DUBAI PART 1 BY OUM HAIRAN.pdf

Author :  Oum Hairan Category :  Taskar Novels

Chapter   9 / 14

24K to 27K   out of 39.9K words

hali ya fara bambamta Haroon baya sallah azumi ma sai yaga dama yakeyi Haroon bai
damu da bawa Hajar abinci ba.
Ana cikin wannan murdadden zaman ne cikin da suka kwantar ya tashi, nan fa sabuwar rigima
ta tashi yace shifa saidai a zubar da wannan ciki saboda baya qaunar duk abinda ya shafi
Salihu, itakuma tace bai isaba ai shine yace su kwantar dashi tun farko.
Shikuwa ya hanata abinci saidai tayi surfau da dakau da wankau ta samu abinda zataci har
cikinta ya isa haihuwa cikin dare naquda ta kamata daqyar ya taso mata wata Mata da suke
haya tare Cristian ce sunanta Alheri itace ta karbi haihuwar cikin hikima ta ubangiji Hajar ta
haifo sunkuceciyar yarta mace kyakkyawar gaske.

Alheri ce tayiwa Haroon albishir na kyakkyawar yarinyar da suka haifa da farko qin zuwa yayi
amma da yaji anata zuzuta kyawun yarinyar sai yazo yaganta kamarta daya da Salihu amma
saboda idanunta da hancinta na Hajar ne sai kamar ta buya amma har kalar fatar yarinyar irinta
Salihu ce wato chocolate colour. Yana ganin yarinyar nandanan Allah ya dasa masa qaunarta a zuciyarsa ya daukita yayi Mata
huduba da Anitah Nan fah Hajar tayi tsalle ta dire tace aa ita Habibatullah sunan yarta nan ma
an samu rikici me yawa kafin kowa ya zabi sunan da zaike kiran yarinyar dashi shi yana kirana
da Anitah Addana tana kirana da Habibatullah.........





*UMMUH HAIRAN CE...✍*
[7/23, 9:24 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ *DUBAI*✈️



*_22/7/2020_*



_Page 15 shine last Free Page, ga wadanda suke buqatar jin qarshen wannan labari zasu biya
kudinsu ta wadannan hanyoyin dake qasa single section da nake posting sau daya a rana 200
VIP da nake posting sau uku a rana 600_






_Idan kinada interested zaki iya biyan kudinki ta wadannan hanyoyin_


_Account number_

_0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar_

_GTB_

_Ko katin waya MTN ta wannan number a WhatsApp_

_09013718241_

_Saiki tura avidance of payment dinki ta wannan number_

_09013718241_

*Episode 17*



Haka Addah take rainona ta dauki son duniya ta doramin tun Ina shan nono Addah takeda tarin
buruka a kaina, babban burinta shine nayi karatun addinin muslumci me zurfi sannan nayi na
boko.
Watanni na goma sha bakwai Addah ta haifi Ibrahim wato Sunday sunan da Pappa yake
kiransa dashi kenan, tsakaninmu da Pappa kullum naira biyu da ficika ce nida Ibrahim itace
abincin rananmu itace ta darenmu gashi kamar ya kafe Hajar bata iya fadawa kowa matsalarta
saidai tayi surfau dakau wankau ta sama mana abinda zamuci.



Taheer tunda nake a rayuwata idan ka dauke kayan jarirantaka zan iya rantse maka baa tabayi
mana sabon dinki ba saidai abamu saqabu musaka wasu ma sunyimin yawa haka zanta bunjim
bunjim a ciki gani Masha Allah ta ko Ina Allah ya qerani baiyimin qirar wasa ba amma babu
kulawa. Duk da mahaifiyarmu tana iyakar bakin qoqarinta abinne yafi qarfinta ci sha sutura omon wanki
sabulun wanka man shafawa duk Addah keyi mana, a haka ta haifi Aishatu wato Hellin.
Nan fa dangantaka ta fara tsami tsakanin Addah da Pappa takai ta kawo Pappa sai yayi wata
biyu yana cikin garin gombe amma baizo inda muke ba Amma hakan bazaisa idan yazo Addah
ta canza masa kallo ba.




Gashi Allah yayiwa addanmu baiwar aihuwa data tashi sake haihuwa sai tayi biyu Fatima da
Idris Wato Ritah da Jumson lkcn inada shekara hudu yar kyakkyawa dani, sanda na fara tasawa
ne al'amura suka qara quntata.
Wani dare da bazan taba mantawa dashi ba a rayuwata daren dana fara fahimtar me rayuwar
gidanmu take cewa, Taheer na fito tsakar gida fitsari ya kamani na shiga bandaki na fito kawai
sai na tarar da Addah zaune kan kujera yar tsugunno tanata rera kukanta.

Nan na matsa gabanta na zauna na riqo hannunta kawai sai naji jikinta da zafi, Ina Shirin yi
Mata mgn naga Pappa ya fito rungume da wata mace a jikinsa yana shafata yana cewa
“madam yau kinyi sugar dubu uku zan baki"




Mamaki ya kamani da naga ya sanya qafa ya hankade addana yace “shashasha da kin dauka
ni dan iskane da zan tsaya Ina wahalar sallah azumi sannan insha wahala na tara dukiya ace
nayi zakkah to bari kiji Hajar wannan addinin naku na wahalallu yayimin tsauri bazan iyaba
Kuma giya da neman Mata yanzu na fara, Hajar bakida wani dadi ni'imarki Habeey ta kwashe
da ganin wannan dundubusar yarinyar ruwazata tara bana wasa ba.
Amma dake abin naki son kaine baki bawa yayana ba sai kika bawa yar tsohon mijinki da mota
ta niqeshi, to ko ruwana da aka diva aka wanke wannan yarinyar idan ta girma saita biyani da
hannunta saboda ni ba bawan wani shege ko shigiya bane"





Nidai sakin baki nayi bata da ina gane ko kalma dayaba Ina kallonsu suka fice Addah ta dago ta
kalleni tace “kije ki kwanta Habbatullah kada ki makara zuwa makaranta kinga gobe akwai
tahfiz"
Banyi Mata musuba na miqe naje na kwanta amma zuciyata cunkushe da tunanin abubuwa da
yawa, abin mamaki Dana tashi da safe banga alamun wata damuwa a fuskar Addah ba tanata
aikinta na dauki tsintsiya nayi Mata shara nayi wanke wanke na taso Fatima da Idris nayi musu
wanka naja hannunsu zamu tafi Tahfiz amma sai naji Pappa ya kirani da sunan dana tsana
wato Anitah.
Babu yanda zanyi haka na juya na kalleshi yace “sakesu dan ubanki kedai da kika gaji wahala
kije kiyi amma yayana bazasuyi wannan wahalar ba"




Tatar qullin kunun da Addah takeyi ta bari tace “wai da gaske kakeyi maigida kayi riddah?"
Batare da tunanin komai ba yace “Ni dama ban musulumta ba balle nayi riddah sani nayi
wannan daqiqin uban naki meci da buguzun bazai bani aurenki ba sai nayi masa basaja
bakisan wani abuba yanzu haka church gudace a hannuna saboda haka Hellin Sunday Ritah da
Jumson Yaya nane bana buqatar ki qara dangantasu da addininki"

Duk da ba komai nake fahimta ba amma kalaman na qarshe sunfi komai girgizani ina tsaye
kamar dashe yazo ya janye qannen nawa ya mayar dasu ciki nikuma addah ta kalleni tace “jeki
makarantarki kinji Habbatullah" hakanan natafi tahfiz din ni kadai.
Tundaga wannan ranar su Aisha suka daina zuwa makarantar islamiyya saida Adda ta koya
musu, ana haka sai Dalson ya tsiro da wata tsiya wai lallai sai Addah ta rinq binsa church,
itakuma tace Allah kasheta bazata ba nanfa dangataka ta qara tsami kullum sai Dalson yayiwa
Addah dukan mutuwa sannan yaje ya shawo giyarsa yazo yayita sheqa Mata amai hakanan
zata wanke kuma ya jibgeta.





Nikam dukan yana damuna amma ban isa na fadaba sai Addah tacemin Ina ruwana ai laifi
takeyi masa shiyasa yake jibgarta, ana haka labari ya ishe liman na cewa Haroon yayi riddah ya
koma kafircinsa.
Nan fa kakanmu yayo tattaki har zuwa garin Ganjuwa yazo domin qwatarwa Addah yancinta
amma fir tace itafa a qyaleta da mijinta zata zauna dashi a haka saboda idan ta tafi bazai bar
mata yayanta ba kuma tasan canza musu addini zaiyi.
Taheer duk yanda Liman zaiyi yayi amma Hajar taqi basa hadin kai har cewa yayi zai bata gidan
zama anan cikin birnin gombe da jari me tsoka sannan zai shigo da hukuma ta qwatar mata
yayanta amma taqi yarda wai ita idan ta rabu da Dalson mutuwa zatayi.




Wannan bacin ranne ya sanya Liman tattara kan zuri'arsa yace ya sallamawa Dalson Hajar ko
mutuwa yayi bayason tazo kan gawarsa.
Tun daga wannan ranar komai ya qara lalace mana duk cikin yaran gidanmu mu biyar ni kadai
nakeyin karatu shima wani Alh ne ya dauki nauyi na saboda nidin qawar yarsa ce Zainurah
amma sauran qannena duk basa arabi basa boko sai tallan burkutu da Pappa yake dora musu
sukai church. Haka rayuwar tayita tafiya cikin qunci talauci da qangin rayuwa, a zahirance Pappa bayada
mahaukacin talauci amma ya rantse daidai da ransa indai Addah batayi riddah ba to bazata
qara samun tallafi daga gareshi ba itakuma tace ya riqe tallafinsa bata buqata.




Daqyar Addah tasamu ta dorani akan tarbiyyar islama saboda tanayi ne Pappa na warwarewa
duk cikin yayan Addah ni da Aisha ne kawai mukebin addinin muslumci sai Ibrahim da naji lbrn
shima ya musulumta yanzu.
Girma nakeyi sosai bana wasaba shekaruna goma sha uku duk wasu halittuna suka gama

bayyana komai nawa na musamman ne, tun a lkcn samarin maza yayan masu halin garinmu
suka rinqa kawomin caffa amma naqi domin zaman gidanmu ya dasamin tsoro da tsanar da
namiji cikin zuciyata gani nakeyi duk wani namiji irin halin Pappa ne dashi sai gashi a hankali
Taheer ka tabbatar min da zatona gsky ne ko babu bambamcin addini akwai zalumci tsakanin
namiji da mace.




Komai ya fara lalacewa Pappa takai ta kawo an qwace church din dake hannunsa saboda
neman matansa da Kuma lbrn da yajewa pastor din cewa baya kula da iyalinsa.
Itama burkutun aka daina siya ko mun fita da ita haka muke dawowa da ita nicema saboda
kyawuna nake danyin ciniki, kawai sai ya yanke shawarar komawa facin motoci.
Bakin titi ya karbi hayar guri ya kama sanaarsa kullum zankai masa abinci zamu zauna muyita
Hira dashi nikam Pappa baya nunamin wani abu na qyama komai zaice yata Anitah hakan yasa
na saki jiki dashi, inda ya dauki buri ya dorawa kyauwuna har cewa yakeyi bazaiyimin aure ba
saina tara masa dukiya. Wata ranar juma'a an tashemu daga makaranta muna tafe nida Zainurah duk wata halitta ta
jikina tana rangaji, munzo wuccewa ta wata majalissar matasa sai wani natashi da ake Kira
Nafi'u Mai saa ya taso ya biyoni nikuma tsoronsa ma nakeyi saboda kisa ba wuya yakeyi masa
ba a gabana wataran ya dabawa wani yaro wuqa.



Aikuwa na kwasa da gudu na shige rumfar Pappa lkcn wata Hajiya tana zaune yanayi mata
facin mota yana ganina ya taso yace “ya akayi kike gudu" fadawa nayi jikinsa Ina haki ya
rungume ni yana shafa bayana.
Saida yaga na nutsu sannan ya tambayeni menene, nan nake zayyane masa abinda ya faru,
nanfah Pappa ya ringa fada itadai Hajiyan nan sai kallona takeyi har na juya zan fita ta kirani
naje tace “ya sunanki?" A gajiye nace “Habbatullah" murmushi tayi ta dauko yan dari biyar guda
biyu tabani tace nasai kayan kwalliya. Nayi gdy na tafi inata murna yau Addata zatayi mana girki da nama saboda ni Allah yayini
dason naci dadi a rayuwata banason qazamin abinci, ban dade da shiga gidaba Ina mayarwa
da Addah abinda ya faru Pappa ya shigo afujajan yana qwalamin kira.......






*UMMUH HAIRAN CE...✍*
[7/23, 4:44 PM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ *DUBAI*✈️

*_22/7/2020_*



_Page 15 shine last Free Page, ga wadanda suke buqatar jin qarshen wannan labari zasu biya
kudinsu ta wadannan hanyoyin dake qasa single section da nake posting sau daya a rana 200
VIP da nake posting sau uku a rana 600_






_Idan kinada interested zaki iya biyan kudinki ta wadannan hanyoyin_


_Account number_

_0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar_

_GTB_

_Ko katin waya MTN ta wannan number a WhatsApp_

_09013718241_

_Saiki tura avidance of payment dinki ta wannan number_

_09013718241_



*Episode 18*




A firgice na tashi na fito daga dakin kaina ko dankwali babu, Pappa ya figi hannuna yayi waje
dani Allah bai bawa Addah ikon yin mgn ba muna fita naga Hajiyan nan ta dazu gabana ya fadi

amma ban iya cewa komai ba.
Inaji sukayi yarensu na tangale tayi masa godiya ya dawo kusa dani nace “Pappa Ina zatakaini
naji kana cewa sai kunyi waya?" Ranqwashi ya sakemin yace “kajini da shegiyar yarinya da
idonta kamar dinya nunanna to unguwa zaki rakata maza shiga mota kuje ku dawo"
Zuciyata bata nutsu ba amma nasan inayin gardama akan Addah ta zai hucce hakanan na
shiga ta kalleni tayi murmushi tace “talaucinku ya yanke Habeey daga yau kedai ki saki jiki duk
abinda aka sanya ki kiyi"




Bance Mata qalaba har muka fita daga. Gombe muka shiga Bauchi inata bin hanya da kallo
zuciyata babu dadi inata tunanin abincin da Addah takeyi mana shinkafa da miya da nama, saiji
nayi tace.
“Taso ki fito munzo" zubawa gurin ido nayi wani makeken gdane me haduwar gaske, nidai a
tsorace na fito na rinqa binta duk inda ta cire qafarta nan nake aza tawa har muka shiga
tsakiyar gidan.
Nan na qara sarewa da wannan al'amari yan matane kamar ni da wadanda suka darani harma
da wadanda suka haifeni birjir a gidan sunata harkokinsu, sunkai su ashirin sai sannu da zuwa
sukeyi mata sunata bina da kallo.




Taheer tunda nake idan ka dauke ranar da naga Pappa ya fito rungume da Debora bantaba
ganin mace da namiji manne da juna ba sai a gdan Hajiya Dala.
Wani daki ta bude ta juyo ta kalleni tace shigo kiyi wanka sai kici abinci" banyi Mata musuba na
shiga dakin kawai sai naga wata mace da wani namiji yana kwance akanta babu komai a jikinsu
sai wani dan mayani da suka rufe al'aurarsu dashi.
Nanfa jikina ya dauki rawa Hajiya tajani ta turani dakin tace “abinda akace kiyi daban abinda
kikeyi daban, maza kiyi wanka kizo kici abinci in killaceki kiyi Kumari nafi samun babban kai
wanda zanyiwa kyautar budurcinki"




Oho nikam dake sauna ce ban fahimci me kyautar budurcin take nufi ba naje nayi wankana
bayan na gama qauyancina a bathroom din na fito na shafa mai tare da daukan wasu riga da
wando da Hajiya Dala ta ajiyemin na sanya suka zauna das a jikina manyan mazaunai na suka
baje a ciki da cikakken hips dina da idan ka kalleni ta baya zakace nayi 18 years nanko ko 14
ban cika ba.
Kama dogon gashina Dana gada gurin mahaifina nayi na daure na sakeshi a baya, ni kaina
nasan nayi kyau abinka da dama kalar hutun, Hajiya ce ta bude qofar ta shigo ta tsaya ta

zubamin ido tana kallon baiwar ubangiji na dago ta dagani da sauri tana juyawa dani tana cewa
“wannan kayan bana yara bane Alh Jafaru zanyiwa surprise dake nasan zaiyi farin ciki"




Direwa nayi qasa nace “Hajiya waye Alh Jafaru?" Dariya tayi tace “zaki sanshi sani na gaske
zaki samu kudi addanki zata daina dakau da surfau indai kika bashi hadin kai"
To banma fahimci hadin kan ba taja hanuna muka fito ta zaunar dani ta kawomin abinci me rai
da lafiya ga wani farfesu a gefe sai tiriri yakeyi, habawa nanfa na bude ciki naci abinci nayi nak
nayi gyatsa na tashi na wanke hannuna na dawo.
Tanata waya na zauna kusa da ita ta gama nace “ni me zanyi miki ne anan Pappa yace rakiya
zanyo miki" murmushi tayi tace “banike yayi a matsayin hannun jari zan kaiki Saudia zakiyi
Aikatau a gdan larabawa"



Gabana ya fadi nace “aikatau kuma addata kuma fah nikam bazani ba gaskiya bayan ance
karuwanci akeyi acan din idan anje" dariya tayi tace “yaro man kaza to banda abinki dama
zakiyi kyau a banza ne ai dama duk wata me kyau jari aka bata na yankar mazan zamani
yarinya zan doraki a hanya tun anan Zaki fara samo mana manyan alhazai suna zazzage mana
jaka tsumaki ma zanyi kinji Habeey wata shari'ar sai a lahira ayita"
A wannan ranar fah munkai ruwa rana da Hajiya Dala kafin ta samu kaina kuka na rinqayi Mata
musamman da dare yayi lkcn kwanciya yayi naganni a cikin dandazon yan matan gdan tsumu
sunata harkokinsu.




Ganin naqi sakin jikine yasa Hajiya jana dakinta tace na kwanta anan hakanan na kwanta Ina
kuka har bacci ya daukeni.
Washegari Hajiya ta fice tabarni hannun wata amintacciyar yar dakinta Barira itama ta kula dani
sosai saboda matsayin kadara nake a gurinsu, a gidan ba maza ba hatta mata idan suka kalleni
sai sunce Masha Allah, amma ba u damar tabani saboda baqin kashedin da Hajiya tayi musu
akaina. Kwana na uku a gidan dole tasa na fara sakin jikina na zama yar gari nima kwaratan da suke
shigowa gidan kowa idan ya qyalla ido yaganni sai yace da Hajiya shifa ni yakeso.




Ita kuma taqi tace badansu ta kawoni ba tafi tafiya na miqawa har nayi wata guda a gidsn
kullum da tunanin Addah ta nake kwana nake tashi idan zanci abinci sai nayi tunanin ko me

Addah taci idan ruwa zansha ma haka wai donma Hajiya Dala na jana a jiki.
Wata rana muna zaune duk matan gudan sun fita yawon ta zubar dinsu dagani sai Hajiya kawai
mukaji an qwanqwasa qofa, kallona Hajiya tayi tacemin “jeki kiga waye" na miqe dagani sai
wando bomshet da riga airmless na nufi qofar na budeta kawai sai naga wani babban mutum ya
tsaya yana qaremin kallo sama da qasa nima Ina kallonsa nikam muninsa kawai nake kallo inda
shikuma yakemin kallon sha'awa.




Kirana Hajiya tayi tace “me kike kallo ne zo ki shige daki ki kwanta dare yayi" tabe baki nayi a
Raina nace Hajiya me kwashe² ko Ina ta kwaso wanna herro din amma

9 / 14