Author : Aisha Maman Teddy Category : Taskar Novels
Aliyou Wannan wani irin mgna ce haka? Na dauka dai Kawai Abun na ka schl friend ship
ne... Aa Ammie nifah Auren ta xanyi. Ganin Abun nashi yana shirin samata Rigima,yasata
cewa"Tom shikenan Haidar,allah ya nuna mun lokaci...Sosai yaji dadin mgnar Ammien
nashi,Don haka ne A washegari Har ita hafsan sai da ya samu ya fade mata abun da Ammien
shi tace,amma sai ta mayar dashi Sakarai". Ana haka sukayi hutu,wanda sosai Hafsa taji dadin
hakan,don ta huta Da damun Haidar....Sai dai Hauwa da take zuwa gida suna taba zumunci".
****************************
Hafsa...Hafsa.... Inna ce tayo kirar diyar nata,wanda yasa Hafsa Saurin fitowa tana amsa kirar
Innan nata daga wajen soron gidan nasu". Kicibus sukayi da Shi hannun ta dauke da manjan da
Inna ta aiketa sayowa....aiko sam bata san lokacin da Ta juye masa manjan a jikin shi ba". Gaba
daya yar farar shaddan tasa ta rine da manja dama ana kafulle an shigo binni daga ruga". A
zuciye ya daga hannun shi yana shirin wanketa da mari,aiko nan Yy saurin rike hannun
nasa,kana suka hau kallon kallo". Cike da xafin murya Maccido ya kalli Aliyou Haidar yana
cewa"kai wanene? Da xan hukunta kanwata kaxo ka rike ni".
.murmushi Aliyu yy kana yace mai sonta! Mene? Ehh yanda kaji".
Zaro ido hafsa tayi,tana ta'ajibi yaakayi Ya taho gidan su,har ya sani....muryar Umar ne taji yana
cewa"Aliyou yayan mu ne,xo mu tafi laifi tayi masa,shigo ka gaida inna!
Jin ance ya taho ya gaida inna yasa shi kutsa kansa cikin soron gidan nasu da yakasance tun
daga farkon sa har karshen sa ginin jar kasa.
Tab dijammm Hafsa,yaudara takkyi dama? Budan bakin maccido abun da yace mata
kenan,wanda cikin sauri tayi wajen gidan don tsoron xuciya irin na Maccido".
Mmn teddyí ¾í·¸
[10/6, 12:59 PM] Maman Teddyí ¾í·¸: *Loading......*
GDN KWARATA!
Na Maman teddyí ¾í·¸
84-85
*@Alheri Writer's asso.í ½í³š*
Ban yarda ki karantamun lbri ba tare da kin biyani Kudin sa ba,domun kuwa lbrn na kudi ne idan
kina bukatan cigaban Lbrn zaki yi mgna ta wannan number 08081202932 . Vip payment #500
mtn card,Normal #200. Idan har kika karanta baki baya ba keda Allah!
Bismillahir rahmanur rahim".
______________________________
"Shikam Omar nufa da Aliyou yy wurin Inna dake kitchen hayaki ya cika tun daga farkon gida
har karshe". Inna Ga Haidar din da nake maki mgn". Omar yy mgnar yana nuna Aliyou Wanda
ya dan risina ya gaida Inna dake ta fama da Hayakin Ice". Cike da harka Inna ta amshe aa
Wannan Ne Aliyoun Hafsatun nawa? Tom maza kai shi daki,ka barshi daga Waje? Inna tayi
mgnar hadi da Sauke idanun ta da sukayi jah sbd icen damunan dake damun ta akan na
Omar...Tom Inna yy maganar yana juyawa hadi da nufah da Aliyou Dakin Innan da kwakkwarar
Leda babu". Wata fatakakkakkiyar Tabarma ya shimfida ma Aliyou kamin Ya zauna,shima ya jah
ya zauna.
Itakam inna Bayan Wucewan su da ido takebin Aliyoun da lokaci daya tayaba da natsuwar
sa,yaron kirki,sam baya da fahari da Girman kai irin na Yaran masu dashi". Murmushi tayi tuno
da mgnar Omar da sukayi da yake cewa"Inna fah Shi Aliyou da gaske yakeyi Aurar Hafsatu
zaiyi".
Nan Inna tayi dariya a xuciyar ta tana fadin" Inbanda Yarinta ina Aliyou Ina Hafsatu? Dukan su
nawa suke,takitaki basu fi shekaru Sha shida ba". Fitowa tayi daga madafin da take tana nufar
Dakin Ta...da yake ba ginin Zamani ba,gini ne ta kasa,kasan ma jar kasa ta yambo,sai kofan
lagye² n ta".
Da shigarta tahau tsokanan Aliyou don ita macace mai harka da barkwanci sosai....Zama tayi
tana debo masa ruwa a kwanon sha,sannan suka cigaba da fira,wanda duk da Haidar ba
gwanin Fira bane,amma sun taba da Inna...koda Hafsatu ta dawo,tun a tsakar gidan take jiyio
firar Inna da Aliyou hakan yasata Yin tsaki,tana mmkin tayaya Aliyou yasan Yayan ta Omar?. A
haka ta yi shirin islamiya sai dai muryar ta daga kofa sukajiyo tana cewa"_Inna Sai na dawo!
Tom Auta na Adawo lfy?. Da hakan ta fice". Shikam Aliyou bai bar gidan ba sai wuraren Biyar
na yamma,kamin nan ya fahimci labr da tarihin Hafsatun duka,don mahaifin ta Allah yy masa
Rasuwa tun bata da wayo,batafi shekaru biyu ba Ya rasu,Dama shi sana'arsa Sai da Manshanu
a kasuwa,don a salin sa bafullatani ne na Zaria garin hunkuyi". Har Halakar ta Da maccido sai
da ya juyo,duk da Inna bata fade masa Wani Abun dake boye tsakanin Maccidon Da Hafsatun
ba! Da mahafin Maccido Wato Hardo da Baban Hafsatu Uwa daya Uba daya ne.Hakan yasa shi
Yana xuwa Kawo masu Inna Ziyara,duk da itama Innan yar Asalin Hunkuyin ce". Wannan
kenan!
Tun daga wannan rana,ba'a kwana biyu Aliyou baizo gidan Inna ba,duk xuwan da yakeyi don
yaga Hafsatu ne,wanda har yanxu kallon shi batayi,Duk da tana tsoron Yah Omar". Tsakanin
Aliyou ko da Maccido sai harara,babu maj kallon wani da sunan Gaisuwar mutuntawa. Hakan
yasa Hankalin maccido tashi,ahaka dai ya koma Rugar hunkuyi,su kuma su Aliyou Aka cigaba
da Zuwa Makaranta,don hutun mako biyu aka masu takare".
Haka xaita shishshige ma Hafsa tana yarfa shi,bai damuwa har ta gaji ta dawo daga rakiyar
shi,Yazama na idan Ammien Aliyou taxo daukar shi sai ta dauki Hafsatu takaita gida,sannan su
dawo da Aliyoun,A haka har Ammie da Inna aka saba,sosai suke mutumci,Don Itakan ta Ammie
Sosai takejin son Hafsatu a xuciyarta,duk da tasan Auren ta Da Aliyiun ba mai yiwuba ne ba". A
haka har suka shiga ajina biyu,aliyou kullum mgnar sa da xarar sun shiga ajin karshe xa'a
tsaida mgnar Auren su,Tun Hafsatu na damuwa takoma rabuwa dashi bata cemasa Komai,don
idan tabi tanashi xatayi ta marin sa a banxa,don bashi xai hana mgn yataso ya fada ba...kullum
firar shi Hafsatu". A ranar Laraba ne sam baiga Hafsatu a makaranta ba,sosai ya kasance baya
da Walwala...ahaka yake saran Ganin ta gobe nan ma bai ga xuwanta ba...Da ya tambayi
Hauwa sai ce masa tayi ai tana lfy,gobe friday xata zo".
A washe garin juma'a nan mababu Hafsatu babu hauwan don duka basu xoba! Hakan yasa
Aliyou yakomakaman majinyaci". A natashin su ya koma gida,Anan ya tadda Ammien shi tana
shirin ta tsaf daalama fita xatayi". Ammie ina xakije? Inaso ki kaini gidan su Hafsa yau?
Kirjin Ammie ne ya buga,nan ta kalli Aliyoun hadi da shafa sumar kanshi tana cewa"Ayya Aliyou
kaga yanxu Asibiti xan tafi,kayi xaman gida,idan na dawo xan biya gidan Su Inna na duba
Hafsat din kaji? Kaman baxai yarda ba,sai kuma yace mata tom Ammie,adawo lfy". Yowa
aamien Haidar dina,sai na dawo?. Tana fadin haka ta fice daga falon shi kuma yana Nufar
Dakin baccin shi don ya watsa ruwa ya samu yy bacci,amma sam ya kasa rintsawa,burin shi
kawai ya gano Hafsatu hankakin shi xaifi kwanciya".
Shityawa yy tsaf yana Shigar sa ta manyan kaya,Yana saka wata lallausar yadi milk da akayi
masa Dinkin zamani,sosai ta amshi jikin shi". Nan ya fara shirin isa Farfajiyar gidan,hadi da kirar
Drivern su don ya kaisa gidan su Hafsatu.
Itakam Ammie da fitan ta hamdalah tayi,kana ta Kwana kan moton ta xuwa gidan Inna,don yau
ake taron bikin Hafsatu da Maccido". Wanda bayan komawan sa rugar su ya tada balli,aifah
abinni da masu son Hafsatu shi baxai hakuri tayi ta boko ta dawo tace bata son shi ba,gwamma
ayi masu aure kawai. Hakan ko yasa Iyayen su Amince da mgnar Maccido yanda aka tsaida
mgnar Auren Hafsatu da maccido a sati hudu kacal.
Tun ranar da Aka hana Hafsatu fita tafara jin babu dadi,sai a yanxu ta fahimci tabbas ta saba da
Aliyou duk da bata son shu,amma ta dauke shi anatsayin kani kuma dan uwan ta". Tuno da
halin da zai shiga na rashin ta,yasata duk tabi ta fada,abinci na bata iya ci na kirki".
*************************
Bayan Driver ya ajiye shi ne ya fito,yana bin mutanen dake Kofar gidan,Kowa fuska cike da
annuri,shelan Wani maroki yaji yana cewa"Ayau an daura Auren maccido da Hafsatu...allah
yakawo xuria na gari....Nan duban jama'a suka amshe da Amin". Wani Abune ya soki xuciyar
Haidar,meyakejin yana fada wannan mutumin? Wata Hafastun? Badai nasa ba? Ji yy anriko
hannin sa,waigowar da xaiyi Omar ya gani,fusjar sa a yamutse bb annuri,yyn dakara waigawa
can wurin mutanen da xaiyi ya hango Maccido da wasu kaya masu sheki,shigen yi shirun ka
maraya,yanata washe baki da mutane". Bakin Haidar na rawa yace da Omar,Wai da gaske
Hafsatu tayi Aure? hafsa ta tafi tabarni? Tayi Aure Omar? Shiru Omar yy yana jiyo tausayin
Haidar na ratsa jijiyoyin jikin shi". Wanda su Inna da Amie kai harda Amaryar Hafsa lbrn xuwan
Haidar tuni ta Iso masu,hakan yasaka Hafsat kasa sukuni,sai data taho har soron gidan,tana
hango Omar da Aliyoun da batasan me suke cewa va,amma dagani kasan yana cikin tashin
hankali ne". Su Inna ma da Ammie hakan ta faru suna gyefe suna addoan Allah yasa Haidar ya
dangana,Amma kuma mene? Cewan Da Omar yy masa Aliyou kayarda da Kaddarar ka,dama
tuncan Allah ya kaddara Hafsaru ba matar ka bace,da gaske ne Hafsatu tayi Aure...ai bai karaki
fadi ba,Aliyou yy baya,don duhu² yake gani can yafara jiyo mgnar Ammie dana inna sama² sai
kuma Yajiyo difff.....
Da gudu Hafsatu tayi cikin gida tana wani irin kuka kaman ranta zai fice,yyn da Hauwa duk
dakiya irin nata saida itama tasa nata kukan.
Aliyou kam bai farfado ba sai a garin Abj. Don can Ammie ta nufa dashi sbd rudewar da tayi,ta
rasa yin komai,da daya tilo....Asalin gidan su Wato nan gidan Danlarabawa ta dawo dashi suka
bar garin Kaduna,wanda koda ya cinci kanshi a gidan,haka ya abuce shi dai kawai
Hafsa,yakoma kamar xatattace...Ammie kuka Shi Kuka,Surayya ma da tun dawowan su taxo
itama kuka take,tana bin Wannan Hafsatun da Allah ya isan ta,tun da ta cutar mata da Cousin
din ta'. Ganin Abun na Aliyou sam yaki natsuwa ne yasa..Daddy cewa a taho dashi Uk su zauna
tare,don a lokacin Daddy yaje karo couse a kasar America,nan Ammie ta tafi dashi....Wanda
acan Alhmdllh Yadan saki ranshi,amma kullum yana aikin Tunanin Rayuwar shi da
Hafsatu,dakuma tunanin ko tana wqni hali ayamxu? Anan ne ya hadu da Jalil don tare da Dad
din shi yake.....dayake Jalil Architecture ne,kullum yana aikin Wahalar Haidar,dob baida aiiki sai
kwatanta masa yanda Hafsatu take ya yi ta xana ta,in yagama yy ta kallon hoton nata....
Itakam Hafsatu wannan kukan da tayi na ganin halin Da haidar ya shiga,ya kular da
Maccido..wanda tun daga nan xaman lfy tayi kaura tsakanin su..kullum fada da hantara,bb dadi
dai xaman nasu,tayi kuka ta share,hadi da kai kukan ta ga mahalicci....Kamin wani lokaci ta
jeme ta lalace sbd wahalar da bata saba,kullum tana aikin daji da Nemo karmami ga xuwa
kasuwq sayar da nono,a haka rayuwa tayi ta gungurawa da ita".
*************************
Aliyou kam bai dawo nigeria ba,sai da ya kammala secondary din shi,wwanda da saukar shi
kasar ya nufo Asibitin Ammie don Yasan baxai tadda ta a gida ba". Tun da ya isa Labour word
don tanan ne xai hau stairs din da xai sada shi da Office din Ammie yake jiyo sautin muryar ta ta
karatun Alqur'ani...suunan tana halin Unconcious ne amma bb abun da bakin ta ke furtawa sai
kalmar Allah". Inna kam sai kaiwa da komowa take,don Hafsatun da cikin ta yakai haihuwa
dawowa tayi,don ta haihu a gaban ta". Dik dauriya irin na Inna sai da tayi ta sharce hawaye".
Inna? Ya kira sunan ta cike da mmkin ganin ta awurin". Saurin juyowa tayi jin muryar da baxasu
taba mantawa dashi a rayuwar su ba". Haidar? Takira sunan cike da mmki? Inna ina Farin ciki
na? Ina Hafsa? Cikin zubar da kwallah inna tayi masa nuni da dakin da take a kwance tana
nukuda". Likitoci da nurses duk suna a kanta ciki kam hards Ammien Haidar". Daga masu xuvar
da hawayen tausaya mata sai masu sharce gumi".
Ganin Haidar a dakin haihuwan yasanya Cike da Tsoro Ammie tace"Haidar meya kawoka nan?
Bai bata amsa ba,illah takawa da yy har xuwa gaban gadon Da hafatu take idon ta a rufe,sai
harshen ta dake fitar da karatun Alqurani cikin Suratul maryam". Cak tajah ta tsaya,kana a
hankali tafara ware idon ta,wanda vata sauke su akan kowa ba,sai akan kwayar idon sa,da
fuskar shi da baxata taba mantawa dashi ba har abada". Haidar? Takira sunan sa cikin wqta irin
wahalalliyar murya". Saurin karasawa gavan ta yy yana riko hannun ta da tadago tana
mikamasa....Hawayen kuncin sa na sauka saman taffan ta". Aliyou kayi hakuri ina mai baka
hkri,akan vun danayi maka,Ka sa aranka ni ba matar ka bace dama...amma ga yata ko dana
nan,na baima ka halak malak ..zan tafi xan koma ga Mahalicci na,ka rike mun su tamkar dan
daka haifa da jinin ka....Ka tarbiyartar mun dasu ta fanin Addinin musulumci...na baka Danako
yata kar ka bari susha wahalar dana sha arayuwa....Ka.....harshen ta ne ya datse,kamin ta hau
kakari tana fitar da wani irin aman bakin jini,sai kuma jikin ta ya saki....daga cijgan da takeyi".
Hafsa...yakira sunan ta da Karfin gaske da saida ya dawo da hnklin inna dake waje".
Allhu Akbar,allah me girma annabi mai dunbin daraja,nan take Allah ya amshi Rayuwar
Hafsa...Maganan likitocin da Ammie yaji tana cewa"a maxa ayi nata Operation don ceto dan
dake cikin ta". Rasa me xaiyi yayi,kuka kome ne? Kawai sao jyawayy yana fita daga
dakin,kwallah na bin kuncin sa,kaman yanxu ne suka fara rayuwa yakeji......moto ya shiga driver
na jan sa hadi da nufar gidan Dan larabawa dashi".
Anyi nasarar fiddo da diya mace,wanda Faroq da inna awannan rana ya xama masu ranar da
baxasu taba mantawa dashi ba,a rayuwa". A ranar mutan Rugar suka taho,kuma anan aka
shirya Hafsatu aka kaita gidan ta na gsky". Bayan kwana bakwai da rasuwarta ne aka maida
sunan Diyarta da Hafsa,wanda Mutan rugar suke kirar ta da Hasile". A hannun inna Aka bar
Hasile,wanda Aliyou kam tundaga wannan rana yakasa Xuwa gidan Inna,Ba lafy kullum yana
cikin ciwo da rashin Hafsa a rayuwar sa". Sai da aka watse kusan Kwanan Hafsa Sha hudu
sannan ya iya xuwa Gidan Inna,wanda ganin Hasile yasa Shi cuno masa dogon famin xiciyar
sa,tabbas kaman Hafsatu tayi kaki ne ta aje". Don kaman su ya baci". Haka xai xauna ya tasa
Ta yy ta kuka...sai Inna ta shigo dakin tayi ta rarrashin sa hadi da masa nasiha. A haka Hasile ta
fara girma,Inna na bata madara,dom Ammie ne ta dauki nauyin komai....Shikam Aliyou
maganar Karatu ya jingine gyefe..kullum bayi da aiki sai raino. A haka Hasile ta kai kusan
shekara biyu,bb wanda ta sani sai nurry dad din ta,da Uncle Farouq,sai inna don daga baya ne
tasan Ammie...
Mahaofin Aliyoune ya sama masa Admission a Uk.wanda badon yasoba yaya fara shirin tfy
karatu can. A inda xai karatan medicine". A kwanakin da Haidat baya nan,Inna bata da
sukuni,Kullum Hasile tana kukan rashun Nurr Dad din ta .idan Ammien Haidar taxo,tayi shirru
tana jirar shigowar sa,abuka ga yarinta idan taga Shiru² bau shigo ba,sai ta kuma saka masu
ihu tana tsalamasu,ahaka xasuyi ta rigi² da ita,suna rainon ta...A haka Aliyou yy Wata uku acan
yagasa sukuni sai da yadawo ganin Hafsan nashi".
A ranar da yadawo shiru sukeji,don sai murna takeyi,shima kam sosai yaji dadin yanda yaga Su
Ammie na Kula masa da Amanar sa...a hakayy sati guda sanan ya koma".
Dawowan da xaiyi na buyu ne,ya tadda Inna Da su Farouq duka basa gidan,da yatmbyi mai
hayan,sai yace masa ai kwanan su Shida kenan da tfy Rugar su,har yau basu dawo ba.
Acan ko Ruga tun da suka je ne,Macido ya kyekyeshe ido,shikawai abashi Hafsa...abar masa
diyarsa...Zuciya irin na Omar nan yace"Sai Inna ta bashi yar shi...Kuma su da rugar Hunkuyi
harabada,sun barta...Haka inna ke kuka ta baima maccido Hafsatu da suke kirar ta da
Hasile,amma da yake shi kafaffafen mutum ne haka yasa hannu ya amsa.
Tun bayan da suka bai masa Hasile,aranar Omar ya ce subar Ruga haka kam akayi,wanda a
hanya ne Inna tace"BazTaxata iya xaman kd ba. Ahaka suka nufo xaria. Tun daganan inna bata
kara komawa kaduna ba...tabbas tasan mutuwa yankan kauna ce,ra rabu da Diyarta kuma
wanda take gani taji sanyi yanxu itama an rabata da ita..tayi kuka kuma ta fammala ma Allah
komai.
A haka suka cigaba da ryuwar su a Zaria,inda Omar ya samu aikin soja...ya fara karatun
sojan..Aliyou kam da Ammie kullum suna saka ran Dawowar Inna da Omar da diyar su
Hafsa,duk shiru har shekaru biyar a haka suka cire rai da dawowan su". Nan shima Aliyou
yabar kaduna yakoma Abj gidan Danlarabawa da zama". Bayan yan watanni Ammie ma ta biyo
bayan sa,don Garin Kd bata masu dadi sam...... Tun daga nan Inna bata kara xuwa Rugar
hunkuyi ba,sai da Hasile takai shekaru Goma,Amma koda taje badan bakin Hasile ina Nurry
Dad din ta? Wanda tambayar yasa Hankslin Inna ya tashi,sai a lokacin ta tuno da koina Aliyou
yake baxai taba mantaww da Hafsa ba,tom amma yaya xaiyi? Uban ta ya yi masu yankan
kauna har da diyarta". Tun daga wannan xuwan Bata kara komawa ba,don Omar sosai yy ta
sababi,yana zagin maccido...don yy fushi dashi kwarai".
Abunka ga uwa tuno mata da Haidar Da Hasilen tayi,yasa Inna nufar kd,amma nan itamataji
labrn barin su kdanan...haka ta koma da jimami da bakin ciki.....
Nisawa Ammien Aliyou tayi,tana kallon Yanda Hasile ke xubar da hawaye,tabbas batasan haka
rayuwarta ta kusa ba!. Itama Ammie hawwyen ta goge kana tace"Wannan shine lbrn ki Hafsa!