Turken Gida Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Complete Novels

Chapter   28 / 48

81K to 84K   out of 141.5K words

na koma na ɗauka na bar masa falon na kuma san ya bi ni da kallo, a ɗaki na je na zube kayan na yi kwanciyata da safe ma ranar shi ya kai yara makaranta suna ta murnan za a ba su hutun salla.
Ban masa mgana ba na ga ya turamin kudi a acct ɗina sai ga kiran shi na ɗauka muka gaisa.

"Na kitso ne da kunshi. Ke da yara."

Nan ma na ce Allah ya saka da alheri. Ba shi ya faɗa mini Gimbiya za ta yi layya ba Musbahu ne da ya kawo mini cefanen kayan miya da naman miya ya ke faɗamin ita ma za ta yi layya sannan raguna uku Yallabai ya siya nawa da na shi sai zai yi ma Alhajinsu ita kuma Nene Mimisco ce za ta yi mata Ya Usman kuma zai yi ma Maman farko da Hajiya iya. Kuma za su yanka sa a cikin gidan gabaɗaya ragu nan ma suna can gidan. Yadda bai nemi na ji ba ni da ba ma mgana muke yi ban masa mgana ba. Mu ma gida Ya Hamza zai yi ma Alhajinmu da Gwaggo sannan Ya Auwal ma zai yi ma Mama da Baba Aminu, kuma sannan dukkansu a gida za su yi salla da iyalan su, wannan salla kuma ni ban yi komai ba cincin kaɗai na kira Saude da Marwa suka taya ni muka yi, ni ban yi kitso ba sai yara gyaran kai na je aka yi min a shagon Amesty. Amma mai lalle ana jibi salla  ta zo har gida ta yi mana ni da yara da Marwa tunda na ce a wajena za ta yi sallah

Har ana jibi salla ba na ma Yallaɓai mgana amma ban fasa  sauƙe haƙkinsa dake kaina ba. Na aure ne dai kowa ya yi ta kanshi in ya na gidana ba na kwana a ɗakin mu sai bedroom ɗin baki, ranar dai a gidana ya ke sai gobe zai koma gidan Gimbiya. Yadda na watsar da shi ne na san ya dame shi, ranar da wuri ya dawo ya shammace ni ban rufe ƙofa ya shigo ɗakin kuma ga su Marwa ba su yi barci ba bana so na ɗaga murya ta.

Ina zaune a gefen gado mun gama mgana da Amina kenan ya shigo ta na faɗa min itama ranar biyun salla ta na tafe. Sallamarsa kawai na amsa ban yi masa ko sannu da zuwa ba na maida kaina kan wayata.
Zama ya yi a gefe na, ni kuma sai na yi saurin matsawa sai kawai ya kalleni kafin ya ce.

"Sadiya wai gaba kike yi da mijin ki?

Kai tsaye na ce" Ba na gaba dakai. Ko ina yi ne?

Na faɗa ina tsare sa da idanuwana sai ya kasa mgana har ya na wani sauke ajiyar zuciya.

"Ina yi maka mgana in mun haɗu. Kai ma in ka yi min magana ai ina amsawa."

"Kina amsawa amma ba haka kika saba  ba Sadiya. Kina jin haushina tun faɗan da muka yi kwanaki ni kuma ya wuce awajena fa"

"Nima ya wuce ai."

"Bai wuce ba Sadiya."

Sai na kalle shi amma ban yi magana ba.

"Bai wuce ba. In da a ce ya wuce me ya sa kika raba mana ɗakin kwana? Ni na taɓa kaurace miki ne Sadiya? Me ya sa ni daga mgana za ki hau gaba da ni,kin daina kwana a kusa da ni, kin daina zama ki yi hira da ni kafin ma na dawo gidan kin shige ɗaki gabaɗaya kin watsar da ni tsakani ga Allah wannan shi ne kike cewa ya wuce?

Sai na yi shuru ban yi magana amma kaina na ƙasa ba na so ma na yi mgana domin na yi alƙwarin daina yin sa'in sa da Yallabai kar wata rana na zage shi lamarin ya lalace."

"Sadiya."

Kallon shi na yi sai kawai ya sake matso ni ya na neman kama hannuna da sauri na matsa jikin gado
Sai ya kaɗa kai kafin ya ce" You see ga shi nan ma kina guduna ne."
Mirmishi na yi masa kafin na ce" Ba gudunka na ke yi ba. Ka ce ni ba ni da alheri ne sai na daina raɓar ka saboda kar na shafa maka rashin alherina."

Baki ya buɗe kafin ya ce" Ki ji tsoron Allah Sadiya ni na ce haka?

Ido cikin ido na kalle shi kafin na ce" E haka ka ce. Ka ce ma Gimbiya ta gama maka komai ni kuma shi yasa ni da ban taɓa maka komai ba na ja jikina daga gareka amma ni ba na gaba dakai."

Na faɗa kai tsaye ina kallon shi sai ya dafe kan shi kafin ya ce"kash! Ni fa ba haka na ke nufi ba. Cewa na yi zuciyarki na saka miki abin da ba alheri ba amma ni wallahi tallahi ban ce ba ki da alheri ba."

"Allah ko?

Na faɗa ina kallon shi domin na ga kamar zai raina min wayau ne.

"Da gaske ni ban ce miki ba ki da alheri. Kuma na da ce Daughter ta ga ma min komai na ce ne ke ba ki yi min? Abin da kika yi ita ai ba ta isa ta yi min shi ba Sadiya? Ke ce Yusuf fa in ba bu ke ai ba zan iya amsa sunana ba."

"Ko'"

Na sake faɗa ina kallon shi a raina ina auna cewa da gaske ne namiji bashi da kunya.
Sai kawai ya matso ni ya matse ni ya shisshigemin ya na mai riƙo duka hannuwana ya na marairaicewa.

"Kin riƙe ni a ranki ne! To don Allah ki yi hakuri kin ji ko? Ba haka na ke nufi ba."

"Na haƙura"

Na bashi amsa saboda ina so ya ƙyaleni amma bai ƙyaleni ba sai da ya rumgumeni ya na faɗin" Ki daina gaba da ni."
"To."
"Ki kuma daina ƙaurace min"
"To "
"Ki daina watsar da sha'anina ba na jin daɗi."
"To"
"Ina sonki. Ƙaunarki na ke yi Sadiya ta."
"To."

Sai ya ɗago ya na kallona kafin ya ce" Shima To ɗin ne?
Sai kawai na kauda kaina ina mirmishi, shige min ya dinga yi ya na lallaɓa ni ban taɓa tunanin zan sake ba ma Yallaɓai wata dama ba sai ga shi na ba shi damar na yarda da maganar nan ta miji da mata sai Allah.
Ni kaina na yi kewarsa sosai, haka na ke ƙamƙame shi ina maida numfashi sama sama, shi ma haka a kunnena ya ke min raɗa.

"Na yi kewar gonar nan mai cike da ni'ima."

A ƙasan maƙoshina na ce" Uhm"

"Wajen ya ƙara sulɓi Madam me ye sirrin?

Banza na yi masa sai kawai ya sumbaci baƙina kafin ya rumgumeni.

"Da gaske na ke yi ina kaunarki Sadiya ta."

A duhun ɗakin na ke kallon shi, ya na mai lumshe idanuwana barci na son ɗaukan shi bayan mun gama tsarkake jikin mu.
Na ƙura ma fuskar shi ido ina kallon shi, na yarda yana sona amma kuma ya raba son gida biyu ɗayan ya ba ma Gimbiya. Itama haka ya ke yi mata in sun kaɗai ce? Innalilahi na fara kira a cikin raina domin tuni kirjina ya fara zafi kishi ya taso min da sauri na juya masa baya ƙwallah ne suka taho mini amma na kasa maida su sai da suka samu nasaran zubowa na yi saurin sharewa ji na yi ya motsa ya ƙara kamkameni ya na sauke min numfashinsa a saman wuyana ajiyar zuciya na sauke ina jin kamar numfashina na min gudun tsere sai da na buɗe bakina ina shaƙan numfashin ta baki domin sai na ji kamar iskar ɗakin ta yi min ƙaranci.



*Janafty*
*TKG*

FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nigeria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622

14.

Tun a daran alhamis Yallaɓai ya kirani a waya saboda ranar ba a gidana ya ke ba. Ce min ya yi mu shirya ni da yara za su zo shi da Gimbiya su ɗauke mu domin zuwa sallar idi na ce masa to, domin ni yanzu tsakanina da Yallaɓai to ne domin na yi ma kaina alƙwarin kome zai yi ko ya ce ba zan ƙara yi masa mgana ba, ma'ana sai dai na gani na yi kamar ban gani ba na kuma ji na yi kamar ban ji ba domin a zauna lafiya.

  Lokaci bayan lokaci ina tuna kalaman da ya jefe ni da su na cewa ba ni da alheri sannan Gimbiya ta yi masa komai ni kuma ban yi masa ba. Wani lokacin kallon shi kawai na ke yi domin ni a wajena ya gams shayar da ni dukkan mamakinsa shi ya sa yanzu komai zai yi ko a nan gaba ba na tunanin zai ɗaga min hankali ko kuma ya ba ni mamaki tunda a zaman auren mu na shekaru sha biyar ya iya buɗe baki ya ce ba ni da alheri sai wacce ya aura ko wata uku ba ta rufe a gidan shi ba ai ban tunanin kuma akwai sauran wani abu da Yallaɓai zai yi ko ya faɗa da zai sake ba ni mamaki.

  Kamar yadda ya umarce mu, Ranar jumma'a da ta kama ranar idin babbar salla mun shirya har da Marwa ma da za ta yi salla tare da mu. Ko kafin su ƙariso mun jima da shiryawa domin tun huɗun asuba muka tashi ba mu koma barci ba har yaran ma gabaɗaya. Ba su shigo ba daga ƙofar gida ya tsaya da mota ya ce mu fito mu wuce mun makara lokacin wajen bakwai da arba'in na safe ne can masallacin cikin gari za mu je su su kan ta da salla takwas da rabi ne gwara ka je da wuri ka samu wajen parking da kuma wajen zama.

Gabaɗaya muka fito ni na tsaya na rufe gidan su kuma su ka fara ƙarisawa. Na ƙariso lokacin Gimbiya a bakin motar ta ganta ta na rumgume yaran har ƙoƙarin ɗaga Baby ta ke yi.

"Kar ki ba kanki wahala ba iya ɗaga ta za ki yi ba."

Na faɗa dai dai ina ƙarisowa da ɗan sigan zolaya haka. Sai muka kalli juna sannan ta yi min mirmishi na maida mata. Ta na sanye da hijabi mai ruwan ƙasa kalan doguwar rigar da ke jikinta takalmin kafanta mai saukaƙƙen tudu ne sannan ta saka safa irin na su dai na ƴan gayu. Ni kuma daman atamfata na saka wata mai purple sai na yi amfani da kalan Hijabin, kafata nima flat shoe ne da safa su Jidda ma Atamfa na saka musu da hijaban da na siya musu har ƙasa haka ma Marwa. Gogan na kalla ya na cikin mota zaune sai dai ya na amsa waya ne shi ya sa bai fito ba.

Hannu ta miƙa mini muka yi musabaha.

"Barkanmu da salla Madam"

"Barka da salla."

Nima na maida mata martani Marwa ta gaiaheta sai ta amsa ta na yi mata kallon rashin sani.

"Marwa. Ɗiyar yayata ce."

Na faɗa ina dafa kafaɗan Marwa ɗin. Sai ta yi mirmishi kafin ta ce" Barkan mu da salla Marwa."
Marwa ta amsa ta na mai ƙara gaisheta, daga cikin motan Yallaɓai ya ce ko a nan ne za mu yi sallar idi? Muna jin haka sai na buɗe gidan baya na ce Marwa su fara shiga ita da yara ni ban ma kawo ma kaina hawa gaban mota ba, saboda na ga Amarya a bakin wajen ta kame shi ya sa na shige baya abuna wata zuciya na ƙara tunatar da ni aka ma raba mijin gabaɗaya ballanta kuma gaban mota.

  "Ina kwana Madam ɗina."

Ya faɗa bayan yaran sun kuma gaishe shi ya juyo ya na musabaha da su. Nima hannun ya miƙa min sai na karɓa ina faɗin.

"Barka da salla Yallaɓai."

Sai ya jinjina min kai kafin ya ce" Barkan mu da salla Amintattaciya ta."
Kallon shi na yi, amma ban yi mgana ba hannuna na zare cikin na shi kawai ina mai cema Baby ta koma ta zauna ko na dake ta saboda sai faman zillo ta ke yi ma mutane kamar za ta koma can gaban motan.

Marwa ma ta gaishe shi ya amsa ya na faɗin" Marwatu barkanmu da salla."
Ta amsa ta na ɗan mirmishi, sai ya juya ya na mai kallon Gimbiya sannan ya ƙara juyowa ya na sake kallona ni kuma tuni na maida hankalina wajen jan kabbarorin da Annabi(SWA). Ya koyar da mu a lokacin tafiya sallar idi.
Allahu akbar. Allahu akbar. Allahu akbar. Walillahil hamdu. Har su Jidda ma na ce su yi ta maimaitawa.

Har mun ɗan fara tafiya muna ta haɗuwa da mutane kowa ya ci sabbin kaya yau ta ke salla Yallaɓai na juya ina kallon keyarsa da yadda ya kafa hula ya na tashin kamshi wata wagambari ya saka mai ruwan ƙasa duk da bai sauko daga motar ba amma ya yi kyau matuƙa shi daman Yallaɓai mai kyau ne kuma ɗan gayu ne komai ya saka a jikin shi sai ya yi masa kyau ina daga gefe ne ta bayan kujeran Gimbiya ba na kallonta amma shi ina ganin shi sai ya ɗan kalleta yana mirmishi ƙila itama murmushin ta ke yi masa sai kuma in ya ɗago mun haɗa ido ta madubi sai ya wani kashe min ido, ai da na ga ya na nemen rena mini wayau tuni na juyar da kaina ina gani  gilmar motoci da waɗanda ke kasa ina jin farinciki a ƙasan raina na ganin hada hadan mutane, a cikin raina ina ta hasaso yanzu haka a gida su Alhajinmu suma sun kama hanyar zuwa sallar idi shi da su Ya Hamza tun jiya da muka yi waya da Gwaggo ta ce sun iso Ya Auwal ma daddaren ya ce min sun sauka shi da yara da Laila. Muna da ɗakuna a gidanmu ga na Mama ga na Hajiya duk kuma a gyare suke, can ƙofar shigowa kuma ɗaku nan su Ya Hamza tun na samartakansu ya na nan in sun zo gida nan sukan sauka har su gama kwanakin su koma sun gyara shi sun saka komai na morewa rayuwa a ciki.

Har muka isa masallaci ban ƙara bi ta kan Yallaɓai da matar shi ba. Mun sauka a bakin hanya ya ce zai nemi wajen parking mu kuma mu karisa bangaren mata in an idar da salla zai kira mu. Daga nan muka ɗau darduman mu guda biyu itama Gimbiya ta zo da na ta, Marwa ta riƙe hannun Jidda ita kuma Gimbiya ta riƙe hannun Baby suna gaba ni kuma ina baya ina ta kabbarori. Mun samu wajen zama muka shimfiɗa sallaya muka zauna ba daɗewa aka ta da salla, bayan mun idar da salla aka fara hada hadan jama'a wasu na kafa sannan ga zirga zirgan ababen hawa waje ya cika makil ko'ina ga waiga jama'a ne kamar ba a mutuwa saboda cikowa.

Mun samu mun fita can bakin titi da kafarmu ni wayata ma a gida na barta Gimbiya ce ta zo da ƙaramar jaka shi ya sa ta ɗauko wayarta ta nan Yallaɓai ya kira mu, ya na ta faɗan wai ya na ta kiran wayata ban ɗauka ba na ce ta faɗa masa ta na gida na baro ta. Mun haɗu da shi a can gaba kaɗan sannan muka shiga motar wannan karon ma Gimbiya a gaba ta kame ni kuma na shiga bayan kamar yadda na zo.

"Ke haka ake yi sai ki bar waya a gida?

Sai na kalle shi kafin na ce" Za ta zame min kaya ne shi ya sa ban ɗauko ta ba."

Sai ya yi shuru bai yi mgana ba, sai kuma can ya kalli Gimbiyar kafin ya ce" Daugther ki koma baya ki zauna."
Sai ta kalle shi kafin ta yi magana ya juyo ta baya ya na faɗin" Ke kuma Sadiya ki fito ki dawo gaba."

Sai na ga ta ɗan yi wani tsam kafin ta ce Ok. Tana ƙokarin buɗe kofar motar ne na yi saurin cewa" Ki yi zaman ki ni fa nan ɗin ma ya isa. Ba duk mota ba ce da bayan da gaban ai duk ɗaya ne"
Sai na ga kuma ta dakata da fitan kenan ta na son zaman gaban motan sai kawai na ga ya wani kalleni ya na wani haɗe rai.

"Na ce ki fito ki dawo nan ki zauna ko?

"Da dai ka bar ni anan ɗin."

"Umarni ba jin ta baki ba. Ki fito ki dawo gaba ita kuma ta koma baya haka na ce."

Ya faɗa har ya na wani tattarre naman goshinsa waje ɗaya na fitina ina jin haka sai na buɗe murfin mota na fito, itama ta fito  sai mu ka sauya wajen zama sai da muka zazzauna sannan ya ta da motar muna tafe a hankali saboda gowslow shi ya sa Yallaɓai tafe ya ke gaisawa da mutane har dai na ga ji na kalle shi ina faɗin.

"Sannu. Wai kai kowa ka sani ne?

Ya na dariya kafin ya ce" Ba kowa ba. Amma saboda aikina ina harka da mutane sosai."
Ai ko na ga harka da mutane kafin mu fita wannan cunkosun Allah kaɗai ya san yawan jama'an da ya haɗu da su sai dai ki ji ana faɗin Injinjiya kai ne anan? Mutane ba su cika kiran shi da Yusuf ba sai Injiniya a gida kuma daman Tafida ne in ka ji Yusuf sai dai irin tsoffin abokan shi tun na makaranta.

Har gida suka dawo damu kamar yadda suka ɗauke mu. Gimbiya dai fuskar nan ba Annuri ina ga ranta ya ɓaci ne da ya ce ta fito ta ba ni waje ni ko ban tsaya ma bi ta kanta ba a raina na ce kina da aiki. Mun rabu da Yallaɓai da cewa in ya maida Gimbiya gida  Gwammaja zai je ya yanka ragunan sallar nan sai anjuma zai leƙo. Yara ma suna ma Antynsu na su bye bye ba ta amsa ba muna dai tsaye suka juya kuma ta na bayan ba ta dawo gaban ba duk da na ga kamar ya juya ya na mata mgana kuma ina da tabbacin ce mata ya yi ta dawo gidan gaba ina ga za ta ce daga baya kenan, ni dai na buɗe gida muka shige a ƙasan raina ina ganin ƙokarinta Allah na tuba mene ne a zama gaban mota tare da miji.

28 / 48