YAKANAH! BOOK COMPLETED BY TAKORI KABARA .pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   9 / 15

24K to 27K   out of 43.2K words


"Don Allah Yaya ki yi hakuri ki yafe min, wallahi ba zan kara ba".
Ta ce, "Ni me ki kai min da za ki bani hakuri? Ke aka yiwa laifi ke za a bawa hakuri. Me kika fishi

ko me kike takama da shi da za ki ce bakya son sa?
Ban da Allah ya kashe ya baki ai Sulaiman ba tsaran ki bane, ba za ki gano gatan da aka yi
muku dukkanin ku ba sai nan gaba. Wannan shi ne karshen kauna da za ki nunawa Hadizah, ki
rungumi iyalinta a bayanta, sai dai in dama ba son ta kike yi ba........!"
Ta kara sautin kukan ta,
"Na tuba Yaya, na bi Allah na bi ku, na yarda zan zauna da Baban Munib ko ba ya so na.......".
"Shi ya ce miki ba ya son ki? Bana son mummunar fahimta, ko bai miki son soyayya ta aure ba,
yana yi miki son 'yan'uwantaka, wadda a hankali in kin sadaukar da kanki gare shi za ta rikide ta
koma soyayyah!.
Sanda aka aura min mahaifin ku ban san shi ba, ban taba ganin sa ba. Haka aka lullube ni aka
kawo ni, ko sunana bai sani ba nima ban san nashi ba. Amma kyautatawa da sadaukar da kai
ya sa a yau ba abin da muke so da kauna sama da junan mu, har muka kai ga haifar ku daya
bayan daya. Kina gani har yau bai taba yi min kishiya ba, bai taba bata min rai ba sai bisa
kuskure.
Bacin raina na nufin tashin hankalinsa, fushina na nufin tabarbarewar al'amuransa. Ki yi auren
BIYAYYA ba SOYAYYA ba ki ga wacce irin riba za ki samu a cikin sa? Idan mun san babu riba
ba zamu ba ki jarin ba".

Fati ta share hawayen ta, cikin zuciyar ta tana cewa, mazan da dana yanzu ai ba daya bane
Yaya! Balle wadannan da suka hantse cikin ilmummukan zamani masu gigitarwa, suka saba
ganin mata iri-iri dai-dai da tsarin rayuwar su. Ina zan iya burge shi balle har ya kaunace ni? Ina
zan iya mai da kaina irin Yaya Hadiza?Yaya ta yi murmushi irin na manya wadanda suka san
cewa ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, sarai ta gane abin da Fati ke nufi; Hadiza 'yar gayu ce,
kuma wadda ta gogu cikin zuzzurfan ilimin boko, ita kuwa 'yar Islamiyyah ce, wadda Allah da
Annabi sune kawai a gabanta, wato dai ita 'yar Arabiyyah ce wadda ta horu ta goge cikin
ilmummukan addini daban-daban da fadin Allah da manzonsa. Wadanda 'yan bokon irin su
Sulaiman ke wa kallon 'yan kauye, wannan banbancin a farrake yake.
Ta ce,
"Fati kowacce mace da kika gani da kissarta aka haife ta, sannan kowacce da yadda Allah ya
halicce ta. Sai dai ra'ayi da akida sun banbanta. Amma fa duk sunan su daya (MACE), kuma
abin da ke jikin wannan shi ne a jikin waccan, ba wadda ta fi wata a matantakar sai dai ko
kazama da mai tsafta. Fati ke mai tsafta ce, har a makaranta tun daga firamare har sakandire an fahimci tsaftar ki an
kuma sha baki kyauta a kanta. Wannan kadai kika rike jigo ne a gidan aure, kuma ya ishe ki ki
yaki zuciyar kowanne da namiji ba Sulaiman kadai ba.
Kamar yadda kika ce baki da abin da za ki burge Sulaiman sai in ce a'a, Fati kina da shi,
HANKALI da sanin CIWON KAI sune manyan halayen da ke burge namijin da ya san ciwon
kansa irin Sulaiman ba kyale-kyalen mace ba.........".
Fati ta dago ido tana kallon mahaifiyar ta,
"Yaya kina nufin Baban Munib bai fi karfina ba?"
Yaya ta yi murmushi a karo na uku, ta ce, "A doke kam idan za ku gabza ai ya fi karfin ki, amma
a zaman aure bai fi karfin ki ba. Tunda kema mace ce kamar Hadiza, kuma a hakan da kike ba
sai kin yi wata kwarkwasa ko kwalisa Sulaiman zai so ki ba. A'a, maintain your own qualities

(rike taki sigar) kada ki aro wadda ba taki ba don ki burge.
Kwalisa, kwarkwasa da yanga ba sa burge namijin da ya san ciwon kansa, sai hankali,
nutsuwa, kamewa, ilimi da sanin ciwon kai. Wadanda dasu ne Hadiza ta samo zuciyar
Sulaiman ba appearance (kamantuwar ta ba).
Saboda haka Fati ki kwantar da hankalin ki, ki yi biyayya ga mahaifin ki, Alqur’anin ki, ba zai
bari ki tozarta a rayuwa ba…..!!".

Ta mike ta na murmushi cike da jin dadin kalaman mahaifiyarta, ko ba komi ta bata kwarin
gwiwa cewa, itama mace ce kamar sauran mata ba mata ta rako duniya ba kamar yadda
Sulaiman ke cewa.
Ta cire mata inferiority complex din da ya bi ya addabe ta, har ta ji za ita iya jure duk wani hali
da za ta tsinci kanta ko da a ce hasashen Yaya ba su zamo gaskiya a kan nata al'amarin
rayuwar ba.
Da kanta Yaya ta zaunar da ita a gabanta, ta sa kibiya ta tsefe mata gashin kanta da ya yi
masifar dauda ya duddunkule saboda rashin gyara har tsayin kwanaki arba'in da biyar. Fati sai
yawan gashi amma babu tsayi irin na asalin Kanawa, sannan ga shi da karfi kamar reza, sabida
ba ta taba shafa mishi relaxer ba, da za ta shafa mishi din da ya mike ya zama mai ban
sha'awa.
Fa'iza ta yi sallama ta shigo tana cewa, "Wai da gaske ne abin da nake ji?"
Ta tsuguna ta gaida Yaya ta amsa. Fati na hararar ta ta sake cewa,
"Don Allah Yaya da gaske ne? Yau an daurawa Fati aure?"
Yaya ta yi murmushi ta ce,
"Eh, haka Allah ya nufa". Ta ce,
"To, Allah ya sanya alheri". Yaya ta ce, "Amin".

Fa'izah kawar Fati ce, tare suka yi makarantar kwana a G.G.C Kano, kuma gidansu nan cikin
layinsu yake babu nisa zuwa gidan su Fati.
Yaya ta ce dama yanzu zan tura Abdulyassar ya kirawo ki, ki zo ki raka ta wajen wankin kai, na
san in na bar ta a haka za ta tafi gidan mijin. Daga nan ku biya ayi mata kunshi".
Fa'iza ta ce, "Gaskiya kam, kawo in karasa mata tsifar".
A daren sai ga kannen Dr. Sulaiman da wata kanwar Inna sun kawo akwatuna hudu shake da
kaya, ga shi ba su gayawa Yaya za su kawo ba balle ta tara masu karba.
Ta kama baki ta ce, "Yanzu Allah sai da aka takura Sulaiman da yin lefen nan yana fama da
halin da yake ciki?"
Ruma ta ce,
"Ai babu komi, abune da idan ba mu yi ba, ba zamu ji dadi ba".
Yaya ta ce,
"To Allah ya amfana, ya sa an yi a sa'a, ya kuma tabbatar da alherin da aka kulla, amin".

Fati kwana ta yi sallah, in 'yar ta yi kuka sai ta dakata ta kula da ita har ta koma barci, sannan ta
ci gaba, Cikin sujjadarta tana mai rokon Allah koma mene ne zai zo cikin rayuwar ta ya zo mata
da sauki.

Washegari ko tsakar gida ba ta leko ba, don gidan ya cika da 'yan uwan Yaya da dangin Malam,
saboda kowa da Hadiza a zuciyar sa babu wanda yake yin hayaniya.
Karfe uku na rana Fa'iza ta kawo mata kayan da za ta sanya, wani leshi mai taushi ruwan zuma
da kananun stones da ta kai Diallo (Zoo Road) aka yi mata dinki express, amma ya yi kyau
sosai, ya amshi dan karamin jikinta.
Fati siririya ce, kuma ba ta kai tsayin Hadiza ba, komi na halittar ta (natural) kamar fata, gashi
da hakora yiri-yiri, kuma farare kal wadanda ba ta wasa da kuskure su da listerine (mouth wash)
a duk lokacin da ta goge su. Shiyasa suke farare tas, kamar kankara
A can gidan Sulaiman shi ma cike yake da nashi 'yan uwan, suna ta gyare-gyare, suka gyara
gidan tsaf, dama tuni an kwashe kayan Hadiza har gadaje da (wardrove) an balle an fitar dasu
an kai gidansu.
Malam Ja'afar ya ba da daki guda aka kulle su, Inna tasa aka sayo katuwar katifa aka aje a
dakin da a yanzu ya zama mallakin Fati kamin a yi mata jere.

Kai! Rayuwa!! Ran dan adam ba a bakin komai ba, kowa ganin al'amarin yake kamar almara,
masu yiwa Hadiza addu'a na yi, masu kokawa na yi, masu korafin anyi gaggawar yiwa
Sulaiman wani aure na yi. Amma a bayan idon Inna, don kowa ya san irin son da Sulaiman
yake yiwa Hadiza. Shi kam bai ma gidan yana asibiti tun safe, ya kama wayoyin shi ya kulle kada Inna ta neme
shi. Don a daren jiya ta shaida mishi wai shi zai je da kanshi Karkasara ya dauko Fati da yara,
shi kuma ya kudire in har shi zai yi hakan, to wallahi sai dai idan ba za ta zo gidan ba.
Zuwa karfe hudu ran Inna ya soma baci da rashin samun Sulaiman a waya, sai dai ta yi mishi
uzri. Ta sani sarai sun takura shi, wanda su sun tabbatar abin alheri suka yi, sun gyara
zumuncin su da iyayen Hadiza, sun kawo wadda za ta rike 'yan jikokin su da gaskiya, sannan
sun aura mishi mai kama da Hadiza, kuma shakikiyarta. Akwai gatan da za su yi mishi da ya wuce wannan? Ta kudurce a ranta za ta tsayawa Fati da
addu'a da yakin zuciyar Sulaiman har sai ya so ta kamar yadda yake son 'yar uwarta.
Don haka sai Inna Talatuwa kanwar Malam da su Ramatu ne suka taho dauko amaryar a motar
mijin Ruma, don motar shi da ita ya fita, ta Hadiza tuni an sayar sai ta amfanin gida rufe cikin
tampol. Cikin girma da mutuntawa aka basu amarya. Yaya ta ce a bar mata yaran bayan sati
daya za a kawo su. Ruma ta ce,
"Yaya baki yiwa Fati nasiha ba".
Ta yi murmushi ta ce,
"Duk nasihar da zan yi mata na yi mata jiya, Allah ya sa ta je a sa'a".

A dakin Malam Ja'afar kowa ya fita ya bar su, ganin irin kukan da Fati ke yi kamar ana zare
mata rai sai zuciyar shi ta motsa. Ya ce,.

"Fadimatul-Zahra'u, ki daina kuka, ban aurar da ke ba sai a hannu na gari, hannun dana san
cewa ba zan taba yin dana sani ba".

Har aka iso gidan, wanda ba bakonta ba ne tana tauna maganar Babanta, me ya sa Yaya da

Baba suke son Dr. Sulaiman har haka? Me ya sa kowa ya budi baki kyakkyawan kalami yake yi
a kanshi? Me ya sa ita ba ta ganin kirkin nashi da nagartar tashi? Kenan ita kadai yake yiwa
rashin kirki, to laifin me ta yi masa?
Babu wanda zai ba ta amsar sai Sulaiman din kansa, wanda ta tabbatar har abada ba za ta ji
amsar ba in har sai shi din ne zai amsa mata.

Inna ta tarbe su ta rungume ta, ta kama hannun ta har dakin da a yanzu ya zan mallakin ta, ta
aje ta a bakin katifa. Fa'iza da Karima kawayenta na gefen ta, wannan ya shigo wannan ya fita,
amma ita tunanin ta ya tafi ga Baby Nanah wadda ta baro a wajen Yaya, ta shaku da yarinyar
sosai ta yadda har take mantawa cewa ba ita ta haife ta ba, ta alkawartawa ranta za ta roki Inna
ta karbo mata ita gobe ba za ta iya yin kwanaki bakwai ba tare da ita ba.
Zuwa karfe goma na dare gidan ya yi shiru, masu tafiya sun tafi, masu gajiya sun kwanta barci.
Su Fa'izah duk sun tafi, Inna ta shigo dakin rike da kulolin abinci guda biyu, ta ce,
"Kin yi barci ne Fati?'
Ta mike zaune rike da carbi a hannun ta, ta ce, "A'ah".
"To tashi ga abinci ki ci, tun dazu na so in kawo miki na san ba za ki iya ci cikin mutane ba".
Ta mike zaune ta karba, jellop din cous-cous ne wanda ya ji kayan lambu a filas din farko, sai
farfesun kayan ciki da ya ji kayan kamshin gargajiya a daya filas din. Inna da kanta ta zuba
mata ta soma ci.
Inna na kallon ta cikin tausayi, ganin yadda take cin abincin hannu baka hannu kwarya. Allah
kadai ya san tun yaushe rabon ta da abinci, mai yiwuwa tunda aka yi mata zancen aure da mijin
Yayarta.
Ta gama ci ta kora da gwangwanin fanta, ta koma ta kishingida Inna ta yi mata sai da safe ta
kwashe kulolin da plate din da gwangwanin fantar ta fita.

Karfe daya na dare Dr. Sulaiman ya shigo gidan, ya tabbatar zuwa yanzu dai kowa ya kwanta
balle a dame shi. Yana shiga dakinsa ya danno kofa ya murza key, hoton Hadiza cikin dan
kankanin ‘frame’ da ke kan ‘side drower’ na gefen gadon shi ya yi mishi sallama, tana
murmushin ta ni'imtacce cikin farar shirt din calvin-klien wato C.K. Ya zare falmaran din suit din shi ya zare tie ya fada a kan gadon, ba tareda ya cire takalmi da
safar kafarshi ba, ya fizgo hoton ya rungume a kirjin shi, ya yi magana cikin muryar kuka,
"Why do you leave me Hadizahh….???
Mai ya sa kika boye min cewa kina da brain cancer? Likitancin ki bai gaya miki cewa babu
ciwon da ba shi da magani ba? Hatta kanjamau ana nan ana kokarin nemo maganin ta. Mai ya
sa baki jira ni mun tafi tare ba? You left me incomplete, shattered….!"
Ya mirgina ya kara rungume hoton ya feso wani irin huci mai zafi.
“Da gaske Allah ba ya barin wani don wani, na tabbata da ba zai dauke ki ya barni ba. Ya za ai
a ce na zama mijin kanwar ki? Wannan cin fuska da cin amanar soyayya har ina? Ba za a yi ta
dani ba! I am for Hadizah only….!! Zan jira wa'adina Hadiza in iske ki acan mu ci gaba da
rayuwar mu a inda babu mutuwa…. balle ta sake raba mu……".

Ya lumshe ido, hawaye suka mirgino, ya budesu a hankali ya kai ‘frame’ din ga siraran lebban

sa, ya yi masa sumba mai tsayi da zurfi, kafin ya yi masa murmushi ya ce,

"I love you HADIZAH….Cikin kowanne hali INA SONKI HADDIZAHH!!!"
****

Masoyan Hadizar na da yawa, domin ita ma a can, Fadima, a dai-dai wannan lokacin, goshinta
na gaban mahalicci, cewa take.
"Ya Allah! Ka yi rahma ga baiwar ka Hadiza, ka yalwata kabarinta da haske da kamshi, ka yaye
mata duhun kabari, ka shayar da ita ruwan Alkhausara, ka bani juriyar cika alkawarin ta duk da
na san ba abu ne mai sauki ba……….".

Kafin gari ya yi haske tuni Dr. Sulaiman ya fice, sai karar motar shi Inna da ke lazimi ta jiyo.
Ranta ya baci sosai, ta dauki waya ta yi kiran sa, anyi sa'a wayar na bude ba shi kuma da hujjar
kin amsa kiran Inna.
Yana amsawa ta ce,
"Dabbobin da ke cikin gidanka za su koma makyankyasar su, sai in ce Allah ya hada mu da
alheri".
Kafin ya yi magana ta kashe. Ya juya wayar a hannun sa, "Dabbobi? Dabbobi? Su waye
dabbobin? Eh, dole ta kira kanta dabba a gidansa, tunda har za ka iya fita tana cikin gidan ba
ka gaishe ta ba".
Jikinsa ya yi sanyi, a hankali ya yi round ya juyo. Lokacin da ya iso gidan har sun faka kayan su
suna sawa a motar Jibril mijin Ruma, tana kokarin fitowa yana kokarin shigowa suka yi karo,
karaf, ya yi saurin ja da baya.
Ya ce, "Inna ki yi hakuri in je in yi signing yanzu sai in dawo in kai ku".
Ta harare shi ta ce,
"Ai ba kai kadai ke da mota ba, tunda ka iya ka kwana cikin gidan ka wayi gari ka fice ba tare da
ka binciki halin da muke ciki ba ai dabbobi ka dauke mu. Ni matsa ka bani hanya bana son
motar taka".
Ya soma magiya,
"Ki yi hakuri Inna, mu koma ciki mu yi magana, wallahi dama ban yi niyyar dadewa ba zan je ne
in dawo kuma ban san yau za ku koma ba".
Ta balla masa harara sai kuma ya ba ta tausayi. Wanda ya san Dr. Sulaiman a baya, ya kuma
ganshi a yanzu, zai yi wuya ya shaida shi in ba ya yi masa farin sani ba. Duk da ya aske
kasumbar da ta cika mishi fuska, hakan bai voye muguwar ramar da ya yi ba.
Ita kanta muryar shi ta canza ta zama mara amo, kamar ta mai fama da mura. Dara-daran
idanunsa sun zurma ciki. Kallo daya za ka yi mishi ka tabbatar da cewa har yanzu mutuwar
matar shi ba ta gama dukan shi ba.
Ta juya suka koma ciki, suka zauna a falo. Ta ce, "Ka kara YAKANAH Sulaiman, a kan wadda
kake da ita. Ka rike Fatima da amana, domin amanar ce a hannun ka. Jiya baka je ka ga ya
take ba, ya ta zo, meye matsalar ta balle lafiyar ta. Sannan yanzu ma ka fita ba tare da ka neme
ta ba”. Ya yi shiru kansa a kasa, a gaskiya! An takura rayuwar sa, an kakaba masa abin da bai san ya
zai yi da shi ba. Ba ya jin ko sautin shi zai iya bai ma Fati. Amma Inna gaskiya ta fadi, dole ya

dinga bincikar lafiyar ta.
A sanyaye ya ce, "Ki yi hakuri Inna, insha Allah, zan kula".
Ta ce,
"To Allah ya yi maka albarka".
Ya ji dadi har kokon ransa, ya ce,
"Za ku jiranin in je in dawo in kai ku?"
Ta ce, "A'a, ka maida hankali kan aikin ka. Ga Jibril zai kai mu, sai mun yi waya, Allah ya hada
mu da alheri".
Ya zaro kudi cikin aljihun sa ba tare da ya kirga ba ya mika mata, "Sai

9 / 15