Author : Oum Hairan Category : Taskar Novels
wani yaro, Habeey ta zubawa yaron ido yana
zuwa sai taga ashe autansu ne Idris yana ganinta yace “lahhh Aunty Habbatullah kece dama
dama tun jiya Addah take kuka tana cewa baqin cikinku ne zai kasheta"
Dago jajayen idanunta tayi tace “addah kuma Idris wacce Addan?" Kallonta yakeyi da mamaki
yace “munada wata Addah ne bayan mahaifiyarmu..." Rungumeshi tayi ta saki wata ajiyar
zuciya tare da kuka a tare tace “dama Ibrahim qarya yayimin yace Addah ta mutu ya tashi
hankalina ashe meye yasa yayimin wasa da rayuwar uwata?" Parking sukayi a wani matsakaicin gida Idris ya fita da gudu ya shiga gdan ya qyarawa Addah
da Ibrahim cewa ga Yaya Habbatullah nan ita da wani" miqewa Addah tayi da sauri ta shige
wani daki ta kulle suka shigo suka tarar da Ibrahim yanayi mata magiyar ta bude Amma fir taqi
matsawa tayi kusa da Ibrahim din tace “nice batason gani ko qanina? Addah ki bude ni inason
ganinki inason na tabbatar da lfyrki Addah kada kiyi fushi dani da qaddarata wlh nayi iyakar
qoqarina na ganin na tsare mutumcina amma na kasa"
Tun tana magiyar ita kadai har saida Taheer yasa baki amma Addah ta qeqashe tace itafa
batason ganin Habbatullah ta fice mata daga gda kafin ta zama ajalinta, Taheer da baqar zuciya
ya matsa gabanta yace “ke kowa ma gudunki yakeyi da qaddararki uwar data haifeki ms tana
gudunki saboda qaddarar da itace sanadin faruwarta Habeey ni bazan taba gudunki ba kizo mu
koma ki haifamin baby na sai muyi aure duniya ai fadine da ita..."
Daga masa hannu tayi cikin kukan nadama da danasani mara amfani tace “dakatamin malam
sanda taka uwar tazo tacimin mutunci banji haushi ba nasan sonka takeyi saboda haka bazaka
rabani da tawa ba Ina ruwanka inma kasheni zatayi, ka fice Taheer ka fita banason ganinka
kaine Taheer Kaine qaddarata kaine ummul aba'isin faruwar komai don Allah ka fita a rayuwata
wlh daga tunda nake bantabajin sonka ba balle naji zan iya barin uwata saboda kai"
*UMMUH HAIRAN CE...✍*
[7/28, 8:20 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ *DUBAI* ✈️
*PAID BOOK*
_Idan kinsan baki biya ba kada ki karanta in kin karanta keda Allah, VIP 600 SINGLE 200_
_Account number_
_0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar_
_GTB_
_Ko katin waya MTN ta wannan number_
_09013718241_
_Yan Niger zaku turo katin Orange Wanda zaiyi daidai da 600 dinmu idan VIP ne idan SINGLE
ne wanda zaiyi daidai da 200 dinmu ta Nigeria._
*Episode 28*
Tsayawa yayi sororo sake da baki yana kallonta ganin yanda take kukan tana yiwa Addah
magiya yasashi juyawa ya fice daga gdan ya nufi hanyar da zata mayar dashi garinsu zuciyarsa
cunkushe da abubuwa da yawa shidai baisan meye yasa duk abinda ya shafi Habeey take
tsaya masa a zuciyarsa ba. Kai tsaye gda ya nufa saida jami'an tsaron gdan gwamnatin suka tabbatar da shine sannan
suka bude masa get ya shiga yayi parking a harabar ajiye motocin ya fito fuskarsa a cunkushe
ya nufi cikin gdan parlourn Mom ya shiga ya tarar da ita hakimce ita da yanmatanta biyu Kubrah
da Bushirah sai wata da baisan wayece ba.
Suna ganinsa suka miqe suka rungumeshi suna murna shidai ya kasa boye damuwar da yake
ciki yaqe kawai yakeyi yana dauke kai saboda kada Mom ta fahimci wani abu, sakinsa sukayi
ya matsa ya zauna kusa da Mom ya kama hannunta yace “mom i hope kina lfy?"
Janye hannunta tayi tace “ance tun jiya ka dawo meye ya hanaka isowa gda?" Shafa kansa yayi
yace “shigowar dare mukayi kuma tare muke da Babe so banson na barta ita kadai nasan idan
nace zan kawota gdannan Zaki iya fada mata mgnr da zata sanya ciwonta tashi..." Katseshi tayi
da cewa “wato dana rabaka da yar iskar yarinyar nan baka rabu da itaba ko Taheer wai kaikam
wanne irin yarone da bakajin mgn wlh kaji na rantse baka isa ka gurbatamin zuri'a da wannan
karuwar yarinyar ba wacce iskancinta ya riqa ya tatura har ta tsallake qasarta ta tafi uwa ba
kwaba take sheqe ayarta ba"
Qasa yayi da kansa ya zubawa Mom idanunsa daya kada yayi jajir yace “amma Mom kinsan dai
cewa komai yana tafiyane bisa rubutun qaddarar bawa meye yasa kullum baki yiwa yayan wasu
fatan alkhairi itama fa yace qaddarorinta ne sukazo Mata a baibai kuma suka hado dani yanzu
Mom idan Bushirah ce ko Kubrah suka samu kansu a wannan halin ashe gudunsu kema zakiyi
kamar yanda mahaifiyar Habeey ta kasa tsayawa ta dubi yarta me qaunarta da idanun rahma
bayan duk abinda ya sameta sanadin uwar tatane, ta sadaukarmin da abu mafi daraja a gurin
kowacce ya mace a lkcn da tafi buqatarsa kawai saboda ta ceci rayuwar mahaifiyarta ashe
uwarma butulci zatayi mata"
Miqewa yayi yana huci yana hada hanya har ya kusa qofar da zata kaishi bangarensa ya juyo
yace “wlh indai irinku ne iyaye masu fifita son zuciyarsa fiye da farin cikin yayansu nikam dama
baa halicceni ba Mom meyesa kikeso watsawa muradai na qasane? Hmmm babu komai
albishir daya zanyi miki ki shirya daukan jika nanda watanni biyu Habeey da kika tsana tana
dauke da cikina watanni bakwai...."
Wata zabura sukayi duka parlourn harda baquwar da baisan wacece ba suka miqe ya kallesu
yayi murmushin gidan boss ya shige bangarensa da sauri yanaji Mom ta biyosa amma ya
shareta ya shige part dinsa ya kulle ya fada bathroom ya cire kayansa ya fara wankansa yanaji
tanata buga qofar ya shareta saboda shi ya qaddara Mom dinsa a matsayin ciwon kansa ya lura
duk cikin ysyanta tafi sanya masa ido.
Kwatan abinda takeyi masa bata yiwa Muheed ta takura masa tasa mawa duk wani motsinsa
ido, yana gama wankan ya fito ya fara shafa mansa bayan ya gama yasa doguwar rigarsa ya
kwanta ya fara kiran wayar Habeey amma bata dagaba, dama baiyi tunanin dagawar tataba ya
bude hotunansu da sukayi tare yanata kallo yanajin sanyi a ransa ya rasa irin son da yakewa
Habeey komanta birgeshi yakeyi.
Cikinta ya zubawa ido yanajin nutsuwa tana saukar masa shima ya kusa zama daddy yayi ajiyar
zuciya tare da kiran wayar kukun gdan ya fada masa abubuwan da yake buqata ya kawo masa
ya zauna yana tsakurar abincin hankalinsa gabadaya yana gurin zuciyarsa, yinin ranar bai iya
hassalawa kansa komai ba har zuwa dare da yaji ana buga qofarsa ya share duk tunaninsa
Mom ce wayarsa ce tayi ring ya dauka sai yaga number Dad dinsa ya kara a kunnensa Dad
yace “ance ka dawo ko to kazo parlour ns inason ganinka"
Ajiye wayar yayi ya fita ya nufi parlourn Dad din qirjinsa yana bugawa Amma sai ya aro juriya ya
sanyawa ransa ya shiga da sallama Dad ne kadai ya amsa masa ya zuba masa ido har ya iso
gabanshi ya rusuna yayi zama irin na daa yace “Dad na sameku lfy?" Furzar da iska Dad yayi
yace “meye yake faruwa ne tsakaninka da Mom dinku?" Shafa kansa yayi yace “ah wani abu tace maka Dad nidai bansan komai ba ohhhh wai ko
maganar jikan da zakuyi ne ta kawo maka, to ai wannan ba tsakanina da ita bane tsakanina da
rayuwata ne......" wani mugun mari Dad ya sauke masa yace “kai wanne irin dan iskan yarone
ne Taheer anya kuwa kai danane jinina ne nikam ina tantama akanka, komai naka daban
tunaninka daban Taheer haihuwa zakayi a titi dan shege kake dangata tsatsona dashi?"
Miqewa yayi a hassale yace “aa fah Dad kads ka qara shegantamin ciki shege a gidan aure
akeyinsa tsakanin ma'aurata nikam cikina saidai ka kirashi kafin fatiha" juyawa yayi zai fice Dad
ya fincikoshi da qarfi yace “baka isaba Taheer ka zubarmin da qimata da mutuncina a idon
duniya dole ka kaini a dauki yarinyar nan a zubar da cikin nan ko kuma a batar da ita da abinda
zata Haifa" Tabe baki yayi ya kallesu sheqeqe yace “wannan ne kuma fah babu wanda ya isa yasani nayi
laifi biyu najima da na zinar mana wanda kune kuka sabbabamin shi amma bazanyi kisa ba
kisanma na abinda nafi qauna a rayuwata Dad yanda nakejin habeey da cikin jikinta wlh zan iya
yafe kowa a duniya please Dad kada kayimin dole kaikam ks tausayamin mana wlh Habeey tafi
Kubrah da Bushirah tarbiyya qaddararmu ce wadannan abubuwan da suka faru wanda Allah shi
kadai yasan abinda yake nufi damu"
Miqewa Dad yayi ya fara zagaya dakin shikuma ya sace jikinsa zai fice Mom tace “zonan dan
ubanka yanzu ba mgnrka mukeyi ba mgnr mafitarmu mukeyi gabadaya wannan abin da kayi
abune da zai taba qima martabarmu da kuma daukakarmu Taheer ka fahimcemu mutuncika
mukeson karewa" juya yayi ya nufi qofa ya fice da sauri ya koma part dinsa bugun duniya yaqi
budewa saboda shidai saidai suyi duk abin da sukayi niyya amma yanason cikinsa kuma yayi
alqawarin indai basu yarda ya auri Habeey ba to a haka za tayita haifa masa yayansa qarshe
ma ya dauketa subar qasar kowa ya huta shi da ace da wata duniyar ma can zasu tafi suyi
rayuwarsu cikin farin ciki ya mantar da ita duk wani damuwa dake damun zuciyarta...........
*UMMUH HAIRAN CE...✍*
[7/28, 6:13 PM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ *DUBAI* ✈️
*PAID BOOK*
_Idan kinsan baki biya ba kada ki karanta in kin karanta keda Allah, VIP 600 SINGLE 200_
_Account number_
_0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar_
_GTB_
_Ko katin waya MTN ta wannan number_
_09013718241_
_Yan Niger zaku turo katin Orange Wanda zaiyi daidai da 600 dinmu idan VIP ne idan SINGLE
ne wanda zaiyi daidai da 200 dinmu ta Nigeria._
*Episode 29*
Ita kuwa Habeey tunda ya tafi ya barta take faman yiwa Addah magiya Amma taqi sauraronta
hakanan ta koma gefe ta zauna ta dora kanta a saman akwatin kayanta taci gaba da
shassheqar kukanta tanajin ninkin nadamar abubuwa da yawa.
Ibrahim ne ya gyara mata wani daki jikin na Addah ya shigar Mata da kayanta yazo ya dauko
Mata abinci yakai mata tare da zama kusa da ita yace “nayi mamaki kuma na tsorata lkcn da
aka Kira wayar Addah ake fada mata karuwanci kika zaba a Dubai kin ma bi saurayinki kun tafi
Malaysia kuma ma cikine dake, bamu zaci haka daga gareki ba Aunty Habbatullah ko kadan
ban taba tunanin hakan zata faru ba" itadai kuka kawai takeyi tana girgiza kai.
Matsawa yayi ya tallafo kanta yace “ya akayi haka ta faru Aunty Habbatullah?" Cikin shassheqa
tara basa labarin komai shima hawaye yakeyi yace “kinyi ganganci da kika rinqa biyewa
hudubar Pappa yanzu gashi ya kaiki ya baroki" miqewa yayi ya fita ya shiga dakin Addah ya
zauna kusa da ita tanata matsar ido yace “ya kamata ko kowa zai juyawa Habbatullah baya
kekam karki juya Mata domin komai ya faru da itane ta sanadin qaryar da mijinki ya rinqayi Mata
da baki da lfy kina asibiti kina karbar magani har tayi sabo da maza Addah hanunka bai taba
rubewa ka yankeshi ka jefa..."
Daga masa hannu tayi tace “ka tsame bakinka daga abinda ya shafeni nida Habibah wlh da
basan irin yayan dana haifa kenan a duniya gara inyi barinsu...." Rufe bakinta tayi saboda
shigowar Habiban ta tsugunna ta riqe qafarta tace “gani gabanki mahaifiyata wlh duk hukuncin
da kika yankemin idan har zai zama sauqi da sassauci wa zuciyarki zan karbeshi nasani Addah
nayi kuskure amma duk da haka Addah ki tausayamin kiji qaina rahamarki ta kwaranyo cikin
rayuwata bani da kowa saike kuma bani da komai saike kw kadai nake tsammanin jinqai da
rahma daga gareki..."
Tureta tayi ta miqe zata fice daga dakin tayi saurin kamota tace “na roqeki da girman Allah ki
yankemin hukunci Koda na kisane Addah duk duniya babu wanda zaice yafini baqin cikin
taskun da rayuwata take a ciki Addah bantabajin kaico da baqin cikin halittata a matsayin ya
mace ba kamar yau...." Hankadeta tayi tace “na tsaneki Habbatullah na tsani ganinki Kin cuceni kin gurbatamin zuri'ata
kinyimin tabon da bazan taba mantawa dashi ba kaico Habbatullah kaico da haihuwar asara
irinki danasani da mahaifinki ya bata zubar da cikinki nayi da wannan mugun tabon da kikayiwa
zuciyata Allah ya is....."
Saurin rufe mata baki Ibrahim yayi yace “Haba Addah da wanne kikeso taji ne don Allah ki
sassauta mata mana kowanne bawa baya wucce qaddararsa kece kike fada mana haka
kullum...." Katseshi tayi da cewa “wlh idan Habibatullah bata bacemin daga qwayar idona ba
saina tsine Mata ta qara tambadewa ta lalace gabadaya" Miqewa Habbatullah tayi idanunta na shararar da hawaye tace “indai hakan yayi miki nima
yayimin Addah amma ki sani duk halin dana tsinci kaina a ciki nan gaba babu hannun Pappa
kece me ruwa da tsaki domin kema uwar da kika haifeni kin gujeni kin qyamaceni Addah
bazanji ciwo ba kuma bazanji haushi ba idan mutanen duniya gabadaya zasu qini"
Tana gama fadin haka ta juya ta fice da sauri ta dauki akwatin ta tana kallon gdan tana kuka a
ranta tanajin anya kuwa ita ba yar tsuntuwa bace, biyota Ibrahim yayi ya riqe akwatinta yace
“wlh babu inda zata Addah saidai ke ki tafi tunda ke kinsan inda zaki ita kuwa fah Ina ta sani
hannun wa zata qara fadawa? Haba haba Addah wannan rashin adalci ne kiji tausayinta mana
a yanda take dinnan ga dare yariga yayi"
Qwacewa tayi tace “wlh tallahi saina fita daga gdannan Ibrahim gara ta kwana cikin salama
koda ni zan kwana a saman juji nasani duk yana cikin qaddarata"
Ficewa tayi da sauri Ibrahim yabita yana roqonta ta dawo ta tsayar da Napep ta sanya kayanta
ta juyo ta dafa kansa tace “kada ka damu qanina zan shiga cikin garin Gombe zan nemi gida na
kama kafin Addah ta sauko nayiwa kaina dakai da Addah alqawarin bazan qara aikata wani abu
na sabo ba insha Allahu ka tayani da addu'a kaji?" Hawayensa ya share yace “amma aunt...."
Rufe masa baki tayi tace “nafi buqatar farin cikinta da nawa kaima kayi biyayya da farin cikinta
kaji Addah tariga ta rantse idan na samu gda zan fada maka sai kazo ka gani"
Kudi ta zaro masu yawa a Jakarta ta basa tace “ka kula da kanka kafin muyi waya kaji qani na"
Napep din ta shiga tana hawaye tana daga masa hannu shima yanayi yana daga mata harta
qule, sunyi tafiya me tsayi kafin su fito gari da yake darene qofar wani hotel yakaita ta sauka ta
biyasa ta shiga ta kama daki suka bata mukulli ta shige ciki tayi wanka ta fada gadon tana rera
kukanta me ban tausayi tanajin wayarta tanata ring amma takasa duba ma wayene saboda ji
takeyi kamar ta kashe kanta ta huta da wannan quncin rayuwar, tambayar kanta takeyi ita
yaushe zatayi farin ciki ne a rayuwarta?.........
*UMMUH HAIRAN CE...✍*
[7/29, 9:18 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ *DUBAI* ✈️
*PAID BOOK*
_Idan kinsan baki biya ba kada ki karanta in kin karanta keda Allah, VIP 600 SINGLE 200_
_Account number_
_0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar_
_GTB_
_Ko katin waya MTN ta wannan number_
_09013718241_
_Yan Niger zaku turo katin Orange Wanda zaiyi daidai da 600 dinmu idan VIP ne idan SINGLE
ne wanda zaiyi daidai da 200 dinmu ta Nigeria._
*Episode 30*
*END OF THE PART ONE*
Ta jima a kwance tana tufkawa da warwarewa kafin ta miqe ta dauro alwala tayi nafila raka'a
biyu ta me neman gafarar ubangijinta a bisa laifukanta da suke bibiyar rayuwarta.
Wannan dare bata kwanta ba sai bayan sallar asuba ta koma ta kwanta tanajin zuciyarta tanayi
Mata zafi tashin hankalinta shine batasan inda zata nufa ba babu inda tasani a cikin garin
gombe balle tace zataje, tananan kwance har azahar tanata juyi wayarta da take charge ta qara
bugawa tayi qarfin halin miqewa daqyar ta dauko wayar tayi murmushin yaqe tace “Ibrahim Ina
cikin aminci kayi hqr kaji don Allah duk ranar da Addah ta sauko ta yafemin ta yarda da
qaddarata a matsayin tata ka fadamin kaji..."
Ta qarasa maganar cikin shassheqa numfashi Taheer ya furzar yace “yanzu kina ina?" Saurin
sauke wayar tayi saboda ko muryarsa bata qaunar ji shine sanadin faruwar komai, tsorone ya
kamashi.
Itakuma ta manna wayar a qirjinta ta koma ta kwanta tana sauke numfashi wannan rana azumin
dole tayi kiran duniya Taheer yayi mata taqi dauka sai bincike suka shiga Allah yasa dan Napep
din daya daukota na gidane shine yayi masa Jagora har hotel din ya bashi kyauta me kauri ya
shiga ciki Koda aka kirata aka sanar da ita mijinta yazo cewa tayi batada appointment dashi.
Saida ya tashi hankalinsu sannan suka rakashi dakin nata yayi knowking bugu biyu ta taso
tunaninta abinci aka kawo mata da hijjabinta qato har qasa ta bude, ja tayi da bsya da sauri
tana danna qofar ya riqeta da sauri ya danna ya shiga ya mayar ya rufe yana kallonta cikin
tsananin qaunarta da tausayin kansu ya matsa gabanta ta janye tace “don Allah ka tafi Taheer
wlh banason ganinka banaso Taheer kaje kawa...."
Cafkarta yayi ya hada bakinsa da nata tanata qoqarin qwacewa shikuma yana qara shigewa
jikinta har suka zube a gadon ya janye da sauri yace “ohhhh meye yasa zakiyimin haka habeey
zuciyata tana gurinki ke kuma kina qoqarin turamin takaici da wanne zanji ne ya kikeso nayi"
Janyewa ta sakeyi tace “nikuma