DUBAI PART 2 HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN.pdf

Author :  Oum Hairan Category :  Taskar Novels

Chapter   4 / 11

9K to 12K   out of 31.6K words

da
kowa ya sani ba tasa aka nema mata babban gida na alfarma a cikin birnin gombe ta siya da
sunan Habeey ta zuba musu komai na more rayuwa sauran ta dora jari sannan ta biyawa
Habeey kudin wata babbar makarantar islamiyya.




Kwana daya suka qara sun gama shirinsu tsaf tace zasu rakata unguwa Habeey tana daki
zaune tanata gwada wayar Taheer taqi tafiya sukaji sallamar mutane a tsakar gidan gaban
Habeey ne ya fadi saboda tunaninta Dr Shattima ne saboda ya takura musu da ziyara cikin
kwanakin nan. Amsawa Idris da Ibrahim sukayi suka fita da sauri itama ta miqe ta fito sanye da hijjab dinta har
qasa saboda dokace Addah ta sanya mata ta tsaya a bakin qofar dakin.
Shigowa sukayi ta dago kanta a dan tsorace saboda jin muryar Governor Waziri ta zuba masa
ido gabanta na faduwa itadai kawai governor Waziri kama yake Mata da wani Wanda ta sani, a
bayansa wasu mutum biyu ne sai Shattima dake biye dasu.



Janye idonta tayi dagakan governor Waziri ta saukeshi akan wanda yakebin bayansa shima ita
yake kallo ga mamakinta sai taga kowa ya tsaya amma shi ya nufota tayi saurin rintse idonta
kawai saijinta tayi a jikinsa ya rungumeta tsam ya fashe da kuka yana fadin.
“Itace wlh azeem Habbatullah yatace yayar Saudat ce Innanillahi wa innah ilaihirraji'un dama
zanganta ashe mafarkina gaskiyane da yake nunamin zuwan wannan rikitaccen lkcn meyesa
Yaya meyasa kuka boyemin bayan kunsan inda take meye yasa baka sanar dani ba Saida aka
daura auren Taheer da Saudat"............ # *UMMUH HAIRAN*

[8/9, 4:08 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *HABEEYTAH*
*_DUBAI PART 2_*


*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
*UMMUH HAIRAN*


*9*


Zamewa tayi a jikin Alh Sahabi ta zube a qasa summamiya Taheer dake shigowa ya hankade
governor Waziri dake riqeshi ya fada kanta ya dagota yana jijjigata yana Kiran sunanta kawai
shima sai ya zame a kanta zuciyarsa na harbawa da sauri, a haka Saudat da Bushirah suka
shigo suka samesu. Saudat ta sulale qasa cikin kuka me gunji tace “ni dama tun ganina na farko da Habibah nasan
akwai wani abu tsakanina da ita wlh na hqr da Yaya Taheer koda soyayyarsa zata kasheni Dad
dama tun kafin nasan da wannan jumurdar ya sakeni saki uku minti uku bayan daura aurena
dashi...."



Salati Dad ya saki cikin sarewa zuciya ya qarasa gabanta ya riqota yace Alh Sahabi ya sunkuya
ya janye Taheer daga jikin Habeey yace “hakan yayimin dadi ya burgeni sosai Saudat yayi
abinda ya dace dama bansan da cewa bashi ya amince da aurenki ba da tun farko bazaayi sa
ba" Addah ce ta shigo daga maqota data shiga sallama ta tarar da gdan cike da mutane da
sauri taja baya saboda hada idon da sukayi da Sahabi tace “Salahu!" Da qarfi tayi mgnr ya
kawar dakai tare da cije lebansa ya kinkimi Habeey ya fice da ita ya sanyata a mota zuciyarsa
na bugawa da qarfi Alh Aminu da governor Waziri sune suka fito da Taheer sai Kubrah da
Bushirah da suka kamo Saudat da taketa gursheqen kukan rabuwa da masoyi tasan Koda
Taheer bai yanke igiyoyin aurensa da aka daura awa da suka wucce akanta ba to bayyanar
Habeey matsayin yayarta shaqiqiya uba daya zaisa ta janye ta sallama Mata Taheer domin
tafita buqatarsa tasani Habeey tafita son Taheer kuma sunmafi dacewa da junansu kasantuwar
jinin dake gudanawa a jikinsu ma iri dayane.




Wani babban asibiti dakenan cikin garin gombe suka nufa Abba gudu yakeyi kamar zai tashi
sama saboda a yanzu ji yakeyi kamar mutuwar Habeey mutuwarsa ce, suna zuwa ya qara
sunkutarta ya nufi cikin asibitin da ita ma'aikatan suna ganinsa suka rinqa darewa suna bashi
guri kasancewar asibitin kansa mallakinsa ne.

Shiga yayi da ita dakin agajin gaggawa yasa aka kira masa likitocin shima ya cire babbar
rigarsa suka baje fasaharsu wajen ceto rayuwar gudan jinin nasa daya dade yana mafarkinta ya
dade yana ganin surarta a baccinsa wannan rans daxai tsaya gabanta yana qoqarin dawo Mata
da rayuwarta da take qoqarin qwacewa ta dade tana zuwar masa a baccinsa.



Sunfi awa biyar a kanta komai na jikinta saida aka cire Mata ya rage daga ita sai under siket
hstta bra saida Abba ya balle Mata saboda kokawa sukeyi da numfashinta da yakeyin sama
suna fincikoshi daqyar zuciyarta kuwa bugunta yayi qasa fiye da mizanin da ruhi zai iya rayuwa
da harbawarta. Daqyar da taimakon oxygen suka samu bugun zuciyarta ya rinqa dawowa a hankali cikin abinda
bai wucce daqiqa talatin ba ya dawo yanda zata iya rayuwar qila wa qala dashi, amma anyi
rashin sa'ar shigarta commar da zata iya shekara guda a cikinta saboda duka jijiyoyin da suke
kai saqon tunani qwanyarta sun tafi hutun wuccin gadi idan aka matsa musu dawowa zasu
iyayin bombing gabadaya.




Wannan dalili ya tashi hankalin kowa dake cikin asibitin musamman Saudat da taketa kuka tana
tsinewa son zuciyarta da yakaisu wannan matakin qiri² saboda rashin tausayinta da son kanta
gashi ta jazawa yar uwarta tilo daya tal a duniya fadawa halin rai kwakwai mutu kwakwai
wannan abu zai dade yana taba zuciyarta. Shima bangaren Taheer yana cikin tsaka me wuya Amma shi da dan dama dama akan Habeey
shi karo na farkone daya samu heart attack akwai yuwuwar nashi ya lafa da sauri.
Granny bata samu labarin abinda ke faruwa ba sai dare aikuwa a daren tace sai ankaita taga
jikokinta, lkcn da tazo Bushirah tana kuka take fada Mata halin da Habeey take ciki ta rinqa
salati tana matsar hawaye tace.




“Ni dama tun ganina na farko da yarinyar nan nasa akwai wani boyayyen al'amari game da
haduwarta da Taheer Allah shi kadai yasan abinda ya boye tsakaninsu yanzu gashi gaskiya ta
bayyana Kuma dole dan baqin ciki yaji kunya wlh Koda Taheer bai saki wannan ja'irar yarinyar
ba sai ubansa ya saketa kuma a daren nan ko Habiba zata mutu saita mutu matsayin matar
Taheer a wannan daren zaa daura"
Hakan kuwa itace ta faru a wannan dare Granny ta gwada ikonta Hajiya tanacan gaho da baki
aka daura auren Taheer da Habeey wannan abu yayiwa kowa dadi duk da daga angon har
amaryar basusan abinda ake ciki ba.

Sai sha daya na dare Dad ya koma gda shida su Kubrah da Saudat ta take dauriya saboda
wani mugun zazzabi daya rufeta, suna zuwa gda ta shige dakinsu taja bargo ta rufe jikinta tana
rera kukanta a zahirin gaskiya ba kukan rashin Taheer takeyi ba saboda a yanzu tanajin so da
qaunar Habeey fiye da kanta. A haka Aunty Zahrah mahaifiyarta tazo ta sameta a kwance cikin halin jinya ta dagota ta bude
idonta da suka kumbura saboda kuka tana ganin mahaifiyarta ta fada jikinta ta rungumeta ta
sake qarawa kukanta sauti tace “nayi baqin cikin zamowata silar shiga tsakanin yar uwata da
bani da tamkarta a duniya da masoyinta haqiqa gsky ne layu'alimul gaibu illallah wlh da ace
nasan Habeeytah yar uwatace da banyi sakacin da soyayyar mijinta ta huda zuciyata ta shigaba
yanzu gashi gsky ta bayyana nice a qasa"




Tana fadin haka ta sake fadawa jikin Aunty Zahrah tace “shikenan Taheer ya tabbata ba
nawaba dama yasha fadamin shi na Habeeytah ne gara nabarshi tun kafin lkc ya sanya
nabarshi ta qarfi yanzu gashi ta qarfin zan barshi aunty naga samu naga rashi ya sakeni saki
uku minti uku da daura aurens dashi ya turomin text massage a baya na qudurce bazan fadawa
kowa ba amma yanzu dole lkc yasa na fada harma an maye masa gurbina da yar uwata
Habbatullah...."
Jijjigata Aunty Zahrah tayi tace “keni kin cikani da shirme wace Habbatullah?" Bushirah dake
shigowa tayi murmushin jin dadi tace “uwar wannan yarinyar" ta nuna Safnah dake kwance a
kafadarta tana baccinta taci gaba da cewa “dama qarya fure take bata yaya rabon gsky ta
bayyana mu qara dangi ne yar uwarmu ta dawo garemu yasa har hakan ta faru ni na tabbata
Koda ace auren nan ya dade to bazaa zauna lfy ba saboda zuciyarsa tana gurin uwar yarsa" ta
juya ta kalli Mom tace “kema yau kaifin harshena bazai tsallakeki ba Mom an dade anayi Ina
sanya ido to yau dai gsky ta bayyana Habeey da kike qi har kike shirka saboda ki rabata da
danki itama jininki ce dake da Abba Sahabi abokan wasane da babansa da babaki uwa daya
uba daya yanzu kije a zuqe jinin Abba Sahabi daga jikinki kinga shikenan kin huta mudai
munason yar'uwarmu sannan aure Allah baiyi hadin naki ba nasa ya qullah Yaya Taheer ya
angwance da amaryarsa Habibatullah dan baqin ciki saidai ya mutu Safnah zata tashi cikin
gatanta ta zama yar gata haihuwar dangi duk wanda ya zagi uwarta kansa ya zaga ka zagi
ubanta ka gingimo dutsin dala dabara ta rage take Mom nidai shawara na baki kiyi maza kije a
zuqe miki digon jinin Dad da Abba Sahabi a cikin jininki"................
# *UMMUH HAIRAN*
[8/9, 4:08 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *HABEEYTAH*
*_DUBAI PART 2_*

*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
    *UMMUH HAIRAN*

_Please ki biya kafin ki karanta,daganan zuwa 10/8/2020 VIP 400 single 150, account
0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar GTB idan katine ta wannan number 09013718241 hoton katin Zaki tura
ko lambobinsa ta wannan number dake sama idan ta account ne Zaki tura evidance of payment
dinki ta number dake sama._


*10*


Dafe qirji Mom tayi tace “Nashiga uku ni Safinah Bushirah me kike cewa ne wlh qwanyata ta tafi
hutu bana gane komai" tabe baki Bushirah tayi ta dauki Pampers din baby Safnah ta fice tana
cewa “kanku dai akeji aure Allah yayi alqawarin Habibah ce matar Yaya Taheer sai ku hadiyi
zuciya ku mutu ku huta" Binta sukayi da kallo har ta fice kalma daya ta kasa fitowa daga bakinsu Mom ta zube a gurin
dabar tare da Dora hannunta aka ta zunduma ihun days firgita kowa suka sake yowa dakin da
sauri, zare idanu takeyi tana kallon kowa ta cafki hannun Kubrah tace “me...meye yake faruwa
Kubrah don Allah fadamin me ake Shirin yimin ne"



Dariya tabawa Kubrah tace “mom kema da abin haushi kike to meyene kuma alqawarin Allah
ne ya cika Taheer mijin Habbatullah kinqi Allah yaso ya qulla abinsa yabarki da kunya amma
Mom ai kina da wani dan ki hadashi da wannan yarinyar mana, dama ai gadon ari sai fanna"
Miqewa Aunty Zahrah tayi tana sharar hawaye tace “ashe dama wulaqancin da kuka shirya
yimin da yayanki kenan Yaya Safinah kuka matsa saida muka baro England mukazo 9ja, tur wlh
kin bani kunya ashe isar taki ta banzace baki isa da danki da mijinki ba Yaya kinbani kunya nayi
nadamar zama qanwarki tunda kin kasa cikawa tilon yata burinta data rayu dashi tun quruciya
har kawo girma"



Fincikar Hannun Saudat tayi tace “duk Dan daya hana uwarsa bacci to yasa a ransa shima
bazaiyi ba zan dauki mataki farin ciki dai Taheer bazaiyishi bs kamar yanda ya hanamin yata ta
warwasa"
Riqeta Mom tayi tace “kada muyi haka dake Zahrah ki muje dakina mubi komai a sannu fadan
ya canza salo halan ke baki fahimci ma abinda suke cewa ba, to bari nayi miki bayani wannan
karuwar yarinyar da nake fada miki Lele ya mutu akansa ta tsaface zuciyarsa ba kowa bace
face yar Hajar matar Alh Sahabi ma'ana babbar yarsa da muka kashe maqudan kudade dan
batar da babinta cikin rayuwar zuri'ar Maje Bauchi"

Wani mugun tsoro ne ya kama Zahrah ta zame qasa cikin tashin hankali tace “nashiga ukuna
Yaya ai ban fahimci abinda yake faruwa ba dama ashe bata mutu ba Mal yacemin zai batar da
ita a duniya zata lalace sannan daga baya a yawon barikinta ta dauko abin kunya ta jajubo cutar
qanjamau ta mutu ashe duk qarya yayimin" Rufe mata baki tayi lkcn da Dad yake shigowa ya bisu da kallo Mom tayi saurin miqewa tace
“dama yanzu nake shirin kiranka Dad kaji abinda yaron nan yayi mana minti uku da daura
aurensa da yar'uwarsa Saudat ya rattaba mata saki uku?"



Kallon inda Saudat take nade yayi yace “haka Allah ya tsara muma godewa Allah da abin ya
tsaya iyanan da baiyi hakan ba da abin ya rikice mana ashe yarinyar nan Habbatullah yayar
Saudat ce ubansu daya kinga kuwa ai da anyi abin kunya duk da kasancewar aure ya halatta
tsakanin Saudat da Taheer tunda a baya ba auren Habbatullah yayi ba Amma ai ana barin
halak ko don kunya musamman da yake Taheer ba Saudat yakeso ba Habbatullah yakeso"
Girgiza kai Mom tayi tace “Lallai kam da anyi abin kunya to Allah yasa hakan shi yafi alkhairi
yanzu Ina suke ance kun dora auren ko?"



Jinjina kai yayi yace “Granny dinsu ta tursasa aka daura auren tace Koda dayansu zai mutu
saidai su mutu matsayin ma'aurata" wani mashi ne ya sake sukar maqoshin Mom amma sai
tace “hakanma yayi yanzu ina suke?" Cikin jin dadin yarda Mom ta Basu hadinkai governor
Waziri yace “a halin da ake ciki ita Habbatullah jin cewa Taheer ya zama mijin qanwarta yasata
yanke jiki ta fadi qanwar matacciya a fadar likitoci sunce zata iya daukar watanni goma a
wannan halin na doguwar suma shikuwa Lale ya samu heart attack yanzu haka yana samun
kulawa daga likitocin asibitin Sahabi dake gombe amma akwai yuwuwar zaa tafi dasu England
acan zasufi samun kulawa"



Cikin tashin hankali Mom tace “taheer din yanzu Kuma mutuwa zaiyi don Allah Dad ayi duk
abinda ya dace" miqewa yayi yace “insha Allahu zasu tashi suyi rayuwa me tsayi sai sun Haifa
mana halattatun jikoki, Ina Safnah yau banganta ba"
Tabe baki tayi tace “tana gurin iyayenta" sai yanzu ya tuna da yayan nasa mata duka matsayin
matan wasu suke, yace “Subhanallahi meye ya hanasu tafiya gidajen mazajensu bayan an
gama komai"
Itadai bata bashi amsa ba ya juya ya fice yayi niyyar tasosu yakai kowacce gdan mijinta Amma
sai yaga har shabiyu na dare kuma Basu gama bidi'arsu ba.

Kallon Mom Zahrah tayi tace “shikenan burinsu ya cika na yata ya wargatse haka kike nufi
Yaya?" Dafata tayi tace “har yanzu akwai quruciya a jikinki Zahrah idan rawa ta canza dole kida
canzawa yakeyi kuma Shirin zaune yafi na tsaye a yanzu nuna qiyayyarmu ga yarinyar nan
baqin jini zaija mana musamman ke, sakin ranmu zamuyi mu nuna komai ya wucce in yaso sai
mu koma gefe mu sake shiri, ai wlh tunda na rantse banasonta bazan taba sonta ba sufa maza
basu da tunani saboda haka mu bisu da yanda sukeso sai muci galaba akansu"



Haka suka rinqa tattaunawa har Hajiya Ummah yayarsu saida suka taso suka fada mata abinda
yake faruwa, tayi dariya tace “kuma tanan suka bullo? Hmmm ku bar yan iska zamu iya dasu
badai a kwance take ba to kuwa a haka zata qare rayuwarta saidai suyita asarar kudinsu a
banza amma bazata tashi ba" Dubanta Zahrah tayi tace “amma Yaya Ummah sai naga kamar yayi tsauri jinya tanada cin
zuciya da jiki mudai nemi wata mafitar wannan batayi ba" harararta Mom tayi tace “bantaba yin
tsafi ba sai akan shegiyar yarinyar nan nifa wlh yanda nakejin tsanarta da zata mutu ma da
zanfi kowa farin ciki, Yaya Ummah shi Kuma wannan gardamammen yaron ya zamuyi dashi?"


Shiru tayi tana tunani sannan ta dago tace “kada ki damu dashi a barshi ya samu lfy ya warke
qalau ita kuma a qara dora Mata jinya kuma ki tubure kice saidai a bashi ita yaje yayi jinyar
matarsa ta hakane kawai zai fara nadamar bijire miki saboda zaiso kusanci da iyalinsa babu
dama zaiso shima yaga matarsa a cikin halin lfy daga haka zai fara tunanin mafita zai fara
danasanin aurenta zaiji tsanarta zai fara tunanin qara aure to daganan ne zamuyi amfani da
wannan damar mu sanyashi sakinta sai mu maye masa gurbi da Saudat kinga shikenan ciki lfy
baka lfy idan ta warke saita dauki jaka ta koma bariki lkcn komai ya kankama tsakaninshi da
Saudat qila ma ta haihu kinga aure ya haramta tsakaninsu indai ba mutuwa Saudat tayi ba"



Wani ihu Mom tayi tace “shiyasa nake sonki kanki naja Yaya Allah yabar mana ke" murmushi
Zahrah tayi itadai har yanzu da sauran imani a ranta amma ya zatayi bata da wata hanyar ceton
yarta saita amince da wannan gurguwar shawarar.
Miqewa tayi ta matsa ta taba jikin Saudat da tayi baccin wahala jikinta zum da zazzabi, gyara
Mata bargo tayi ta kwanta a kusa da ita tana shafa kanta tana tausayawa tilon yar tata tasan
zafin rashin masoyi tun akan Abba Sahabi lkcn daya gujewa aurenta yaje ya auri Hajar, tana
tuna irin azabar data rinqaji a heart dinta tana tunz irin wahalar da gangar jikinta ta shiga a lkcn,
hawaye ta share tace badan wata kusan tafi wata ba da bazan bari a cutar dake ba Habibah
duk da kasancewar harda sanya hanuna a lalacewarki amma bayyanarki da abubuwan da suka
faru sun sanyayamin jiki lkcn da Yaya Safinah ta shigemin gaba wajen bata rayuwarki sai ya

kasance kuma da gudan jininta kuka lalace ita ta tsarawa boka tanaso kiyi cikin shege yanzu
gashi ita zata goya yar da ta assasa zuwanta duniya tabbas akwai matsala gaba bamusan
meye zai faru ba, Amma Kuma ni Yaya zanyi da tawa yar idan naqi basu hadin kai".............……
# *UMMUH HAIRAN*


[8/9, 4:08 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *HABEEYTAH*
*_DUBAI PART 2_*

*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
    *UMMUH HAIRAN*


_Please ki biya kafin ki karanta,daganan zuwa 10/8/2020 VIP 400 single 150, account
0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar GTB idan katine ta wannan number 09013718241 hoton katin Zaki tura
ko lambobinsa ta wannan number dake sama idan ta account ne Zaki tura evidance of payment
dinki ta number dake

4 / 11