Turken Gida Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Complete Novels

Chapter   8 / 48

21K to 24K   out of 141.5K words

ta na son Yusuf? Domin ga waliyanshi sun iso domin nema masa auranta. Da rawan jiki da na zuciya ta amince, a cikin office ɗin ta bayan Anty Bahijja ta kira ta ta ce an ɗaura auran ta da Tafida sai da ta faɗi ta yi sujjudar shukur ta na hawayen farinciki atleast dai yau burinta ya cika tabbas kar bawa ya cire tsammani duk abin da ya ke rabon ka ne ko ya hau sama sai ya faɗo a kanka. Alhamdulillah.

Bangaren Tafida Kawu Sa'adu ne da su Abba suka karɓa masa auran Sadakin kuma Nene ce ta biya da kuɗinta saboda yadda ta ke son Tafida da Saudatu. Bayan an gama ɗaura aure kuma acan gidan Hajiya aka fara ɗora girki na sadaka, bakinta har kunne ta kira sauran Ƴayanta a waya duk ta sanar da su kafin ka ce kwabo labari ya zaga Rano da kewayenta.  Abba shi kan shi ya yi mamakin auran nan cikin gaggawa da Mimisco ya yi mgana ita ce ke yi masa bayanin yadda lamarin ya fara. Amma Yusuf bai iya ba, domin lamarin kamar a mafarki ya ke gani. Duk roƙon da ya yi musu sai da Bahijja ta ɗora a status a tunaninta ta cire Sadiya ko ta manta da Ma'u ne?

  Ko Tariq da ya ji yadda asalin lamarin ya faro ya ji wani iri. Duk da Gimbiya ƙanwarsa ce kuma ya na yi mata murna, amma bai ji daɗin yadda Tafida ya amince aka ɗaura aure ba tare da ya yi mgana da Sadiya ba shima Abba haka ya ce amma sun yi ta ba sa shawaran da ya koma gida ya sanar da ita gudun samun matsala, amma sai ya ji ya kasa ya na gani ta na tura masa saƙon Anniversary ɗin su sai a lokacin ma ya tuna muhimmancin ranar a gare su, sai dai ina ranar kuma sai ta rikice ta koma rana mara daɗi ga Sadiya ba zai iya kashe mata karsashinta wannan ranar ba, shi ya sa har ya gama nuku nukunsa ya koma gida ya kasa iya faɗa ma Sadiya wai shi ya ƙara aure ba tare da ta sani ba. Ya kusa shafe sama da awa ɗaya a waje ya kasa iya shigowa ga shi dai ba abin kunya ya aikata ba amma yana jin tsoro da kunyar haɗa ido da Sadiya a wannan yanayin.

Lokacin da ya shigo gidan suka haɗa ido da Sadiya sai ya ji kunya kwataƙwacin kamar ya ci amanarta haka ya ji. Ya kasa iya sarrafa kansa a gabanta. Har aka wayi gari yana cikin wannan yanayin sai daga baya ne ya fara warwarewa. Bai taɓa tunanin Sadiya ta ji mganar auran shi ba, duk da dai mganar ta zagaya dangi tunda ana ta kiran shi ana masa fatan alheri. Ya yi ta mamakin duk labarin ya je ma kowa, a tunanin shi Sadiya ba za ta sani ba shi ya sa ya ke ta shirye shiryen yadda zai tunkare ta da maganar sai ga shi duka shirinsa ya rushe. Ga shi shagon da ya kama mata har ya biya kuɗin shekara key na hannun shi, kunya da nauyin sun saka ya kasa yi mata mgana, balle yanzu in ma ya nuna mata a zuciyarta za ta ce ba domin Allahya yi ba saboda ya yi mata kishiya ne shi ya sa ya kasa bata. Ya tuna jiya har sai da Musbahu ya yi masa mganar shagon.

"Yaya Tafida wai ƙasa za mu koma ne?

Sai ya girgiza masa kai a lokacin. Domin shi kan shi bai san mafitan shi a lokacin ba. Sanin da Sadiya ta yi ba tare da ya faɗa mata ba ya yi masa mumnunan duka, saboda yanayin da ya ke ciki tun da aka ɗaura auran sau biyu suka taɓa waya da Gimbiya gidan ma sau ɗaya ya je suka haɗu bayan kuma gaisuwa wata mgana mai tsawo ba ta shiga tsakaninsu ba, ya fi so sai ya gama da Sadiya sun samu daidaituwa kafin wata mgana ta biyo baya. Ya tsara a jiya zai yi mata mgana ya sanar da ita sai kuma Allah bai so ba ya yi tunanin yau ɗin in ya koma gida amma tun haɗuwarsa da Yaya Abubakar gabaɗaya tsarin sa ya ruguje mafita ya ke nema ya rasa mafitan. Shi ya sa ya kasa iya komawa gida da wuri ya kama hanyar gidan da dadaddren kenan kuma sai ga kiran Nene ya riskeshi.

******

Ya na cikin motan bai fito ba sama da mintina talatin. Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi. Wayar sa ya laluɓo a gaban Aljihunsa ya sake kiran Abba.
  Yana ɗauka bai ko jira sun gaisa ba cikin roƙo ya fara faɗin" Don Allah Kawu ka taimaka min ka zo gida gobe ka ta ya ni fahimtar da Sadiya don Allah."

   Daga can bangaren Abba ya ce" Sai kuma ka yi. Wallahi ba in da zan zo. Kai ba ka da baki ne? Ko kai ba Namiji ba ne?
A sanyaye Tafida ya ce" Kunyar ta na ke ji fa."
"To ai sai ka murje kunyar ka sanar da ita. Duk da dai bakin alƙalami ya riga ya bushe. Sai dai ka yi gyaran mgana daga baya."
 
"Kai yanzu don Allah ba za ka zo ka yi mgana da ita ba?

"Wallahi ba zan zo ba. To ni me ye nawa! Ni ne mijinta? Kai ne mijinta kai ya dace ka zaunar da ita ka koyo kalaman haƙuri da kare kai har sai ta fahimceka. Kai fa namiji ne kuma ka fi ni sanin matarka sosai ka san kuma hanyoyin da za ka bi da ita har ta fahimceka. Amma ni dai na roƙe ka don Allah ka daina saka ni a cikin wannan mganar."

Ko ma ya jira cewar Tafida ya kashe wayarsa ya bar sa cikin damuwa da tararradi Ya daɗe zaune yana tufka ya na warwara amma duk in da ya kamo ya fara tufka sai ya warware ya kasa samun mafita guda ɗaya da zai kama. Dole dai ya buɗe mota ya fito a kasalance kamar mara lafiya ya wuce cikin gida saboda dare ya yi kowa na cikin ɗakin shi, ɗakin Maman Farko ya leƙa suka gaisa daga nan ya wuce shashen Nene falon shuru har sun rage haske alamun sun kwanta da ya yi sallama ne ya ji muryan Nene daga ciki ta na amsa masa, sai ya cire takalminsa nan ƙofar falo ya shiga har cikin bedroom ɗin Nene

Ya iske ta har ta kwanta ma ganin shi ya sa ta miƙe zaune bayan ta miƙe kafafunta ta na faɗin" Tafida sai yanzu?
Ya na sosa kansa ya ce" Wallahi na tsaya gamawa da Office ne Nene"
Ya faɗa dai dai ya na zama gefen kafafunta a gefen gadon. Gaisawa da tambayan iyalan shi ya ce suna lafiya kafafunta ya ɗauka ya ɗora a saman cinyarsa ya na matsawa.

"Suna ciwo ne yanzu?

Ya faɗa ya na kallonta lokaci ɗaya kuma yana ƙara matsa mata kafafun duka biyun.

"Ba sosai ba. Saudatu na shafa min man zafi in zan kwanta."

Kallonta ya yi kafin ya ce" Amma yau dai ba' a  shafa ba ko? Ban ji zafin sa ba "
Ya faɗa ya na shinshina hannunsa.

"E. Ba ta jin daɗi yau kanta ke ciwo ta ce min da wuri ma ta baro wajen aikinta."
Cikin nuna jimami ya ce" Subhanallah ta sha mgani?
"E. Ta sha da sauƙi ta ce bari ta kwanta ne. In ka tashi tafiya sai ka shiga ka duba ta." Sai ya amsa mata da toh sun ɗan fara taɓa hira ganin dare ya yi ya sa ta kalle shi kafin ta ce" Kan mganar Saudatu ne daman."

Sai ya maida hankalinsa a kan Nene ganin haka ya sa sai ta cigaba da faɗin" Na ga an kusa yin sati da ɗaurin auran ku kuma ban ga kana zuwa ba, ballantana ma ku yi mganar yadda za ku tsara tarewar na ta."
Shuru na wani lokacin kafin ta ƙarƙare da faɗin" Shi ne daman na kira ka na ce ka zo na ji ko lafiya?

Shuru ya yi kafin ya sauke numfashi.
"Nene."
Ya kira ta amsa kafin ya ce" Daga ke har Gimbiya ku ɗan ƙaramin lokaci don Allah"
"To shike nan"
Nene ta faɗa ta na kallon shi a yanayinsa kawai ta gane akwai damuwa.
"Akwai matsala ne Tafida?
Sai ya gyaɗa kai  da sauri ta sauke kafafunta ƙasa ta zauna dakyau ta na faɗin" Sadiya ce?

Sai ya ƙara gyaɗa mata kai ya ce" Ta ji labari Nene ta ji labari."
Cikin mamaki ta ce" Ta ji labari? Ba ka gaya mata ba ne daman?
Nan ma kai ya gyaɗa mata kafin ya ce" Na kasa faɗa mata ne. Ina ta riƙe mganar daman yau na ke shirin faɗa mata sai kuma na haɗu da yayanta wajen jana'iza sai gashi yana min murna kuma ya ce ita ta faɗa musu na ƙara aure."
Ya karishe faɗa kamar zai yi kuka Nene ta dafa kanshi kafin ta ce" Ka kwantar da hankalinka. Kuna da fahimta kai da Sadiya. Yanzu ka tashi ka tafi gida ka zaunar da ita ka yi mata bayani na san za ta fahimta.'

Sai ya gyaɗa kanshi kafin ya kalli Nene ya na faɗa min" Nene abin mamaki a ina ta ji! Kuma wa ya sanar da ita?
Nene ta ce" Sanin wanda ya faɗa mata sai Allah. Amma ba abin mamaki ba ne domin ta ji labari. Magana in ka iya rufe bakin wani, ba za ka iya hana wani mgana ba. Ka yi kuskure da tun lokacin ba ka faɗa mata ba, amma yanzu ma baka makara ba ka tashi ka je gida ka zaunar da ita ka yi mgana da ita cikin Sigar da za ta fahimcen ka ka ji ko?
Sai ya gyaɗa mata ɗan shafa kanshi ta yi kafin ta ce" Tashi ka je. In sha Allahu ba matsala."

Da haka suka yi sallama bai fita ba sai da ya ga ta koma ta kwanta har ya ɗan rufa ma ƙafafunta bargo ya kashe mata fitilan ɗakin sannan ya fita. Har ya kai ƙofa zai fice sai ya tuna da Nene ta ce  ya shiga ya Duba Gimbiya sai ya fasa fitan ya dawo zuwa ɗakin da Gimbiyar ke ciki ya ƙwaƙwansa sau biyu daga ciki ta ce a shigo sai ga shi ya buɗe a hankali ya shiga da sallama.

Ta amsa masa sallamansa tana zaune a gefen gado amma ta saka wani ƙaramin hijabi hasken ɗakin a kunne ya ke alamun ita ta kunna.
Sun haɗa ido ita dashi sai ya yi mata mirmishi itama sai ta mayar masa. Tura ƙofar ya yi ta rufe kanta sannan shi kuma ya fara takowa zuwa gabanta da jikin wadrope ɗin da ke ɗakin ya Jingina wanda a baya babu shi a ɗakin ita Gimbiyar ne ta saka a ka yi mata anan garin.

"Sannu ya jikin?
Kan ya daina ciwo?

  Ya kauda shurun da ke tsakaninsu tun bayan gaisuwan da ya shiga tsakaninsu.

"Da sauƙi."

Ta faɗa a hankali, cikin sanyin murya. Sai ya yi mata fatan samun sauƙi kafin ya ce" Kin sha mgani?
Sai ta ɗago ta kalleshi kafin ta ce" E. Na sha."
Shuru na wani lokaci ba tare da tsammani ba kanta na ƙasa ta ga ƙafafunsa a gabanta kafin ta ɗago kanta ta ji tattausan hannunsa bi sa goshinta sai da ta runtse ido cikin wani yanayi.

"Uhm na ji kan na ki ba zafi sosai."

Haka ya faɗa ya na yin baya kaɗan.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali saboda yanayin da ta ke ciki.
Ya juya kamar zai fita daga ɗakin ya na faɗin.
"Allah ya ƙara lafiya. Ki kwanta ki huta kin ji ko?
A ƙasa ƙasa ta amsa da Amin.

Har ya saka a hannu a jikin handel ɗin ƙofar sai kuma ya juyo daman itama kallon shi ta ke yi sai suka haɗa ido.
"Daughter."
Ya kira sunanta kamar yadda ya saba.
"Na'am Daddy."
Shuru ya yi na wani lokaci kafin ya ce" Na faɗa ma Mamanki ke da ita ku ɗan ƙaramin lokaci kaɗan. Ina so na ɗan gama da wasu abubuwan ne first daga baya sai na zo mu yi mgamar tarewar ki ko?

Ya faɗa ya na mai kallonta da sauri ta sunkuyar da kanta kafin ta ce" To."
Ta na mirmishi, shima mirmishin ya yi mata sannan ya juya ya na faɗin" Sai da safe."
"Gud night."
Itama ta bashi amsa har ya fita ya rufe mata ƙofa ba ta daina mirmishi ba ya na fita ta faɗa gado ta na tsalle da kafafunta lokaci ɗaya ta na rufe bakinta. Ta ji shigowarsa falon Nene tun farko har leƙensa ta yi bai sani ba ta na ta Allah Allah ya shigo ta gan shi ko za ta ji daɗi sai ga shi Allah ya amsa roƙon ta. Wani irin rawa zuciyarta ya ke yi na soyayya da ƙauna har yanzu ba ta daina godema Allah ba domin ya gama yi mata komai. Ubangiji ya gama ba ta komai anan duniya tunda har ya mallaka mata Yusuf. Za ta iya jiransa ko nan da shekara ne ba dai an ɗaura ba ai an gama mai wahalan.

*****

10:50pm

Goma da minti Hamsin Yallaɓai ya shigo cikin bedroom ɗin mu. Ina kwance da waya a hannuna ina dannawa shi ya sa ma na duba lokacin. Na so na yi barci kafin ya dawo barcin ne ya ƙi zuwa dole na ja wayata na kunna data ina ta shige shige. Mun yi chart da Amina sai Munnira. Sannan kuma mun yi waya da Sameena ƙanwar Gimbiya yadda ba ta min mganar auran Yallaɓai ba, nima ban yi mata ba na san ta sani kawai ba ta so ne ta fara ɗauko min mganar amma mun yi hira da ita sosai.

Ni Munnira ke ba ni mamaki ta ƙi yi min mganar ni a tunanina ko wani zai ɓoye min su sai su ɓoye min amma ina jiran su wallahi sai na yi musu wankan soso da sabulu. Datti ma da daren nan ya kira ya na ce min ashe Yallaɓai ya yo amarya Amina ke faɗa masa shi bai damu ba dariyan shi ya ke yi  to daman su maza ina ruwan su ko uku Yallaɓai ya ƙaro min lokaci ɗaya na tabbata cewa za su yi ya yi dai dai. Ko a jikinsu tunda daman duk halinsu ɗaya na son kansu.

Kafin ya dawo ba tunane tunanen da sheɗan bai gayyato min ba, in na runtse ido sai na riƙa hasko shi da Gimbiya a cikin yanayin da kan iya haifar min da hauhawan jinina sama. Lokacin da ya shigo da sallama na yi niyyar ne na ƙi amsswa amma sai na taushi zuciyata na amsa masa ta gefen ido ina kallon shi, domin ni kawai na saka a raina ya na wajen Gimbiya wato tun kafin ta tare ya fara raba ma na yini saura kwana kenan.
Wanan malolon abun da ya ke cikin ƙirjina tun san da na ji labarin auran sa da bai wuce ba har yau shi ne ya taso min.
Daƙyar na iya daurewa a shaƙe na yi masa sannu da zuwa sai na ga shima bai kalleni ba ya amsa kawai.

"Ya gidan ne? Ya kika je kika samu su Alhajin?

Ashe ya tuna in da na je. Ba ya kallona kayan jikinsa ya ke tuɓewa. Nima sai na kauda kai kafin na ce" Duk suna lafiya."
Daga haka na cigaba da duba waya ta a IG har Volume na ƙure da gangan saboda haushi bai kalleni ba, kuma bai ƙara mgana ba bayan ya bar gajerun wando na ga ya fita sai na ji ƙaran ƙofa kenan ya shiga Tiolet wanka ya yo ya fito ina nan in da ya barni kwance, ina ta nazarinsa ta gefen ido, har ya gama shirin barcinsa na ga bai yi min mgana ba kuma ya na shirin kwanciya sai na daure na waiwaya ina kallon shi kafim na ce"

Abinci fa na Dinner."

Sai ya kwanta a can gefensa sannan ya ce" Ba na jin cin wani abu yanzu."
Daga haka sai na ga ya juya min baya kawai ya yi kwanciyarsa. Mamaki ya kamani amma na kasa mgana sai nima ma juya masa bayan ina sakin ƙaramin tsaki kuma na tabbata ya ji ni. Amma bai yi wani motsi ba, da gayya na yi ta shiga Yuotube ina shiga waƙoƙi ina ji domin na dame shi amma har na gaji bai motsa ba, ba ni na kwanta ba sai 12pm sannan na ijiye waya da na ji barci, ina yin addu'an barci na runtse ido sai barci.

Zai da ya tabbatar da ta yi barci sannan ya juya yana kallon bayanta.
Dole ne ya sa ya yi avoiding ɗin Sadiya ya rasa da idanuwan da zai kalleta abin da ya yi shi ne dai dai. Bai ma ɗauka zai zo ya same ta idanuwanta biyu ba. Ajiyar zuciya ya sauke ya yi kwanciyar rigingine ya na kallon rufin ɗakin na POP. Ya na kuma tunanin ta ina zai fara? Duk in da ya yi tunanin zai fara ta can sai ya ga hanyar ba mai ɓullewa ba ce, ya daɗe bai yi barci ba ya na faman juye juye amma har garin Allah ya waye bai samo mafita ba.

****

Saboda rashin barcin da bai samu a daram jiya ba ya sa tun bayan da ya dawo sallar asuba ya ke kwance ya na barci sai kiran wayarsa ce ta tashe shi.
Sai ya ga Nene ce ke kiran shi da sauri ya miƙe zaune ya na daidai ta yanayinsa.
Sannan ya ɗaga kiran.
"Tafida."
Ta kira shi bayan ya yi mata sallama.

"Na'am Nene ina kwana."

"Lafiya lau. Kana gida ne?
Sai ya amsata mata da E.
"Ka yi mgana da Sadiya jiya!
Cikin kasala da muryan barci ya ce" Ban yi ba Nene."
"To ka jira ni. Kar ka yi mata mgana."

Cikin mamaki ya ce" Me ya sa Nene?
"Akwai dalili. Ka jira ni."
Daga haka ta yanke wayarta sai ya bi wayar da kallo yana mamaki bai koma ya kwanta ba amma ya kishigiɗa da gado ya harɗe hannayensa a ƙirji ya na hasoso tunanin Nene na cewa ya jira ta.
Bai taɓa tunanin shirin Nene na zuwa gidan shi ba ne sai bayam mintina talatin da wayarsu da Nene ya ji kamar ana buga get duk da ya san Sadiya na can cikin gida baya tunanin za ta ji, shima domin ya na cikin bedroom

8 / 48