Author : Sumayya Abdulkadir Category : Romantic Hausa Novels
fuska kamar wani soja idan ya ganta.
Fati na mamakin wannan wace irin kiyayya ce Sulaiman yake mata ta babu gaira babu dalili?
Kamar ita ce ta kashe Hadiza?
Yana da wata kima a idon ta kasancewar shi wanda ya auri ‘yar uwarta da ba ta da ya ita a
duniya, ya zauna da ita, ya rayu da ita cikin so da kauna da kyautatawa har ta koma ga
mahaliccin ta, ba ta taba fadan laifin sa ko aibunsa ba, ko wani abu da ya yi mata na rashin
dadi. Sannan da kasancewar shi Baban ‘ya’yan da take so sama da komi a duniya. Idan ba zai so ta
ba ai ta ci albarkacin Hadiza.
Amma yadda yake nunawa kamar ko a hanya basu taba hada wata alaka ba, idan ta biyewa
wulakancin da yake mata ta ce za ta dinga bata ranta a banza, ita ce za ta cutu, ta dorawa
kanta ciwon zuciya da hawan jinin da ko duba ta ba zai yi ba, balle ya rubuta mata magani.
Don haka ta debe tsoro da shakku, bayan sun dawo yana kwance a falo yaran shi sun baibaye
shi suna ta yi mishi tadi, shi kuma yana aiki cikin kwamfutar da ke bisa ruwan cikin sa.
Ta lallabo ta fito uwa munafuka, tana goye da Nana ta rabe a gefe, Muniba ta taho ta zauna a
cinyar ta. Sai a lokacin ya ankara da shigowar ta falon, ya juyo da sauri kamin ta yi magana ya
mike, ya aje computer a fusace.
Ta runtse ido tana jiran saukar mari a lallausan kumatun ta, ya ce,
“Don’t I warned you? Idan ban neme ki ba ki daina zuwa inda nake?”
Cikin makyarkyatar murya da gigicewa ta ce, “Ka yi hakuri, kayan cefane ne suka kare, sannan
babu kayan abincin makarantar su Munib”.
Ya yi tsaki “Tsuuu!” Kamar ya tsinke harshen sa, ya ce, “Na ji shikenan ko?” Ta mike a salube
gwiwa babu karfi ta koma daki, don ita ba abin da ta tsana a rayuwarta irin a yi mata tsawa.
Su kansu yaran sun tsorata da tsawar da Baban su ya yiwa Antin su, sun yi zuru-zuru, suma ya
nuna musu hanya ya ce su bita. Da gudu suka tafi har suna faduwa, ya kashe komai ya fice
daga gidan.
Washegari Alti ta dawo, ba karamin jin dadin dawowar ta Fati da yara suka yi ba, ko ba komai ta
samu mai taimaka mata da debe mata kewa, don Goggo Alti mutum ce mai barkwanci da ban
dariya.
Sai ga Malam Ilu yana shigowa da kayan abinci nau’i-nau’i. Suka zaun ita da Alti suka gyara
komai suka adana na adanawa a firij, suka markada na markadawa suka adana a ‘freezer’
Washegari ta tashi da wuri da taimakon Alti suka kammala komi da wuri, suka shirya yaran da
abincin su, karfe bakwai da rabi Babansu ya kwashe su ya wuce dasu, sannan ya dangana ga
ofishinsa.
Kuma ranar ne su Yaya Haulatu kanwar Yaya da wasu daga aminan arzikin ta suka zo suka yi
mata jeren kayan gado dai-dai karfin iyayen ta da dan uwanta Mukhtar.
Falon ba ya bukatar komi, masu gidan sun riga sun tsara abin su dai-dai da rayuwar su ta masu
murza tsinin biro, sai ba’a taba komi ba, iyakacin su dakinta.
A kwanaki bakwai da Alti ta yi tare dasu, ta fahimci irin zaman kare da kyanwar da ake tsakanin
Fati da maigidanta Dr. Sulaiman. A ranta ta ce,
“Yarinya kyakkyawa kamar Hadiza, ga hankali da addini, ko meye nakasunta da Dr. Sulaiman
ya kasa son ta?”
Ta ce, “Ko da yake so ba’a nan yake ba, abune wanda ke faruwa kawai a duk sanda ya so, ga
duk wanda ya so, cikin iko da kudurar Allah.
A yau suna yankar alayyahu ita da Alti, domin yin miyar wainar masar dare. Suka jiyo motsin shi
yana shigowa kitchen din, tuni Fati ta soma makyarkyatar jiki, kan ka ce meye wannan wuka
kakkaifa ta shiga cikin naman hannun ta.
Don ita ko gyaran muryar shi ta ji gigicewa take ta fita hayyacinta kada ya yi mata tsawar nan
tashi mai dimauta ta.
Jini ya soma bulbula a dai-dai lokacin da ya idasa shigowa kitchen din. Alti ta ce, “Ya salam! Kin
gani kin yanke, na yi na yi ki daina amfani da wannan wukar kin ki, ta fiye kaifi da yawa, sannan
gaki da saurin gigicewa”.
Ya ji hankalinsa ya tashi ganin yadda jini ke gudu amma ba ta dago ba. Ta dukar da kai ko
motsi ta ki yi. Ya basar Ya ce, “Babu sauran ruwan roba ne Baba Alti? Firjina babu komai,
sannan ina jin kishi”.
Ta mike zuwa store ta dauko mishi katon na FARO ta dawo, ta kama hannun Fati ta ce, “Babu
kananzir balle in sanya miki, bari a daure da tsumma”.
Ta tsaga zanin ta tana kokarin daure mata. Ya kalle ta a kaikaice ta kasan ido ya fita, zuciyar shi
babu dadi, don ya tuno yadda ta nuna damuwa ranar da ya yanke nashi hannun.
Mamaki ya kama Alti, ashe Baban Munib ba shi da kirki? Matarka ta yi irin wannan yanka amma
ko kallo ba ta ishe ka ba?
Tana daure mata Fati ta fara kuka yankar ta fi karfin daurewa da tsumma. Alti ta biyo shi, ba ya
falon yana dakin sa. Ta tura Munib wanda ke ta wasan game cikin computer ta ce ya kirawo
Baban shi.
Jim kadan suka fito tare shi da Munib, yana rike da gorar ruwan yana sha. Cikin takaici ta ce,
“Zan kai Fati asibiti ne”.
Ya sunkuyar da kai duk jikin shi ya yi sanyi, ganin bacin rai kwance a fuskar tsohuwar da bai
taba ganin bacin ran ta ba tsayin shekaru shida da suka yi tare da ita, ya dukar da kai sosai ya
ce,
“Bari in diba ciwon nata”.
Ya koma daki ya dauko first aid box ya same su a kitchen din, jinin na ta zuba har yanzu.
Sanye yake da brown getzner ta sha dinkin Mohammed wanda shi ne dinkin sa kawai, ya
russuna dai-dai inda take sunkuye, ya kama hannun ta. Wani sanyi ya tsirga a zuciyar ta. Dago
idon nan da za ta yi sai idanun su cikin na juna, wadannan kwayan idon na Sulaiman suka
birkita ta, kamar yadda suke birkita zuciyar duk wata lafiyayyar macen da ta san cewa akwai
tsokar zuciya a tare da ita. Amma ga shi Sulaiman, gani yai ta rikide mishi ta koma Dr.
Hadizah……
“Wannan yankar sai an yi dinki”. Ya fadawa Alti.
Cikin sanyin murya ta ce, “Ai shi ya sa na ce muje asibitin”.
Ya ce, “Ba damuwa bari in dinke mata”.
Ya fara da yi mata allurar ‘anaesthesia’, sannan ya fara dinkewa. Idanunta a rufe ba ta bude ba
har ya gama.
Bayan ya gama ci gaba ya yi da rike hannun bai saki ba, ita kuma ba ta sani ba cewa ya gama
ko bai gama ba.
Alti ta yi saurin fita ta bar kitchen din. Ya soma samun wani sassanyan sauyi a tare da shi, ya
dinga hango rashin kyautatawar sa na tsanar jinin Hadiza da ba ta tsare mishi komai a rayuwa
ba.
Auren su da aka yi ya tabbata ita ma ba da son ranta a kai ba, soyayyar Hadiza da ta yi mishi
yawa, ita tasa yake kin kowacce mace. Ita kuwa Fati ba zai ce ga dalili ba.
Ya danganta hakan da rashin haduwar jini kawai, ina ruwan shi da tsarin rayuwar ta? Tunda ba
a goshi zai lika ta ba? Ya soma kokarin goge muguwar kiyayyar da yake yi mata ta hanyar
baiwa zuciyar shi uzuri iri daban-daban ga duk muguwar hujjar da ta kawo.
Sai dai muhimmin abin da iyayensu suka hada wato AURE da mu’amalan auratayya, baya jin
zai taba iya yin shi da wadda ta zamo kanwa ga Hadiza. Duk da ba haramun bane shi kam ya
haramtawa kansa, an halicce shi kadai don Hadiza, kuma har ya koma inda Hadiza take ba zai
kara mallakawa wata diya mace soyayyar shi ba, babu gurbin da zai iya jogana son wata. Sai dai shi kansa yana mai kalubalantar tunanin sa na cewa zai iya dauwama a haka ba tare da
mace ba, kasancewar ta wani bangare na rayuwar dan adam, da kuma ganin tun ba a je ko ina
ba ya fara kwana cikin halin ha’ula’i. Dole ya dau matakin da zai kawo karshen duk wannan,
wato ya yi nisa da Fati, tun YAKANAR ta, kyautatawar ta, hakurin ta da juriyar ta basu ciwo
galabar tattaurar zuciyar sa ba.
Jin ya yi shiru ba ya dinkin kuma bai saki hannun ta ba, Fati tayi saurin bude idon ta, suka yi ido
hudu da Sulaiman dan Sulaiman da Inna Halima. Ashe haka Baban Munib yake da kyau? Ban
taba sani ba? Fati ta ce a zuciyarta.
“Ina ma a ce yanda yake da kyan nan haka zuciyar shi take da kyau?”. Zuciyar ta kara
tambayarta. Ta samu kanta cikin wani sabon yanayi da ba ta taba tsintar kanta a ciki ba.
A wannan daren mai dimbin tarihi a rayuwar kowannen su, daga Fati har Sulaiman babu wanda
ya runtsa, soyayyar junan su ke neman samun muhalli a zuciyar kowannen su.
Amma sun sa kafa suna fatali da ita da gan-gan, don a ganin kowannen su bai dace ba.
Sannan ita Fati ta riga ta yiwa Dr. Sulaiman mummunar fassara zuwa na makiyinta, mai nuna
mata kiyayya karara, kiyayyar da babu wani mahaluki da ya taba nuna mata a rayuwar ta.
Don haka a kan me za ta so shi in ban da sharrin zuciya, don haka take ta ciccijewa, ita lallai
karya zuciyar ta take yi ba son shi take yi ba.
Shi kuma a can nashi bangaren, Sulaiman, ya kasa sukuni, ya kasa runtsawa ne a dalilin
abubuwa da dama na yarinyar a yau da suka fizge shi.
Ga dai kamannin Hadiza, sannan ga wasu (extraordinary qualities) da ya lura dasu a dan
zaman watannin da ya yi tare da yarinyar. Don haka ya kwana cikin yiwa kai da zuciya hisabi,
don tantance al’amarin da ke shirin faruwa da shi a kan Fatima Ja’afar Mai-Yadi.
Sakamakon ba mai saukin fadi bane a gare shi, halayen ta da yakanar ta da juriyar ta wajen yin
abubuwan ta don Allah ba don ya yabe ta ko ta burge shi ba, sun taimaka kwarai wajen sayo
mata soyayyar dole, wanda ke nufin Fati ta yi nasara kenan a kansa? Shi kuma ya fadi game
din da suke bugawa. (He is the loser, and she is the winner! Idan ya yi sake hakan ya bayyana gare ta shikenan za ta raina shi, GIRMA YA FADI! Ya manta
cewa a magana ta aure babu raini tsakanin mace da mijinta.
To amma ina zai kai jin kan? Na tunanin kankanuwar yarinyar da yake rainawa ta yi winning a
kansa? Don haka tunanin sa na ya yi nisa da Fati, don gudun RAINI ya kara kamari a tare da
shi.
A kwanakin da suka biyo baya, duk hanyar da ya san za ta hada shi da Fati a gidan yana kauce
mata. Ita ma Fatin hakan, tun daga ranar da ta yanke hannu, ga shi har ciwo ya kame.
****
Basu Kano ba su Abuja shi da wasu daga cikin likitoci ‘yan uwansa, suna fafutukar ‘visa’ zuwa
jami’ar Chicago domin halartar wani kwas na shekaru biyu a kan dashen zuciya (heart
transplantation) da ‘federal government’ ta tura su.
Ko Inna ba ta sani ba, sai da ya gama dukkan shirye-shiryen sa, shi lallai dole yana yaki ne da
zama da Fati kada soyayyarta ta rinjaye shi, shi ya sanya ya sanya kanshi cikin ‘yan tafiyar, don
da babu yadda shugaban su bai yi ba ya shiga cikin tawagar amma ya ce a’a, duk da matukar
bukatar shi da kwas din da asibitin ke yi, don haka da ya zo da kansa ya ce zai tafi, ba karamin
jin dadi shugaban su ya yi ba.
Suka fara shirye-shirye, har zuwa yau da Allah ya nufa suka kammala, sai tafiya kwanaki uku
masu zuwa.
Ya cimma su ita da Alti a kicin don su nan ne ofishin su, suna ta suyar dambun nama. Ya hada
giran nan sama da kasa lokacin da idanuwansa su kai arba da na Fati, ita ma ta hade tai murtuk
kamar ta ga mala’ikan daukar ranta, wannan gigicewar da take yi in ta gan shi yau ba ta yi ba,
sakamakon jimawa da ta yi ba ta sanya shi a idon ta ba.
A can wani gefe daga karkashin zuciyar ta, wani sanyi ne ya sauka a zuciyar ta wanda ba ta
san dalilin shi ba. Hakika ta azabtu da rashin ganinsa a dan tsakanin, saboda yadda ganin sa
ya zame mata SANYIN IDANIYA, yake gusar da duk wani bacin ranta, yake rage mata zugin
rashin ‘yar uwarta da ke cin zuciyar ta, duk da rashin alherinsa gare ta kuwa. Babu ko tantama ta fada a ‘soyayya,’ a inda take da yakinin cewa ba za a taba son ta ba, in
haka ne zuciyar ta ta gingimo mata babban aikin da ba ta san ya za ta yi da shi ba.
Yana duban sashin da Fati take kasa-kasa ya gaida Alti, sannan ya dauke kanshi a sashin
Fatin, ganin yadda ta yi murtuk da fuska. Ya yi murmushi ya ce da Alti,
“Ku yi shiri zan je in watsa ruwa mu wuce Bakori yanzun nan”.
Alti ta ce, “Allah ya sa lafiya?”
Ya yi murmushi ya ce, “Lafiya kalau Goggo Alti, yara sun kwana biyu basu ga Inna ba, suna ta
tambaya ta”.
Ta ce, “To bari mu yi sauri mu karasa”.
Taso ta ce da shi, “Har da Fati?” Ta ga wannan ba abin da ya shafe ta bane sun fi kusa, wai
harshe da hakori.
Ita ma Fatin da ba a ce da ita ba kawai sai ta hau shiri, domin tana son ganin Inna ainun. Ta
zuba Abaya kirar Kuwait, ta kawo katon hijabin ta har gwiwa ta zuba.
Bayan ta shirya yaran dukkanin su, ta fi son ta goya Nana, maimakon ta yi ta rike ta a hannu ko
a kafada.
Har Sulaiman kan yi mamaki ya ce a ransa, ita wannan ba ta gajiya da goyo ne? Duk sanda zai
ganta goye da Nana zai ganta. An ce mai da wawa, kulawar da take yiwa ‘ya’yan shi ya taka
rawa ba kadan ba, wajen sayo mata soyayya ta kwarai a zuciyar shi.
Kafin wani dan lokaci sun kimtsa tsaf suna falo suna jiran shi, ya fito cikin wagambari shudiya
mai hasken sararin samaniya, wato navy blue, hannun shi na hagu daure da agogon RADO na
bakar fata, haka takalmin da ke kafar shi wanda ya kasance budadde na fatar damisa.
Babu gilashi a idon shi sai fararen idanun shi ke sheki da daddadan kamshin ‘Chris Adams’ da
ya baibaye su.
Yaran suka nufi jikin shi, ya kama hannun kowannen su suka nufi harabar adana motoci, ita
kuma ta koma kitchen ta juye dambun naman da suka yi gaba daya ta taho da shi don ta kai wa
Inna.
A wajen shiga mota ne ake dirama, yana son ganin in da za ta zaba don zama don son sanin
matsayin da ta aje shi, tunda ‘yar gaisuwar da ta ke mishi ma a darare ta hakura ta daina, tunda
baya amsawa.
Ta bude gidan gaba su Munib suka shiga, sannan ta sunto goyon ta shiga baya ita da Alti.
Har suka hau titin Kabuga babu wanda ya yi magana, sai yaran da ke ta rigima a tsakanin su a
kan jirgin sama mai batir na Munib da Muniba ta dage sai ta amsa.
Ita dai Alti shiru ta yi tana nazarin su, ga dukkan alamu kowannen su ya sauya, ya yi sanyi,
amma an rasa wanda zai sauke ya bi dan uwansa. Tana son ganin wanene zai yi jarumtakar
tsaga billensa ya bi dan uwansa?
Wadannan ma’aurata suna ba ta dariya, ganin har ta cikin mudubi satar kallon juna suke, amma
in daya ya kama daya sai a yi maza a fuske, a dauke fuska, wato babu shiri babu alaka.
Tafiya ta yi nisa a kan kwalta, barci ya fara daukar Alti, yaran tuni sun yi barci har Nana, ya mika
hannu ya rage musu karfin na’urar sanyaya mota.
Kawai Sulaiman ya faka motar a tsakiyar daji, ya wani irin juyo ya dube ta, an yi sa’a ita ma a
lokacin ta dago daga madara da take bai wa Nana, idanunsu cikin na juna, wani miracle ya yi
aiki cikin ‘yan dakikai, ya haifar da wani al’amari mai GIRMA a zuciyoyin su.
Ji yake kamar yana yi mata kallon karshe ne, ya tuhumi kanshi da rashin sauke wani nauyi mai
girma da Allah ya ce ya yi, ga shi har zai tafi, tafiyar da babu tabbacin zai dawo ko ba zai dawo
ba, tunda rayuwar ba a hannunmu take ba.
Ya samu kansa da son tausasa mata, ko babu komi yana son goge mugun tabon da ta yi mishi
a zuciyar ta. Ya tabbata idan Inna ta san har zuwa yanzu bai kula ta ba, la shakka za ta dauki
mataki, duk da ya san da wuya Fatin ta gaya mata, tunda ba ta da magana.
Amma in Inna ba ta sani ba ai Allah ya sani, kuma ba zai kyale ba.
Ya mika mata hannu, “Kawo ta in taya ki rainon”.
Ta galla mishi harara, sannan ta kara kankame ‘yarta. Ya yi murmushi ya ce,
“Ko ‘yar gaisuwar da kike min kin daina, why Fati?”
Wannan karon ma ba ta yi mishi magana ba, amma ta tsuke baki ta juyar da kai.
Ya yarfar da hannu, “Tunda kin ki mu yi hirar bari mu karasa gaban Inna, watakila ita za ki yi
mata bayanin dalilin ki na daina gaishe ni a matsayina na