DUBAI PART 1 BY OUM HAIRAN.pdf

Author :  Oum Hairan Category :  Taskar Novels

Chapter   11 / 14

30K to 33K   out of 39.9K words


yankamin lasisi na shiga na fantsama duniya naga me take cewa"




Dariya Alh yayi yace “kin nemawa kanki mafita yanzu dama nan da sati biyu jirgin Dubai zai
daga sai ki shiga sahu, wani ihu ta saki ta rungumeni nikam kallonsu kawai nakeyi.
Zamanmu a gdan Alh Yunusa gwanin dadi da farko ya rinqa kawomin maza yan duniya amma
Dana nuna masa bana raayi sai ya qyaleni ina kallo zaazo a dauki Aysher bazata dawo ba sai
safiya ban taba damuwa ba har sati biyun ta cika ya kawo mana Visa biyu yace “abinda yasa
kema Habeey na yanke shawarar na kaiki Dubai saboda can Commercial City ne ko wacce irin
sana'a kika zaba zaki siyar Visar Shekara uku akayi muku zaku biyani a cikin shekara daya ke
na zaba miki gdan aiki Koda yake tare xan hadaku da Aysher a hankali kema saiki waye"




Hakanan muka sake lulawa sai gamu a *U.A.E* wato *United Arab Emirates* *DUBAI* qasar
data zama mafarin mummunar qaddararta dazan mutu da tabonta qasar dana hadu da mutane

ma bambamta qasar dana hadu da abubuwa masu taba zuciya da gigita tunani.
Wasan ya farane daga ranar da muka isa gidan aikinmu babban gidane me bangarori daban
daban cikin saa sai aka kaimu bangare daya nida Aysher ita tana kula da yaran gdan guda biyu
ni kuma matar gdan ta bani aiki mafi wahala wato kula da gyaran bangaren mijinta dana qanin
mijinta. Muka fara aiki ka'in da na'in hanasa wasa a lamurana Taheer, kasan meye illa ta? Kyau Taheer
mutane da yawa sunason kyau amma ni nawa saiya zamemin masifa kuma gudumar tarwatsa
rayuwata kaico da kyauwu irin nawa me daukar hankalin maza Taheer kullum inajin dama Allah
yayini a cikin jinsi mafi muni qila dana tsira daga rudin zuciya da rudaddu kuma shagalallun
mutane.........





*UMMUH HAIRAN CE...✍*
[7/25, 1:55 PM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ *DUBAI*✈️

_Subscribe discount of payment_

*_25/7/2020_*



_Kamar yanda sanarwa ta fita a pages din da suka fita kafin wannan, littafin *DUBAI* ya koma
na kudi da sabon farashi VIP 1k single 300_

_So abisa qorafe qorafen da na rinqa samu daga masoyana sunce kudin yayi musu tsada
wannan dalilin yasa na rage kudin daga yanda na sanar a baya, VIP dana ambata masa 1k ya
koma 600 single dana ambata 300 ya koma 200_



_Idan kinada interested zaki iya biyan kudinki ta wadannan hanyoyin_

_Account number_

_0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar_

_GTB_

_Ko katin waya MTN ta wannan number a WhatsApp_


_09013718241_

_Saiki tura avidance of payment dinki ta wannan number_

_09013718241_



*Episode 22*



Farko zaman namu kamar zaiyi dadi, dawowar Nazan gdan shine mafarin warwarar duk wani jin
dadina.
A Scortland yake karatu shiyasa baya dawowa sai shekara shekara, zuwanmu gdan yayi daidai
da lkcn dawowarsa, satinmu biyu a gdan ya dawo, sunata rungume rungumensu nikuma inata
kallonsu, saida suka nutsa ya shiga bangarensa matar gdan tace nabisa da kayansa.
Hakanan na dauki kayan zuciyata tana rayamin abinda ya faru Dani a Saudi zai iya sake faruwa
dani, hakadai na daure na isa bakin qofar na taba qararrawar batare da batamin lkc ba yace na
shigo.




Na bude qofar na shiga na ajiye kayan tare da juyawa zan tafi kadai naji ya riqoni ta baya, na
tsaya da sauri ya zagayo gabana yace “barakillah" tare da sakeni ya nufi bathroom dake ya iya
turanci sosai yacemin na fito masa da kayan da zaisa.
Hakan na fito masa da kaya na koma na zauna babu kunya ya cire towel din jikinsa ya tsaya tik
a gaban mirror nikuma na rintse idona gabana na bugawa da qarfi tunda nake a duniya bantaba
karo da mara kunya irin Nazan ba.
Banyi aune ba saiji nayi ya riqo hannuna yace “ki shafamin cream" wata muguwar faduwar gaba
ce da bantabajin irinta ba ta dirarmin a Raina nace wannan yafi kowa ma dama na sani zamana
nayi a Saudi.




Sake shigewa jikina yayi yana furzar da numfashi ya damqo hannu na ya dora saman
duwawunsa yace “ahhhhh" tare da matseni a jikinsa ya bude idonsa akan fuskata dake malalar
da hawaye yace “bana sha'awar mace nafi sha'awar namiji amma naji zan iya tarayyah dake"
Janye hannuna nayi ya sake kamawa ya matsamin man a hannu na yace “bana yiwa mutum
dole ki yarda ki bani komai nima zan baki komai kinji" karkada masa Kai nayi hakan ya bashi

haushi ya tureni na fadi ya fara shafa mansa bayan ya gama ya kalleni yace na fice masa.
Ficewa nayi na nufi dakinmu Ina shiga na tarar da Aysher tana shiryawa dake ita dama bata
kwana a gdan nace “don Allah Aysher ki zauna ni tsoro nakeji shima wannan Nazan din dan
iskane"




Dariya sosai Aysher tayi tace “har yanzu da sauranki nikam yau idan na tafi ma bazan dawo ba
dan wani Dan majalissar tarayyah na saqalo baki ganshi ba kyakkyawa, yamace zai kamamin
hotel.
Riqeta nayi nace “aa kada ki yarda cutarki zaiyi nikam ko shekaran jiya da mukayi waya da
Addata tace kada na kuskura na bawa namiji kaina don kudi nayi iyakar yina wajen Kare kaina"
Dariya Aysher take yimin Saida na rufe bakina tace “ashe kuwa kina ruwa yarinya wlh garama
kiyi ki samu kudinki ki biya buqatun rayuwarki saboda anan dai a Dubai bazaki tsira ba Habeey
duk wacce kikaga ta zama karuwa baso take ba wata qaddararta ce haka wata son zuciya wata
kuma sanadin talauci"



Zama nayi inata saqawa da warwarewa bangarorin zuciyata suna fadamin tunda nan ba masu
sa ido bane nabi Aysher mana mu tafi in yaso na nemi wani abunyin acan, jikina da kwanyata
basu bani qwarin gwiwa ba saboda haka na kwanta naja bargo saboda ciwon da kaina yake
yimin na kwanta ta gama shirinta ta fice daga gdan nikuma zazzabi me zafi ya rufeni. Inanan kwance har dare ya raba inata juyi bacci yaqi zuwarmin sai haki nakeyi dake dama tun
Ina qarama inada ciwon sarqewar numfashi wato Athmer, ji nayi an bude dakin an shigo so ban
wani damu ba saboda wani lkcn matar gdan tana shigowa.




Jin an mayar da qofar an rufene yasani bude idona da sauri amma duhu bai bani damar ganin
waye ba jinayi ana lalubata nayi saurin yunqurawa zan miqe ya riqemin breast dina daya.
Wata azaba ta ratsani na saki qara yayi saurin kifowa jikina tare da qara damqe nonona nikuwa
azaba sai ratsani takeyi Ina dukansa ta ko Ina har yayi nasarar rabani da kayana shima ya cire
nasa ya fara qoqarin budani ya shigeni ta qarfin tsiya.
Ihuna ne ya janyo hankalin me gidan ya nufo dakin da sauri ya bude ya shigo tare da haskemu
da fitila hakan yasa Nazan sakina na miqe da gudu babu komai a jikina na nufi inda me gdan
yake a guje na riqeshi Ina kuka.

Tureni yayi ya dauki wani mayafi ya yafamin ya fara yiwa Nazan fada nanfa suka rinqa
hayaniyarsu nidai Allah ya bani saa na zura rigata ko bra babu na samu na silale na tafi wani
bangare a bayan gdan.
Anan na qarasa kwana da safe na shiga gdan nayi ayyukana me gdan ta kirani ta bani kudi tace
naje nayo mata cefane naje nayo na dawo na kwanta har yanzu banida lfy.
Ina kwance wayata ta fara ring na daukota gabana na faduwa na daga muryar Pappa naji yace.
“sai ayita kiran wayarki baki dagawa to ki turo da kudi uwarki tana fama da hawan jini da ciwon
qoda ance maganinta kadai na farko dubu dari biyu da ashirin nikuwa a halin yanzu ko naira
dari biyu da hamsin banida ita"




Duk da ciwon qirjin dake damuna Saida na zabura na miqe saboda Addah tanada muhimmanci
a rayuwata banason rasa Addah nace.
“Nashiga ukuna Pappa Ina kudin da nake turo maka a siya Mata maganin mana a ciki abar
ginin tunda ba dole bane..." Tsawa ya dakamin yace “kaji shashasha wanne gini duk tabi takan
kudin ta tumurmushe har wani farfesu takeyi ita yarta tana qasar waje"
Nasani kwarai sharrinsa ne saboda haka nace “wlh Pappa banida ko dubu hamsin watana biyu
da fara aiki kuma Alh Yunusa nake biya kudinsa tukunna amma ka ranta in yaso saina nema na
turo maka"




Fada ya rufeni dashi kamar zai ari baki yana cewa “Ke komai naki babu albarka a cikinsa kin
tsaya biyewa uwarki kinje inda arziki yake kin kasa diba waike tsoron Allah, meye amfanin
kyawunki meye amfanin quruciyarki da bazata iya yimiki maganin matsalarki ba, nan Alh
Yunusa ya kirani yake fadamin manyan mutane ne idan sukaga hotonki sukeson harka dake
amma dake jinin Hajar ne ns tsiya ke yawo a jikinki kinqi basu hadin kai.
To nidai babu abinda ya dameni uwarki ce ba uwataba nanda awa ashirin da hudu idan baki
samu kudin nan kin turoba labari zai iya canzawa matsiyaciya kawai"..............







*UMMUH HAIRAN CE...✍*
[7/25, 8:27 PM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ *DUBAI*✈️

*PAID BOOK*

*HAƘƘIN MALLAKAR*
             
*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
*(UMMUH HAIRAN)*

*_6/7/2020_*

_Kamar yanda duk Wanda yaga status dina na yau ya sani cewa, littafin *DUBAI* ya koma na
kudi  da sabon farashi VIP 1k  30 people's kawai nakeso single 300_

_Idan kinada interested zaki iya biyan kudinki ta wadannan hanyoyin_

_Account number_
            
     _0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar_

_GTB_

_Ko katin waya MTN ta wannan number a WhatsApp_
         
_09013718241_

_Saiki tura evidance of payment dinki ta wannan number_
          
_09013718241_



*Episode 23*



Wannan kalma ta matsiyaciya tanayimin ciwo musamman idan Pappa ya dangantata da
Addana, wannan rana ban iya hassala komai ba saboda damuwa da tashin hankalin da nake
ciki.
Idan na tuna Addana tanacan babu lfy Kuma babu kudin da zaa siya Mata magani sai naji
hawaye yana shararomin qannena da ya kasance Addah ce kawai gatansu suna fadomin
kukana yana qara tsananta.
Qarfin hali nayi na tashi naje gurin madam dita na tsugunna Ina kuka ta kalleni tare da
tambayata matsalata, yanda tayimin mgnr ya sanyaya zuciyata na karkace na zayyane Mata

damuwata ta nuna alhininta sosai.




Nan na dada Mata alfarmar da nake nema ta albashina na wata uku zan tura a nemawa
mahaifiyar tawa magani, jummm tayi na dan lkc sannan ta dago ta fara yimin dogon larabci
wanda bashi nake buqata ba sannan tacemin ita yanzu bazata iya bani kudi ba saboda Nigery
sun damfareta da yawa. Haka na miqe jikina babu qwari na koma daki na dasa sabon kuka ganin kukan bazaikai min ba
na tuna shawarar da Addah take bani kullum idan na fada Mata cewa banason zaman
qasashen nan matsayin bauta.
Miqewa nayi nayi alwala nayi sallah raka'a biyu na dauki qur'ani Ina karantawa inajin wani sanyi
yana zagaya zuciyata a hankali na miqe na dauko wayata da taketa ring.




Nandanan annurin fuskata na halitta ya dauke na danna wayar na kara a kunne na baiko amsa
sallamata ba yace “sunce nanda awa goma sha shida zata iya mutuwa kudin ma ya qaru daga
dari biyu da ashirin ya koma dari uku da hamsin saboda harda aikin tsiron mahaifa zaayi Mata"
Qitt ya yanke wayarsa na zubd saman carpet din Ina furta innanillahi wa Innah ilaihirraji'un
hawayen ma ya tsaya ya daina zuba a idanuna sai tafasar zuci kawai wani tuquqi yana tasomin
daga qasan maqoshina wanda nakejin kamar zai fito da raina.
Inanan zaune cikin tunanin rashin makoma wayata ta soma Ring kamar bazan dagaba nadaiyi
qarfin halin tashi zaune na dauko wayar number Aysher ce na sauke ajiyar zuciya tare da
karawa nace “Aysher Ina cikin matsala"




Salati tayi tace “badai fyade Nazan yayi miki ba ko?" Numfashi na sauke nace “wlh da zaiyimin
ya bani abinda nake buqata yanzu da zan bashi Aysher Addana zata mutu saboda rashin
kulawar Pappa duk kudin da nake turawa ya cinye yanzu kudin magani ya gagaremu"
Ajiyar zuciya Aysher tayi tace “kema kinada matsala Habeey kinada hanyar da zaki samu duk
abinda kike buqata amma kin matse abu a cikin cinya yanzu dai ba wannan ba kizo muje
Beachwood Jabir ne yayi baqo dan governor Usman Waziri ne na Bauchi Amininsa yazo shine
zamuje taronsa"



Numfashi na sauke nace “nidai inajin tsoro Aysher...." Katseni tayi da cewa wannan itace kawai

mafitarki kiyi ki shirya ki fito yanzun zamuzo"
Kashe wayar mukayi a tare na sake zaman dirshan har zuwa wani dogon lkc wayata ta qara
dokawa na daga tace “na dauka zamu tarar dake a waje" miqewa nayi na dauki doguwar rigata
na saka na fito a salube na dauki wayata da jakata da wasu cikin kayana.
Da nasan inaso saboda na riga na zabi duk abinda qaddara tazomin dashi yau duk abinda zai
faru saidai ya faru amma nima na gama zaman gdan aiki zaman hantara da gyara da
wulaqanci, a wannan rana na haqiqancewa kaina cewa a yau duk wanda ya nemi wani abu a
gurina saina bashi indai Addata zata tashi taci gaba da rayuwa a doron duniya.



Madam dita tana sama na fito naci karo da Nazan yana saukowa yana ganina ya nufoni da
sauri yana fadin “Habeebaty Ina zaki?" Bai samu ko kallon tsiya a gurina ba balle na arziqi na
qetareshi na wucce na fito harabar gidan Ina fitowa na hango wata zundumemiyar mota me
numfashi a gabana na. Isa nayi gaban motar Aysher ta budemin na kalleta tayimin murmushi tare da rungumeni tace
“wow! Habeey ke kadara ce me tsada" yaqe nayi na shiga bayan motar saurayin Aysher Jabir
sai kallona yakeyi nace masa “sannu" daqyar ya iya amsawa idonsa na kaina Aysher tace “ya
kaga babyn na fada maka babban kayane ba matar talaka bace"



Ajiyar numfashi yayi yace “muje dai tukunna inajin tsoron jizgin Taheer duk yanda kike tunanin
mutum me izza Taheer ya wucce nan sannan shi a tsarinsa baya bare budurwa fah.
Gabana dokawa yakeyi saboda jin hirar tasu da nakeyi duk akaina ne, haka har muka isa
airport sunata hirarsu duk akan abokin nasa nidai bana sanya musu baki saboda ni ba
ma'abociyar shiga abinda babu ruwana bace.
Mun dan jima a airport din kafin fasinjan su fara fitowa na zuba musu ido Ina kallonsu har suka
kusa qarewa sannan naga wani matashin Saurayi me cikar zatin halitta Gant kyakkyawa
wankan tarwada ya fara saukowa riqe da yar qaramar akwatu a hannunsa, zuba masa ido nayi
Ina kallonsa shima idonsa akaina yake duk da bana fahimtar hakan saboda baqin glass din
idanunsa.




Jabir naga ya nufeshi da sauri sun rungume juna tare dayin kissing kuncin junansu sukayiwa
juna murmushi Aysher ta miqa hannu domin karbar jakar hannunsa amma saiya janye tare da
daga mata hannu alamar jinjina ya miqawa Jabir ya karba sannan suka iso gurin motar nidai
inata kallonsu cike da sha'awa da Kuma faduwar gaban dana rasa dalilinta. Bude masa gaban motar Jabir yayi ya shiga sannan shima ya shiga Aysher ta tabani nayi firgigit

daga duniyar tunanin dana lula daidai lkcn da wayata ta dauki ruri muka shiga motar lkc daya
da Aysher sannan na dannan pick na fara mgn da cewa “Pappa meye kuma ya faru?" Katseni
yayi da cewa “saura awa shidda uwarki ta karci qasa bisa sakacinki idan ta mutu kece da asara
sannan tace na sanar dake indai baki samo kudin da kika ceto rayuwarta ba cikin sa'o'innan da
suka rage nononta da kikasha bata yafe miki ba...........






*UMMUH HAIRAN CE...✍️*
[7/26, 10:47 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ *DUBAI*✈️

*PAID BOOK*

*HAƘƘIN MALLAKAR*
             
*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
*(UMMUH HAIRAN)*


_Don Allah idan kinsan baki biya ba kada ki karanta VIP 600 single 300_

_Idan kinada interested zaki iya biyan kudinki ta wadannan hanyoyin_

_Account number_
            
     _0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar_

_GTB_

_Ko katin waya MTN ta wannan number a WhatsApp_
         
_09013718241_

_Saiki tura evidance of payment dinki ta wannan number_
          
_09013718241_

*Episode 24*


Wani mugun shock naji tare da zuba sun fara ketomin a hankali nake furta Allahummah la
sahla...." Har zuwa qarshenta ni kadai nasan irin zugin zucin da nake fuskanta a daidai wannan
lkcn.
Rintse idona nayi na dora kaina saman bayan kujerar inajin wani zazzabi me dafa qashi yana
saukomin bansan ina muka nufaba Saida aka tsaya suka fita gabadayansu wannan baqon ya
cire glass din idonsa ya sauke qananun lumsassun idanunsa akaina kamar me nazarin wani
abu game dani. Aysher ce ta janyoni tace “tashi muje muci abinci mu wucce gda naga kamar na takura miki
ko?" Hadiye wani Abu nayi me nauyi sannan na zuro kyakkyawar qafata qasa na sauketa na
miqe baqon ya bini da kallo tun daga sama har qasa.




Ya girgiza kai kawai yayi gaba Jabir yabi bayansa muma muka rufa musu baya sun danyi
gaishe gaishensu nidai ko kalma daya bata shiga tsakaninmu dashi ba har muka isa gurin cin
abincin.
Sukayo order kowa ya zabi abinda yakeso ni kuwa lkcn da aka miqomin menu din girgiza kai
nayi kawai na kalli Aysher hawayen da naketa qoqarin shanyewa suka zubomin karaf idanuna
ya fada cikin na baqon ya lumshe idonsa tare da sake budewa a kaina muka sake hada ido.
Qasa nayi da kaina saboda wani yanayi da nakeji game da baqon,

11 / 14