jijiyoyi n jikin sa sun tashi
, gargasar hannayen sa sun mimmiƙe . A hankali ya furta " Shikenan Baba Allah ya basu zama
lafiya." Amin su Baba suka amsa .
***
Tun daga wannan Rana Umair barci ya gagare idon sa. Yayin da zuciyar sa ke saƙa masa
abubuwa da yawa da zaiyi akan Umaima ,don har tunanin yasa a sato Masa ita sai da yayi , ya
kulleta a tare dashi suyi rayuwa har mutuwa . Amma tuno da karamcin wannan gida yasa shi
fasa yin hakan . Kullum a tunani yake a kuma shan barasa . Zaune yake shida Julayb ,Julayb
ne ya aje karan sigarin kana yace "Wai Umair kana da hankali kuwa? Akan mace kake kokarin
kashe kan ka ?. Jubi fa kwalebe nawa ka shanye na barasa baka tunanin lafiyar ka?. Banza
Umair yayi masa kana cikin Muryar maye yace " Kaje Garin su Umaima yau ka gani an ɗaura
mata Auren?. Kallon sa Julyab yayi kana yace " Idan an ɗaura to me xakayi? . Cireta a rayuwa
ta zanyi. Murmushi Julayb yayi ba tare da ya bari Umair ya fahimta ba yace " To yau zan tafi
,tun da kasan yau ne ɗaurin Auren ..
***
A yau asabar ƙarfe biyu aka ɗaura Auren Umaima da Angon ta Ashiru . Wanda tun da Aka
ɗaura Auren nan Ashiru fara'a bakin sa yaƙi rufuwa ,haka mutane da dama sun halarta wannan
daurin Aure ,don Baba aƙwai shi da mutane kwarai.
Tun da aka ce an ɗaura Auren , Umaima hankalin ta ya fara tashi , babu tunanin wanda take yi
sai maganan Umair.! Yaudara ta zakiyi???. Wani irin bugawa ƙirjin ta yayi tuno da wannan
maganan tasa . A haka ta wuni babu walwala . Wanda da misalin yammaci aka kawo mota aka
ɗauki amarya zuwa gidan mijin ta wato Ashiru . Don basu da nisa daga layin su Umaima sai
inda aka kaita . Gidan yawa ne don a cikin gidan aka yi mata ɗan Platt Mai ƙyau. Mata ne
kusan bakwai a gidan kowa da mijin ta da yayan ta . Kuma duka yayyun Ashiru ne .
Su Fati kuwa sai fara'a ake ,ana ta shiga da fita , wanda wuraren ƙarfe takwas kowa ya watse .
Abun da Umaima bata taɓa gani ba shi ta gani. Bayan Mutane sun watse ne , Ashiru ya shigo
da yayyun sa mata don shine karamin su , acewan su sun rako Auta ɗaki. Wani sarawa kan
Umaima yayi cikin ta na murdawa sakamakon jin ƙamshin turaren Angon nata , wannan yasa ta
saurin miƙewa tana sauke mayafin da aka rufa mata . Muryar babban yayan su taji tana cewa "
Alhmdllh Mun kawo Angio....kamin ta rufe baki ne Umaima ta fara amai , kaman zata fidda
hanjin cikin ta ...!
*P*
*Littafin THE SEXY BOSS na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun ba tare da kin biyani haƙƙi na
ba... Regular group ₦300...Vip group₦500... Special ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha
keystone bank ko kuma ki tura katin MTN ta wannan number 08081202932 Idan VTU transfer
zakiyi ki tura kai tsaye ta wannan number 09061466409*
*NIGHT UPDATE*
Tsayawa Duka dangin Ango Ashiru sukayi kana Yaya Hadiza tayi saurin nufo Inda Umaima ke
tsugune tana sheƙa amai kaman zata fidda ƴan hanjin ta . Tallabota Yaya Hadiza tayi kana tace
" Umaima lafiya dai ko. Babbar yayan su Ashiru ne cike da masifa ta kalle Umaima tana cewa"
Wani lafiya ,ai dagani kun san babu lafiya wannan. Sam Ashiru ba zai ƙwana a ɗakin nan ba ,
sai an tabbatar Wannan yarinyar ba ragowa bace. Subhanallah Yaya Uwauwa wannan
maganan bai dace ta fito daga bakin ki ba ,da girman ki fa?. Cewan Ashiru cike da damuwa .
Kai da Allah wuce ka rufe mun baki , Kai yaro ne , Kalli fuskar ta , kasan a haife na haifi
Umaima don na kusa jika da ita . Ba yau nafara ganin mace watsatstsiya ba. Don haka A
kiramun Safara'u maƙociyar mu yanzu ,tazo tayi gwajin fitsarin Ta ,ko anan zamu fahimta
gaskiyar Al'amarin. Juyawa Umaima tayi tare da durƙushewa anan wurin. Tana sakin wani
marayan Kuka kana ta fara cewa " Umair ka cuceni ,ka cuta Rayuwa , Bazan yafe maka ba
,wayyo Ni ,wayyo Rayuwa.! Juyawa Yaya Uwauwa tayi tana kallon Yaya Hadiza kana tace "
Kunji magana ta yafito ko?. Hummmm a jura zuwa rafi dai . Shiru Falon yayi kowa da abun da
yake saƙawa a zuciyar sa na tsawon minti ɗaya . Kana Yaya Hadiza ta cika hannun Umaima
tare da jan wani dogon tsaki . Ai dama wannan shaka shaka na wannan yarinyar Ni tuni ina
zargin ta . Allah shi kyauta kai ka nace gashi nan ta jawo mana Abun magana a maƙota da
dangi ,a koma ana cewa ka Auri karuwa.! Yaya Hadiza ke maganan cikin matsanancin fushi
tanayi tana kallon Ashiru da ya sauke hular shi yana firfita don wani irin gumi ke karyo masa .
Yaya Uwauwa ce ta amshe Hadiza da cewa " Ai wannan tafi ragowa karuwa dai ,gatanan ƴar
malam taƙi halin malam ,waye bai san mahaifin ta ba , shi fa yake kirar sallahn masallacin layin
nan , wallahi kin fita Zakka a cikin yan uwan ki da gidan ku baki ɗaya . Kin kuma jawo mana
Abun kunya a idon duniya . Tana gama faɗin haka ta juya fuuuuu. Yaya Hadiza ce ta kalli Ashiru
dake tsiyayar da ƙwallah . Umaima.! Ya kira sunan Umaima da a yanzu kukan ya gagara mata
sai sauke ajiyar zuciya ,tana cura ji take kaman ta haɗiye ranta ta mutu ta huta. Tana nan zaune
ne taji y Kira sunan ta , wanda sam ta kasa Amsa shi ,sai numfarfashi da take yi ,ji take ƙirjin ta
na mata zafi kaman zai ɓalle wani ya fito mata ta huta . Umaima me yasa kika yi mun haka?. Ba
laifi na bane , Shi ne ya mun haka?. Auwalu??? Ashiru yayi maganan cike da fusata ,don shi
har a yanzu bai ɗigon raguwar soyayyar Umaima a zuciyar sa ba ,sai ma wani wutar soyayyar
da yake ƙara mamaye zuciyar sa. Kaman ba zata basa amsa ba , sai kuma tace " Sir Umair
Ahmad moddibo.! Wani irin bugawa zuciyar Ashiru yayi ,don tabbas yasan Umair ba ƙaramin
mutum bane a Nigeria baki ɗaya ,ba state ko ina na Nigeria ambaton sunan matashin ake yi.