Author : Sumayya Abdulkadir Category : Romantic Hausa Novels
YAKANAH!-1
Agogon ‘alarm’ da ke gefen makeken gadon ya buga karfe shidda dai-dai na safe, Dr. Hadizah
wadda ke kwance a gadon doguwa ce ba can ba, irin tsayin nan gare ta mai tsari da ban
sha'awa. Tana sanye cikin rigar barci mai santsi fara sol. Ta yi mika a hankali tare da koro
addu'ar (Alhamdulillahil lazee ahyana, ba'ada ma amatana wa ilaihin nushour). Ta mika hannu
side din da maigidanta ke kwance, wayam! Tayi hanzarin mikewa daga kwanciyar don a
zatonta, ta makara.
Daga can kitchen ta jiyo motsin mai aikinsu Goggo Alti tana karakaina da kwanuka. Tana shirin
mikewa ta ji motsin maigidanta Sulayman a shower, don haka ta yi ajiyar zuciya mai sanyi, a
kalla ko ta makara kadan ne. Ita ma ta fada bandakin don ta taimaka mishi wajen wanka kamar
yadda yake a al’adarsu. Wasu ma’aurata ne wadanda samun masoyan da suka shaqu da juna suka kuma yarda da
juna, suka aminta da juna, suke matukar kaunar junansu kamarsu a wannan zamanin zai yi
wuya.
Suka fito kowane daure da towell, shi iya kugun shi ita iya cinyoyin ta. Jiki ne da ita lukui-lukui
kamar atafa. Jiki ne da shi na MANYA, kuma kasaitattun maza, wadanda suka dama, suka
kutsa cikin manyan ilimummuka daban-daban.
Yana da duhu, amma duhun mazan Marocco ne. Dogo ne sosai ma'abocin karfi da kyawun sura
ta ko’ina. Idan baka san asalin shi ba, za ka yi tsammanin ya fito ne daga Sirreleone, amma a
zahiri Bakatsine ne dan asalin garin Bakori. Wanda Bakorin ta bi sunan shi, ta boye
Sulayman-Sulayman din, ake kiran shi Dr. Bakori. Ta bude wardrove ta dauko mishi bakaken Spanish-Suit mai hade da farin tie mai santsi. Ita
kuma ta fiddo wata atamfa super shudiya mai ratsin rowan hoda da hasken sararin samaniya,
riga, zane da kallabin su, ta dora da farar rigar su ta likitoci. Tuni ta fito a Dr. Hadizarta. Tana
tsuke mishi tie ya ja zankalelen dogon karan hancinta in appreciation din (cike da jin dadin) irin
kulawar da take mishi. Ya ce
"Allah ya bar min ke Dr. D.Z". Ta ce
"….Ya bar min kai nima, likitan zuciyata…..". Ta manna mishi kyakkyawar sumba a kirji,
kasancewar ya kere ta a tsaho, ita iya kirjin shi ce. Ta dauko tashi rigar likitocin ta zagaya ta
bayan shi ta rufa mishi, ya zura hannun shi kana a hankali ya janyo ta ya rungume ta. Sun dau
tsawon lokaci a hakan, suna sakin ajiyar zuciya mai sanyi cike da matsananciyar kauna wadda
biro ba zai iya rubutawa ba, kamin su saki juna ba don sun so ba, sai don tunanin dimbin
al'umma masu larura da suka yi sammako suke jiran su.
Sai da suka gama kammalawa tsaf sannan suka fito, tana rike da gilashin idonta a hannu, yayin
da shi yake rike da jakarta da brief case din shi. Kai tsaye dakin yaransu suka nufa, inda suka
tarar tuni Alti ta shirya su tsaf, kasancewar yau garin an tashi da lullumin sanyi mai tsanani ya
sanya ta sanya musu rigar sanyi mai kauri a ciki, ta sanya musu fararen socks ta rufe musu
kafafu cikin farin cambas.
Yaran su biyu ne mace da namiji, namijin dan kimanin shekaru hudu, macen 'yar kimanin
shekaru biyu da kadan. Dole in ka gansu sai ka sake marmarin kallon su, sun kuma baka
sha'awa.
Munib sak Babansa, yayin da Muniba komi nata na Dr, Hadiza ne. To ba Mamin ba, ba Daddyn
ba, kowanne ji yake da kyau tamkar shi ya yi kansa. Akwai shakuwa, fahimta da soyayya mai
yawa a tsakanin wannan family.
Hadiza ta rage tsawo ta russuna ta rungume diyarta Muniba,
"Gud morning my dear......."
"Morning Mummy….".
Munib ma ya ce
"Gud morning Daddy…..".
Ya amsa da
"Morning my Munib, an tashi lafiya?"
Su dukka suka nufi tebir domin yin kalaci.
Goggo Alti ta fito daga kitchen za ta wuce bangaren ta, daga Hadiza har Sulayman suka gaishe
ta, kamin ita ta gaida su. Wannan dabi'arsu ce da ke karawa dattijuwar jin dadin zama dasu,
saboda yadda suke ba ta girma kamar ba a karkashin su take ci ba. Hakan ne yake kara mata
himmar kula musu da yaransu saboda Allah. Hadiza ta bude ma'adanan abincin ta soma serving kowannen su da abinda yake so. Sinasir ne
da miyar ganye, sai farfesun kayan ciki, sai kuma soyayyen dankali da kwai domin su Munib da
bazasu iya cin mai nauyin ba.
Ga al'adarsu sun fi cin abinci mai nauyi da safe, don ba za su kara ci ba sai dare in sun dawo
aiki, sai 'yan ciye-ciye da ba a rasa ba a office.
Hankalin Dr. Sulaiman yana kan 'ya'yan shi, sai da ya tabbatar sun koshi sannan ya ci nasa.
Zuwa bakwai da rabi sun gama komai sun fito, suka yiwa Goggo Alti sallama suka wuce rumfar
adana motocin su.
Akwai motoci har guda uku, daya ta Sulaiman, daya ta Hadiza, daya ta amfanin gida. Sai da
suka aje yaran a makarantar su (Maitama Sule) da ke dab da asibitin da suke, wato (AKTH)
sannan suka karasa cikin asibiti, kowanne ya nufi bangaren sa.
Dr. SULAIMAN-SULAIMAN BAKORI shi ne consultant na (cardiology), yayin da Dr. Hadiza
Ja'afar Mai-Yadi take likitar mata wato (gynaec) a labour ward take. Sai da ya fara sauke ta
sannan ya wuce ofishinsa, ya soma attending dimbin cases din da ke gabansa.
Karfe sha biyu na rana ya zame ya je ya debo yara ya kai ma Goggo Alti, sannan ya dawo.
Wannan shi ne tsarin rayuwar su a kullum.
***
Shekarun su biyar kenan da aure, amma har zuwa inda yau ke motsi, babu abinda ya canza na
daga soyayyar da suke yiwa juna, sai ma abin da ya karu.
Hadiza dalibar shi ce irin yaran likitocin nan da ake koyarwa a (teaching hospital). Ya fahimce ta
yarinya ce mai matukar kwazo a tsakanin tsararrakin ta. Wani abin mamaki da ya fara bincike a
kanta 'yar talakawa ce likis, amma iyayenta sun tsaya tsayin daka wajen daukar nauyin karatun
ta, duk da tsadar shi kuwa, da dukkan iyawarsu.
Soyayya ce mai tsabta irin ta wadanda suka wadata da ilimi suka gudanar kamin aure. Ga
Hadizah ba karamar sa'a ba ce, kuma ba karamin abin alfahari bane samun mutun kaman
Sulayman (as a husband). To haka shi ma.
Hadiza ta tara duk wasu qualities da yake nema ga diya mace, ga dai kyau ga kyan hali, ga
addini da kyakkyawar zuciya, sannan uwa uba ta samu ingantacciyar tarbiyya daga iyayen
kwarai.
Iyayenta suna nan a unguwar Karkasara dake cikin birnin Kano, sana'ar mahaifinta shi ne
yadiddika yake sayarwa, yana da shago a nan kantin Kwari.
Hadiza ita ce ta biyu a cikin 'ya'yan gidansu, akwai Yayanta Mukhtar wanda ke aiki da (Zenith
Bank) a Kaduna, kusan da tallafin shi ne Hadiza ta samu ta kammala karatun ta.
Duk da haka shi ma mahaifinsu a tsaye yake a kan karatun su, don yaga amfanin da karatun
yayiwa Mukhtar. Sai kanwar ta Fati, budurwa ce 'yar kimanin shekaru sha bakwai, a bana ne ta
kammala karatun sakandire. Sai Hamza da Yusuf, da dan autan su Abdulyassar.
Duk cikin kannenta Hadiza ta fi son Fati, wata irin yarinya ce mai sanyin hali, sanyin kyau da
sassanyar zuciya. Akwai wata irin shakuwa ta musamman tsakanin Hadiza da 'yar uwarta Fati.
Jininsu ya hadu sosai ta yadda Hadiza ba ta iya shawara da kowa kan al'amuranta kamar Fati
saboda hankalin ta. Fati yarinya ce mai tsananin son addini da nutsuwa, ba ta da rawar kai ko kadan irin na
'yammatan zamanin nan, komi nata cikin hankali da nutsuwa yake. Ita da Hadiza kamar an
tsaga kara, sai dai Hadiza fara ce sol, yayin da Fati ta kasance wankan tarwada. Amma hatta
yanayin tafiyar su da murmushin su iri daya ne.
****
Sulaiman – Sulayman Bakori, mutumin garin Bakori ne ta jihar Katsina, daga kallo na farko
mawuyaci ne ka bambance daga kabilar da ya fito, wani mutum ma'abocin cikar zati da kamala
da duk wani nau'in daidaito na rayuwa, ga dimbin ilimi a cikin fannonin kiwon lafiya
daban-daban. Ya ci sunan mahaifinshi ne don haka a gidan su ake kiran shi mai sunan Malam. Mahaifin shi Malam Sulaiman, Malami ne mai karantarwa, yana baiwa magidanta anguwar su
karatun buzu. Duk wani da ya kwana ya tashi a garin Bakori ya san Malam Sulaiman
Mai-Gafaka. Mutum ne da al'ummarsa ke matukar ganin girman sa, kuma ya yi fice a garin
Bakori baki daya saboda ilimin da Allah ya ba shi, kowa yana daraja shi. Shi ne da na biyu a gidansu, yayar shi Jummai ta rasu wajen haihuwar fari, sai kannen shi
Ramatu, Saude da Ruma, duk suna gidan aure. Sai Khalid wanda ke karatun sakandire a halin
yanzu.
Sulaiman ya yi dukkan karatun shi ne da taimakon gwamnati da mahaifiyar shi Inna Halima,
wadda duk lokacin da hidimar karatun ta tashi take fitar da kadararta ta siyar ta yi masa. In dan
ta Malam ne sakandire ma kawai ta isa. Burinsa Sulayman ya zauna a gida ya tallafa mishi
kasuwancin shi na fata, ya yi aure ya haifa mishi jikoki shi kuma zai yi masa komai. Amma Sulaiman ya ki, ya dage ga son cimma burinsa na son zama likita. Ba abin da yake so a
rayuwar shi irin yau a ce ya zama likita yana yiwa mutane allura.
Irin yaran nan ne gifted tun suna kanana, wato 'yan baiwa. Wata irin kwakwalwa gare shi da ba
duk mutane Allah yake baiwa ba, duk inda yayi karatu malaman shi sai sun san shi, sun kuma
ja shi a jiki, sun so shi saboda hazakar shi.
Ya yi gaba dayan karatun shi daga jami'ar Najeriya (NSUKKA). Bayan ya kammala MBBS din
shi ya yi nasarar samun scholarship zuwa jami'ar (Manchester) inda ya yi specializing a kan
zuciya da duk abin da ya shafe ta. Bayan kammalawar shi da dawowar shi ya soma aiki da
federal Government, hakan ne ya sa ake yawan canza mishi wajen aiki. Daga wannan gari
zuwa wancan cikin jihohin Najeriya.
Ya fara ne da aiki a babbn asibitin koyarwa na Ibadan, daga baya suka mai da shi ABU
Teaching Hospital. Nan din bai dade ba suka dawo da shi nan AKTH na Kano, inda Allah ya
hada shi da Hadizah.
HADUWAR SULAIMAN DA HADIZA
Haduwar su haduwa ce special kuma haduwa ba ta dadi ba. Yana tare da patient da ya yiwa
aiki satin da ya wuce, Hadizah Ja'afar, da wasu abokan karatun ta suka shigo domin daukar
lacca kamar yadda suka saba. A matsayinsa na consultant dinsu, basu samu kallo daga gareshi
ba, balle ya tantance kamannin su, kasancewar Allah bai dora mishi lalurar yiwa mata kallon
kurilla ba. Tsakanin shi da kowacce diya mace, kallo daya ne, da kau da kai. Wannan a jinin
Sulaiman yake.
Suka samu kujeru suka zauna, kowacce da jotter din ta da biro a hannu. Yana ta yi musu bayani
cikin lafiyayyen turancinshi na Birtaniya mara surki, wani zubin ya yiwa mara lafiyar tambaya ta
ba shi amsa.
Wata amsa da patient din ta bayar ta sanya su murmushi dukkanin su (ban da Hadiza), cikin
kalaman ta za ka fahimci kwakwalwarta ta tabu sakamakon bacin zuciya da damuwa.
Ta ce,
"Likita nifa 'yar sarauta ce ba mara lafiya ba!".
(Wannan ne ya sanya su yin murmushi). Ya ce,
"Wacce sarauta gare ki don mu fara girmama ki?"
Gaba daya daliban suka yi dariya don yadda yake biye ma shirmen matar dole ya baka dariya.
Ta ce,
"Sarautar Kano gare ni".
Ya ce, "Wacce ke nan?" Ta ce,
"Nice 'yar ruwatan Kano".
Gaba daya suka yi murmushi, wannan karon ma ban da Hadizah, wadda a lokacin hankalinta
baya tare dasu, yana ga halin da ta baro Mamansu a ciki na rashin lafiya mai tsanani.
Ba zato Dr. Bakori ya jefo tambaya, "Mene ne delusion?" Ya kuma nuna Hadiza da ya lura
hankalinta ba ya tare da shi matsayin wadda za ta amsa mishi tambayar shi.
Ya yi mata magana ya kai sau uku ba ta san yana yi ba. Hadiza ta damu da Mamanta sosai,
kasancewar ta jarumar Uwa mai hidimtawa rayuwar su, tun daga yarinta har a girman su. Yaya,
(Sa'adatu), ba ta huta da dawainiyar su ba. Don haka jin ciwon ta suke tamkar a gangar jikin su.
Duka kawayen ta babu wadda ta zungure ta, don sun san da ta ji za ta ba da amsa a yabe ta
kamar yadda manyan likitoci suke yabon ta a kullum saboda kokarin ta.
Ya buga tebir din gaban shi da karfi har ta razana, ya nuna mata hanyar waje ya ce, 'You can go
out..... in kin gama tunanin kya dawo".
Ta mike sumi-sumi ta fita, murna gun su Hafsat kamar su yi yaya, yau Allah ya nuna musu
likitan da ya yi maganin 'yar gaban goshin likitoci. Ya yi (referring patient) din zuwa psychiatric,
su kuma ya sallame su.
Ya koma gida a wannan ranar, bayan ya gama duk abubuwan da ya saba na al'adar rayuwar
shi kamin ya kwanta, kamar shan fruits da exercise saboda shi da daddare yake exercise din sa
kasancewar da safe ba shi da lokaci.
Amma abin mamaki ya kasa runtsa idonsa, tunanin fuskar dalibar da ya kora a yau ke gilma
mishi, ya hana shi sakat, ya hana shi sukuni, ya yi duk kokarin da zai yi don ya samu barci
amma hakan ya faskara. Ya ko kasa runtsa idon sa, wani bakon al'amari ne mai takura zuciya
da bai taba tsintar kansa a ciki ba. Hadiza ba wata muguwar kyakkyawa ba ce cancan, tana da kyau dai-dai nata, sai dai kuma
yarinya ce mai aji na karshe. Fuskarta zagayayya mai dauke da dara-daran fararen idanu masu
sheki da walainiya, hancinta kamar an sanya ruler an ja shi an daidaita shi a kan (oval -shaped)
fuskarta. Bakinta dan karami kamar cokali baya shige ba. A kan tsinin hancinta tawwadar Allah
ce da aka haife ta da ita, fara ce sol! Irin farin nan da wadataccen ilimin boko ke taimakawa
wajen zahharar sa.
Bai taba ganin yarinyar da (lab-coat) ta yi ma kyau kamar Hadizah ba. Ba sai ya tsaya wahalar
da kanshi wajen tunanin abin da ke faruwa da shi ba, ya tabbata son Hadiza ne ke ratsa
kowanne sako a jikinsa.
Abin haushin ko sunan ta bai sani ba, zuciya ta kwashe shi ya yi abin da ya zo ya dame shi. Bai
taba tsintar kansa a kwatankwacin irin wannan yanayin ba, a kan diya mace.
Sai dai shi a ce ana son sa yana hura hanci, kada hakan ya janyo raini, baya fatan hakan ya
kasance sakayya ce Allah ya yiwa dimbin matan da ke binsa agindi-agindi don ya so su yana
yakice su. Tare da yi musu wulakancin da ko a hanya suka ganshi bazasu yi fatan ace sun san
shi ba. Ya fahimci dalibar (obstetric and gynaecology) ce, daga (ID Card) din ta. Yadda ya ga rana
haka ya ga dare, ko na second daya bai runtsa ba. So da kaunar student (daliba) Hadiza na
narkar mai da zuciya.
Abin kamar sihiri, daga ranar bai kara ganin Hadiza ba, bai kuma san ya zai yi ya tambaya ba,
tunda ko sunanta bai sani ba. A matsayinsa na babban likita, mai juya sauran likitocin bangaren
su, ba karamin zub da kima bane a ji shi yana tambayar wata yarinya cikin masu daukar darasi
a wurin su. Duk da haka bai fidda rai ba, yana da yakinin watarana Allah zai sake hada shi da
yarinyar ko da a mafarki ne.
Ita kuwa Hadiza ba ta dawo TH ba sai bayan sati uku, tana gida tana jinyar Maman su da suke
kira Yaya, da ke fama da ciwon hanta. Tana ganin likita a Murtala, har suka kwantar da ita sati
guda.
Kawarta Surayya ke daukar musu lacca tana kuma sanar da ita duk abin da ke faruwa ta waya.
Ranar monday Maman su ta ji sauki sosai, don haka ta shirya ta dawo.
Ba zato babu tsammanin shi, yana ganawa da wata patient din suka shigo ita da Surayyah, ya
zare gilashin idonsa a hankali, ya saki wata sassanyar ajiyar zuciya irin ta wanda ke neman
abu, ya wahala ya dade, kamin ya samu. Duk hankalin sa da attention din sa sai ya koma
kanta, ya manta abin da ke gabansa, ya samu kansa da rudewa. Abin da bai taba yi ba a kan
diya mace, akwai wani sassanyan kallo cikin kwayar idon Hadizah, da ba duk mata Allah ya
mallakawa ba.
Suka gaishe shi cike da girmamawa, sannan suka samu kujeru suka zauna. Hadiza dai a
darare take, ko kanta ba ta dago ba. Daga gefe-gefen idon ta take satar kallon likitan da ya
hargitsa mata tunani 'yan kwanakin nan. Tunda ya kore ta ba ta kara samun nutsuwar zuciyarta
ba, har zuwa yau da ta sake tozali da shi a karo na biyu. Ta tambayi kanta, shin ko mutane nawa ne a duniya masu ilhamomin Dr. Bakori? Yana da wasu
ilhamomi na musamman a tare da shi da ba ta taba ganin su a da namiji ba, ko yadda yake
duban mutane daban ne da na sauran likitocin da ta sani. Tsarin maganar sa cikin seriousness
shi ne babban abinda ke burge ta da shi, ga kamun kai da sanin mutuncin kai, hadi da rashin
son wasa ta ko’ina. Dr. Sulayman Bakori, ya shiga cikin rukunin wasu mutane da take ganin
matukar kima da mutuncin su, sannan kuma ya bi ya manne a zuciyarta, ta yadda dai-dai da
minti daya ta kasa manta shi cikin satittikan da ta yi tana jinyar Mamanta.
A gurguje ya basu laccar ya kuma sallami mara lafiyar da suke tare da ita. Suka mike da nufin
su tafi, baya fatan wannan damar da kubuce masa, don haka bai yi kwauron baki ba, ya yi ta
maza (in ji