YAKANAH! BOOK COMPLETED BY TAKORI KABARA .pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   2 / 15

3K to 6K   out of 43.2K words

mata) ya ce da Hadiza cikin wata irin lallausar murya da ya kasa yarda cewa tashi
ce.
"Wato fushi kika yi? Kika daina halartar karatun ki sabida na kore ki a kan kin yi min laifi?"

Ta yi ajiyar zuciya a hankali ba tare da ta juyo ba, ta ce,
"A haba Doctor! Wane ni in yi fushi? Mum dina aka kwantar a asibiti kuma ni nake jinyar ta sai
jiya aka sallame mu".
Ya nuna tausayi tsantsa a kan kyakkyawar fuskarsa, a fili kuma ya ce,
" Am sorry….!"
Ta juyo don ta yi mishi murmushi, suka yi ido hudu da dan Inna Halima, wani chemistry yayi aiki
cikin 'yan dakikai, ya kimsa wani al'amari mai GIRMA a zuciyoyinsu mai wuyar bayyanawa.

Gwiwoyinta suka yi sanyi, zuciyarta ta karye, duk wata soyayya da Allah ya halitta a zuciyarta
ta hadu ta tattare ta dunkule a waje daya. To haka shi ma. Jikin shi ya ba shi wannan ita ce
matar auren shi, wadda za ta samar mishi da 'ya'yan da zai yi alfaharin fitowar su daga tsatson
ta. Ya ce.
"A bani address zan zo in duba Mamar mu".
Muryar Dr. Sulaiman har tsakar kan Hadiza.
Daga ita har Surayyah sai suka yi mutuwar tsaye, domin abune da ko da wasa basu taba
kawowa ba. Kowa ya san shi da halin ko in kula da yake nunawa a kan mata, musamman
dalibansa, wanda ke burge kowa. Don haka sun sha mamaki.
Ita Hadiza ta kasa magana, sai Surayyah ce ta rairayo mishi adireshin Hadiza. Ya ce,

"Idan na zo wa zan ce?"
Ta ce,
"Hadizah!".
Ya ce,
"Hadizahh, am I welcome?"
Ta yi murmushi ta ce, "
You are welcome, our humble consultant!!".


(The beginning of everything kenan ).

Tun daga wannan ranar kakkarfar soyayya ta kullu tsakanin Malamin da dalibarsa, kullum suna
tare, a gida ne ko a ofis. Abin ya soma bayyana ga abokan aikin shi da abokan karatun ta, da
manyan likitoci mata na bangarensa da ke yi mishi asirtacciyar soyayya.
Wannan ya janyo ma Hadiza hassada karara a wajen mafi yawan abokan karatun ta, to ita ma
sai ta share su, saboda ta san Surayyah kadai ke kaunar ta saboda Allah.

***Auren su, wani abu ne da ya bar dimbin tarihi a asibitin Malam Aminu Kano, domin mafi
akasarin likitocin cardiology department kabilu da Hausawa sun halarta. Ba a taba ganin daurin
auren da ya tara 'yan boko tsantsa, manyan likitoci ziryan a unguwar Karkasara irin na Hadiza
ba. Suka tare a gidan Sulaiman da ke cikin asibiti, cikin wata irin soyayya mai wuyar fassarawa. Aure ne auren soyayya mai tsabta, wanda babu ha'inci, yaudara ko karya a cikin ta. Kar-ta-san
kar, kowa ya san asalin kowa. Dr. Sulaiman ya sha mamakin samun Hadizah a cikakkiyar mace
(virgin) wani abu da bai taba zuwa cikin hasashen sa ba, musamman in aka yi la'akari da
matakin karatun ta. Ba gaskiya bane zargin da ake yiwa da yawan 'yammatan (medicine), kawai
dan iska dan iskan kansa ne, amma da yawa abin da ya kai su shi ne a gabansu.

Cikin shekaru uku da auren su ta yi mishi tukuicin kauna da Munib da Muniba, wannan ya kara
sayowa Hadiza matsiyaciyar kauna a zuciyar Sulaiman. Daga baya ne da ya kammala ginin da
yake yi a Janbulo suka bar cikin asibiti suka koma, daga nan ne likitocin aka rufe bakin mahaifa
ruf, aka fuskanci cigaba. Hadiza ta kare karatun ta cikin nasara, da taimakon mijinta. Ita ce
(overall) a year din su. Da gudu aka rike ta a (labour room) wato dakin haihuwa. Sannan ba ta
tsaya a nan ba, ta ci gaba da halartar kwasai-kwasai a kan bangaren ta. Har kawo matakin da
ta ke kai a yau, na cikakkiyar likitar mata.

****
Karfe hudu na yammacin ranar litinin aiki ya tsagaitawa Dr. Hadiza, babu yawan marasa lafiya,
don haka ta soma hada 'yan komatsanta don barin asibitin.
Tun safe yau kanta ke damun ta da ciwo, gida kawai take so ta je ta huta. Amma dole sai ta fara
ganin Sulaiman tukunna, akwai wasu kudi da take son karba a wajen sa za ta biya ta kai ma
Fati tayi (registration).
Ta bude motar ta kenan ta zuba shirgin hannun ta, wata Nurse ta karaso da gudu tana haki tana
kiran ta,

"Dr. Hadizah!"

Ta juya tana kallon ta har ta karaso. "…….Don Allah ki taimaka, wata ce aka kawo yanzun nan
da alama ba za ta iya haihuwa da kanta ba, sai bleeding (zubar jini) take".
Ta kama kanta dake sarawa ta ce, "Lokacin tashina ya yi, yanzu Dr. Surayyah za ta zo.........”
Nurse din ta katse ta,
"Ki ceci rai kamar yadda kika saba, sakayyar ki na wajen Allah! Daga matar har Babyn suna
cikin hadari, ga shi babu likita ko daya duk sun shiga meeting. Sannan Surayyah babu wanda
ya san lokacin da za ta karaso".
Hadizah mai sanyin zuciya, matar ta kashe mata gwiwa da tausasan kalamanta. A take ta
manta da ciwon kanta, ta rufe motar ta koma gun mai haihuwa.

Wannan halayyar ta ce da ta sha banbam da ta sauran likitocin labour room da kowa ke kuka
dasu. Zuciyarta mai laushi ce, shi ya sa daga likitocin har Nurses zuwa labourers ke son ta,
suke jin dadin aiki da ita. Hadiza is simple, komi nata a saukake yake.
Da gaske ne matar ba za ta iya haihuwa ba. Ta kai matuka wajen galabaita, ta soma ba ta
dukkan taimakon da ya dace. Tana cikin aikin Dr. Surayyah ta iso, suka tsaya tare a kan matar
nan.
Cikin dan lokaci sun yi nasarar fitar da jaririn amma ba rai. To alhamdulillahi an samu uwar.
Tana zare safar hannunta ta ce da Surayyah,
"Ko da ban zo gobe ba, don Allah ki kular min da matar nan, haka kawai nake jin tausayin ta,
dube ta yarinya karama, ga dukkan alamu ba ta isa auren ba suka yi mata. Allah ne ya taimake
ta sun zo asibiti da wuri, da babu mamaki VVF ya same ta, wannan stitches da me yayi kama!".
Surayyah ta ce,
"Matsalar mutanen karkararmu kenan, ban san yaushe za su hankalta ba. A kullum fadakarwa
ake a radio da talabijin, amma kamar ana kara zuga su. Allah ya kyauta. Balle ma me zai hana
ki zuwa idan da rai da lafiya?"
Ta girgiza kai ta yi dan tsaki, ta ce,
"Bana jin dadi ne".
Surayyah ta ce,
"To Allah ya kawo sauki, a shafa min kan Munib":
Da haka suka yi sallama ta fita.

Da yake yau kowa a motar shi ya zo, wato itada Sulaiman, kasancewar lokutan ayyukan nasu
sun banbanta. Akwai tazara sosai daga inda ta yi parking zuwa cardiology. Tana tukin tana duba
agogon ‘gucci’ da ke daure a damtsen hannun ta na hagu. Yau Dr. Sulaiman aikin kwana gare
shi, kudin Fati sun tsaya mata a rai, ga shi jakarta (is empty). Sannan is too late ta je banki ta
fitar da kudi (lokacin ba ATM).

Ba al'adar ta ba ce tambayar Sulaiman kudi ba, saboda duk wata yana cika mata account ba
tare da la'akari da albashin ta ba. Ita da kudin ta sai dai ta yiwa iyayen ta da 'yan uwanta hidima,
amma duk wani nauyin rayuwar ta Sulaiman ya dauke shi.

Sau tari, ta kan ji kawayen ta da ba suyi aure ba irin su Dr. Surayyah, na tattaunawa a kan
abinda ya hana su yin aure, su kan ce da ka yi aure shi ke nan ka shiga matsalar da namiji
(wulakanci, rashin tsayawa ga mace daya, rowa da sauran su).
To ita dai yau shekaru biyar cif, ba ta ga ta inda nata da namijin ya kuskuro ta ba;

Matakin iliminsa bai sa shi ya zamo cikin kowanne irin aikin ashsha ba. Bai sa shi ya zamo mai
tauye mata hakki ba, bai sa shi ya zamo mai girman kai a gare ta ba. Kullum tambayar shi,
"No problem Haddizah (babu matsala Hadiza)?"

Ta kan tambayi kanta, yadda neman mata ya zamo ado ga akasarin mazan wannan zamanin,
masu matakin rayuwa irin nashi, mai ya sa ban da Sulaiman? Duk da kasancewar shi cikin
rukunin mazan data ke da tabbacin suna bukatar mace fiye da daya. Ta yadda duk juriyar ta
wani lokacin har ta kan nuna gazawar ta. Allah ya halicce ta da rauni a fannin auratayya. Ta
taba tambayar shi a wani dare cewar,

"Don me ba zai kara aure ba?"

Sai ya kankame ta. Ya ce,
"Haddizah you are okey for me, in dai ba za ki yi min rowar ni'imtaccen jikin ki ba........." Ta ce,
"Baban Munib gani nake ina kwarar ka, you seem not o.k........"
A hanzarce ya ce,
"Ni na gaya miki?"
Ta girgiza kai. Ya ce,
"To kar ki kara yi min wannan zancen, silly girl kawai".

Ta yi murmushi, da tunanin ta ya zo nan. Dai-dai lokacin da ta iso cardiology, ta yi parking a inda
aka tanada don adana motoci ta fito rike da jakarta. A nutse ta karasa (male ward) inda office
din Sulaiman yake, ta tura kofar bayan ta murda tare da sallama.

Da alama aiki ya kacame masa, yana ta rubutu cikin file-file dake gabansa, ya daga kai yana
duban ta duba na so da kauna, kuma na nutsuwa kamar yana son karanto ainihin damuwar da
ke fuskarta.
Ya mike ya baro kujerar sa ya zauna a masangalin kujerar da ta zauna, wato ta ganawa da
patients, ya zare mata gilashi, ya goge gumin dake tsakanin hancinta yace,
"Ya ya ne Dr. Hadiza, you look exhausted!" (Da alama kin gaji likis).
Ta lumshe zara-zaran gashin idonta ta ce, "Migraine ke damuna (ciwon kan barin kai guda)".
Ya kai lallausar tafin hannun shi goshinta, har sai da ta ji wani shock kamar yau ya fara taba ta.
Ta yi saurin ture hannun sa, za ta yi magan Dr. Abdullahi ya turo kofar ya shigo, da sauri ya
koma yana “excuse me plzzz.......!" Duk suka yi murmushi.
Ya ce,
"Kin sha magani?"
Ta girgiza kai,
"Ina so in je Karkasara ne".

"Amma lafiya na gaba da komai ko?'
Ta ce,
"Zan biya emergency in amsa kamin in wuce".
Ya kai hannu cikin rigarta wai zai ji temperature na jikin, ta yi saurin rike hannun ta ce, "Haba
Sulaiman......."
Shi ma ya ce,
"Haba Hadizahhh….! Ni kadai zan kwana fa, babu dumin jikin ki Hadizah…..?"
Ta yi murmushi ta rusunar da kwayar idon ta cikin jin kunyar furucinsa, domin dai ita mace ce
mai tsananin kamun kai a gaban mijinta da jin kunyar sa, kai ka ce basu haihu tare ba. Kullum
girmansa da kunyarsa da kimarsa karuwa suke a idanun ta. Yace.

"Ke kwanta in duba ki, ban yarda dake ba, har yanzu ba ki cire wannan loop din bane (IUCD)".
Ya soma laluben ta. Ta rike hannun shi ta marairaice tace,
"Wallahi na cire".Ya ce,
"To ko ke fa?
'Ya'ya nake so Haddizah, ki yi ta cika min gida dasu. Bamu da wani sauran abinyi a gaba banda
rainonsu da tara su. Bani da harshen da zai iya bayyana hakikanin son da nake miki, you are
my life Hadizah….., kada Allah ya rabamu.......". Ya shiga nuna mata son, practically (a aikace)
irin yadda bai taba yi ba. Murmushi tayi. Ta ce, "Sulaiman naka son ka sani, amma baka san nawa ba.
Sannan ban san yaya zan yi in fassara ba. All I can say (abinda zan iya cewa shine) ina son ka
Sulaiman, son da nake yiwa raina......”.
Ya kai hannu ya toshe mata baki, wayar shi ta yi kara ya juya yana amsa call din amma bai saki
hannunta ba. Ya gama ya kashe ya maida aljihun shi, yana yi mata wani sassanyan kallo ya ce,
"Ki yi min alfarma ki taya ni kwana ko hira ce ki dinga yi min ina aikin".
Ta ce, "Ka yi min afuwa Baban Munib, Fati zan kai ma kudi za ta yi registration gobe".
Da sauri Ya ce,
"Registration din Fati ya fini?"

Ta bude baki ta rufe da hannun ta, ta kasa cewa komai. Ya tsare ta da sexy eyes din sa, masu
kassara ta, ba shiri ta sunkuyar da kai, don ba ta iya jure kallon idanuwan nan na Sulaiman din
ta, masu rikirkita kowacce lafiyayyar diya mace, balle ita matarshi ta sunnah, data fi kowa sanin
sirrinsa na zahiri da badini. A raunane ta ce,
"Ban so ka yi min wannan fahimtar ba".
"Sai wacce kike so in miki?"
"Irin wadda ka saba, understandable (ta fahimta)".
Ya yi murmushi ya mike daga kujerar ya koma mazaunin shi, duk ya shafa mata mayataccen
kamshinsa na turaren ‘Chris Adams’. Nutsuwar matarshi da haibarta na burge shi, magana take
cikin nutsuwa da haiba, kamar ba daga bakinta furucin ke fitowa ba, dauke da matsananciyar
kauna a cikin kwayar idanun ta. Son ta da kaunar ta na kara kwarara a zuciyarsa, ya rasa inda
zai sa kansa. Ya kama kanshi da hannuwan shi biyu.Ya ce,

"Hadiza bana so ki tafi ne, sai in ji ni lonely kamar maraya........!"

Ta ce,
"Alfarma za ka yi min Sulaiman, muna tare muddin rayuwar mu".
Ya mika mata hannu ta kama, ta isa gare shi. Ya miko mata kumatun shi ya ce, "Kiss me
plzzzz……???".
Ta ji kunya sosai, ta boye kanta a kafadun shi, ita ba ta iya wannan keke-da-keken ba.
Ta ce,
"Kudin da zan kai mata za ka bani Sulaiman, ba kudi a waje na".
Ji yake in zai iya ba ta ranshi, to zai ba ta. Balle duniyar da abin da ke cikinta. Bai tambaye ta
me za ta yi dasu ba, ko adadin da take so, ya kwaso duk abin da ke cikin aljihun shi ya zuba a
jakar ta.

Allah sarki! Kamar ba za su rabu ba, a lokacin har duhun dare ya shigo, likitoci uku ne da ke
karkashin sa suka kwankwasa suka turo kofar suka shigo. Dole Hadiza ta dau jakarta da
lab-coat hadi da gilashinta ta fita, yana kara jaddada mata ta yi tuki da kula.

Dan banzan go slow ne ya tare ta a titi, ba ta isa gidansu ba sai tara da rabi, Maman su da suke
kira Yaya, tana zaune a tsakar gida da rediyo a hannun ta tana sauraron Jakar Magori. Autan su
Abdulyassar yana gefe yana hada motar kara.
Yaya Babar su Hadiza ba wata tsohuwa ba ce cancan, don irin auren wurin nan aka yi mata,
shekarun ta arba'in kenan.
Hadiza ta yi sallama Yaya ta amsa, Abdulyassar ya watsar da kayan wasan shi da gudun shi ya
kwaso ya rungume 'yar uwar shi, kasancewar ta mai jan su a jiki tare da nuna musu kauna.
Yana tambayar ta ina Munib?

Daga can dakinta na 'yammatanci, wanda a yanzu ya zan mallakin Fati, sautin Abdurrahaman
Sudais ke tashi a hankali cikin suratul Al-Imran, wannan ya tabbatar mata Hafiza FATIMA
JA’AFAR na gida.
Ta samu gefen Yaya ta zauna, Yaya ta mike daga kwanciyar da ta yi bisa tabarma. Kai da ganin
kyakkyawar fuskarta ka san ta ji dadin ganin diyar tata, ta ce,
"Da daddaren nan Hadiza? Shin ba Sulaiman ya hanaki tukin dare ba?”
Ta ce, "Wallahi Yaya, Dr. ne ya tare ni da magana, tun dazu na tashi, aikin kwana zaiyi shiyasa
bamu zo tare ba, na kawo ma Fati kudin ne".
Ta ce, "Amma kin kyauta, don da ta yi ma Yayan ku maganar ta waya ya ce ba zai samu zuwa
Kano wannan satin ba, ga shi baban ku kwanan nan kasuwar ta ja baya, kuma ta ce daga
wannan satin za a rufe".
Ta ce, "Baba bai dawo bane?"
Yaya ta ce, "Ya dawo tun yamma, ya tafi dubiyar dan gidan Malam Abdu ne babur ya buge shi
dazu".
Ta ce, "Allah ya sauwake, Fati na ciki ko".
Yaya ta ce, "Yanzu ta gama cin abinci ta shige ciki tana rehearsal, jibi za su yi musabakar jiha
kuma ita za ta wakilci jihar Kano, kin san Fati ba daga nan ba".

Cikin alfahari da kanwar tata a zuciyarta, Hadiza ta tura kofar dakin cikin sallama ta danna kai,
Fati ta diro daga gado ta rungume 'yar uwarta tana yi mata oyoyo.
Hadiza ta dubi Fati sama da kasa, yau sai ta ga ta zame mata cikakkiyar budurwa sosai. Ta
kama baki.
"Fati girma haka?"
Fati ta yi murmushi, kumatunta duka suka lotsa gwanin sha'awa, wushiryarta ta fito siririya da
ita.
Hadiza ta ce, "Wane course aka samu?"
Ta ce, "Course din da na nema ne (B.A Islamic Studies)".
Ta ce, "Masha Allah, da an je kuma sai a samo saurayi, irin wannan girma haka Fati?"
Ta ji kunya, ta boye fuskarta cikin tafukanta, ta ce,
"Ai hijabi zan ke zumbulawa irin mai hannun nan, kada a ce ana so na".
Hadiza ta ce me za ta yi ba dariya ba, duk girman Fati baka raba ta da wauta.
Ta kirgo kudi a jakarta naira dubu ishirin ta ba ta, Fati ta yi godiya ta ce,
"Allah Yaya Hadiza kwana biyu ba’a kawo su Munib ba".
Ta ce, "Makaranta ta boye su, amma da anyi hutu suna nan tafe insha-Allah". Sai sannan ne ta
ga hakoran Fati. Ita shaida ce kan cewa ba abinda Fati ke so a duniya irin ‘ya’yanta Munib da
Muniba.
Ta ce, "Ashe kuma musabaka za a yi Fati ba labari? To Allah Ya ba da sa'a".
Ta yi murmushi ta ce,
"Ameen".
Tana shirin fita Baban su na shigowa, ya ce,
"A'ah, manyan likitoci ne yau a gidan namu? Ina matas da abokin?"
Ta yi murmushi ta tsuguna har kasa ta gaida tsohon ta, ta ce, "Suna nan lafiya basu samu hutu
bane,

2 / 15