Author : Maman Fateema Category : Taskar Novels
katsewa kana ta daga tasa a kunnenta. Daga can taji
Yana fadar "Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu".
A zuciyar ta a amsa Dan da gaske in dai zata ganshi ko taji maganarsa kasa samun nutsuwa
take.
Sake maimaita sallamar yayi, da kyar ta amsa masa tare da fadar " Ina kwana?"
Shiru taji ba'a amsa ba kamar ma an sauka daga layin, amma ga mamakinta tana dubawa sai
taga Yana nan, itama shirun tayi kudin sunata tafiya saita saka handsfree ta aje wayar kusa da
daga gefe tana kallon ikon Allah.
Saida ya mula Dan kansa "yace ya jikin naki I hope kin shan maganinki?"
"Eh" ta fada a takaice.
"Fine"yace shima a takaicen.
Ita mamaki ma yake Bata har wani turanci yake jefawa a magana kamar gaske.
"Sai an jima ta fada tana kokarin katse Kiran.
"Kada ki kuskurs ki kashe min Kira" ya fada in serious tongue.
Shiru tayi tana mamakinsa sai wata izza yake Mata kamar wani abin azo a gani.
Muryarshi ta tsinkaya Yana fadin ki bude data na turo Miki sako idan da abinda kike bukatar ayi
ko a Kara sai ki fada min, take care".
Kit ya kashe kiran.
"Kutt!" Ta fada "amman gayen nan yama Raina ni wlh Wai kada na kashe Masa waya"
Kwafa tayi "zakaga na kiraka ganin idon ka" ta Jafar da wayar tana mita.
Taso yin barci Amma ta kasa dole ta hakura, wayar ta Kara daukowa tana kare Mata kallo.
Number din Hameeda ta Fara sakawa tunda taga sabon layi ne ya dauke natan, ga mamakinta
sai taga sunan Hameedar ya bayyana ba bata lokaci ta kira.
Tana ta ringing kamar baza'a dauka ba sai Kuma ta daga da sallama ai tana jin muryar Zahra ta
Fara mita "yanzu Dan Allah kin kyauta tun jiya nake neman layinki Amma shiru na Kira Mama
nace ta Baki tace min bakya Jin Dadi kina barci, wallahi Kinga yanda hankalina ya tashi kuwa ki
Bari lokacin da Sajida ta fada min halin da ake ciki wallahi daba final muke ba Allah da barinta
zanyi c/o na taho gida har fada mukayi da Salma Wai ai sai inje na baiwa Mushahun hakuri ya
dawo ya aure maganganu dai gasu nan ki Bari kawai ai jibi zamu Gama in Sha Allah komai
dare a gida zan kwana".
"Allah ya yarda ki Bari kawai wallahi Ina cikin yanayi akwai damuwa Dan Allah kizo ko naji sauki
abubuwan".
Ta fada tana share hawaye, sukayi sallma Dan it ma Hameedar kukan take.
Wai ita Mushahu ya yiwa haka, duk wadanda suka fasa aurenta Bata taba Jin Wanda ya Bata
Mata Rai ya Kuma tsaya Mata kamar wannan ba ai ko wace irin matsala ce ita ya kamata ya
Fara fadawa ba ya yanke mu'amala da ita ba a lokacin da take matukar bukatarsa ya manta
shakuwar dake tsakanin su da alkawarirrikan da suka yiwa juna.
Kwantawa tayi tana tunanin baya a haka wani wahalallan barci yayi gaba da ita.
**********Tun Yana tsammanin ganin ta bude data ta duba sakon har ya cire Rai da hakan.
Lambar Abdul Hakeem ya Kira sun jima suna waya kafin suyi sallama.
Laptop dinsa ya janyo yaci gaba da aiyukansa sai kusan azzahar ya Gama. toilet din cikin dakin
ya shiga ya dauro alwala,a masallacin hotel din Yaya sallah lokacin daya fito Kiran Habib ya
shigo Masa "Wai Dan Allah kana Ina ne tun dazu muke nemanka kazo masu aikin hada
furniture's din Nan ne suka Gama da cabinet din kitchen". "Ok gani Nan inaga kada kayi nisa zuwa an jima su Aunty zasuzo suga gurin"
Ya fada.
Yana nufar gurin da ya saba aje lifan din Habib.
Wayar Ammah Abdul Hakeem ya Kira ya fada Mata Mahmud yace a turo a gano gidan an
Gama gyaran, dakin Mama Ammah ta shiga ta fada Mata sannan Kira Aunty Hasana ta fada
Mata kafin ta wuce gurin Alhajin ta fada Masa tunda shiya dawo daga gidan gonar sai su Abdul
Hakeem ya baro suna yiwa shanu Allura da Basu magunguna. Wurin karfe biyar Aunty Hasana ta debesu a mota harda Sajida suka nufi Hayin bankin cikin
jagorancin Habib, lokacin Inna Bata Nan taje MIYA gurin wata aminiyar ta da sukayi aikin Haji
shekara daya.
Duk cikinsu ba wadda Bata kadu da ganin gidan ba domin ba karaya an narka mahaukatan
kudi a gidan bazaka tab'a cewa renovation akayi Masa ba, bedroom's ne guda uku biyu suna
kallon juna dayan Kuma daga gefe da alama yafi sauran girma Kuma shi kadai ne a rufe, sun
zagaya ko Ina sai santin gidan Sajida tace tana ta daukar video, falon kadai abin kallo ne duk
da ba komai a cikinsa sai fitilu da aka kunna sai Kuma AC da aka ware.
Hajiya mama ce ta kasa hakuri ta leka ta Kira Habib Nan falon ya shigo Yana fadin "gani
Mama"
Yana Dan rankwafawa.
Aunty Hasana mama ta kalla "Hasana Dan Allah ki tayani tambayar yaron Nan tunda shi namu
ne na gida baze cucemu ba, Wai wannan yaron sana'ar me yake daya iya Kama hayar wannan
uban gidan"?"
Kara risinawa yayi Yana fadar "ba haya ya Kama ba Baba malam ne ya bashi kyauta, sai Kuma
kungiyar yake yiwa aiki suka kawo masu aiki suka yiwa gidan 'yan gyare -gyare harda kayan
daki ma suka zuba masa, Bismillah Bari na bude muku ku gani yanzu ba dadewa zuka Gama
hadawa da kitchen din suka tafi". Dakin ya bude musu ba Hajiya mama da take ta kwana biyu ba, ko Aunty Hasana da Sajida
Saida suka Zama 'yan kauye Dan tunda suke Basu taba ganin irin wanna gadon a zahiri ba, ita
kanta aunty Hasana lamarin Yana neman ya gagari tunaninta fa ance Almajirin Baba malam to
Amma idan aka saka mizanin hankali abin yafi karfin yanda aka fada to wane irin NGO's ne da
suke irin wannan aikin akan daidaikun ma'aikatan su haka?" Gaskiya abin akwai abin dubawa.
Lokacin da suka fito harabar gidan ne wata Hilux ta shigo da kaya a bayan motar mutane uku
ne a motar bakar fata biyu fari daya Kamar balarabe Kamar kwara.
Kameme Hajiya mama ta hanasu tafiya sai da aka sauke kayan ta gani abinda da suka Gane
irin katuwar plasima din Nan Mai cin Rabin bangon Nan ne kawai amman sauran tarkacen
Basu Gane komai ba, haka suka kada suka tafi mama nata mitar "A'a da sake Alhaji ya titsiya
yaron Nan saiya nuna Iyayen shi kafin a Kai Masa yarinyar Nan haka kawai aje ayi kitso da
kwarkawata mutanen yanzu ba abin yarda bane sai kaga mutum har mutum Amman a Baki
malam a ciki Kuma Fir'auna".
Maganar data Basu Aunty dariya kenan.
❤️
❤️
❤️
AUREN HUCE HAUSHI
❤️
❤️
❤️
STORY
AND
. WRITTEN
BY
MAMAN FATIMAH
PAGE EIGHT
Lokacin da suka shigo gidan ana ta kokarin daura alwalar sallar magariba.
Sai bayan sallar insha'i ne Mama ta shigo dakin Ammah suka hadu da Aunty Hasana suna
fadawa Ammah yanda suka gano gidan da Kuma yanda abin ya daure musu kai.
Nisawa Ammar tayi tana fadar "Mama ki Sami Abban kiyi Masa bayani yanda ze fahimta
kinsan yanda suke da malam bana tunanin wannan abun ze saka ya canza ra'ayinsa duba da
yanda ya yanke hukuncinsa Bai nemi shawarar kowa ba".
"Aiko dai ya kamata ayi wani Abu gaskiya Nima lamarin ya tsaya mini a cikin zuciya".
Aunty Hasana ta fada.
Sun jima suna tattaunawar kafin Mama ta koma daki tabar Autty Hasanar da Ammah.
Zama Aunty Hasanar ta kyara ta fuskanci Ammar ta Kira sunanta "Anya wannan Mahmud din
ba abinda yake boyewa kuwa Ammah Kinga gidan kuwa ga wannan uwar wayar daya canza
Mata kinsan kudinta kuwa ? gaskiya I doubt much, ni dai kiyiwa Abban magana da kanki
Kamar zefi daukar abun serious akan na Mama". Can Kuma sajida ce tasa Zahra a gaba tana ta faman zuba.
"Innalillahi! Kinga gidanki kuwa? Allah ya bamu ya taku wallahi Zahra ki godewa Allah. Wallahi
Allah ya Gama miki duk wata ni'ima ta ko Ina kinyi gaban da Nan kurkusa dai kafin a fiki za'a
Dade ana lalube. Zahra Naga mijinki har mun gaisa ada Ina adawa da auren Amma tunda na
ganshi Naga Yana yinsa nasan yanzu ne kikayi aure da mijin daya Dace ke.Kawai dai matsalar
za'ace ba Mai kudi bane,amma a yanda gidan da zaya ajeki yake wallahi ko minister ne sai
hakan, akwai abinda na gani a gidanki wallahi ban taba gani a gidanki kowa ba duk yawona
sai dai a film amma dai a zahiri A'a ban taba gani ba Allah Bai kaini gurin ba".
Tunda ta Fara zuba Zahrar ke bin sajida da idon lokaci daya duk ta wani rude sai zuba take
Kamar 'ya 'yan kanya.
"Kin Gama?"
zahrar ta tambayi sajidar.
"Eh na Gama aini an ma yanka ta tashi na fasa tafiyar zanyi waya da Mom taje can Rimin
sumailar gurin Baffan kawai, tunda Daman zatazo nan din ba suna kwantagora".
"Ke Kika sani dai tunda Naga kina nema ki Zama wata daban ko dai an canza min ke da wata
ne ko Kuma wani abun ya fada Miki ya goge Miki hadda ne?".
"Eh da alama Kam Dan ya fiki iya lafazi gaskiya inaga na Zama 'yar team dinsa fa tunda Naga
ke Baki da wayo".
Ta fada tana dariya.
Washe gari tun safe Abba yasa aka Kai furniture's din Zahra gidan Daman Aunty Hasana sunyi
magana da Wanda zasu hada musu kayan, kayan kitchen da sauran kayayyakin duk suna
gidan Aunty Hasana daga can aka ringa daukowa, masu aikin su suka hada komai na gidan
hatta kitchen su suka gyara komai, gidan ba karamin kyau yayi ba, ba karya duk Wanda yaga
gidan yasan na 'yar gata ne.Dan wasu irin mahaukatan Turkish furniture's ne wanda kakanninta
ta gurin uwa sukayi Mata duk wani abun more rayuwa akwai shi a gidan Nan, bangaren
electronics ma sai a cikin lockers aka zuba wasu, komai yayi.
Lokacin da aka Gama gyaran Aunty Hasana da sajida ne sukazo gani ba karamin burgesu
gidan yayi ba Dan sai yanzu ne ya fito a asalinsa na kyau da kayatar da Mai gani, komai na
gidan unique ne Masha Allah.
A waya sajida ta daukowa Ammah komai. Ita kanta Ammah Kai Kawai take jinjinawa Dan ba
karamin burgeta abin yayi ba, sai dai can kasan ranta rudani ne kala-kala domin abin ne duk
yazo a hagunce.
Tana tsoron lamarin sosai sai da har abada baza iya jayayya da Alhajin ba Dan da gaske ubane
tsayayye Wanda baya nuna banbanci tsakanin abinda ya Haifa da Wanda yake bashi ya Haifa
ba, amma harga Allah tana zulumin wannan AUREN HUCE HAUSHIN da Alhajin yayiwa 'yar
marainiyar Allah, mazan yanzu sunce suna sonka ma ya kukan kare idan Zama yayi Zama
ballantana matar cushe ta San komai Daren dadewa ranar da yaga irin matar da yake so Sai
dai zahra tayi hakurin zama Kawai, duk da tasan Bata da haufi akan yarinyar Tata Dan macece
har mace abin alfaharin kowa ne namiji ace ya mallaki Kamar ta, to Amma shi lamarin so daban
yake duk kyan mutum da asalinsa ba lallai ne ace yana burge kowa ba domin shi dai so
makaho ne.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali duk jikinta yayi Mata wani irin Sanya ta kalli Aunty Hasana tace
"Hasana Ina jin wani irin rauni a zuciya ta game da lamarin nan Ina tausayin yarinyar nan
rayuwa tana ta walagigi da ita sai nake ganin Kamar laifi nane Dana kafe a barmin yarinyar Nan
na hana kakanninta ita ni Kuma nayi sakacin da aka maida rayuwar ta Kamar kwallo ana ta
dokata daga Nan zuwa nan".
Ta karasa maganar hawaye na zubo mata.
Abinda tunda Allah ya kawo Aunty Hasana duniya Bata taba gani ba a zahiri gurin Ammah Nan
da Nan hankalinta ya tashi sajida ma kukan ta Fara duk da batasas takamaimai man abinda ya
saka Ammah kukan ba, tashi tayi ta fice daga dakin jin an Fara Kiran sallar magariba.
Aunty Hasana ce tace "Haba Ammah duk yanda Kika jure bakin cikin baya na abubuwan da
suka faru Baki taba zubar da hawaye ba sai yanzu da Allah ya nufa akayi ai godiya Zaki yiwa
Allah daya kawo karshen wahalar ba kuka ba".
Gefen zani tasa tana goge hawayen.
"Hasana Ina hango abinda ke bakya hangowa ne,masu iya magana suna cewa matar shige
Bata daraja ba irin wannan rayuwar na sowa Zahra ba to sai dai kana naka Allah Yana nasa
Kuma nasan ne gaskiya. Ba komai haka Allah ya tsara komai mukaddari ne daga gare shi, naji
Alhaji Yana maganar zuwa juma'a za'a kaita".
*******Tun bayan kammala karatunsu na bayan insha'i da suke na littafin iziyya yake zaune a
kusa da Baba malam har kowa ya watse ya rage saura su biyu tunda malam yaga haka yasan
da magana a bakin Mahmud ne.
"Ya ya akayi ne Mahmuda?"
Malam ya jefo Masa tambayar, Kara dukar da Kai yayi kafin yace "Daman maganar kayan lefe
ne dazu Oga Sameer ya kirani yace ya hado tasa gudunmawar kenan, shine nace Bari na fada
maka Dan kasan da zuwansu".
"Ikon Allah shi wannan yaron baya gajiya ne Kamar baisan ciwon nema ba tunda yazo ya riski
maganar Nan yake Yi kan jiki kan karfi. Allah ya saka Masa da Alkhairi yabar muku zumunci".
"Ameen" ya amsa.
Harya Mike ze tafi sai malam din ya dakatar dashi, dawowa yayi zauna.
Gyaran murya malam din yafa kafin ta jefo Masa tambayar.
"Sai zuwa yaushe ne kake ganin zamuje ga mahaifan naka kaga dole muje musu tunda wannan
lamarin ya faru".
Kai ya sadda kasa Yana fadin "zamuje in Sha Allah Amma Dan Allah a Kara min lokaci da kaina
zanyi maganar ayi hakuri".
"To ba laifi Allah ya iya Mana kaje ka Samu su Habibu kuje acan gidan ku kwana kaga sun zuba
dukiyar kasan yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba".
"To in Sha Allah za'ayi hakan amma ni Ina Nan sai dai su Habib din suje".
"To ai hakan ma yayi Allah yayi Albarka".
Saida ya dudduba dakunan yaran ya tabbatar da komai lafiya lokacin sha biyu ta wuce, dakinsu
ya nufa wanka yayi ya saka kayan barci sannan ya hau gado ya bude laptop dinsa. Email dinsa
ya shiga Yana duba sakknnin daya samu sakon daya shigo ne ya dauki hankalinsa.
"Ya Salam!".
Abinda ya iya ambata kenan sai Kuma sautin daddad'an ringtone dinsa ya karade dakin.
"Sameer!" Ya fada a hankali yasan za'ayi haka, ya haga wayar Yana fadin "Ta Yaya hakan ya
faru?"
Daga can bangaren Sameer din yadan furzar huci Mai zafi Yana fadar "wallahi nayi duk yanda
zanyi Amma abun yaki yuwuwa dole ka daura ka kawar da komai muje gaskiya Dan kasan
tunda akaje Nan zuwan nake ne Kawai mafita".
"Amman ai kasan halin da ake ciki so kake ace na gudu nabar 'yar mutane Eyeh?".
"Cool down Mana my man abin Bai Kai nan ba aikin daine ya taso na gaggawa Kuma dole sai
da Kai za'ayi Dan haka suyi hakuri su aje maka ita zuwa sanda ka dawo ko Kuma ka dauko
abarka ku tafi, kaga ai tafiyar tafi yi maka armashi ko?"
Ya fada cikin zolaya.
"Dan Allah ka Zama serious mana, kayi duk abinda ya kamata a Nan goben ka hakura da
zuwan ka turo wannan friend din naka tunda yasan gurin ya kawo kayan kawai, Kai Kuma ka
Kira Baba malam ka fada Masa daga can sun nemi ganin wakilansu na kasa da jahoshi da
kananan hukumomi nasan dai kome ake ciki baze wuce kwana buying zuwa uku ba kaga
lokacin na tare a gidana nafi son na barta a Nan gidana akan na tafi Bata tare ba".
"Ko dai.......?"
Sameer ya fada Yana dariya.
"Allah ya shiryeka ko dai me? kasan ni salihn ne ba ruwana da wannan sabgar sai ku".
Kit ya kashe wayar sannan yayi switch off dinta.
Misalin karfe Sha biyun Rana wata tamfatsetsiyar mota Parker a kofar gidan malam.
Akwatuna Yara suka dunga saukewa suna shiga falon malam saida suka Gama sannan baki
nufi falon malam din bisa jagorancin Habib sun gaisa sosai da malam suka gabatar Masa da
kayan daga Sameer.
Malam yayi godiya ya saka Albarka ba adadi.
Falon malam ya bar musu sukaci abinci suka huta sannan Habib ya rakasu can gidan suka
gaisa da Mahmud din.
Sai bayan Azahar suka tafi malam yayi musu Sha Tara ta arziki.
Kayan malam yace suje su duba su gani saboda da an jima za'a Mika musu can gidan Alhajin.
Kaya ne na gani na fada an zubasu Kamar ba gobe, an shigarwa da iya Abu ciki ta gani malam
yace ta turawa makotanta na kusa suzo su gani anjima za'a Mika musu.
Bayan fitowa daga sallar la'asar ne Malam Bukar ya fadawa Alhaji yanzu su malam Mudi da
Alaramma malam Haruna zasu kawo kayan Zahara'u.