Author : Oum Hairan Category : Taskar Novels
babensa,
wannan canji ya tashi hankalin Granny da Bushirah dake jinyar Habeey da farko sun dauka
mgnr auren nasa ce tasashi a busy amma sai Bushirah ta lura shima auren ba wani murna
yakeyi dashi ba kullum ka nemeshi zaka sameshi a garden ya hade kai da gwiwa yanata
karatun wasiqar jaki"
Yau ta kama asabarce wadda tayi daidai da satin Habbatullah hudu a asibiti misalin qarfe biyu
na rana ta fara motsa qafafunta tare dayin attishawa daga Kubrah har Bushirah da Granny
dama Addah da ciwon yar tata yasata saukowa shima Bushirah ce tayi tattaki taje ta sanar da
ita. Dukkansu kanta sukayo ta muqar da hannunta tare da amsa kalmar shahadar da Addah take
laqaba mata ta riqe qam tanayi tana girgiza kanta, fita Bushirah tayi da gudu ta fadawa likitan
abinda yake faruwa daidai lkcn da likitan ya iso daidai lkcn Taheer suka shigo shida Saudat a
zahirin gaskiya shi kansa baisan Saudat ta biyosa ba saboda kaca² suka rabu dutsi a hannun
riga amma sai gashi sun shigo tare kafadarsu na gugan juna.
A lkcn ne Habbatullah ta fara bude idonta a hankali tana kallon kowa dake dakin da fuskar
rashin sani har takai ga sauke idonta akan Addah ta zabura zara miqe likitan yayi saurin riqeta
tare da cewa.
“Kibi a hankali Hajiya zaki tashi insha Allahu" a sanyaye da murya ta alamun jin jiki tace
“Ad...Addah ashe zakizo gurina ashe har yanzu kina sona Addah ina qannena Aysha da Fatima
ina Taheer Addah ki kiramin shi don Allah" juyawa Kubrah da Bushirah dama kowa dake gurin
sukayi inda yake tsaye yana danna wayarsa. Wani mugun kallo Addah takeyi masa a cikin kwana ukun da tayi a asibitin yaune ta fara
ganinsa taja ajiyar zuciya hakanan takejin tsanar Taheer a ranta kuma ta qudurce a ranta indai
yarta zataji mgnrta to zata rabata dashi rabuwa ta har abada.
Matsawa Bushirah tayi kusa dashi ta warcr wayar hannunsa tace “haba Yaya kanaji sai kiranka
Habbatullah takeyi Amma ka wani basar...." Bata rufe bakinta ba ya sauke Mata wani gigitaccen
mari ya sakeyin bal da ita yace.
“Wata banza dake Zaki qwacemin wayata saime to dan wannan banzar ballagazar ta kirani
dama jira nakeyi ta warke Kuma alhmdllh ta warke banida haqqinta zata iya komawa inda ta fito
Amma karki sake ki daukarmin yata inason abata Saudat zata riqemin ita, yawwa ladan
haihuwar kyakkyawar baben nan da kikayimin na mallaka miki gidana dake layin gdan sarkin
Bauchi ki duba wayarki nayi miki transfer ta million hamsin nasan ta isheki ki qarashe rayuwarki
na bakisu a matsayin fansar budurcinki"
Yana fadin haka ya ajiye Mata want a saman cinyarta ya juya zai fita ta bude bakinta jikinta na
rawa tace “na roqeka da girma da matsayin ubangijin daya sanya tausayi da jinqai tsakanin
bayinsa kada ka juyamin baya Taheer karka manta kayimin alqawarin duk tsanani bazaka
gujeni ba bazaka juyamin bayaba wlh na amince zan aureka Taheer kada ka wofintar dani lkcn
da nake tsananin buqatar jin qanka...."
Ta qarasa mgnr cikin sarqewar numfashi baiko qarasa jin abinda zata fadaba ya fice kamar iska
yaja motarsa a guje yabar harabar asibitin ta kuwa zabura ta miqe zata bisa Dr Shattima yayi
saurin riqeta ya hadata da jikinsa yace “tabbas kina cikin jarabawar ubangiji kamar yanda nake
cikinta Habbatullah banyi tunanin wannan lkcn zaizo ba kiyi hqr zuciyarki a kumbure take idan
kika mutu bashida asara saboda saura kwanaki biyar ya angwance da sabuwar
amaryarsa...........
_Gareku masoya garabasa gareku saboda murnar bikin babbar sallah daga yau 3/8/2020
zuwa_ _10/8/2020 na rage kudin da ake biya domin samun wannan_ _rikitaccen labari me cike
da turka turka single Zaki biya 150 VIP 400 idan ta account ne._
_Account 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB, saiki tura evidence_ _of payment ta wannan
number 09013718241_
_Idan katine kuma Zaki biya 200 VIP 400 ta wannan number_ _09013718241 kada ki manta
lambobin katin ake buqata ko hotonsa._
# *UMMUH HAIRAN*
[8/9, 4:07 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *HABEEYTAH*
*_DUBAI PART 2_*
*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
*UMMUH HAIRAN*
*7*
Zamewa tayi daga jikinsa ta zube a qasa numfashinta yana sarqewa ta dafe qirjinta jikinta yana
rawa Dr Shattima ya matso da sauri ya kamata ya dorata a gadon ya zaro wata allura ya danna
nata nandanan jikinta yayi laushi ta suma Granny ta juya ta kalli Saudat data zubawa Habeey
ido cike da tsananin tausayawa hawayenta na zuba a qasa tace. “Meye kuma abin kukan Saudatu kunyi nasara tabbas kuyin nasara Allah ya baku saa kun raba
tsakanin Taheer da Habeey, Saudatu badai Taheer kikeso ba gakinan gashi daukar yarinyar
dake bacci tayi ta miqa Mata tace “ga yar mijinki nan ki dauka ki riqe kwafi samun nutsuwa
amma kafin wannan lkcn inaso kisan wani abu qwaya daya ita duniya juyawa takeyi saboda
haka kada kiyi tunanin dawwama cikin farin ciki kin rabashi da farin cikinsa kin yankewa Habiba
nata farin cikin shakka babu lkc na zuwa da zakiyi naki kukan babu hawaye"
Kubrah ce ta dubeta tayi “murmushi tace “haqqin rai biyu ne akanku Saudat koma nace uku
saboda ke yaya yaci mutuncin Habiba saboda ke ya rabata da yarta saboda ke komai zai iya
faruwa dashi kansa yayan, Abu daya nima da zan fada miki shine quncinki sai yafi wanda kika
sanya zuqatan masoya sannan babu ubanda ya isa ya raba Safnah da mahaifiyarta harsai idan
sune sukace bazasu riqe ba"
Addah ce ta girgiza kai tace ku bashi yarsa kawai bsmu buqata Allah ya rayata a duk inda take
wannan qaddarorin na Habbatullah sinyi yawa Allah ka sassautawa baiwarka haka" hawayen
saudat ne ya qara tsinkewa tace “wlh tallahi bansan meyene ya kawo wannan sauyin ba
Granny yanzu kafin mu taho har zagina Yaya Taheer yayi akan Habeeytah ya rantsemin ya qara
kan cewa koya aureni saiya sakeni ni zuwa nayi idan ta farka na roqeta ta nemamin alfarmar ya
hadamu ya auremu"
Murmushin takaici Granny tayi ta juya zauna daidai lkcn da Dr shattima ya sake shigowa yace
“nan da 30 minutes zata iya farfadowa don Allah a kawar mata da duk wani Abu dazai sanyata
damuwa" jinjina kai sukayi ya sake fita, haka kuwa akayi 35 minutes da fitarsa ta farka a firgice
tana Kiran Taheer kada kayimin haka don Allah wlh nafi kowa sonka kada ka rabani da yata ita
kadai na mallaka duk duniyar nan kada ka sanyama yata maraicin uwa a halin uwarta tana raye
kada ka qara tabbatarwa da zuciyata namiji tuwon rezar ne miyar Allura ashe wannan ranar
zatazo Taheer Kaine da kanka kayimin gori?"
Kuka takeyi Addah na riqeta tace “da nasan wannan ranar zatazo Dana roqi Allah ya kasheni
kafin lkcn, wayyoh Allah qirjina Allah ni yaushe zanyi farib cikine kamar kowa...."
Ta qarashe mgnr tans kakarin amai kamar zata amayar da kayan cikinta amma aman yana qara
tsanani sai jini, wani ihu Addah tayi ta qanqame yar tata Saudat ta nufota da gudu itama ta
riqeta tana kuka tace “nashiga ukuna Taheer kada kayi kisa don Allah ka dawo ka janye
kalamanka Taheer asheni ba sonka nakeyi ba ga wacce take sonka..." Daqyar cikin taimakon Allah Dr Shattima da Dr Zainab suka samu aman ya tsaya suka daura
mata na'urar shaqar iska saboda Athmer dinta data tashi tanata gwama numfashi Dr Shattima
cikin tashin hankali yaketa fadan ya akayi aka bari ta tuna abinda ya faru?
Wannan rana sunga ikon Allah dukkansu anan suka kwana akanta Kiran duniya Bushirah
tayiwa wayar Taheer amma a kashe saita Dad ya Kira ta fada masa abinda yake faruwa shima
ya shiga rudu saboda zuwa yanzu tausayin Habeey ya gama ratsa jikinsa yace su jirashi
gashinan zuwa. Haka kuws akayi jiransa sukayi bai dadeba ya iso.
Granny ce tayi masa bayanin komai ya zauna yana salati tare da tunanin mafita a fili yace
“aikuwa saidai ya hada biyun ya aura wannan ma zalumcine ya gama lalata mata rayuwa
sannan yace bazai aureta ba" da sauri Addah tace “aa kada ayi haka Alh tunda yace bayaso ku
qyaleshi matar mutum kabarinsa qila dama ba matarsa bace" duk yanda Dad yaso yabawa
Addah hqr ta tubure qarahema tace itafa indai ta isa da Habeey bazata auri Taheer ba.
Jikin kowa yayi sanyi Dad ya dauki takarda da biro yayi rubutu ya miqawa Addah yace “ku riqe
wannan don Allah kafin a daidaita komai ina ganin Taheer ba a cikin hayyacinsa yake ba"
girgiza kai tayi tace “bama buqatar komai daga gareku ranka ya dade iya hakama min gde Allah
ya qara daukaka" Daqyar ya roqeta ta karba check din kudin sannan ya debe yayansa suka tafi amma banda
Bushirah da takejin ciwon abinda ya faru kamar ita akayiwa, sai dare Habeey ta farka ta bude
idonta tana kallon silling din maganganun Taheer sunayi mata yawo a kwanya “ballagaza banza
me zanyi da ita karuwar yarinyar nan..."
Wata qara ta saki Dr Shattima daya kasa ya tsare ya miqe da sauri ya isa gurinta ya fara dubata
ya cire mata abin taimakawa numfashin da aka maqala mata ya zare mata allurar drip din yana
Mata murmushi ita kuma sai kallonsa takeyi hawaye na zuba a idonta.
Zama yayi a gefenta yace “idan baki manta da komai kin fawwalawa Allah ba Zaki kashe kanki
Habbatullah akwai darasi me yawa a cikin rayuwarki kuma ita qaddara bata shawara lkcn da
zata fadowa mutum wlh a iyakar kwanakinki a asibitin nan bantaba sanin Taheer ba mijinki bane
sai kwanaki uku da mahaifiyarki tazo, shima waya naji tanayi tana kuka tana fadawa wata halin
da kike ciki"
Shassheqar kuka takeyi ta yunqura zata miqe yayi saurin kamota ya tallafa mata ta zauna yace
“kiyi hqr muyi addu'a Allah yayiwa kowa zabi na alkhairi amma ni dama nayi tunanin faruwar
hakan ba yanzu bako a gaba"
Itadai batace komai ba har ya zauna ya zuba mata ido zuciyarta suya takeyi sosai qaddarorinta
sun fara bijirewa kwayarta a firgice ta dago tace “ina yata?" Dago idanunsa yayi da suka kada
sukayi jah tunda yake aiki baitabajin tausayin wata mace kamar yanda yake tausayin
Habbatullah ba yace “babanta ya dawo ya dauketa kiyi Mata addu'a duk inda take zata isheta"
miqewa yayi da sauri ya fice saboda zuciyarsa ta gama karyewa.
A cikin kwanaki biyun da suka qara sosai Addah da Granny ke qarfafa mata gwiwa tare da kafa
Mata misalai da hujjoji da zasu sanya ta manta da Taheer a rayuwarta saboda juyin duniya Dad
yayi dashi akan ya koma kodan safnah su daidaita da Habbatullah suyi aure Amma fir yaqi yace
shifa baisan meye yasa masa tsanarta ba ko sunanta aka Kira gabansa faduwa yakeyi. Ganin yanda ran Dad ya baci ne yasashi fadawa jikinsa ya fashe da kuka yana cewa “wlh Dad
qasan zuciyata danqare take da qaunar Habeeytah amma jikina da ruhina tsanarta suke qarayi
Dad bansan meye ya canzamin qaunar Habeeytah da tausayinta zuwa qiyayyarta ba, alfarma
days zakayimin Dad kada ka daura aurena da Saudat wlh idan ka daura mutuwa zanyi kabarni
na rayu da yata ta isheni rayuwa nayi maka alqawarin kare kaina nayi maka alqawarin zan
rinqayin azumin litinin da alhamis"
Lamarin ya fara girmamewa tunanin Dad duk yanda yake tunanin Taheer ya wucce nan
kamashi yayi ya dagashi zuwa yanzu ya daina ganin baqin dannasa tausayinsa yakeji a
sanyaye yace “bazan taba takura maka ka auri abinda ranka bayaso ba amma zamanka haka
risk ne kayi hqr ka auri yar uwarka Saudat nasan zakaji dadin hakan a gaba Taheer inajin
kunyar na kira sahabi na fada masa na fasa aurawa dana yarsa shi tunani yakeyi na isa dakai
kayimin wannan alfarmar Taheer"
Miqewa yayi yana hada hanya ya shiga bangarensa ya fada gado yanajin qirjinsa yana zafi ya
zubawa qaton hotonsa da Habbatullah ido yana kallon yanda suke cikin nishadi lkcn da
sukayisa yana kukan zucci qaunarta tana qwaqular qasan zuciyarsa amma ya kasa gane hakan
yanda ya zuba mata ido yana kallonta har wani buda hannunsa yakeyi wai ta shiga qirjinsa.
Kwana biyu suka qara Granny ta rakasu har Gombe har sukaje Habeey na kwance a kafadar
Granny zuwa yanzu ta daina kukan rabuwa da Taheer kukan rabata da yarta takeyi a sanyaye
tace “don Allah Granny ki kawomin Safnah naganta nayi Mata addu'a Ina roqon Allah kada
yakaita lkcn da zata dandani irin abinda ubanta ya dandanamin, Allah kaji qanta ka tausaya
Mata kada ka juya sakayyar bataji ba bata gani ba a kanta Allah ka rayamin ita rayuwa me
albarka, shikenan yanzu Granny bazan qara ganinta ba?"..…......
_Gareku masoya garabasa gareku saboda murnar bikin babbar sallah daga yau 3/8/2020
zuwa_ _10/8/2020 na rage kudin da ake biya domin samun wannan_ _rikitaccen labari me cike
da turka turka single Zaki biya 150 VIP 400 idan ta account ne._
_Account 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB, saiki tura evidence_ _of payment ta wannan
number 09013718241_
_Idan katine kuma Zaki biya 200 VIP 400 ta wannan number_ _09013718241 kada ki manta
lambobin katin ake buqata ko hotonsa._
# *UMMUH HAIRAN*
[8/9, 4:08 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *HABEEYTAH*
*_DUBAI PART 2_*
*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
*UMMUH HAIRAN*
*8*
Sosai kalamanta suka ratsa zuciyar Granny jin kukan nata takeyi kamar tana dora mata dutsi
aqirjinta a hankali taci gaba da rarrashinta har suka isa gidan sukayi sallama da Granny akan
cewa idan an gama biki zasu dawo suga yanayin jikin Habeey.
Tunda suka shiga ta qule daki taja bargo ta rufe jikinta sanyin zazzabi yana ratsata tana nunka
nadamarta tanajin ninkin tsanar jinsin da namiji a zuciyarta, ashe dama muguntar da Taheer ya
shirya mata kenan ya nace saita soshi saida ya koya mata sonsa sannan ya juya Mata baya ya
rabu da ita rabuwa mafi ciwo a lkcn da tafi kowa buqatarsa.
Kuka takeyi sosai tana juyi a cikin bargon tana ambaton ya Allah tare da danna qirjinta son
Taheer qila ita kuma shine ajalinta, a galabaice ta miqe ta sauko tana dafa bango ta shiga
bandaki ta kama ruwa ta dauro alwala tazo ta tayar da sallar azahar tana kuka tana fadawa
Allah damuwarta. Bayan ta idar ta dauki qur'ani data gani a gefe ajiye ta fara karantawa tanajin sassaucin nauyin
da qirjinta yayi bayan ta idar ta daga hannunta tana kuka kunyar ubangijinta takeji ta kasa bude
baki ta nemi yafiyarsa gani takeyi kamar bazai dubeta da idon rahmaba.
Amma data tuna Allah gafuru al rahim ne sai taji sanyi a ranta ta fara neman yafiyarsa da zuciya
me tsarki ta jima tana Istigfari sannan ta rufe qur'anin ta koma ta kwanta tunanin baya yana
dawo Mata da irin alqawurran da Taheer ya rinqa yimata lkcn da yana kwadayin jikinta.
Safnah tafi komai tsaya Mata a ranta tunanin kalmar da zata fadawa yarinyar lkcn data girma
taji irin hanyar da sukabi suka samar da ita takeyi.
Toshe bakinta tayi da hannunta saboda ita kanta tagaji da kukan da takeyi so take ta saba da
wannan rayuwar data samu kanta a ciki saboda tasan itace qaddararta, Addah ce ta shigo da
waya a kare a kunnenta ta zauna kusa da ita ta dafata tace “na fada miki banson damuwar nan
da kike sanyawa kanki Habbatullah muyi hqr komai yayi farko zaiyi qarshe ga yar uwarki zakuyi
mgn"
Kara Mata tayi a kunneta tayi sallama da murya me rauni Fatima tace “Yaya Habeey ya jikinki
ince dai kin warke?" Ajiyar numfashi tayi tace “gangar jikina ta warke amma zuciyata zafi takeyi
Fatima nafi buqatar mutuwa akan wannan rayuwar da nakeyi mara albarka na rasa farin ciki ta
ko ina..." Saurin katseta tayi da cewa “ki daina wannan zancen Yaya wata rana sai lbr don Allah
kiyi hqr ki manta da wannan mayaudarin insha Allahu Allah zai saka miki"
Lumshe idonta tayi tace “don Allah Fatima ku dawo gda kada kiyi sha'awar yin rayuwa irin tawa
babu komai a cikinta sai tozarci da qasqanci ki fito a kamoki ko ki bawa argent dinki number ta
ya kirani na bashi kudinsa ku dawo mu nemawa rayuwarmu makoma, bana fatan rayuwarku ta
lalace kamar tawa nikam nasan babuni babu farin ciki a rayuwata"
Jikin Fatima yayi sanyi matuqa sukayi sallama ta Addah ta dubeta ta kawar dakai tasani duk
itace ta jefa rayuwar Habeey cikin wannan gararin, miqewa tayi a kasalce ta nufi nata dakin
tana kukan zuci dana zahiri yarinyarta me biyayya dason faranta mata yau gata tana kuka
saboda wasan da tayi da rayuwarta ta rabata da gatanta ta kawota ts hadata da muguwar
rayuwar data zabawa kanta yanzu ta Yaya ma zata tunkari Salahu da mgnr wata ya dake
tsakaninsu balle har ya karbeta ya a matsayin jininsa bayan an fada masa cewa cikin ya zube?
Hakanan suka yini a daki kowa zuciyarsa babu dadi sai yamma sannan Habeey ta qarfafa
jikinta a qoqarinta na sanyawa kanta dangana da rungumar qaddararta ta fito tsakar gidan ta
zauna Addah na gyaran kubewa ita kuma tana gyara Mata ganyen ugo saboda rashin
wadataccen jinin da Habeey ke fama dashi shiyasa ta bayar aka siyoshi zatayi mata miya dashi.
Rayuwar Habeey da mahaifiyarta da yan'uwanta gwanin dadi cikin kwanaki ukun gata sosai
suke nuna Mata basu barinta da damuwar komai ko yaushe cikin sanyata dariya suke, biye
musu takeyi amma qasan zuciyarta ta kasa cire Taheer a cikinta kullum mafarkinta shine ko
magana akayi mata wani lkcn shi take ambato. Lamarin da yake damun Addah itadai da gaske batason ko wani abu daya shafi Taheer so
takeyi ya fita cikin qaddarar yarta har cikin ranta dadi taji days karbi yarsa, cikin kwanaki ukun
ne Addah tasa aka ciro Mata kudin da governor Waziri ya basu kudine ba kadan ba batare