DUBAI PART 2 HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN.pdf

Author :  Oum Hairan Category :  Taskar Novels

Chapter   5 / 11

12K to 15K   out of 31.6K words

sama._


*11*


Haka kwanaki suka rinqa turawa kwanan Taheer biyar a kwance ya fara samun sauqi tunda ya
farfado habeeytah kawai yake kira wani lkcn har sai an hada masa da Allurar bacci sannan
yake samun nutsuwa, cikin kwanakin zuciya da jikin Mom sunqi hutawa duk inda zasu shiga su
fito sun sun shiga. Itadai Zahrah burinta a sake mantar da zuciyar Abba Sahabi Habeey Amma abin ya faskara
qarshe bokan nasu da suka bawa amanna ya sanar da ita indai ta cika matsawa zata bata
gomanta daya bata gyaruba dole ta hqr sukabar lamarin tsakanin Habeey da Taheer.



Kudi ba qanqana ba Mom ta kashe akan lallai a cusawa Dad aqidar qin bijirewa mgnrta haka
kuwa akayi cikin lkc qanqani take juya ragamar governor Waziri.
Kwanaki goma Taheer yayi ya samu sauqi sosai zuciyarsa wasai da kyakkyawan albishir din da
Dad yayi masa na musanya masa Habeey a matsayin matarsa farin ciki a gurinsa kamar zai
zauce, Saida ya gama murnarsa da kukan dadinsa sannan yace “yanzu Dad tana Ina koma kun
gama bikinku ban sani ba ankaimin ita gdana?" Shafa kansa Dad yayi yace “kayi har an samu matsala lkcn da Habeey taji labarin an daura
aurenka da Saudat ta yanke jiki ta fadi har yanzu batasan waye yake kantaba tana tsakankanin
mutuwa da rayuwa Taheer likitoci sun tabbatar mana cewa bazata farfado ba sainan da watanni
goma...."

Katse Dad yayi da cewa “what Dad! Kuma shine kuka tsaya kuka zuba Mata ido saboda
bakusan ciwonta ba so kuke ku kashemin mata haba Dad haba Dad yaushe zaku fara daukan
Habeeytah a matsayin da kuke daukar sauran yayanku...."
Shigowar Abba ne yasashi yin shiru Abba ya dafa Taheer yace “kayi hqr Granny ce ta takura
Saida aka daura aurenka da Habeey a halin tana cikin jinya, Taheer naso ace sai Habeey ta
warke akayi bikinku kukayi farin ciki kamar kowacce amarya da ango"
Girgiza masa kai yayi yasa hannu ya share masa qwallarsa lkcn da tasa take saukowa yace
“inason ganinta Abba ka rakani naganta don Allah"




Miqewa yayi ya nufi qofa Abba da Dad suka miqe suka rufa masa baya har dakin da Granny
take jinyar jikanyar tata ya tsaya a bakin qofar ya zuba mata ido yana hawaye ya rinqa jan
qafarsa a hankali har ya qarasa gadon ya durqushe a gabanta tare da kama hannunta yana
kallon na'urorin da aka daddaure qirjinta dasu. Wasu hawaye masu dumi suka kwaranyo masa suka zuba a saman hanun Habeey ya sake
rungume hannunta a qirjinsa cikin kuka me sauti yace “rayuwata dake a haka tafimin dadi fiye
da na rayu da matan duniyar nan Habeeytah ko tausayawa masoyinki me qaunarki domin Allah
kada ki yankemin farin cikina wlh nayiwa wannan rayuwar tanadin farin ciki me dorewa har
abada Habeeytah nayi alqawarin da sanina bazan qara sanyaki zubar da hawaye ba duk ranar
da kika zama mallakina, ki tashi Habeeytah don Allah ki tashi kamata yayi ace a daidai wannan
lkcn muna kwance a dakinmu ne a gadonmu na sunnah kina kwance a qirjina Ina shafa wannan
dogon gashin naki"




Yakai hanunsa ya shafo gashinta dake baje saman pillow wanda kullum sai Granny ta gyara
matashi sai sheqi yake baqi sudik dashi, ya shagala sosai da kallonta da shafa sumar tata ya
zubawa dan qaramin bakinta da smile face dinta idanu gani yakeyi kamar murmushi takeyi
masa ya dago ya kalli Abba yace. “Zo ka gani Abba murmushi takeyimin don Allah ka fada Mata karta mutu akai gift din da
nakeson bata wacce na siyeta tun ranar farko dana fara saninta mace, na ajiyeta a matsayin
kyautar da zan bata duk ranar data zama mallakina Abba ka fada mata da hannunta nakeson ta
karba don Allah"

Ba Abba da ciwon yar tasa yakecin zuciyarsa ba hatta likitar dake kula da ita kuka takeyi cike
da tausayin Taheer din tunda take bata taba ganin kojin lbrn irin wannan soyayyar ba, Tasha
ganin irin wannan usue din da zarar namiji ya fuskanci mace batada amfani a gurinsa zubar da
ita yakeyi Amma shi yanzune ma ya fara sonta itakam zataso jin mafarin wannan sarqaqqiyar
qaunar.
Da wannan tunanin ta dafashi tace “kayi hqr zata warke insha Allahu saita haifa maka yan biyu
munzo Bauchi munsha suna yallabai" miqewa yayi yace “na gode Dr amma ya kamata kema
kiyi wani taimakon wata goma yayi yawa inajin tausayin matata ni banida matsala wlh ko a haka
zata dawwama zan zauna da ita zan sallama lkcna wajen kula da matata"



Dafashi Dad yayi yace “dama jiran warkewarka mukeyi zaku tafi Germany na tanadar muku
gdan da zaku zauna da likitan da zaike kula da ita gdan kusa da Royal hospital Germany yake
daganan likitocin zasuke zuwa dubata ga kuma abbanku kusa daku"
Granny ce tayi saurin cewa “anya Aliyu wannan tsarin babu wauta a cikinsa jinyar mace sai
mace kuma yaushe ma zakace zaka bawa Taheer wannan yarinya ya tafi da ita shi kadai nidai
wannan shiri bai kwantamin ba"
Shigowa Mom tayi itada Zahrah tayi saurin cewa “wannan tsarin kwata² baiyi ba shima Taheer
din ai zai iya kula da matarsa gsky bazasuje ko inaba kabarta anan yake kula da matarsa ga
qanwarta nan saita zauna tare da ita"




Saurin kallonta Saudat tayi ta qifta Mata ido ta juya ta kalli Taheer ya zabga mata wata uwar
harara yace “amma dai sainaji kamar baa sanyaki cikin maganar nan ba ko" daga masa hannu
Dad yayi yace “hakan zaayi Taheer kawai a hqr da tafiyar nan tunda zatazo da matsala ko ya
kagani Salahu?" Jinjina kai yayi yace “duk yanda kukayi ma daidaine amma Saudat bazata gidan Habbatullah ta
zauna ba kamar yanda na datse duk wata alaqa ta kusanci tsakanin Habbatullah da
mahaifiyarta Hajar haka na datseta tsakanin Saudat da Habeey harsai zuwa lkcn data samu
sauqi dakanta ta nemeki kinji ko?" Daga Kai tayi cikin qunar zuciya tace “naji Abba Amma..." Daga mata hannu yayi yace “kune
musabbabin faruwar koma saboda haka banson jin komai daga gareki Taheer ka kula da
matarka Allah ya taimaka maka zan nemo muku yan aiki biyu da zasuke tayaka jinyarta"




Murmushi yayi yace “na gde Abba amma bana buqatar tallafin kowa wajen kula da matata zan
iya komai nasani idan nine a irin wannan halin Habeey bazata taba yarda wani ya kula dani ba

ita zatayimin komai saidai idan fin qarfinta akayi"
Sosai zuciyar Abba tayi sanyi yaji dadin kalaman Taheer duk da yasan hana tafiya da Habeey
din wani salon makirci ne saboda sarai yana hango qiyayyarta a idanun Mom da matarsa
Zahrah.
Itakuwa Saudat a duk lkcn da taga yanda Taheer yaketa jagwalgwala Habeey sai taji wani
shauqi yana shigarta duk da tasan cewa yayi Mata nisa amma ta kasa daina kallonsa da fuskar
qauna inda shi Kuma bata hangen komai a idonsa sai qiyayyarta.




Ran Mom baiso hakaba taso aja maganar har rai ya baci amma sai taga akasin haka suka fice
zuciyar kowa babu dadi suka nufi gida Mom ta daki sitiyari tace “wannan abin yana firgitani
anya kuwa Taheer mutum ne"
Tabe baki Saudat tayi tace “to wai Mom meye yasa kika tsani Aunty Habbatullah ne nifa indai
danni kike wannan abin kima daina nariga na sallamawa yar'uwata mijinta dama tun farko
rashin sanine yasa nayi yunqurin shiga tsakaninsu, Mom abin yayi yawa da wanne zasuji ne
sunason juna kuka cusa musu tsanar juna lkcn da muke tunanin haqanmu zai cimma ruwa lkcn
ne kuma Allah ya zartar da nasa hukuncin ya qullah auren da bakwaso...."




Wani bugu Zahrah takaiwa yar tata tace “shashasha mara kishin kai dama ashe kema haka kike
inata kashe kudina don ginaki ke kina qoqarin rusani to wlh kika sake tausayin wannan makirar
yarinyar ya ratsa zuciyarki sai ta rabaki da duk wata fada da kike taqama da ita uban naki ma
saiya daina kallonki" Shiru tayi batace komai ba qasan zuciyarta yana tunano mata yanda taga Taheer yana shigewa
jikin Habeey tayi saurin kawar da tunanin ta dauki wayarta tana wasa da ita har sukazo gdan.
Kwanaki biyu Habeey ta qara a asibitin aka sallameta zuwa gda Taheer yaso su tare a gdan da
Dad ya mallaka musu amma fir Dad yace saidai ya bari idan matarsa ta warke saisu tare,
hakanan badon ransa yasoba saidon nasihar da Abba sahabi ya rinqa yi masa, shine dalilin da
yasa ya hqr ya zauna a cikin government house din bangare guda aka ware musu aka zuba
musu yan aiki sosai....
# *UMMUH HAIRAN*
[8/9, 4:08 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *HABEEYTAH*
*_DUBAI PART 2_*


*12*


Ranar da suka tare kwana yayi yana kallonta yana hawaye yau ga Habeey dinsa yar uwarsa

jininsa matsayin matarsa amma saidai ya kalleta.
Miqewa yayi ya dauro alwala ya tayar da sallah yana kuka yana nemawa rayuwarsa lafiya gurin
Wanda yake da ikon canza al'amura sai asuba ya kwanta bacci ya dan daukeshi yana rungume
da ita yanajin dumin jikinta na ratsashi.



Takwas ya tashi ya zuba Mata ido yana murmushi ko yaushe a kowanne hali fuskarta bata rabo
da annuri ya share hawayensa ya sunkiyo daidai bakinta yace “kinaso nayi miki wanka?" Zuba
mata ido yayi kawai sai yaji kukansa yana qara qarfi ya kwantar da kansa a jikinta yana lasar
jajayen lips dinta da suke kullum kamar tasanya musu jambaki. Dagata yayi a hankali ya cire mata komai dake jikinta yanajin faduwar gabansa na tsananta, ya
dade yana kallonta daqyar a galabaice ya dauketa ya shiga da ita bathroom ya sanyata a ruwan
wankan daya hada Mata ya diba ya watsa Mata a fuskarta duk ta rame yayi murmushi yace
“nasan zakiso ramawa ko?" Diba yayi ya watsawa kansa yayi dariya yace “komai kikeso sh
izanyi miki ko kaya zansa sai wanda nasan zakiso HABEEYTAH"



Yanayi mata wankan yana wasa da jikinta yanajin feel dinsa na qaruwa daqyar ya gama yimata
wankan hakanan yaji yana sha'awar ya daura Mata alwala yayi Mata alwala ya daukota ya bude
cikin wardrobe ya zubawa wardrobe din ido kayansa ne da nata a jere komai sabone yayi ajiyar
zuciya wannan yasan aikin Abba Sahabi ne. Wata baqar doguwar riga ya dauko ya juyo ya wareta ya kalleta yace “kinasonta baby?" Zuba
Mata ido yayi sai kuma ya ninketa ya mayar yace “nasan bakison baqin kaya bari na dauko miki
ja" wata jar doguwar riga ya dauko ya bude wata wardrobe din ya dauko jajayen band da
dankunne fashion shima ja ya dawo ya ajiye ya dauko wasu mayuka masu masifar kyau da
tsada ya matsa ya shafa mata ya taje Mata kanta a hankali sannan ya sanya band din ya daure
mata ya kama jelar gashinta ya tufke kamar yanda yaga tanayi masa.




Kayan ya saka mata ya fesa mata turare ya koma gefe yana kallonta yana ajiyar zuciya tare da
murmushi yace “Rayuwata inasonki" shima wanka yayi ya dauko wani blue din jeans yasa ya
dauko jar riga yasaka ya kalleta yace “nayi miki kyau My life?" Murmushi yayi ya matsa ya
lakace mata hanci ya fita yana cewa jirani na dauko alluranki..." Turus yaja ya tsaya ganin Mom dinsa a tsaye a parlourn ita da Saudat ya kallesu a wulaqance,
a zahiri kallonsa ne a haka indai ba saninsa kayi ba zakace tsabar iskanci ne, jikin Saudat rawa
ya fara yasa hannu ya karbi Safnah dake hannunta yace “lafiya da safen nan?" Yanda Mom
taga yanayinsa babu damuwa da Kuma kalaman da taji yana furtawa ya fadar Mata da gaba
amma saita dake tace “dama munzo ganin jikin matar takane" murmushi yayi daya bayyanar da
kyawawan haqoransa yace da sauqi fa sosai shiga ki ganta Mom har kwalliya nayi Mata".......

# *UMMUH HAIRAN*
[8/9, 4:09 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA:      HABEEYTAH
*_DUBAI PART 2_*



*13*



Zaro ido Mom tayi tace “kwalliya kuma gawar kayiwa kwalliya?" Tsuke fuskarsa yayi yace “aa
Mom banason ki qara cewa matata gawa qila saima ki mutu ki barta waike meye yasa kullum
bakinki baya taba fadin alkhairi akan matata ne nifa banson irin haka wlh rai zai iya baci"
Sakin baki tayi tana kallonsa har ya gama fadansa ya juya ya koma dakin ya kwantar da Safnah
kusa da mahaifiyarta ya miqe domin fitowa suka hada ido da Mom ya sake tsuke fuskarsa yace
“banason a dameta muje parlour" murmushin takaici tayi tace “indai wannan hoton hotiho dince
da kanka zata isheka Taheer tunda ta zama Liability komai sai kayi mata"


Ko sauraronta baiyi ba ya dauko feedar Safnah ya zauna ya daukota yana Mata wasa ya hada
mata madara ya jorner mata ganin bashi da niyyar basu guri yasata cewa da Saudat “ki zauna
ki tayashi aiki"
Dagowa yayi ya watsa mata wata uwar harara ya mayar da kansa wa yarsa har saida Mom ta
kusa ficewa daga dakin yace “dallah malama ki bacemin da gani anan banza mayya uwarki zaki
tsaya kiyimin nida matata sai ansamin ido idan wani abin nayi niyyar yimata jiya da ubanwa
muka kwana" Tsorone ya kama Saudat tasan tana cewa wani abu jibgarta zaiyi ita ta rasa Ina Taheer ya
kwaso wannan baqar zuciyar tasa, bin Mom tayi da sauri har ta fita ta dawo tace “am Yaya
Safnan fa?"




Wata uwar tsawa ya daka Mata yace “uwarki ce ta haifamin ita da yazama dole na baki ita?"
Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata tace “amma dai Yaya kasani yar yar'uwata ce nima
inada haqqi akanta..."
Wani kallo da yayi matane yasata ficewa da gudu ta nufi bangaren Mom din tana zuwa tayi
kicibis da Mahfuz ya daka Mata tsawa yace “ubanme kike yiwa wannan uban gudun ballagaza
kawai kizo ki shirya ni bazan iyada da zafin 9ja ba komawa inda na fito zanyi bandama su Dad
da abinsu wani ni zaace na tafi dake ke wlh bama zan tafi dakeba kawai kice musu na tafi" Yana gama fada Mata haka ya juya ya fice da sauri ta tabe baki tace “banza a banza duk
izzarka baka kama qafar Hussain dinka ba, batakai nakeyi ba"

Shiga ciki tayi ta fara hada kayanta tare da cin alwashin ba zata qara kwana uku a 9ja ba ko su
Abba bazasu koma ba ita zata tafi,
Itakuwa Mom tana shiga dakinta ta dokawa Hajiya Ummah waya tace “gsky Ummah banga
alamun nasaraba shegen yaron nan bazai sare ba wlh bakiga yanda yake rawar qafa akan
yarinyar nan ba abin haushin iyayensa sun daure masa gindi duk wasu shagunansa Dad ya
sanya yaransa a ciki zasuke juya masa dukiyarsa sannan har wani albashi ya yanka masa hatta
mara lfyr saida ya yanka Mata salary"




Dariya Ummah tayi tace “shine me da har zai sanya ki sare Safinah yau da gobe fah sai Allah
wlh dole sai Taheer ya gaji da jinyar yarinyar nan Kuma duk ke kika bata abin aida kin bari sun
tafi wajen inda babu wanda zai taimakeshi da komai"
Shiru tayi tana tunani kafin tace “Germany fah zasu tafi nafiso su tafi inda basuda kowa..."
Katseta tayi da cewa “ki aiwatar da aikin da aka baki kawai kice da Excellency ya kadasu su tafi
acen din komai zaifi tafiya daidai kuma kada ki yarda a bar miki yarinyar nan ya tafi da kayarsa
kinga itama qarin wahala ce"



Dake lusara ce haka ta yarda cikin farin ciki ta rinqa gudanar da al'amuranta cikin dare ta tashi
batare da kowa ya ganta ba ko tsoron girman gdan bataji ta shiga bangaren nasu Taheer tayi
saa ko lkcn daya fito zai raka likitan Safnah ta fara kuka ya koma da sauri bai dawo ya rufe ba
bayan yayi Mata wanka ya hada Mata madararta ya bata ya dorata a kafadarsa tayi bacci ya
kwantar da ita a gadonta ya koma ya daga Habeey ya gyarata yayi mata wanka ya dawo dawo
da ita ya kwantar da ita.
Shima ya gaji saboda haka yana kwanciya bacci ya daukeshi har cikin ransa yafi tausayin Abba
Sahabi fiye dashi kansa saboda yanda duk ya susuce akan ciwon na Habeey yau sun dade
dashi suna tattaunawa akan ciwon yana cewa dashi yana shirya musu tafiya Saudia Wani
Islamic Hospital akwai abokinsa acan yace yawanci irin wannan ciwon biyu ce take haduwa
kodai tanada junnu a tare da ita ko kuma an jefeta dasu abin ya tadda ciwon, saboda haka Dr
Manzir ya bashi shawarar a kawota nan a dorata akan magungunan Islamic.




Yaji dadin shawarar ta Abba Amma yace da abban yayi Shiru harsai komai ya kammala na

tafiyar, nan Abba yake fada masa cewa mahaifiyar Habeey dinma batada lfy cikin dare aka jita
tana ihu kamar mahaukaciya tun daga lkcn itama ta daina magana saidai kallo kawai ta
kwatance Kuma bama kowanne mutum take ganewa ba yanzu haka tana Ɓillire gidan
mahaifinta anata sauke mata qur'ani. Jinjina kai Taheer yayi yace “amma lamarin da daure kai kuma Ina mijinta da yayanta maza da
sukayi saura?" Girgiza kai Abba yayi yace da Taheer “tun ranar data tashi da ciwon da safe
kafin kowa yazo kanta akace yazo ya tattare yayansa maza ya tafi dasu har jiya baa qarajin
duriyarsu ba" da wannan tunanin bacci ya dauke Taheer nasararsa daya shi ko bazaiyi nafila ba
baya kwanciya babu alwala Kuma ko iskancinsa yayi daya gama yake wanka wannan dalilin
yasa hatta Habeey da batasan waye a kanta ba sai ya daura Mata alwala duk lkcn da zaiyi
sallah.




___________Itakuwa Mom tana shigowa ta kunna turaren tsafinta ta banka a parlourn ta tsaya
idanunta a rufe hayaqin yabi ta qasan qofar dakin ya shiga daidai lkcn Taheer yana saman
sallaya yayi sujjadah yana nemawa matarsa sauqi gurin me duk.
Bajewa hayaqin yayi sannan ya nufi jikin Habeey

5 / 11