AUREN HUCE HAUSHI 1 COMPLETE BY MAMAN FATIMA.pdf

Author :  Maman Fateema Category :  Taskar Novels

Chapter   4 / 43

9K to 12K   out of 127.3K words

zaune gaban gadon da aka
kwantar da Zahrar. Sunan Ammah ta gani sai lokacin ta tuna Ashe Bata fad'a Mata ba.
" Assalamu Alaikum Ammah".
"Wa'alaiki Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu, wai Ina Kika tafi ne babu ke Inna
maimuna ma Bata Nan Hajiya kaltume ma banganta ba".

Dan Jim tayi har Saida Ammah tace "kina jina?"
"Eh inaji Ammah duk muna tare dasu, muna Nan gurin Zahra Bata Jin dadi ne Amman da sauki
yan haka barci take".
"Wane irin zance ne wannan kamar Bata Jin dadi Kinga Hasana fadi min gaskiya yanzu kina
Ina?".
" Muna F.M.C wlh jikin da sauki sosai kawai sunce ana dai San ta huta ne, kada ki tada
hankalin Dan Allah".
"To Allah ya kyau Amma Ina hankali ze kwanta".
Waje Aunty Hasanar ta fito gurin su Baba tabawa da sajida tace
"Baba tabawa Dan Allah kuje gida da sajida tasan inda aka aje abubuwan da zasu bawa
kawayensu tunda yau zasu wuce sai ki fad'a musu tana gida gurin Abba, ta kalli Sajida ke Kuma
duk tmbayar da saying Miki kice Baki Sani ba mu barsu a haka".
Kudi ta mikawa Baba tabawan sannan ta karasa gurinsu Inna maimuna da Hajiya kaltume,
Suma bayi tayi musu na Kiran Ammah tace suje gidan Dan hankalinta ya kwanta.

*********
Da kyar Amma ta Bari akayi sallar magariba ta shiga bangaren Alhaji Jafar ta same shi da
Hassan da Abdul Hakeem suna magana akan Zahra Hassan Yana ta mitar meyasa Abban yayi
haka ai da hakuri kawai akayi har lokacin da Allah ze kawo Mata wani.
Dan murmushinsu na manya yayi Yana "fadin wannan ma in Sha Allah Babu Dana Sani a
cikinsa ni nasan nagartar Dana gani tare da yaron yasa na bashi, Kuma ko bayan Raina
zakuce na fad'a muku".
Jiki ba kwari Amma ta gaishe da Alhajin tana Masa ban gajiya tare da godiya.
Sannan ta Dora da fadin "Dan Allah ko zaka Bari naje Naga jikin nata?"
Tsai yayi Yana kallon ta "da kinyi hakurin zuwa Suma da anjima zasu taho gida yanzu ma daga

cen muke ko zuwan mu Bai isar ba?"
Cikin Jin nauyinsa tace "A'a ya badatar"
Ta tashi ta nufi kofa da kallo Abban ya bita ita kanta tausayi take sashi da gani zuciyar ta ba
Dadi.
Da sallama suka shiga dakin lokacin Aunty Hasana tana sallar insha'i ita Kuma zahra
farkawarta kenan tana kokarin tantance Wai inane ma Nan din inda ta gani idan dai ba gizo
idanunta ke Mata ba kamar asibiti.
Sallamar ce ta katse Mata tunani ta Dan dago kanta kadan sukayi arba dashi Ido cikin Ido da
sauri ta runtse idanunta zuciyar ta na wata irin bugawa tana ambaton Allah a zuciyar ta, meya
kawo wannan dodon nata gurinta, Kara rufe idanun tayi it fa wallahi zata iya rantsewa Allah duk
duniya ba idanun da suke figitata kamar nasa.
❤️ AUREN HUCE HAUSHI ❤️


Strory
&
Written
By
MAMAN FATIMAH


Page five

_______ Shiru dakin ya dauka har zawan lokacin da Aunty Hasana ta idar da sallar.
Dan juyowa tayi kadan tana fadin "wa'alaikumus Salam warahamatullahi ta'ala
wabarakatuhu, sannunku da zuwa Bismillah ga kujeru nan ku zauna".
"To mun gode Aunty" Sameer ya fada.
Cikin ladabi da mutuntawa suka gaishe ta tare da tambayar Mai jikin, ta amsa musu da sauki,
sai kuma dakin ya Kara daukar shuru Zahra dai tunda ta rufe ido Bata Kara gigin budewa ba, ita
ji take duk ya cika dakin ita tun ganinta na farko dashi a duniya ya birkita Mata lissafi, Kuma
saboda Allah meya kawo shi gurinta asibiti duk da tasan mutumin Ya Abdul Hakeem ne Amma
sai taga kamar ba sai yayi Masa Kara ba, ko Kuma yazo wata sagbar ne asibitni ya Sami
labarin shine ya shigo ya dubata.
Magaji ne ya shigo dakin da sallama sai Kuma ya Dan tsaya baiyi tunanin ganinsa ba Sam da
fara'a ya karaso Yana fadin "Ashe Kuna Nan ai tare muke da Ya Abdul Hakeem ma".
"Ok" abinda Mahmud ya fad'a kenan
Shi Kuma Magajin ya karasa gurin Auntyn Yana gaishe ta.
Abdul Hakeem ne ya shigo Yana rike da wayarsa a hannu da sauri ya karasa gurinsu Mahmud
din Yana fadin "A'a angon ne da kansa" Yana Mika masa hannu.
Saroro Aunty Hasana tayi ita wace iri ce kawai dai taga sun shigo sun gaisa wallahi Sam Bata
kawo ba ita da akace Mata Alamajirin Baba malam ne ai ta dauka irin wannan gaddawan ne, yo
ta Ina wadannan sukayi wani Kama da kolaye ai ita zallar ilimi ta gano da wayewa a tattare

dasu.
Hanyar wajen ta nufa tana janye da hannun magaji duk sai taji kunya ta kamata Ashe sukanta
ne.
Ita kuwa Mai gayya Mai aikin ai tana jin an ambaci ango ta bude idonta girjinta Yana wata irin
dokawa "ango a nan to waye a tsakaninsu da suka shigo tare?
Abdul Hakeem ne ya kalli gurin gadon Yana fadi.
"Masha Allah! Ashe kin tashi, ya jikin?"
Ya fad'a Yana karasawa jikin garon Sameer ma Dan matsawa yayi Yana dubata Kai kawai ta
gyada musu, tana kallon Ya Abdul Hakeem din, kallo irin na neman Karin bayani.
Yi yayi kamar Bai Gane ba ya juya yana yiwa Sameer magana suka fita.
Har suka fice Bai dago ba Yana ta faman tab'a waya sai da ya Mula Dan kan shi sannan ya
tashi ya tunkari gadon.
"Ya jikin?"
Ya fad'a Kai tsaye, Bai Kuma jira ta amsa ba Dan ko kwakwkwaran motsi ta kasa sai tunanin
da yake Mata Kai komo.
"Badai wannan bane ake nufin an daura min auren dashi Amman da Naga ta kaina".
Shine ya katse tunaninta.
"Ki kwantar da hankalinki ki daina saka damuwa a ranki da kannan shekarunki, ki kuma dagawa
Ammah í nata hankalin, idan nine bakya so ba damuwa Nima kusan hakan take. Amma kada
mu watsawa iyayen mu kasa a ido Mana tun yanzu gara ki nutsu ki kwantar da hankalinki
daga baya sai a duba Mai yuwuwa tunda nasan bazaki so Zama da almajiri marar karatun boko
mai zurfi, ga karqncin wayewa ga rashin madafa ta yau da kullum, Nima kasada ce tasa na
yarda da tayin da akayi min tunda Naga nema ake a tozarta min da iyayen a kunyata su a idon
duniya aci mutuncin su".
Ita da'i ko motsin kirki ta kasa da gaske gani take duk ya cika dakin, ga wani fitinan kamshinsa
duk ya cika Mata hanci.

A bazato taji ya Dan shafi gefen fuskarta idan ba kunnenta ne suka jiyo Mata ba da'i dai ba sai
taji kamar yace "my previous" a hankali sannan ya Mike Yana fadin "Bari a kawo maganin ki
saimu wuce gida tunda doctor yace zamu iya wucewa, Amman yace ki rage yawan tunani Yana
haddasa cututtuka".
Har dakin Amma Abdul Hakeem ya raka Zahra lokacin duk yawancin bakin sun tafi sai 'yan
uwan Amma na Mubi Dana Jimeta sai Kuma Aunty Hasana da take dakon dawowar su, ai
tunda magaji ya Kara Kora Mata bayani akan Mahmud ta tafi daga asibitin tunda Mai
dungurungum din yazo ita bataga ta Zama ba. Saida ta matsawa Zahrar tayi wanka Tasha tea da magungunan ta kwanta sannan tayi haramar
wucewa gida.

Sai wurin karfe Tara sannan Hajiya mama ta shigo dakin tana fadin "wallahi daga idar da sallar
ta barci ya dakeni sai Dana tashi zilai Mai wanke wanke take fad'a min an dawo da Zahra har
sun shigo sun duba ta".
"Wallahi kuwa ai jiki da sauki yanzu Tasha magani ta kwanta"

"To Allah ya Kara lfy, Wai Hajiya wanene mijin yarinyar Nan ne naji ana fadar Wai cikin
Almajiran baba Malam ne, shine nace haba yaushe Alhaji zeyi wannan danyen aikin ya rasa
bazai bawa aure Sai a cikin Almajirai".
Inna maimuna ce tace "ai mu Hajiya ko waye Alhaji Jafar ya aurawa Fatima wallahi mun karba
da hannu biyu mun gode tunda mun San har abada Babu cutarwa a tsakanin Asama'u da dashi
da ita Fatiman da abinda ya Haifa bamu taba ganin banbanci ba, Dan haka mun karba da
kyakykyawan niyyarsa Allah ta tabbatar Mana da Alkhairi". Gaba daya suka amas "Amin"
Hajiya mamar ta Dan jima a dakin kafin ta koma dakinta.
Bayan Zahra tayi sallar Asuba ta gama Azkar dinta komawa tayi ta kwanta har lokacin kanta
Yana Mata ciwo kadan kadan, sai gurin takwas da rabi Inna maimuna ta tasheta tana fad'a Mata
tayi maza ta kimtsa Abbansu Yana nemanta.
A gurguje tayi wankan ta fito lokacin an kawo Mata kunun gyada da fanke, kunun gyadar kawai
tadan Sha kadan ta shafa lotion dinta ta saka doguwar rigar atamfa ko dankwalin Bata daura ba
ta fito cikin takunta na nutsuwa Wanda da yawa mutane ke gani a matsayin yanga da jiji da Kai.
A tsakar gidan suka rinka gaisawa da tsirarun yan uwansu na Mubi da sauran ma'aikatan gidan
Mata.
Da sallama a bakinta ta shiga falon Abban nasu, tayi mamakin ganin kusan duk 'ya'yan Abban
suna Nan sai su Ammah da Inna maimuna da kanwar Abban Maman lafia.

"Zo nan kusa dani Uwata".
Abban ya fad'a Yana murmushi, itama murmushin tayi ta karasa kusa dashi ta zauna nata fadar
"Abbana Ina kwana?".
"Lafiya kalau Alhamdulillahi Uwata".
Sannan ta juya tana gaishe da jama'ar gurin.
Said Kuma dakin yayi shiru.
Abban ne yacewa Imam "Mai sunan Malam ayi Mana addu'a".
Ya jima Yana addu'a sanan aka shafa. Sannan Abban ya Dora da cewa.
"Alhamdulillahi ala kulli halin, dole ne mu godewa Allah s.w.a a cikin kowane Hali mutum ya
Samu kansa, kowa yasan yanda lamarin Auren Uwata ya ringa kasancewa a baya abune ba
Mai dadin maimaitawa ba, to wannan karon ma tarihine yaso maimaita kansa Amma na yanzu
sai yafi sauran tada hankali ni Kuma Naga a wannan gab'ar bazan Kara bada wata kafa ba
wadda za'a dunga walagigi da rayuwar yarinya karama ba kamar Uwata. Sunanta Ya kira
Fatima dago ki kalleni, cikin girmamawa ta dago kanta kamar yanda yayi Mata umarni.
Hannunsa yasa ya nuna kansa yace kina ganin zan iya zaluntar k?" Da sauri ta girgiza Kai
hawaye na zubo mata.
Yace "To Fatima na daura Miki aure da bakon yaron Nan Mahmud na wajen Aminina Malam
Bukar". Duk da taji haka daga bakinsa a jiya Amma Bai hanata kara shiga rudu ba saboda
wannan taji daga bakin da bazeyi Mata karya ba, Nan da Nan ialahirin jikinta ya shiga rawa
wallahi ita a jiyan jinsa kawai take gani take kamar almara ce kawai. Muryar Abbansu ce ta Kara katse Mata tunani "kiyi hakuri Uwata kowa da irin jarabawar da
ubangji yake Masa ki dauka taki jarabawar kenan, ki yadda da kaddararki sai Ubangiji ya jibinci
lamarinki wannan ba hadin kowa bane hadin Allah ne, kiyiwan mininmi biyayya in Sha Allah

zakici ribar rayuwa, ki cire yaron Nan Musbahu daga zuciyarki ki rungumi abinda Allah ya baki.
Allah yayi Miki albarka yanda Kika yi min biyayya Allah ya Baki 'ya'ya Wanda zasuyi Miki
biyayya kema, Allah ya albarkaci aurenku ya tsone idon makiya da mahassada".

Hajiya mama ce ta fasa Kuka tana fadin "Haba Alhaji wannan wane irin danyan hukunci ne? ya
zaka dauki 'yar marainyar Allah ka baiwa Wanda ba'asan asalinsa ba, ai duniya saita zage ka
Dan Allah ka janye maganar Nan da wannan ba gara kaba salmaun gidan Hajiya Dago ba
tunda ya jima Yana son yarinyar Nan Amma ka Hana shi" Kowa a falon kallonta yake ba Wanda ya tofa sai danta Hamza yace "haba mama menene haka
kikeyi Dan Allah kiyi shiru da wannan maganar salmanun me Allah ya sauwake me za'a da
wannan zuri'ar".
Hannu Abban ya dagawa Hamza Yana fadin "ya Isa haka tunda ka Bata amsa basai nace
komai ba, Amman ki rubuta ki aje in Sha Allah sai wannan auren ya Zama abin kwatance
Kuma abin alfahari duk Wanda ze zageni ya Dade Bai zageni ba, Kuma duk Mai ganin zalunci
ne yasa na aurawa Fatima Mahmud na barshi da Allah wallahil Azeem ban taba kallon Uwata a
matsayin 'yar wani ba kullum Ina Mata kallon 'yata malak malak a makaranta ne kawai ban saka
Mata sunana ba shima nayi haka ne Dan tasan nata mahaifin ta rinka Yi musu addu'a".
Addu'a Abban yasa Imama yayi yaba kowa izinin tafiya Amma yace Ammah ta tsaya ita da
Hajiya mamar da Inna maimuna da Maman lafia.


Aunty Hasana ce ta kamo hannun Zahra zuwa dakin Ammah tana kuka, yarinyar tausayi take
Bata kamar yanda Abban ya fad'a ana walagigi da rayuwar ta.
Cikin bed room din Ammah suka wuce, bayan sun zauna ne Auntyn ta riko hannun Zahrar "kiyi
hakuri kinji Allah Yana sane da halin da kike ciki, Dan Allah kad'a ki watsawa Abba kasa a Ido ki
bijirewa auren nan wallahi irin wanna auren Yana albarka fiye da tunanin".
Wasu sabbin hawayen ta goge. Cikin shashhshekar kuka tace "wallahi Aunty nifa tsironsa nakeji
idan muka hada Ido wani Abu nake gani a idonsa".
Sororo Auntyn tayi kafin tace "ban Gane ba tsoronss kamar Yaya, Daman kinsansa ne runtuni?.
Kai ta gyada Mata alamar Eh.
"Allah ya kyauta" kawai Auntyn tace.
"Ko meme ma dai wannan tsakaninku ne kin gyarota can".
Ta Mike tana fadin "Bari na koma gida sai zuwa an jima zamu shigo da Sajida da Amatu itama
Bata tafi ba jiyan.

********Tun bayan suka dawo daga sallar Asuba Mahmud yake ta faman aiki a cikin laptop
dinsa, Yana kallon Sameer Yana kwasar barcin gajiya. Bai gama aikin ba sai kusan karfe
takwas na safe, kai tsaye toilet ya nufa ya jima a ciki kafin ya fito daure da towel a kugunsa
karami Kuma a hannunsa ya goge sumar kansa me baka sidik Mai laushi Saida ya shirts cikin
wani farin yadi filtex marara nauyi ya feda turarensa Alburaq sannan yaje gefen bedside ya
dauki wayarsa ya kunna.
Abinci ya bukata a kawo musu, yana Gama wayar Kira ya shigo sunan Habib ya gani, ya daga
da sallama daga cen Habib Fara fadar.

"Habe Dan Allah dukka tadawa Baba malam hankali baka kwana a gida ba abinda baka Saba
ba Koda wasa duk dare zaka dawo Amma jiya daga Bari kaje ka dawo shi kenan kayi layar
zana Kuma ka Kama ka kulle waya".
Dariya yayi Yana cewa "kana tunanin Kona bi dare nayi Gudun auren dole ko?"
Shima Habib din dariyar yayi.
"Ka Gudun Mana idan ka Isa mai wannan tsaleliyar Ina zaya ya barta koka gudu ka dawo da
kafarka, kawai da malam ne ya matsa yaji kana ina".
"Ok shi kenan Bari na kira shi Dan hankalinsa ya kwanta Ina Nan tare da Oga Sameer shine ya
rikeni nayi Masa wani aiki".
Yana kashe wayar ya nufi sofa ya zauna yana janyo stool din da aka Dora abincin.
"Oh ni Sameer yaushe na rikeka? ka rikeni dai ka Hanani tafiya ka barni da kame kame ga
madam can tana fama da kanta ba mataimaki gaskiya yau in Sha Allah sai kano".
Ya fad'a yana nufar toilet shima.
Can hayin bankin suka Fara zuwa gurin masu aikin gidan Masha Allah aikin yayi nisa kamar ba
jiya aka Fara ba Sam an canzawa gidan fasali kamar bashi ba, duk abinda ake bukata Sameer
ya danka shi a hannun Binya.
Sannan suka nufi cikin gari.
Wani mall suka shiga Mahmud ya jido kayan fruits dasu kayan tea sai chocolates dasu farm
fresh yogurt da fresh milk. Leda uku aka cika manya Saida suka dauki hanya Sameer ya kalli
Mahmud yana fadin "wadannan kayan fa yallabai na waye".
"Dubiya zamu saika Bata tunda ni dai kowa yasan bani da kudin sayansu.

❤️ AUREN HUCE HAUSHI ❤️

Page six

P️

________Sun jima a gurin Baba Malam Yana yiwa Sameer godiyar dawainiyar da yasha akan
wannan lamarin, sannan yayiwa Baba Malam din sallama akan zai wuce sai hutu ya Kare
zasuzo da mutanen su suna son su kawo wasu ayyukan da za'ayi.
Har gurin mota Malam dasu Habib sukayi Masa rakiya, Baba malam Yana fadin "Bari muyi
addu'a".
Nan yaja doguwar addu'a akan Allah ya tsare hanya, har Sameer ya shiga mota ya fito ya nufi
Malam Wanda har ya Fara tafiya, sai Kuma yaja ya tsaya Yana jiran karasowar Sameer din.
Dan risinawa yayi Yana fadin "ko za'a samu Wanda ze rakani na Kara dubo jikin wannan
yarinyar?"
Wani kallon kasan ido Mahmud ya bashi dashi "Wai yarinya".
"To! To! Masha Allah ai sai kuje da Mahmud din da Habibu kuga jikin, ai wannan tunani ne Mai
kyau.Nima na shiga da safe gurin Alhajin naji yata kwana".
Har cikin harabar gidan Sameer ya shiga da motar, Abdul Hakeem Habib ya Kira kafin su shigo
ma ya fito Nan Harabar gidan Yana jiransu.
Shi yayi musu jagora zuwa falon Abban, yayi murna sosai da ganinsu sun gaisa sosai sun masa

godiya sosai da karamcin da yayi musu, yaji dadi sosai Dan har ya ringa tsokanar Sameer
Yana fadar "wato tunda kazo gabatar da aikinku ban sake ganin kafarka ba a gidan Nan sai
yau dana baku Mata ko? Dan na lura baka da aminin daya wuce Mahmud a garin nan. Masha
Allah, Malam ya fada min duk Fadi tashin ku akan lamarin Allah ya saka da Alkhairi yabar
zumunci".
Suka Amma da "Amin ya Rabbi".
Mahmud Alhajin ya kalla Yana fadin "kayi hakuri fa Mahmud munyi maka nauyin kuka".
Kai ya gairgiza Yana fadin "ko daya wallahi ba komai nagode, Allah ya saka da Alkhairi ya Kara
lafiya Nisan kwana Mai albarka"
"Allahumma Amin. Allah yayi

4 / 43