AUREN HUCE HAUSHI 1 COMPLETE BY MAMAN FATIMA.pdf

Author :  Maman Fateema Category :  Taskar Novels

Chapter   3 / 43

6K to 9K   out of 127.3K words

An raba kayayyaki na alfarma na bikin, sai magariba taron ya tashi, zuwa yanzu 'yan Qananan
maganganu sun Fara fita a tsakanin kawayen Zahra tunda har zuwa lokacin ba wani duriyar
Ango ko wani nasa, sai Dan kus-kus ake abinda yafi bada mamaki bai wuce ganin anata faman
programs ba normal.

Su Mahmud Basu samu kansu ban sai bayan sallar insha'i lokacin suka zauna Dan wuni guda
suna ta faman sunturi daga can zuwa can abin dai ba sauki dan su sameer suna zuwa gidan
suka babbago aikin da sai anyi sati ba'a Gama ba Dan sunce tsarin gidan gaba daya za'a sake,
basunda ta cewa tunda oganninsu ne sai godiya suka dunga zubawa harda su Bashir. Gurin karfe goma malam ya Kira Mahmud a waya yace yazo cikin gida ya same shi.
Saida ya leka falon iya Abu suka gaisa tana faman jansa tana ita ce ta karfen Dan haka ita zata
koma sabon gidan a kawo Amarya nan.
Da haka ya karasa turakar malam Yana zaune a falo Yana sauraren wa'azi a TV, yayi sallama
Malam din ya bashi izinin shiga, Nan kasa ya zauna Yana gaishe da malam din.Wasu manyan
ledoji malam din ya nunawa Mahmd Yana fadin.

"Dauko wadan can kayan ka duba daya Wanda nasa a kawo maka ne biyun Kuma wadannan
masu kungiyar ne ta taimakon tsangayu suka kawo ga lemuka can da ruwan roba sun kawo

yafi catoon dari sunce kada ayi abinci ma duk za'a kawo, har na rasa da wane bakin zan gode
musu, sai dai Ina rokon Ubangiji s.w.w yafi mu yabawa, naji su Habibu ma sun ce sun dauko
aiki Mai yawa a wancan gidan ko?"
"Eh wallahi munyi-munyi su Bari suka Kiya Wai haka aikin Qungiyar yake in dai kana musu aiki
idan wani Abu ya sameka Mai Dadi ko marar dadi su zasu tsaya maka".
"Alhaji yace min kun shiga dazu bayan sallar magariba har da bakin kunyi Masa godiya, kun
kyauta haka ake so".

Lokacin Mahmud ya koma dakinsu Habib baya Nan gurin da yake aje makullin lifan dinsa ya
duba ya kuwa you sa'a yana nan, lodojin ya zube a kan gado ya dauki makullin ya rufe dakin ya
hau mashin din yayi gaba.
Bai dawo ba sai kusan Sha biyu da rabi har lokacin kuma Habib baya dakin yasan suna can
suna kujuba kujuba.

Yauma Zahra taso kwana a dakin Aunty Hasana saboda tana bukatar kadaicewa Amma Sajida
ta matsa Mata da mita Saida suka tafi Amma fa zuciyarta Bata da nutsuwa gashi tana ankare
da Aunty Hasana tun jiya da dare a taje can gida cikin gari Bata da nutsuwa ko alama Amma
tana ta kokarin ta basar sai dai ko Yaya mutum ya shiga damuwa indai kayi Masa farin Sani
zaka fahimta, ita Abu mafi Bata mamaki yanda aketa kwaramniyar bikin ba wani canji sai dai
abunda baza'a rasa ba duk da Daman ba wata muguwar bidi'a ba ta had'a, walima ce kawai
Bata Sami ba saboda tace ita malam Tijjani Ahmad zeyi Mata Kuma bayanan yana Umara.
Tunda tayi sallah ta kasa tashi daga gurin tana kallon su Sajida sunata sabgarsu, Amma ita da
wata irin faduwar gaba ta tashi ta rasa nutsuwarta kwata kwata da kyar ta tsahi sauko kasa
gurin Aunty Hasana a fall ta sameta tana hadawa Abbansu Haidar break fast.
Gurin dining din ta karasa tana gaishe shi sannan gaida Auntyn.
Dakin Auntyn ta shiga kwanciya tayi tana ta faman sakawa da kwancewa zuwa yanzu dai tasan
tabbas da matsala sai dai yanda ba Wanda ya fad'a Mata shi yasa itama ta zubawa sarautar
Allah Ido taga iya karshen film din tasan ko menene yau dai za'a yita ta Kare tunda yau ne
deadline duk wata kunbiya kunbiya za'a zazzageta.
Tun karfe goma Mai yiwa Amarya make up tazo Amma kememe Zahra tace ita bataso a kyaleta
aka dunga yiwa kawayenta, ganin guri ze kure ne Sajida take ta fadawa Aunty Hasana Saida
tazo sannan akayi Mata light makeup Amma fa duk da hakan tayi karshen kyau, farin material
ne ta sakata Mai touching din sky blue sai aka daura Mata head shima sky blue din takalman da
pos din duk sky blue din ne.
Wani san sanyan kyau tayi na ban mamaki, komai na Zahra Mai kyau lallai zaharar ce Dan duk
cikin kawayen Bata da mahad'i.

A babban masallacin juma'a za'a daura auren Masha Allah, ango ya fito Shar abokansa sai
mamakinsa suke Basu taba sanin kyawunsa da cikar haibarsa ya Kai haka ba sai daya fito sun
Sha mamakin kwarai har wasu suka Fara kokonto a kansa, Yana kallon yanda idanun sukayi
Masa caa. Dan dakakkiyar getzener ta saka ga takalman da agogo ga hula, Sam bazaka taba cewa Wai

alamajirin malam bane ba, ga wani irin kamshin tunda ta tumkaro taron abokanensa kamshin ya
hade gurin.
Daga gefe sameer ne da abokinsa Naraddeen suna tsaye lokacin da Mahmud ya fito Sameer
ya kalli Naraddeen din yace "wallahi wannan guy kwallon Dan duniya ne na rasa Gane kan
alkiblar daya kalla Wai aure zai daura shi kadai kamar marara gata, ni so nake Naga karshen
wannan wasan kwaikwayon nasa. Daga inda yake tsaye ya kafe Sameer da Ido ko Bai fad'a ba yasan me yake nufi tun jiya yake
tuhumarsa aka zuwa da abokinsa da yayi duk da ya nuna Masa wannan ba wata matsala bace
Amma har yanzu Yana hukunta shida idanunsa.

Masha Allah dubban mutane ne suka shaida daurin Auren FATIMAH ZAHRA AHMAD SANI da
Angonta MAHMUD MUHAMMAD DANGE akan sadaki dubu dari uku lakadan ba ajalan ba.

Daurin aure daya bawa dubun mutane mamaki bare wadanda sukazo daga bangaren Mushahu
sunyi mamaki kwarai sunan Amarya dai shine Amma ba mijin daya gayyato su bane yayin da
yan unguwa ya Zama abin kasawa a faifai ana yawo dashi, da yawa na ganin beken Alhaji Jafar
na aurawa bakon da ba'asan asalinsa ba yarinya kamar Zahra yayin da wasu ke fadar ai Dan
ba 'yarsa bace shi yasa yayin wannan danyan aikin.
.......
💋❤️AUREN HUCE HAUSHI 💋❤️


Page four🔷


___________''📖🖋️


Wata marokiya ce irin dattawan Nan da suke bin manyan marok'a ta biyo tawagar masu
dawowa zuwa gida kasancewar gidan ba nisa daga masallacin juma'ar, itace ta rangad'a guda
har sau uku ta Kara da fadin "Alkawarin Allah ya tabbata an daura auren Fatima Zahara'u da
zukeken Angonta Mahmud Ubangiji Allah ya bada zaman lafiya da kazantar daki Bata shara ba,
munzo much arziki mubar arziki a gurinsa.
Kamar saukar aradu haka maganar ta shiga kunnen Hajiya mama, batasan lokacin data
tsallake mutanen falonta ta fito ba dankwalinta a hannu, tana fadin "me naji ana fad'a wa aka
daurawa aure da Mahmud naji kowa".
"Eh haka ne Kam Alkawarin Allah ya ciki Zahara'u ta Zama matar Mahamuda"
Ta debo wata gudar ta Kara rabsawa.
Dai dai lokacin Hajiya kaltume aminiyar Ammah ta fito ta dukulawa wannan marokiyar kudi
sannan ta Mika Mata babbar leda Mai abincin biki har da ruwa da lemo.
Cikin rashin nutsuwa Hajiya mama ta nufi dakin Amma ko sallama Babu ta Fara fadar "Hajiya
kinji abinda naji ko kunnena ne ya jiyo min ba dai dai ba?".
Kallonta duk 'yan dakin suke kafin Ammar tace Mata "nima haka naji kamar yanda kikaji sai dai

ko shirme takeyi ita Mai rokon tunda ba sanin su tayi ba".
"Eh gaskiya Kam sai dai hakan".
Ta juya ta koma daki. Bata zauna a falon ba uwar daki ta wuce, Asabe ce ta rufa Mata baya, a
tsaye ta sameta ta Goya hannu a baya tana Dan Kai kawo a tsakanin gado da madubi.
Waiwayowa tayi tana kallon Asaben kafin ta zauna a bakin gado, kusa da ita Asaben itama ta
zauna.
Tana fadar "Haba Hajiya Dan Allah ki nutsu bana son ki bada wata baraka a sabgar Nan keda
na fad'a Miki Daman malam na BANDE yace wannan karon aure sai anyi Amma ba da
Mushahun ba, Amma abinda yake daure min Kai malam na banden yace Wanda zata aura a
nesa yake Kuma yaga haske so sai akan lamarin duk yanda yaso ya Bata lamarin abin Bai
yuwu ba shine nace kawai a kyale tunda dai Wanda muke son a fasa da shin din aikin ya yuwu,
nasan dai da wuya ta Sami irin Wanda ta rasa a bay".
"Haka ne Amma abin dubawar waye wannan din sanan me yasa aka kudundune zance? Wai fa
Dan munafurci Hajiya Asma'u cewa tayi Bata Sani ba ke kin yarda Alhaji ze aurar da Zahra Bata
da masaniya, ko meye ma dai kyawaun ya kare a auren Hadi tunda nasan ba wani sai
Mushahun shi Kuma ya Kara gaba kamar sauran". Ta fad'a tana kwafa, mikewa tayi tana gafar "Bari na fita sai Naga kul uwar daka".
"Allah ya taimaki uwar dakina, aikinki Yana kyau".
Asabe ta fad'a tana mikewa itama.
**********
Daga gurin daurin aure Kai tsaye gidan gonar Alhaji Jafar suka wuce har tawagar angon bisa
umarnin Alhajin tun safe ya turo Mai sunasa (magaji) yaje ya fadawa Baba malam.
Anci an Sha kamar ba gobe mutane sunyi mamakin irin wannan karamar arzikin dan duk zarin
mutum sai dai yaci ya Bari ruwa da lemo kuwa kamar banza.
Abokan Mahmud kuwa sai Dan biki suke Masa.
A gidan malam ma Masha Allah anci an Sha Yara sun san ana biki a gidansu, Iya Abu ma tayi
nata taron komai baja baja makotanta ma sunsan ana hidimar arzki a gidan Kuma Suma sunzo
Mata harda masu riko abin arzikinsu su kawo Mata.



******** A guje Faruq ya Fado falon Aunty Hasana,danta ne na uku Yana rungume da babbar
rigarsa ta daurin aure daya saka Yana Fadi "Aunty Zahra wallahi Naga mijinki ba wannan Uncle
din bane na kano wallahi wanna yafi shi kyau Baki gani ba yanda yake rabawa marok'a kudi ba,
Kuma Dan gayu ne sosai Naga Uncle Abdul Hakeem ma ya rugume shi Yana ta dariya, Dana
tambayi Auncle Imam yace min sunansa uncle Mahmud".
Tunda ya shigo Yana karadin Nan ta zuba masa Ido tana sauraren abinda yake fad'a, kana
ganinsa kasan har zuciyarsa abinda yake fad'a din gaskiya ne, wani irin gingirin taji kanta yayi
mata, nan ta sulale ta kwanta kan kujerar ta saka hannunta ta rufe fuskarta wasu hawaye na
zubo Mata masu zafi. Sajida da Amatu suka nufi gurin Faruq din suna neman Karin bayani.
Yayin da wasu da yawa suke ta sabgar ciye ciyensu Dan Suma Kam an kawo koma enough.
Kamar yanda ya fad'a haka Suma ya mayar musu Dan su harda Karin bayanin yayi musu

kasancewarsa Mai surutun tsiya.
A hankali Sajida ta kamo hannun Zahra Dan Bata fatan wani daga cikin bakinsu su fuskanci an
samu matsala gaskiya, kamar masu you shawara suka shiga dakin Auntyn saboda Nan ne
baza'a shigo ba.
Bakin gadon ta zaunar da Zahra ita Kuma ta janyo stool ta zauna har lokacin Bata saki
hannunta ba,tana Jin yanda ilahirin jikinta yake rawa.
Hannun ta Kara jimkewa cikin nata tana fadar.
"Cool down Mana bestie haba take it easy, kada ki tada hankalinki Taya Zaki kama maganar
faruq kinsan dai ba wani hankali ya Gama Masa jiki ba".
Kai ta shiga girgizawa cikin muryar Kuka tace.
"Wallahi Saji akwai matsala kema Kuma kin sani sai dai kik'i fad'a idan ba matsala Ina su
Maryam da mukayi dasu zasu zo tun kwana ukunda suka wuce Ina shi kanshi uban gayyar ina
su Deeni dasu Aliyu, kowa ka Kira sai dai kaji switch off baka haka ba".
Ta fad'a tana fashewa da wani irin Kika.mai taba zuciya.
"Kiyi shiru Dan Allah kada ki janyo hankalin mutane Mana kinga ga Amatu can zataji dasu ki
nutsu har muji meye gaskiyar maganar Mana".
"Ki barni nayi kuka wallahi na gaji nikenan kullum matsala daga wannan sai waccan na rasa a
Ina matsalar take ni wallahi bana son kowa ma a kyakeni haka Nan bana son auren, bana so
wallahi ni nagaji Allah Jordan zan tafi bazan zauna ba, bazan Kara Zama a kasar nan ba".
Ta fusge hannunta daga na Sajida ta yunkura ta tashi ita dai Sajida Bata San ta Yaya akayi ba
sai ganin Zahra tayi ta kifa kan gadon tana wata irin fuzga da gudu ta karasa kusa da ita tana
jijjigata tana fashewa da kuka tana fadin "ki tashi Dan Allah wayyo Allah na".
Baba Tabawa ce ta bude kofar ta shigo, Dan tunda tana kusa dasu Faruq ya shigo da wannan
maganar duk da tasani Dan Aunty Hasana Bata rufe Mata komai ba ta fad'a Mata tun jiya, shi
yasa data ga sun nufo dakin hankalinta ya kasa kwanciya ta biyo su tasan koya Sajida zatayi
Mata kalamai ba kamar ita ba tunda abinda babba ya hango yaro koya hau iccen rimi bazai
gano ba.
Turus tayi tana kallon Sajida dake Kuka bil hakki tan jijjiga Zahrar.
Da sauri ta karaso tana fadar "ke 'yan Nan menene haka?".
Hawaye jage-jage Sajida ta dago tana fadar "wlh Baba Tabawa kawai tana kuka tana
maganganu tana tashi kawai sai Naga ta yanke jiki ta Fadi?.
Wani ruwa Baba Tabawar ta dauko a kan bedside fregde din Nan ta zubawa Zahrar a fuska
Amma shiru ta Kara watsa Mata Nan ma shiru cikin tashin hankali ta lalubo Yar wayarta rakani
toilet ta mikawa Sajida "ungo maza Kira min Aunty zakiga an saka Maman Ali yi sauri".
Bugu biyu Auntyn ta dauka tare da sallama, gani Sajida ta rasa me zatace ne yasa ta mikawa
Baba Tabawa wayar.
Can Kuma tana ta faman" hello Baba"
Abinda taji kenan lokacin data Kara wayar a kunne cikin sauri Baba tace "yi sauri ki turo a Kai
Zahara'u asibiti wallahi gata Nan a suma min yayyafa ruwa a banza".
Bata jira taji me za'a fad'a ba ta kashe wayar.

Abdul Hakeem Aunty Hasana ta lalubo a waya lokacin suna tsaye shi da Mahmud suna
magana wayar Abdul Hakeem dince ta Fara ringing Sunan Aunty Hasana ya gani ya daga har

zai Fara Mata abunda ya saba ta tsayar dashi tana fadin "Dan Allah maza kaje gidana ka
dauko Zahra ku wuce asibiti mu hadu a can wai Suma tayi"
Kit ta kashe wayar.
"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un yake ta Nanatawa da sauri Mahmud ya tambaye shi "lafiya
meya faru".
"Bari kawai ba komai Ina zuwa yayi gaba da sauri jikinsa har rawa yake Yana tafe Yana laluben
key din motarsa. Da sauri Mahmud ya biyo bayansa' Sam baiji key din ba sai daga baya ya tuna
tana hannun mustapha yaje gari ya dawo.
Tsaki yayi daidai lokaci da Mahmud din ya karaso Yana fadar"Dan Allah Wai menene Naga duk
a rude".
"Bari kawai Wai Zahra ce ba lfy zan kaita ASIBITI".
Kallon yayiwa Abdul Hakeem din kafin yace "shine Kuma zakaqi fad'a min".
Hannu yasa ya yafito Sameer, cikin bada umarni yace
"Dauko motar can kuje da Abdul zaku Kai madam asibiti". Ya juya ya koma gurin su Habib.
Har sukaje gidan Auntyn Abdul Hakeem Bai daina mamakin Mahmud ba, yanayin yanda yayi
maganar kawai kasan da abinda ya taka umarni fa ya bada, su dai a zahiri ai Sameer ne uban
gidan Mahmud tunda kowa yasan aikin NGO's ya kawo shi garin har suka hadu da Mahmud din
suka dauke shi yake musu aiki a sauran makarantun tsangayun na cikin gari Dana kauye. Da sauri Abdul Hakeem din shiga gidan Auntyn ta kofar baya gurin kitchen ya shiga koridon
dakunan barcinta.
A tsaye cirko cirko ya samu su Baba Tabawar har lokacin numfashinta Bai dawo ba.
Da sauri ya karasa gaban gadon yasa hannu ya dauketa kamar wata Baby yayi waje da ita.
Sajida da Baba Suka rufa Masa baya.
Da sauri Sameer ya bude Masa seat din baya ya sakata Sajida ta shiga ita da Baba shima
Abdul Hakeem ya shiga gaba da gudu Sameer ya fizgi motar. Saida ya daidaita a titin sannan
ya kalli Abdul Hakeem din "ina muka nufa?".
"F.M.C zamuje tunda yafi kusa".

Nan da Nan aba karbeta likitoci suka rufu a kanta, suna Nan tsaye Aunty Hasana tazo ita da
Inna maimuna sai Hajiya kaltume.
Suma tsayawa sukayi a gurin Baba Tabawa tana maida musu yanda akayi ita dai Sajida ba
baka sai sharar hawaye take.

Su Abdul Hakeem suna suna gefe daga zuwansu Mahmud ya Kira akai sau biyar idan ya Kira
Sameer sai ya Kira Abdul Hakeem, daga Jon yanayinsa kasan Yana cikin damuwa abinda ya
Kara daure Abdul Hakeem Kai yandq Sameer yake amsa wayar Mahmud cikin kulawa da bada
girma. Sun dauki a kalla minti arba'in kafin babban likitan ya fito sannan sauran Suma suka fito.
Su Abdul Hakeem sun bin bayan likitan kamar yanda ya bukata Amma ganin an gungoro Zahrar
a gadon daukar marasa lafiya yasa suka nufe ta da sauri suda su Aunty Hasana.
Wanda ya turo gadon ne yace "ai ta farfado ba wata matsala ana so ne dai ta samu hutu sosai
jininta ne yaso Hawa Amma cikin ikon Allah anyi controlling dinsa".
"Oh no 'yasu Allah ka dubi lamarin wannan 'yar maraiya duk da Bata tashi da rashin gata ba sai

yanzu ka kawo Mata Tata jarabawar Allah ka shiga cikin lamarinta".
Aunty Hasana ta fad'a itama tana goge hawaye.

Baba Tabawa dasu Sajida suka amsa da "ameen ya Rabbi"
Dakin 'yan da'i da'a aka kaita tunda tana bukatar isolation.
Saida komai ya Zama dai dai an saka Mata drip sannansu Sameer sukaje gurin likitan. Fad'a
yayi so sai akan yanda akayi har karamar yarinya kamar wannan damuwa tayi Mata yawa har
har take barazana ga lafiyar ta.

A can gidan biki Kuma Amma ta rasa inda su Hasana da Inna suka tafi Dan hankalinta Bai
kawo Mata Hajiya kaltume ma Bata Nan ba sai da abokiyar zamanta tazo sannna ta fuskanci
itama Bata Nan din wayarta ta dauko ta Kira Hasana, lokacin tana

3 / 43