Chapter 12 Reading ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE M SHAKUR .pdf HN Novels

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE M SHAKUR .pdf

Author :  M Shakur Category :  Taskar Novels

Chapter   12 / 37

33K to 36K   out of 109K words

yawuce yafita daga kitchen din itama tabiyoshi tafito, Baba
dake kallonsu yace “go and get ready Khairy malamin ki zaizo by 12” sama tawuce agurguje ta
shirya tafito falo lokacin ba kowa Baba yakai Mama dakinshi, by 4 malamin yatafi su Manaf
suka fita da ita basu dawo gidan ba sai around 10 tana zuwa lafiyan gado tabi.

Gabaki dayan gidan yau basuyi bacci ba sabida yanda jikin Mama yay tsanani, amai tadingayi
na jini both tabaki da hanci, jikinta yay zafi sai maganganu take dabama sa ganewa, saida
safen nan bacci ya dauketa.

6 ta tashi tana kallon agogo mamaki ma take ya akayi take lattin tashi late this days, wayanta
dataga yay haske yamika hannu tadauka 2miss calls tagani na Aliyu saikuma message
dayamata bude message din tayi. “I miss you” murmushi tayi ta ijiye wayan sanan ta tashi
tawuce bayi wanka tayo tareda alwala Dan yau tanada morning lectures, tana fitowa tasa kaya

tai salla sanan tabude kofa tafito su Ya Manaf tagani a falon sama kwakkwance kan kujera suna
bacci, mamaki tayi amman ta tabe baki tai hanyar dakin Mama bude kofan tayi zaune taga
Baba kan kujeran dakin yabude Al Qur’ani yana karantawa itakuma Mama na kwance kan gado
tana bacci yarufa mata bargo, saida yakai ayar sanan ya kalleta tace “Good morning Baba”
murmushi yamata yace “morning daughter, Mama is sleeping jiya dukanmu bamuyi bacci dawuri
ba munata hira yayyinki na nan falo suna bacci suma” gyadamai kai tayi tace “eh nagansu”
Gyadamata kai yayi yace “jeki breakfast yau Monday 8 kikeda lectures i want you to be serious
kigama da good grade” gyadama Baba kai tayi sanan tajuya tafita tana kallon fuskan Mama
dake bacci peacefully sanan tasauka falo ahankali, kitchen taje tea tadafa musu duka sanan ta
soya chips zama tayi dinning zataci amman hakanan taji takasaci jikinta yamata wani irin sanyi
kodan ita kadai ke yin breakfast dinne oho, tashi tayi tawuce sama tana kallon su Manaf da still
ke bacci ta shiga dakinta dan shiryawa.


Shiryawa tayi tsaf cikin wani black abaya mai bala’in kyau tai rolling gyalen akanta ko kadan
batai kwalliya ba but she looks kaman wata Somalian queen, jakanta tadauka sanan tafito,
dakin Mama tabude takalli Baba dake karatu har lokacin tace “Baba natafi” saida ya idasa Ayan
sanan yadago kudi yaciro yamika mata karba tayi tana murmushi tace “thank u Baba, kacema
Mama natafi idan ta tashi bye” murmushi Baba yayi yace “to yarinyar Mama” maida kofan tayi
tarufe yasauke ijiyan zuciya Noo yagaji Khairy deserve to know Maman ta is sick, he’s tired of
hiding it from her, bari Maryam ta tashi zai gayamata is time sufadi ma Khairy, Khairy is grown
up she can handle it.


Fitowa tsakar gida tayi tana tafiya ahankali hakanan jikinta kawai yamata sanyi yasaki tarasa
mesa kawai she’s feeling sad and week ma yanzun nan, karasawa wajen motanta tayi Adamu
na shiga itama tana shiga baya daidai sunajin horn mai gadinsu na budewa, motar Baffan ne ke
shigowa gidan Hafiz ke tuki, sai motar Ammi biyeda su da driver ke parking sai kuma motan
Mom, bude kofan motar tayi tafito tana murmushi da saurin ta tai wajen motan Baffa, daidai
lokacin Baffa na bude baya yana fitowa yana mata murmushi yace “yan makarantan bokoko”
dariya tadanyi tace “Baffa ina kwana, Ya Hafiz Baban Baby ina kwana, Laaaa Ya Hassan da Ya
Hussain harda ku akazo yau” kafinma suyi magana Baba yace “wuce tafi school karki latti”
yanuna mata motarta da Adamu yatada yana jiranta shiga motan tayi tana waving Mom dake
saukowa daga motanta dan har yanzu motan Ammi bama abude ba kuma bamata iya ganin
cikin banda driver shima ta glass din gaba taganshi dan motan tinted ne, jan motan Adamu yayi
suka tafi nai gadi yamaida gate din gidan yarufe daidai lokacin Baba da Manaf suka fito.


Ahankali aka bude kofar motar Ammi, wani clean white kafane ya sauko dake sanye cikin wani
hadadden sandals na Prada black, nails na kumban kafan are so fresh and white, gently
yakarasa saukowa daga cikin motan yana yatsine fuska yana gyara bakin sun glasses na
idanunshi na kampanin rayban, yana sanye cikin milk color yadi dayay dinkin jumper dashi daya
bala’in amsan jikinshi, yanada tsayi dan wajen gabaki dayansu yafisu tsawo babu wanda baya

ganin kanshi, yanada cika dakuma fadin kirji, kana ganinshi kaga Ammi kaman tai kaki ta tofar
saisa yafi kannenshi kyau dansu Hafiz da Baffa suke kaman, yanada wani irin black very very
dark saje dake kyalli kaman na bature, lips dinshi is so pinkish, gashin kanshi a kwance suna
shinning, hannunshi ya daura agogo Rolex akai, ita kanta Ammi anytime ta kalleshi she feels
proud da Allah yabata Zayn as her son, Zayn is definition na handsome guy, kyakkyawan namiji
da babu macen data isa tamai yanga, ganin Baba yataho wajensu yasa ahankali yakai
hannunshi yazare eye glasses na idanunshi yadan sunnar da kanshi kasa Baba nazuwa cikeda
mamaki yakama hannun Baffa yace “d’ana Zayn nake gani haka” murmushi daga Baffa har
Ammi da Mom sukayi, Baffa yace “da asuban nan yashigo gida” anatse Zayn yace “ina kwana
Abba”? Hannu Baba yabashi ahankali yasa nashi hannun cikin na Baba, daidai sukaji muryan
Maheer yana ihu. “Babaaa” Dawani irin sauri Baba yasaki hannun Zayn yay ciki Baffa da
kowama suka bishi sama sukayi, dakin Mama Baba yashiga yatarar da Mu’az yarike Mama
dake aman jini sosai tai lakur babu karfi kodaya ajikinta, wajenta Baba yayi yakamata daga
hannun Mu’az yadau tissue yana share mata bakin ganin tadena aman, shigowa dakin Mom
tayi takalli Baba tace “Alhaji bari mu chanza mata kaya” girgiza kai Mama tayi ahankali tana rike
Baba gam batare datai magana ba, kallonta yayi sanan yakalli Mom yace “abarshi tukunna”
karasowa gaban gadon Baffa yayi yaja kujera yazauna yana kallon Mama dabata iya bude
idanunta da kyau yace “Maryam mutafi asibiti”? Girgizamai kai tayi ahankali, ajiyan zuciya
yasauke yay shiru, shigowa ciki Ammi itama tayi tasami gefen gadon tazauna ahankali tana
kallon Mama murya chan kasa tace “kina bukatan wani abu Maryam mezaki ci?” Girgizama
Ammi kai tayi hakan yasa itama tai shiru, ahankali Baffa yajuya yakalli Zayn daya tsaya chak
abakin kofa shima yana kallon Mama sanan Baffa yajuyo da kanshi ya kalli Mama yace
“Maryam ga Zayn dakika ce nakira miki yazo” dan yunkurowa kadan tayi da duka karfinta,
dasauri Baffa ganin haka yasa yace “Zayn come” karasowa gaban gadon Zayn yayi ahankali
sanan gently ya tsugunnawa gaban gadon yana kallon Mama dake kallonshi kallon dakasan
baa hayyacinta takeba yace “Mama I am here” hannunta daya tacire daga jikin Baba data
rikeshi gam gam jin haka yasa Baba yatayata , kama hannun Zayn tayi hawaye yazubomata
daga idanunta sanan kadan tabude bakinta dasauri Zayn da zuciyanshi ta katse yace “Mama I
am here mekike so tell me” yakai kunenshi saitin bakinta, magana tashigamai a kunne wanda
harta Baba dayake rikeda ita baiji abinda ta Fadima Zayn ba sanan takoma jikin Baba ta
kankame shi, Maheer dataga yana kuka sosai mara sauti abakin kofan ta kalla hannu
tamikamai ahankali yataso yazo kawai kankameta yayi yahau kuka sosai ahankali yace “Mama
dan Allah kiwarke, Mama please karki mutu kibarmu” motsi sosai bakin Mama yafara hakan
yasa Baba ya janye Maheer daga jikinta kankame Baba tasake yi takama hannunshi tarike gam
gam kaman dats the only thing dake mata dadi sanan cikin wata kalan murya dabata fita da
kyau dan hakoranta sun datse tace “Baffa, Ammi, Mom, dukanku yarana ina rokonku gafara ku
yafeni idan nataba bata muku, idan Ummulkhair…..” wani kalan nishi tayi tana kuka sosai
dabayama fitowa sosai tace “kuce mata nace tayakuri tayafema Maman ta, i hide everything
sabida nasan idanda tasan banda lpy bazata dauki abin da kyau ba, Baban Manaf” tai maganan
tana kankame Baba tace “ka kulamin da Khairy dan Allah, Baffa nabaku amanan Khairy da
duka yarana, Khairy is fragile, and innocent please ku rikemin yarinyata amana ita nafiji araina,
zanbar duniyan nan amman Khairy ce araina sabida ita kadaice diyata mace yayyinta maza ne”
ajiyan zuciya Mama tasake saukewa sanan ahankali tace “idan narasu Khairy taki kwantar da

hankalinta kabata Littafin nan danabaka ka ijiye mata Baban Manaf” gyadamata kai Baba yayi
ahankali hawaye na taruwa a idanunshi Baffa ya bubbugamai kafa alamun karyay kuka,
ahankali Mama tace “Baffa kamishi aure dazaran na rasu banson yarana su rasa uwa, Manaf
kurike Matar da mahaifinku zai aura kaman ni kada kubata ciwon kai” gyadamata kai Manaf
yayi, Ammi kallon Mu’az yayi dake bakin kofa tayi ya tsugunna idanunshi sunyi jajir tace “zo
wajen mahaifiyar ka Mu’az” mikewa yayi tsaye da kyar shigowa yayi zuwa wajen gadon kawai
yadaura kanshi kan gado yadaura hannunshi kan nata dan that’s what Maheer da Manaf duk
sukayi, yanda tazo tana nishi yasa Baffa ya gyadama Baba kai ahankali Baba yasoma karanto
mata kalman shahada, saukar da kanshi kasa Zayn yayi, ahankali Mama ta amshi kalman
shahadan karfe 12:03 daidai tacika da imani daidai lokacin Khairy ta tashi daga kan kujera sun
gama lectures zasu fita jitayi kafafunta sunyi sanyi kawai tai baya zata fadi kaman tai paralyze
Rabi dake bayanta ta tareta tace “ke Khairy are u okay” ? rike Rabi tayi tana taba kirjinta tace
“gabana fadi yakeyi sosai kafana ba karfi” zaunar da ita Rabi tayi tace “kinyi breakfast kuwa”?
Girgiza kai tayi hakan yasa Rabi da sauran kawayenta sukai dariya tace “yunwa ce muje kici
abUinci”.



2️⃣5️⃣



Almost good 10min na silent ne yacika dakin, at this point Baba jiyayi kaman shima yamutum ne
dan he could feel yanda hannayenta suka sassandare ajikinshi kasa koda motsi yayi hakan
yasa Baffa yay taking over, daga Baba tsaye yayi, ahankali Baba yasauke kanshi kasa yana
kallonta in disbelief, yadade ahaka sanan yakai hannunshi ya kulle mata idanu kafin yaja
bargon yarufeta saikawai yazauna akasa dabas baimasan mema zaiyi ba dan he’s still in shock
idan ya kalli su Manaf daduk suke kuka saiyaji zuciyanshi yakara tsinkewa, kafadanshi Baffa
yakama ya matsa hakan yasa ya fuzar da iska kafin ahankali yasa hannunshi yakamo su Manaf
daya bayan daya duka yarikesu ajikinshi kam kam, juyawa Baffa yayi yakalli Hafiz dashima yay
mutuwan zaune hakama su Hassan ahankali yace “Hafiz jeka dauko Khairy daga makaranta”
Tashi Hafiz yayi ahankali yafice daga dakin tafiya yake but jiyake kaman iska ke kadashi yana
tuna all memories dinshi da Mama shikenan daba danta data haifa ba balle kuma yaranta yaya
zasuji.

A famfon gaban flower ya tsaya saida ya wanke fuskanshi tass sanan yakarasa wajen mota
shiga yayi yatada motan yana kallon yanda mai gadi ke budemai gate he just wish yanada
karfin sanar da su, amman ina motarshi yaja yafita daga gidan zuwa school din su Khairy, har
gaban department dinsu yaje accounting yay parking yakai kusan good 20min zaune acikin
motan baida courage na facing Khairy, da kyar ya iya gyara mood dinshi sanan yakashe motan
yafito yamaida yarufe yana kallon ko’ina kafin ya shiga ciki, Khairy nabashi labarin how popular
she is a school so yasan ganinta bazai tabamai wahala ba, wasu yammata guda uku dasuka
sauko daga bene yatare yace “hello ladies dan Allah kunga Khairy” daya daga cikinsu ce tace

“yanzun nan muka rabu da ita ga ajinsu chan wanchan floor din suna lectures” thanks yace
musu sanan yawuce sama zuwa gaban class din excuse yay taking hakan yasa lecturer yafito
dan yana ganinshi yasan Wanan baimai kala da dalibin makarantan nan ba, dawowa cikin ajin
lecturer yayi yace “Ummulkhair” dasauri Khairy dake zaune ta kwantarda kanta kan table takalli
lecturer tace “yes sir” waje yanuna mata yace “ana nemanki” tashi tayi ahankali tana daukan
jakanta tafito tana tafiya kadan kadan dan sosai kafafunta basuda karfi ganin Ya Hafiz yasa
tabude baki cikeda mamaki takarasa gabanshi da sauri tace “Ya Hafiz mekazo yi a school
dinmu”? Hararan ko’ina yayi yay gaba abinshi tana binshi da sauri yace “me zanyi a school
dinan naku Baffa yace nakawo ki” dasauri tace “Allah sarki Baffa yana ina tare kukazo kenan”
“yana gida” yafadi kai tsaye batare daya juyo ya kalleta ba daidai suna karasa sauka kasa tana
binshi abaya tace “Ya Hafiz wani laifin nayi ne wanan da dazu dasafen nan nabar Baffa agida
mekuma nayi” juyowa yayi yakalleta daidai yabude mota yay murmushi yace “yarinya laifi
dayawa” zare idanu tayi cikeda tsoro tace “hala saisa gabana keta faduwa wlh” tada motan yayi
tashigo ganin duktai wani irin yasa yace “common babu abinda kikayi so relax” murmushi tayi
dasauri tana sauke ijiyan zuciya but dudda haka she’s not just feeling ok hakan yasa tai shiru
kaman ba itaba danda tacikashi da surutu shima shiru yamata baice mata komi ba ahaka har
suka shigo layinsu, tundaga nesa take hango tulin mutane ata kofar gidansu maza na alwala
hakan yasa ta gyara zama tace “Ya Hafiz maiya faru a anguwan mu”? Hango gate din gidansu
abude awangale gakuma mutane yasa taji kawai gabanta nafaduwa ba kakkautawa, shiga cikin
gidan sukayi daga baki baki Hafiz yay parking dan compund din yacika da mutane wasu
tsaitsaye wasu zazzaune hango mai gadinsu da Adamu direbanta na kuka yasa kawai taji wani
karfi yazo mata tawani bude kofan taduro juye juye tafara tana juwa juwa tanabin all mazan da
idanunta kan sauka akansu tana kallo, kaman daga nesa taji dodon kunenta yaji wani magana.
“Itace diyar Hajiyar data rasu” kafafunta da tun dazu sukai sanyi jitayi karfi yazo mata acikinsu
kawai tahau gudu tai flat dinsu dataga kofar abude tashiga uwa an jefota tanabi kowa na falon
da kallo matan anguwansu ne makotansu sunci mayafai some da charbi a hannu, stairs tayi
dawani kalan mahaukacin gudu kawai neman mutum daya take dan gidansu she wants to know
what’s happening idanunta ma sun rufe zuciyanta na bugawa batama ganin gabanta bum! Taji
sunci karo da mutum da sauri takoma baya sanan tazaro idanunta tadaga kanta takalli wanda
ke gabanta kaman yanda shima yake kallonta, batasan wayeshi ba but she could see kamannin
shi da Ammi wani kayatyaccen kamshi nafitowa daga jikinshi, ahankali bakinta ke motsi
numfashinta na neman gagaranta yi sabida yanda kirjinta ke bugawa ba kakkautawa ahankali
tace “I……ina…….ina….”? Idanunta ne suka sauka kan gawar dataga an shimfide anan falon
sama da aka suturta, sai yanzu ma talura da mutanen dake falon saman, Baffa, Baba, Ammi,
Mom, Ya Manaf, Ya Mu’az, Maheer, Ya Hassan da Hussain Mama ce kadai batagani, still
numfashinta na bala’in katsewa tabi idanun kowada kallo barinma Maheer dake kallonta yana
wani irin kuka harda majina da she just think that answers her question, gently tadaga kafanta
tana wani kalan kyafkyafta idanuwanta tana dambe da numfashinta dake kokarin daukewa tana
kokarin tai taking just a step forward kawai tajita blank tai baya straight, wani irin tareta yayi
dawani irin sauri Baffa yataso yana kallon Zayn daya tareta yace “Zayn kwantar da ita akasa
she’s asmatic, Manaf get me her inhaler” dakinta Manaf yashiga yafito da sabon inhaler dago
kanta Baffa yayi yadaura akan kafanshi yakai inhaler bakinta yana bubbuga kumatunta da kyar
ta shaka tai wani irin nishi tadawo Baffa takalla tashi tayi zaune kaman bata hayyacinta tace

“Baffa ina Mama na”? Ganin Baffa yay shiru yakasa bata amsa yasa takalli Ya Manaf tace “Ya
Manaf ina mama ya akayi banganta ba” saukar da kanshi kasa yayi, ahankali Baffa yace
“Ummulkhair” wani irin gyadamaikai tayi jikinta ko’ina na ta rirrike Baffa, all this while Baffa has
been mai taurin zuciyan but for the first time yaji Khairy kaman itace zata karyashi, dakewa yayi
yace “listen to me Khairy, kinaji” gyadamai kai tayi jikinta har kafafunta bari suke ta rirrike Baffa
wani irin zufa na keto mata agoshi, anatse yace “dukanmu anan da mazajen dakika gani a waje
ke kawai ake jira domin inaso kima mahaifiyarki addu’a, Ummulkhair inaso kizama yarinya mai
Imani da kaddara mai kyau ko mara kyau sanan kisani cewa kullu nafsin za’ikatul maut, i want
you to calm down don’t shout and don’t cry kinga kinada Asma karkije kima kanki illa,
Ummulkhairy Allah yayiwa…..” Baffa yadanyi shiru ganin yanda tazaro ta kwalalo manyan
idanunta waje kaman zasu fado kasa yanda jikinta ke rawa zaka dauka ajikin injin markade
take, daurewa Baffa yayi ahankali yace “Allah yayiwa mahaifiyar ki, Maman ki rasuwa
Ummulkhairy”.



2️⃣6️⃣



Wani kalan shuuuuu taji kunenta nayi, itadai tasan taji koke koke, taji maganan Baba, su Ya
Mu’az har maganan Ammi tasan taji sama sama kafin chan kuma taga tabude idanunta tana
kallon kowa dake kanta, kala batace musu ba rarrafe ta shigayi har zuwa gaban gawan zama
tayi dirshan tana kallon farin likafanin hannu tamika zatakai tabude saikuma tai shiru kafin
ahankali tasa hannunta taja likafanin kasa fuskan Mama ya bayyana tai wani haske ga alamun
murmushi tanayi wani kuri tayi da idanu kaman tahaukace sai kawai idanunta aukahau mata
yana kaman Mama murmushi take mata dariya tayi sanan tajuyo ta kalli Maheer dake kuka tace
“Ya Maheer dena kuka kaji zoka gani ga Mama nan namin murmushi, Mama bata mutu ba bacci
take wlh gashinan zoka gani” babu zuciyan wanda bai tsinkeba adakin ahankali takai bakinta
saitin fuskan murya chan kasa tace “Mama Mama, world best tashi kiji, Mama ai bacci kikeyi ko”
tasake shiru, ganin ko motsi Mama batayi yasa tai tagumi tana kallonMama tace “zan jira harsai
kin tashi kinmin magana” ahankali Baba yataho yazauna kusada ita dasauri tajuyo takalleshi
kaman mai karantan wani abu akan fuskanshi, kafadan Khairy yakamo sanan ahankali yace
“Ummulkhairy mamanki has been bathling with cancer for so long, blood cancer bataso kisani
cus tasan abinda zakiyi kenan idan kikaji she has few days left, u will not take it likely, saisa
taboyemiki all this while mamanki has been sick, seriously sick amman taki yarda kisani duk
ciwon da mamanki keyi taganki she will pretend she is fine” hawaye masu bala’in dumi ne suka
zubo mata dasauri tasa hannu tashare, ahankali Baba yace “karki sakawa Maman ki hakan nan
Khairy inhar she’s your world best, kimata

12 / 37