Author : Janafty Category : Complete Novels
ne ina ga kammani ya gani ya buɗe min ƙofa na shiga ina jan kafa har wani duhu duhu na ke gani.
A ƙofar shiga falon na duƙe ina jin amai na taso min bayan na buga mata ƙofa. Amai na ke yi ruwa ruwa tun da bakomai a cikina. Na kasa tashi har na ji an buɗe ƙofar na ji muryan Amina ta na kiran sunana.
"Ya Sadiya?
"Ke ce?
Ɗagowa na yi ina kallonta da idanuwana da suka yi laushi. Hannuna na miƙa mata ta kamani lokaci ɗaya ta na faɗin" Innalillahi Ya Sadiya me ya same ki?
Ni dai ban bi ta kanta ba, nan na watsar da jakata da akwatin Amina ta kamani zuwa cikin falonta kan kujera na yi yarf kwance domin sai na ji kamar ruwan jikina ya ƙare da gudu ta koma ta ɗauko jakata sannan ta jawo akwatin zuwa tsakiyar falon. Ni kuma amai ya ƙara taso min sai na tashi ina tangaɗi na yi bedroom ɗin ta da gudu ina jin ta ta biyo bayana ta na faɗin.
"Subhanallah Ya Sadiya."
Sama sama na ke jin ta sai da na dangana da tiolet ɗin bedroom ɗin sai gani zaune a ƙasan tiolet domin ba zan iya tsayuwa ba, ji na ke yi kamar ba ni da ruwa ba ni da jini, ina amai amma ina ji kamar hanjin cikina za su yo waje, kakari kawai na ke yi ni dai na ji Amina ta buɗe ƙofar tiolet ta na ƙara kiran sunana amma ina kamar a wata duniyan na ke jin ta ,kaina da ya yi min nauyi na jingina da jikin garon Tiolet ɗin ina jin kamar fitsari na bin jikina.
Ya illahi fiteari na ke yi a zaune saboda jikina ya yi mugun sakin da ba zan iya motsa koda ɗan yatsa na ba ne.
"Innalillahi na shiga uku Ya Sadiya."
Na ji ta kamani ta na ƙoƙarin miƙar da ni tsaye amma ina jikina gabaɗaya ya saki. Idanuwana suna lumshewa amma sai da suka gano min jan abu da na ga ya na zirarowa ta ƙasan kafafuwana. Kamar jini na gani. Ba kama ba ne jini ne ke bin ƙafafuwana ba fitsari ba ne.
Sai na yi ƙoƙarin tashi ina mai dafe bango Amina na riƙe ni har ta fara murya kamar za ta yi kuka.
"Mun shiga uku Ya Sadiya jini kike zubarwa."
Na ƙara bin ƙafafuwana da kallo jini ne da gaske har ya gangaro ya ɓata farin tayels ɗin Tiolet ɗin. Ina ƙoƙarin na tsaya da kafafuwana amma na kasa. Kamar an ɗauke ni daga wannan duniyar haka na ji kamar ɗaukewar iska shuu.! Sai na tafi yaraf na faɗa a jikin Amina. Bakina na motsi ina so in yi magana a lokacin sai komai na duniyar ya tsaya mini cak kamar an zare rai daga gangan jikina.
*Ƙarshen littafi na biyu.*
*ZA MU TAFI HUTUN KWANA BIYU KAFIN MU ƊORA A LITTAFI NA UKU IN SHA ALLAHU.
NA GODE DA JIMARIN BIBIYAR WANNAN LABARIN.
*16. Jan 2025.*
*Janafty*
.
.