Author : Maman Fateema Category : Taskar Novels
yanzu yasa an dauko su
ba Wanda yasan inda ya kawo su daga Rukayyar har Sameer din ba Wanda yasan takamaimai
Ina ne asalinsu an kawo su ita da baiwar Allah an killace su a wannan uban gidan kamar
resident na matar shugaban kasa.
Sai da Rukayya ta Dan tabata lokacin da suka tsaya a kofar parlourn Dan da gaske tayi mugun
zurfi a tunanin Dan zabura tana Fadi. "wallahi har naji tsoro".
"Ai ke dince Ina ta magana Amma kinyi Zurfi a cikin tunanin, ki rage yawan tunani saboda
lafiyarki kinsa Yana shafar lafiyyar Dan Adam".
"In Sha Allah Zan Dena na gode".
Ta yungura ta fito Bata jira ba ta nufi kofar shiga tana fadin oga Sameer sai da safe kaina yake
Dan Sara min a shafa min Kan Abeed"
Dariya Sameer.
"Zeji in Sha Allah Banda mamansa ko?"
"Kaina bisa wuyana na Isa ayi min gaisuwa, zanzo muyi jegon tare".
Wani kallo Rukayya tayi Mata tayi wani killer smile ta matso daidai kunnen ta "saurin me kikeyi
in dai jego ne kamar yaune kinsan Yayana ba rago bane daina gaigaye zakiçi tumo".
Tayi gaba abinta kamar Bata Fadi komai ba. Ido Zahra ta zaro tabi bayanta da kallo, ta fuske
kamar ba ita ta Fadi maganar ba.
Ganin haka yasa Sameer ma ya basar ya dauko wasu ledojin yabi bayan Rukayya data dauko
wasu.
A Nan parlour sukayi sallama da Sameer ya tafi, su zilan Basu tashi daga kallon ba suka Yi
musu sannu da zuwa tare Da tambayar ya jikin nata, bata jima ba ta dauki kedar cosmetic din
da robar ice cream Daya da biscuits da chocolates ta nufi hanyar masaukinta tunda yace Mata
ba komai a gidan da tsaro sosai ta Sami kwari gwiwa da kwanciyar hankali, tana barin gurin ta
dauko wayarta ta kasheta gaba daya tana fadin.
Wallahi kwana kusa ba zasu gaisa ba tunda shi wani irin mutum ne marar Alqibla. Kuma tafiyar
ta zatayi ta koma inda ta fito haka kawai Kullum ita kenan cikin matsala gara ta koyi jajurcewa
itama kowa ya samu dama saiya ringa dokata kamar wata ball impossible wallahi".
Ta fada tana zura katin bude kofar ta shige ciki, a Kan sofa ta zube kayan ta shiga cire kayan
jikinta Daman duk sun dameta, wanka ta shiga Dan wallahi barci takeji, barcinta zatayi tasan
mutum Bata wuce kaddararsa.
******
A gajiye ya shigo masaukinsa yau throughout bai samu hutu ba, hankalinsa gaba Daya yayi
gida so yake ya ganta ra'ayal ain bawai ta wayar ba yaji dumin jikinta ya tarairaiyi kayarsa suyi
barci tare su tashi tare ya gaji da watangaririyar Nan gara ayi wadda za'ayi kawai game din ya
Zama over. Saida yayi wanka yayi order coffee sannan ya janyo wayar ya shiga nemanta da gaske yayi
kewarta ba kadan ba, shifa yana ganin yarinyar Nan itace weakness dinsa duk inda take tana
manne a kirjinsa ko barci yake itace a cikin barcin idan ba ganinta yayi ba ko yaji muryar da da
akwai damuw, yaga alama any nan gaba ze iya kulla wani abun arziki kuwa? tun yanzu da
gishiri bai Sha Kan kazar ba yana jinsa haka Yaya idan labarin ya sauya salo?
Abin mamaki wayar switch off.
Zuru yayi Yana kallon wayar "me kenan?"
Yasan dai ba matsalar charge bane, Sameer ya Kira, duk da basu Dade da Gama waya ba.
Sameer yayi mamakin ganin wani Kiran nasa.
Kafin Sameer ya Kai ga magana Mahmud ya Riga shi.
"Meya faru ne a Asibitin naji wayarta a rufe ko jikin ne ta tashi da akayi Mata gwaje-gwajen?"
"A'a gaskiya normal muka dawo har muka biya nan Murtala Muhammad way sukayi sayayya
Kasan Rukayya bataso a zauna lafiya,idan tajita da kudi ba zaman lafiya. Dan Allah ka daina
turo mata kudi har madam tabar garin nan, kasan Ruky da yawo Kullum aka fita saita qirqiro
zuwa wani gurin, wani Abun ne ya faru yanzun ?"
"A'a ba komai, kada ka manta da maganar kayan da za'a sauke gobe a Nan kanon a turasu can
Azaren munyi magana da Habib dazu".
"Ok in Sha Allah".
Sukayi sallama, ji yayi baze iya fada masa komai ba. Wayar ya aje kusa dashi wani tunani yayi
sai yaji dariya ta kubce masa "zakiyi bayani da yaren garinku yarinya duk yanda akayi taji wata
maganar yanzu a Asibitin yasan Haseena farin sani yanda yaji ta damu da sanin relationship din
dake tsakanin sa da zahra yasan zatayi duk yanda zatayi ta shigo da wata maganar wadda
zatayi touching dinta tunda shekarun da wayonsu ba Daya bane.
Itama Zahra kasa cin komai tayi fridge ta bude ta saka ice cream din da chocolates tayi
kwanciyar ta bayan tayi Addu'a, amma barcin Kuma yace baisan zancen ba, tashi tayi zaune a
tsakiyar gadon tana tariyo rayuwarta ta baya "ko yaushe Zan Zama stable a rayuwata? sai
hawaye suka zubo Mata "Ubangji ka hanani ganin bakin cikin gidan Aure, lamarin Yana neman
yafi karfina ka jibinci lamurana Dan isar fiyayyan halitta Annabin Rahama Muhammad s a w.w.
Bansan ko waye ba wannan bawan naka, kafini saninsa ka amintar Dani a cikin lamarinsa daka
barni na tozarta, ka kareni daga dariyar makiyana Ubangiji kasan ko suwaye suke mini yankan
Bata a cikin lamarina, kayi min kariya ka bani juriyar abinda ka jarrabeni dashi kasa ya zamar
min kaffara. Tasa tafin hannunta a fuskarta taAUREN HUCE HAUSHI.
MAMAN FATEEMAH.
Page 40.
______ karfe takwas saura Zahra ta fito cikin shigarsu ta asali doguwar Riga baka Mai aikin
zare maroon sai kananan stones har kasa,tayi rolling da maroon din veil, cikin takunta na
rausaya take gannaro steps din, tana baza sansanyan kamshi, ba kowa a parlourn sai wani
sanyi da kamshin freshners ke tashi, Dan Jim tayi tana tunanin ta koma kota zauna sai Kuma ta
jiyo alamun motsin kwanuka a kitchen gurin da taga suna shiga ta nufa tunda ba sanin Kan
gidan tayi ba, tunda ta shigo iyakarta Nan sai Kuma bedroom din da take, tana dosar gurin wani
kamshin girki yayi Mata sallama, babban kitchen ne na zamani Mai kunshe da na'urori birjik
kamar a wani babban Hotel ko irin modern restaurant din nan iya Rahane ta gani tana yanka
wani Abu yayin da zilai ke tsaye tana duba wani abu a tukunya.
Sallama tayi musu tana fadin "Ina kwanan ku".
A tare suka juyo suna amsawa tare da fadin "ya Kika kwana da jikin?".
Dan juya Kai tayi tana fadin. "Nifa Babu abinda ke damuna kawai dai Dan a dunga yawo ne da
Bata lokaci, wallahi har kunya nake ji" .
"A kul Kika Kara fadar haka tunda mijinki yace Kizo a duba aga menene matsalarki kada ki
watsa Masa qasa a Ido ki sage Masa gwiwa akan kokarinsa, kije idan Allah yasa Babu komai
shike Nan idan Kuma anga abinda ke kawo ciwon a magance shi".
"Wannan gaskiya ne".
Zilai ta fada tana sauke girkin.
"To in Sha Allah na daina iya".
"Yauwa kokefa fa ai idan Kika Fara da haka ko lalular da tafi haka baze Maida hankalinsa ba
duk da ba fata ake ba".
"Dan Allah Aunty zilai bani wayarki na Kira Ammah tawa tun jiya ta kashe kanta taki kunnuwa".
Ta fada tana istigifari a zuciyar ta Dan tasan karya ta shara.
" To Bari na dauko Miki tana can a daki"
Ta wanke hannunta ta nufi kafar fita Zahrar tana biye da ita, sai da suka fito zilan ta kalli Zahra
"uwar dakina Dan Allah Wai Kinga kuwa dakin da aka ajeni a ciki Dan Allah muje kiga wannan
duniyar da aka sakani kamar dakin gidanki,to acan dai bana Hawa gadon Amma wannan akai
na kwana har naso in makara Allah yasa ita Iya Rahane Bata makara ba". Dariya Zahra tayi tana fadin "daina fada Aunty zilai sai a Raina mu wallahi, muje Naga dakin
naki Daman ban San inda kike ba Koda tsoro ze kamani sai nayo gudun hijira".
A parlour na biyu suka shiga wani corridor bazaka taba cewa da dakuna a gurin ba steps ne
kamar goma suka haura sama Nan ma wani parlourn ne da two three bedrooms biyu suna
kallon juna sai Daya daga gefe.
"Masha Allah" Zahra ke fada a zuciyar ta tana mamakin gidan Wai wane irin gida ne wannan
gari guda compartment guda kawai ya hada irin wadannan mahaukatan falukan da bedrooms
din Nan to yaya sauran parts din suke?.
Dakin dake hannun hagu ta nufa ta bude, daga inda Zahra take ta hango wani Royal bed milk
Mai azabar kyau, Bata Kara gaskata maganar zilan ba Saida ta shiga ciki, a gefen bed din
Zahra ta zauna tana fadin "Bari na Dana gadon Aunty zilai".
Dariya sukayi su suka "kin gani ko wallahi nifa a jiya da kyar nayi barci duk zulumi ya isheni ji
nayi Ina tsoron gidan yayi girma da yawa, na jinjinawa matar gidan".
"Wai Mai gidan Bai taba aure ba a gaba dai ze kawo matar".
Baki zilai ta Kama tana fadin "to shi wane irin kudi ke gareshi da ze Gina irin wannan gidan
Yana saurayinsa".
"Bani wayar Aunty zilai wannan hirar ba karewa zatayi ba kada lokaci ya kure yau daga Asibitin
cikin gari zamu gidan su oga Sameer na gaishe da mommy". Wayar ta Bata suka fito tare ta
Kira Ammah suka gaisa sun jima tana fada Mata abubuwan da akayi mata jiya da Kuma
komawar da zasuyi yau, karfafa Mata gwiwa itama Ammar tayi tana fada mata ta kwantar da
hankalinta In Sha Allah ba komai. Lokacin da suka fito har Iya Rahane ta shirya table din Rukayya ma ta fito.
Kallon su Rukayyar takeyi ganin daga bangaren da suka fito.
"Aunty Rukayya Ina kwana?"
Zahra ta fada.
",Lafiya kalau matar big bro, ya Naga kin fito daga bangaren mu".
"Au kema a can Kika zauna kika ki zama a dayan dakin kusa Dani".
Baki ta bade tana kallon Zahra. "Na shiga dakin Mai gidan na zauna tab ai wannan part din sai
ku".
"Mu suwa daga zuwa bakunta sai mu zaqe Ina laifin can din wallahi transfer zanyi, Ina dalili Ni
kadai kamar mayya kufa Nan ku uku ko ihun neman taimako kayi an taimaka maka amman Ni
kuwa ko kasheni za'ayi sai dai a dauki gawar da safe".
"Tab wallahi ba inda Zaki zauna a Nan ba haka big bro yace ba,a can yace ki zauna Dan haka
Babu Mai canza wannan Umarnin".
Dan turo Baki tayi "Ni na taba ganin haka mutum ya ringa saka doka a gidan mutane inaga
baisan girman gidan ba shi yasa yake bada wannan Umarnin, gaskiya da sake".
Time Rukayya ta duba a waya kizo muyi break yanzu zakiga ya Sameer yazo tunda da wuri
za'ayi Miki sauran gwajin".
Suna cikin break din Sameer yazo Saida ya jira a mota suka Gama sannan suka tafi, a ANC
department suka samu doctor Haseenar sun awon ciki.
Ba yabo ba fallasa ta tarbesu ba kamar jiya ba ko yanda suka ringa Yi jiya da Rukayya yau ba
haka bane daga gaisawa Bata Kara cewa komai ba, itama Zahra saita Kama kanta Rukayyar
ma haka. Gwajin jini ta Kara tura Zahrar ta hadasu da wata ma'aikaciyar su ta rakasu main lab
aka dauki jinin. Lokacin da suka dawo sun Gama ante-natal din gwajin jira ta dauko da scanning din ta Kira
Sameer tana fadin mu hadu a office dina".
Ta kashe tana fadin Bismillah Ruky muje office dina tunda mun Gama da Ante-natal sai zuwa
anjima zamu Fara gyne".
A kofar office din suka samu Sameer din ya rigasu zuwa.
Sai da suka zauna sannan suka gaisa da Sameer din, bayani ta farayi Masa na gwaje-gwajen
jinin jiya "a cikin jininta ba wata cuta ko kadan kawai scanning ne ya nuna Mana akwai matsala
a mahaifarta ta fibroid amman be wani girma sosai ba za'ayi aiki a cire mata tun kafin ya girma
Amma zamuyi admitting dinta zuwa one week tana karbar magani kafin ayi surgery din, Dan
haka sai ta Kira mijinta ta fada masa yazo da mutane muna son jini leda biyu, zamu jira results
din Nan ya fito total blood count za'ayi Mata".
Rukayya ce tayi farat ta tambayi doctor Haseenar "yanzu dole sai tiyata baza'a iya Shan magani
ba a warke?"
Kallon tsab Dr Haseenar tayi Mata kafin tace "hanya mafi saukin rabuwa dashi ta sai dai aikin
gaskiya".
Tunda doctor Haseena ta Fara bayani gaban Zahra ya yanke ya Fadi idan da abinda taki jini a
rayuwar duniyar Nan to tiyata ce.
Nisawa Sameer yayi kafin ya samu karfin halin fadin.
"Thank you so much doctor kome kenan zakiji idan munyi communicating da mijinta saina kiraki
later"
"Ok.ba damuwa Allah ya sauwaqe".
"Amin".
Rukayya ta fada Dan zahra ba bakin magana har suka shiga mota tana cikin tashin hankali,
kuka takeyi irin na zuci din Nan sai dai hawaye kamar an bude famfo.
Saida suka fita daga Asibitin har sun shiga court road sannan Sameer ya Dan juyo, Madam kiyi
hakuri in Sha Allah ba wata matsala idan Allah yasa yin surgery din ne yafi Alkhairi ayi kawai
Kinga kema saiki huta da zulumin ciwo duk wata".
Rukayya ce juyo tana fadin "gaskiya kada ki yarda a yanka ki haka kawai Ni banma yarda da
maganar Haseena ba, kawai ta jawo Miki wahala Ni Daman da anyi shawara Dani da Babu
abinda zesa Haseena ta duba matar big bro haka kawai taje ta jawo Mata matsala da gangan
bakaga yau sai wani share mutane takeyi ba, wani ya Hana big bro din ya aure ta". Wata uwar harara Sameer ya zubawa Rukayya "Billahillazi Zan saukeki a Nan ke wace irin
mutumce da bakinki bashi da controlto me kikayi ke Nan? wannan ai shashanci ne keda Zaki
kwantar Mata da hankalinta shine Kika sokawa zancen wuqa".
Ita dai Zahra maganganun Rukayya sun daga Mata hankalin kenan da wata jikakkiya a tsakanin
wannan likitar da Mahmud.
Wallahi ko likitoci sun Kare wannan ba zata Kara dubata ba shi yasa Kennan jiya ta damu da
sanin waye mijinta da dangartakar ta da Mahmud.
Tunda Sameer ya yiwa Rukayya buyagi Bata kara magana ba har sukazo junction din gidan
shatima. "Wai yaushe mommy taje gidan Hajyr makwararin?".
"Dazu da safe na kaita Wai zasu karbi lefen mujahida".
"Ok Allah ya Sanya Alkhairi. Dan Allah ya Sameer Zan sayi alawar Madara idan ka tsallaka Zan
kaiwa Hajiyar makwarari".
"Kice dai Zaki saya bawai Zaki sayawa Hajiyar makwararin ba".
"Allah tana son shi sosai"
A kofar gidan Hajiyar yayi parking Babar mommy ce.
Da karadi Rukayya ta shigo gida yayin da Zahra da Sameerke biye da ita a baya, suna runfa
ana hira da kunnen Rukayya da 'ya'yan dangi da mommy masu karbar lefen basu Fara zuwa ba
gaishe dasu yaran sukayi suka fice, sukabar mommy kawai. Cikin nuna kulawar mommy ta kalli
Rukayya dake gaba. "Ba dai har kun gama da asibitin ba?" " Mun Gama kin ganta Nan Wai doctor Haseena tace zata yankata tayi Mata tiyata Dan nace
ban yarda da ita ba shine ya Sameer yake ganin bekena".
Sallama Zahra tayi tana Dan tsugunnawa tana gaishe da mommy cikin muryarta Mai sanyi da
nutsuwa da Kuma alamun tasha kuka.
Mommy kallonta tayi tana fadin "Masha Allah tabarakalla sannu ya jikin naki?"
Da sauki sosai".
To Allah ya Kara lafiya naji Rukayyar na fadin tiyata za'ayi Miki".
"Eh haka suka fada"
Hajiyar makwararin ce ta fito tana fadin "wa nakeji kamar Rakiya a gidan nan waye ba lafiya naji
ana magana tiyata".
" Kin ganta Hajiya, matar Mahmud mutumin ki ce".
Mommy ta nuna zahra.
" Wai Amaryar ce? Sannu kinji menene ya sameki?"
Rukayya ce ta fada Mata.
Mommy ta kalla "Ni Zan hada Mata maganin wannan lalurar ba sai anyi Mata aiki ba, ki huta
Rukayya ki shiga Nan kurmi ki sawo min abin hada maganin a Nan na hada Mata insha Allah
sai dai ya narke yabi jinin al'ada.
"Amma gaskiya ba wanda ze yanka ta Kamar kabewa ku 'ya'yan zamani komai a yanka ta haka
ne daji yake shiga ai ta fama da rai idan yazo da karar kwana kiga an mutu, daina kuka, samiru
kiwawo min mijin nata na fada Masa da bakina Babu me yi Mata danyan aiki ko haihuwar fari
Bata yi ba a jawo mata tsuguniya mazan yanzu marasa hakuri". Ta fada tana nufar uwar dakanta.
Ita dai mommy Shiru tayi Saida Hajiyar ta shige sannan ta dubi Rukayya "Wai Ke Sai yaushe
hankali ze Gama Miki jiki? Kinzo kin kwatsa zance gashi Nan kin tubzura Hajiya Mai hanata
hada maganin Nan sai Allah, itama Kuma Mai lalurar maimakon ki kwantar mata da hankalinta
A'a tashin farko kin sokawa zancen wuka, ai kin kyauta". "Wallahi ba haka bane mommy Kinga dai muna good term da Haseena amma wallahi yau
kamar ma Bata taba gani na ba sai cin magani take yiwa mutane da dacin rai want ya Hana Ya
Mahmud din ya aureta taga yarinya ta gigice zatayi mata illa haka kawai".
Maficin dake kusa da ita Mommy ta jefawa Rukayya tana fadin fita ki bani guri tunda kin Zama
babbar kwabo kin tasa yarinya gaba kina fadar abinda be Dace ba".
Wata uwar harara Sameer ya saukewa Ruky ji yake kamar yayi Mata duka duk ta cakude
lamarin tana kokarin ta saka jinin yarinyar mutane ya hau, tun sassafe Mahmud ya Kira shi
Yana fada Masa ya kira Rukayya yace ta fadawa Zahra ta bude wayarta ya manta shaf sai fa
yanzu ya tuna. Wayarsa ce ta Fara ringing "shine ya kira" ya fadawa mommy.
"Ka dauka kayi Masa bayanin halin da ake ciki".
"Nasan Haseena ce ta fada Masa shine ya Kira yaji".
Wayar ya saka a speaker yanda zahrar ma zataji.
Bai jira komai ba ya Fara fadin "Sameer wace magana naji Haseena tana fada min? kada ka
Bari su taba min yarinyar nan Zan kaita inda ya Dace, naji tana fada min wasu nonsense wallahi