YAKANAH! BOOK COMPLETED BY TAKORI KABARA .pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   5 / 15

12K to 15K   out of 43.2K words

kina titi, bayan mijin ya tsare miki dukkan bukatun ki na rayuwa?" Surayyah ta ce, "Ke din ce dai kawai kin yi sa'a Hadiza, amma ba ko wadanne maza ne irin Dr.
Sulaiman ba".
Kishi ya motsawa Hadiza ta hadiye shi mukut, amma ta san Surayya gaskiya ta fada, Sulaiman
is unique, akwai wani simpleness a tare da shi wanda maza da yawa basu da shi.
Hadiza ba ta samu kwanciyar hankali ba sai da Dr. Surayyah Yahya ta kawo mata katin auren ta
da Dr. Bashir Bunza, cike da shakiyanci ta nunawa Sulaiman. Ya karanta ya ciji yatsa,
"Shege Bunza, ya kasa ni!".
Ta kyalkyace da dariya ta ce, "Eh, to kai ne ka tsaya sanya".
Ya harare ta da idanun kauna, "Haka ma za ki ce? Bayan ke kika kashe min gwiwa, ai da tuni
na karkata hula nasa kai, wallahi da ni zan kasa shi".
Ta sake yin dariya ta ce, "Oho dai, sai abi wani sarkin ba Ado ba".

****











Asabar ce sassanya mai dauke da wani irin lullumi mai sanya nishadi a zukatan dan adam, ana
saura kwana biyar a kama azumin watan Ramadan, kamar kowacce asabar din karshen wata.
Dr. Sulaiman ya zuba 'ya'yan shi a mota suka nufi Bakori ainihin gidan iyayen shi kamar yadda
suka saba, can za su wuni, wani zubin har yamma ko dare. To yau ma hakan. Gidan ya rage daga Hadiza sai Fati, don Alti ta je kauyen su Kukawa ganin gida za ta yi sati
biyu tunda yaran ma cikin hutu suke. Fati ta tura Hadiza kitchen kamar yadda ta bukata, ita tana
girki Hadiza na mata hira.
Ta ce, "Fati yau shekara guda cur da faruwar al'amarin nan, nayi-nayi ki kara neman wani
admission din amma kin ki, kina nufin haka za ki yi ta zama kina yi min bauta ni da iyali na ba
karatu ba aure? In don nice wallahi bana cikin matsala a halin yanzu I can take a good care of
myself (zan iya kula da kaina) ko da a ce ni kadai ce a cikin gidan nan". Fati ta sauke tukunya ta dora wata, ta yarfar da hannu don zafi. Sannan ta dubi 'yar uwarta,
"Yaya Hadiza ba zan iya barin ki ke kadai in tafi makaranta ba, ko na tafi tunanin halin da kike
ciki ba zai barni in mai da hankali a kan karatun ba".
Ta yi murmushi, "Cewa nake watarana aure za ki yi Fati?"

Nan da nan Fati ta yi kicin-kicin da fuska, ta juya mata baya ba ta ce komi ba.
Hadiza ta ce, "Ko baki ji ni ba? Aure za ki yi Fati dole ba da jimawa ba, don haka ki tsaya ki gina
rayuwar ki kamar yadda muka gina tamu, bana so saboda amfanin kaina ke in tauye ki. Don
haka na baki kwana biyu ki yi tunani, an fara sai da JAMB na wannan shekarar, don haka ki
nutsu ki kama abin da zai taimake ki ranar da bani. Duk wata kauna da dan uwa na gari zai nuna wa dan uwansa kin nuna min ita, sakayyar ki na
wajen Allah.
Sai dai ba zan bari ki kari rayuwar ki baki dandani zakin ilimin ko auren da na dandana ba, dole
in samar miki future kafin Allah ya yi hukuncin da ya so a kaina....".

Fati ta yi saurin juyowa ta dubi Hadiza, domin a da ta bata baya ne. Ba ta gane abinda take nufi
ba. Hadiza ta yi murmushin karfin hali ta ce,
"Fati zan gaya miki wani abu, amma bana so ki daga hankalin ki. Bani da lafiya Fati, amma don
Allah ko Yaya ban yarda ki gayawa ba balle Sulaiman.
Fati na dade ina fama da ciwon kai wanda nake yi lokaci-lokaci, Sulaiman ya sani ina yawan
fama da (migrain) amma bai taba zurfafa bincike ba, don ban taba gaya masa tsananin zahirin
yadda nake jinsa ba.
Ba tare da sanin sa ba na je wajen Dr. Bunza mijin Surayyah, da ke likitan kwakwalwa ne, cikin
sirri ya yi min bincike mai zurfi inda ya sanar dani ina fama da kansar kwakwalwa (brain
cancer)".

Fati ta zazzaro ido ta sulale ta zauna a kasa, ta kai hannu ta dafe kirjinta, sai ga hawaye suna
shatata! Hadiza ta yi murmushi ta matso da kujerar ta inda Fati take, ta dora hannu a kanta.
"A'a, Fati kada mu yi haka da ke, amanar rayuwata nake gaya miki, wadda bani da wanda zan
bawa sai ke. Ba wanda zan iya gayama wa sai ke, ciwon bai yi tsanani ba, kuma ina shan
magani a boye, ko Surayya ba ta sani ba.
Fati abin da ya sa na gaya miki don ki tallafa min ne, Sulaiman likita ne wanda ke bukatar
kwanciyar hankali don samun (confidance) wajen gudanar da aikinsa na ceton rayuwar
al'umma, idan ya ji wannan maganar ba zai taba samun kwanciyar hankali ba.
Fati Sulaiman yana sona, sosai, irin son da zai iya bani rayuwar shi, bana son abin da zai
dagula masa lissafi, ki rike min amanata, ki rike min 'ya'yana, ki basu tarbiyya irin taki kada ki
bari Sulaiman ya tagayyara a bayana. Ina son shi yadda yake so na, na so in ci gaba da rayuwa
tare da shi, in ci gaba da haifa mishi 'ya'ya kamar yadda yake so, amma ban san ya ya Allah zai
yi dani da rayuwata ba. Ki rike min Sulaiman Fati... bana so rashi na ya tagayyara shi........".
Zuwa wannan lokacin duka 'yan uwan biyu sharbe suke, na hawaye da majina.
Girki yana ta kauri, amma ba su kula ba. Fati ta rage sautin kukanta, ta ce,
"Shi brain cancer ba’a warkewa?"
Hadiza ta ce, "Ba a warkewa gaba daya, ko ya lafa zai tashi, amma ina kula da shan magani".
Fati ta yarfe hawaye ta ce, "Wannan ba abun boyewa bane Yaya Hadiza, ki daina fidda rai da
rayuwa saboda ciwo. Insha Allah ke za ki aurar da Munib da Muniba, ya kamata ki sanar da Dr.
domin ya taimaka miki da addu'a, duk wani hali da zai shiga ai shi musulmi ne ya san duk son
da yake miki ya san bai kai wanda Ubangijin ki yake miki ba. If the condition become worse, ba

tareda saninsa ba ba zai taba yafe miki ba.......!"

Hadiza ta yi shiru tana mamakin zurfin hankali irin na Fati, yarinya karama sai tunanin manya.
Ta ce,
"Zan duba shawarar ki Fati, Allah ya kara min YAKANAH, ya bawa 'ya'yana tarbiyya irin taki. Ai
dai za ki kula min dasu ko Fati?"
Cikin kuka ta ce,
"Yaya Hadiza ki daina yi min wannan maganar, bani da jarumtakar sauraron ta……".
Ta ce, "Na rantse da Allah idan baki yi min wannan alkawarin ba nima ba zan bi shawarar ki ba".
Cikin makyarkyatar murya ta ce, "Eh.......eh......na yi alkawarin zan kula dasu!!".
Ta ce, "To nima zan bi shawarar ki, amma ba yanzu ba. Tashi sauke tukunyar can tana kauri".
Ta share idonta ta mike ta sauke, ilahirin jikinta sai rawa yake. Ta kashe komi ta maido Hadiza
falo, ta yi dakin su ta rufe ta fada kan gadon su ta soma girka kuka. Ta ga kukan ba zai amfane
ta da komai ba, sai ta je bandaki ta dauro alwala, ta shimfida sallaya ta soma sallah, a kowacce
sujjadarta tana yiwa Hadiza addu'ar Allah ya ba ta lafiya. Wayar Hadiza ta yi kara, a lokacin tana bisa sallaya tana azkar, don haka ba ta daga ba har ta
tsinke. Sai ya yo text, ta dauka ta duba.
Sulaiman ne yake gaya mata suna bisa hanya har da Inna Halima za ta zo ta duba ta kuma za
ta ga likita, don haka a gyara mata daki don za ta kwana biyu.
Hadiza ta ji dadin zuwan Inna, domin Innar Sulaiman mutum ce har mutum, ma'abociyar raha
da sanin mutunci. Don haka ta kira Fati a waya ta ce ta kara yawan abinci da ta aje a falo, ta
kuma canza shimfidar gadon dakinta, don kullum a gyare yake Fati ba ta wasa da tsabtarsa.
Tara na dare dai-dai suka shigo, Inna dauke da Muniba da tayi barci a kafadunta. Hadiza da
Fati suka yi mata sauka ta ban girma. Sai lokacin kwanciya ne aka kai ruwa rana da Inna, don
ta ce ba za ta zaunawa Hadiza a daki ba, sai tare da 'yan jikokinta, dole suka kyale ta.

Duk juyin da Inna Halima ta yi a wannan dare, Fati take gani a kan sallaya, ta yi sallah, ta yi
lazimi. Da asubahi kuwa ta soma rero (Suratul Yaseen) da sauti irin na Abdurrahman Sudaith.
Kai ka ce daga masallacin Madinah aka kunno karatun. Saida tayi sallar asubah sannan ne ta
dan samu barci. Karfe shida ta fada kitchen ta soma aikace-aikace, Inna na hankalce da damuwar da yarinyar
ke ciki, ta rasa abin da ke damun ta kankanuwa da ita haka. Bata uhm bata umhumh. Lokaci
lokaci tana sanya gefen hijabinta tana dauke hawaye.
To haka a washegari ma, har cikin kitchen wannan yarinya ba ta rabo da hijabi da carbi, tun
tana burge ta har ta koma bata tausayi.
Washegari litinin bayan sun yi kalaci, Inna da Sulaiman suka wuce asibiti in da za ta ga likitan
ido (ophthalmologist), ba su dawo ba sai da rana ta take, yana sauke Inna ya juya ya koma ofis.

Sun fara cin abinci ita da Hadiza a kan darduma irin traditional carpet din nan na fata, an kuma
shimfida ledar cin abinci. Don Fati ba ta cin abinci cikin mutane, loma ta farko, ta biyu, ta uku
Hadiza ta soma kelayo amai kamar ta amayar da 'yan hanjinta.
Da sauri Fati ta shigo, Inna na rike da Hadiza, ita kuma ta kawo ruwa da roba Hadiza ta kuskure
bakin ta. Fati ta sa moper ta gyare wajen, ta koma kitchen don hidimar abincin dare.

Ko me take yi cikin kitchen bakinta ba ya rabo da ambaton Allah, duk a kan lafiyar 'yar uwarta.
Ita dai Inna haka nan ta ji Fati tana burge ta, tana bata sha'awa. Zahidah ce, babu duniya a
gabanta, gata da dan banzan kyau da fata lafiyayya, amma ba sa gabanta, lahira take nema da
harshen ta da goshin ta da gwiwoyin ta, ba ta furuci sai wanda ya zame mata dole, ko in an
tambaye ta.
Amma a kwanaki bakwai da ta yi, Inna Halima babba ce mai cikakken hankali, ta lura Sulaiman
ko ganin Fati a gidan shi ba ya son yi, don dai ba yadda zai yi ne, kuma bai son abin da zai bata
ran Hadiza.
Suna falo ita da Sulaiman misalin karfe sha daya na dare suna hira a nutse irin ta da da mahaifi,
ta ce, "Wai ni mai sunan Malam me yarinyar nan kanwar Hadiza ta yi maka ko kallon ta ba ka
yi? Dazu da safe ina kallo tana gayas da kai ka dauke kai ka fita, haka tun zuwana ban taba
ganin ka yi mata magana ba, balle wasan nan irin na mijin ya da kanwarta. In kana wuri ta shigo
sai ka tashi, in kana falo ta ganka sai ta koma ta yi ta zaman daki. Ita da ganin 'yar uwarta sai in
baka nan, mene ne manufar hakan?"
Ya juyo yana kallon Inna kasa-kasa, yace, "Wacce yarinya kike magana?"
Ta ce, "Fatima".
Ya ce, "Fati wai?"
"Eh, ita".
Ya yi shiru kamar bazaiyi magana ba yayinda Inna ta kura masa ido cikin tsananin son jin
amsarsa, ya rausayar da kai ya ce,
"Raini ne bana so, kuma ni ban iya wani wasan kanin miji ko kanin mata ba".
Ta yi sakale tana jin sa, ta ce, "Hala wani laifi ta yi maka? Har Hadiza na lura ranta yana baci da
irin halin ko in kulan da kake yiwa 'yar uwarta. Ban san ka da bakar zuciya ba, kada ka a fara a
kan FATIMA, domin mutum ce cikin 'yammatan da babu irin su a yanzu, wannan yarinyar tana
da halayen 'yan aljanna, ka yi a hankali baka sani ba ko waliyya ce". Shi abin ma sai ya ba shi dariya, ya ce, "A wannan kalatacciyar duniyar tamu dama akwai
sauran waliyyai Inna?"
Ta harare shi ganin ya bagarar da zancen cikin wata siga ta daban, ta cigaba da magana cikin
kakkausar murya.
"Dariya ma kake min?”
Ya yi saurin cewa, "A'a, yi hakuri Inna ba dariya nayi ba".
Ta ce, "To ka gyara ma'amalar ku, zai fi kyau a ce akwai kyakkyawar alaka a tsakanin ku ko
saboda Hadiza, in ta gaishe ka ka dinga amsawa cikin walwala da sakin fuska, wanda ya rike
ibada ba ya wulakanta a duniya da lahira Ubangiji kansa girmama shi yake. Baka sani ba ko ta
fi ka matsayi a wajen Allah, ka canza takun ka a kanta, rayuwa baa yi mata haka, don sauyawa
take kamar WAHAINIYA ta inda bama tsammani. Ai ba haka na ga kana yiwa su Ruma ba, to
matsayin ta daya dasu a gare ka, ka ji na gaya maka".
Bai ce komi ba ya jawo wata hirar, don dai a sauya wannan. He is not interested at all (Fati is
not the kind of person he wanted to relate with), wato ba ta daga cikin irin mutanen da yake son
yin mu'amala dasu akan dalilai masu yawa. Wadanda in aka ce ya zano akan karan- kansa sai
ya ji su masu rauni da rangwamen muhimmanci (null and invalid ). Amma daga ciki ya san
akwai gudun RAINI da rashin son sa da WASAN KANIN MIJI. Sauran hujjojinsa kuma ai a
sarari suke; jinin su bai hadu ba, don yana son Ya, ba dole sai ya yi wata kakkarfar alaka da

kanwar ta ba, bayan wadda musulunci ya ce, don haka ne baya damuwa ba ‘hypothesis’ din
kowa akan ma'amalar sa da Fati, ai ba abokiyar wasan shi ba ce, kanwar shi ce.
****

Kwana bakwai din da Inna Halima ta yi jinyar Hadiza suke ita da Fati, komai ta ci sai ta amayar,
ga zazzabi da ciwon kai mai zafi, sai ta rike kanta idan ciwon ya motsa mata tana wani irin kuka
mai keta zuciyar duk mai imani.
Sulaiman da farko bai sani ba, don ya dauka laulayin ciki ne irin wanda ta saba, kuma ciwon
baya tasar mata da daddare lokacin da suke tare kenan. Ita ma Inna ta lura ta san laulayi ne na
sabon ciki, amma wannan buga kan da Hadiza take yi a jikin bango da kukan da take yi na
azaba ta fahimci akwai dai wani abun, amma tana ganin dukkan su likitoci ne sun san abin da
ke damun ta, kuma ta ga Hadiza tana shan magani, sai ba ta yi magana ba, amma dai ba ta
taba ganin irin wannan laulayin cikin ba.
Don haka ta kara sati saboda lafiyar Hadiza wadda ta daina cin komai sai ruwan bakin lipton da
ruwan tsamiya. Gaba daya ta rame ta fita hayyacin ta, ba ta taba yin cikin da yake wahalar da
ita irin wannan ba.
Tun Sulaiman bai gane ba har ya fahimci Hadiza ba ta da lafiya sosai, wannan ya wuce laulayi
kuma wannan (migrain) yana bukatar bincike.
A daren ya fito daga wanka yana tsane kanshi da dan kankanin towell, tana kwance rigingine a
gefen gado, cikin doguwar rigar barci mai santsi mara hannu ruwan madara, kyawawan
kafafunta da cinyoyin ta a mike sambal, a haka sai ka rantse lafiyar ta kalau ba ta tare da wata
lalura. Son matarshi da kaunar ta na kara girgiza zuciyar sa, yana hargitsa gangar jikinsa. Ta kure
fanka da A.C amma ba ta daina zufa (gumi) ba. Da sauri ya karasa zarga igiyar pyjamas din shi
ya yiwa kanshi kyakkyawan matsuguni a bayan ta, ya daura hannu a kan goshin ta, zafi rau!
Dole ya hadiye nashi bukatan ya soma ba ta kyakkyawar kulawa ta hanyar sanya karamin
towell a ruwa yana goge mata kanta don zafin kan ya ragu. Sannan ya soma bin gabban jikinta
da message don ta ji dadin kasusuwan ta. Ya juyo ta ya rungume ta ganin wani irin gumi na
tsatsafowa daga cikin kanta, a yau ma ya sake cewa,
"Cikin kowanne hali, INA SON KI HADIZAH!"
Ta bude idanunta a hankali, wadanda suka kankance suka yi jawur don azabar data ke
dandana, tana kallon abin son ta, shi ma kallon ta yake kallon yaya zan yi da raina? Me zanyi in
sama miki lafiya? Ya ce a galabaice,
"Gobe zan dauko Dr. Bunza ya duba ki".
Gabanta ya yi wani irin faduwa, ta runtse idon ta da karfi ta ce,
"Bana so, kada ka dauko shi, idan kuma har ka dage sai ka dauko shi to zan koma Karkasara".
Ya girgiza ta da karfi ya ce, "What do you mean (me kike nufi)? In barki a gida kina ciwo ban
nema miki magani ba? Bansan hakikanin me ke damunki ba? Allah sai ya tambaye ni, iyayen ki
da suka danka min amanar rayuwarki su tuhume ni. Wannan ciwon kan bana wasa bane yana
bukatar bincike". Ta ce, "Ai ba yau na fara ba ka sani, kuma da na sha magani shi ke nan yake lafawa".
"Ina maganin? Dauko min in gani".
Ta ce, "Ya kare dazu, da safe nake shirin in aiki Fati ta siyo wasu".

Ya ce, "Wane magani ne?"
Ta yi shiru.
"Tambayar ki nake yi, ina maganin? Ya ya sunan sa?'
Ta ce,
"Panadol".
A mamakance ya maimaita
"Panadol?"
'Eh".
Ya ce,
"You are silly, ko in ce you are a nonsense Doctor! I did not trust you.........". (kina shirme, ke
shashashar likita ce, ban yarda dake ba).
Ya tashi a fusace ya fizgi waya ya kira Dr. Bashir, ‘consultant’ na ‘neurology’, Surayya ce ta
dauka, bai ko amsa gaisuwar da take mishi ba ya ce,
"Ina mijin ki?'
A ladabce ta amsa.
"An kira shi a ‘emergency’ kuma

5 / 15