Author : Janafty Category : Complete Novels
dawo hayyacina sai na ga Marwa ce ke kirana. Da sauri na ɗauka kamar a cikin wayar za a faɗa min abin da zai kwantar min da hankali.
"Marwa."
Na faɗa cikin sanyin murya.
"Umma ina kwana."
Nan muka gaisa na tambayi Yaya Aina da babanta ta ce duk suna lafiya.
"Umma kin ji ni shuru ban dawo ba ko?
Kafin na amsa mata ta cigaba da faɗin" Yau ne na je asibitin da zan yi pratical ne zaa kai report. Zan zo anjuma in sha Allahu."
Sai na amsa mata da toh kafin na ce" Allah ya sa ba kaya kika zo ɗauka ba?
Tana dariya ta ce" Sai dai na zo Umma."
Na ce Allah ya kawo ta lafiya sannan muka yi sallama. A cikin raina na ke jin da gaske yanzu zan so ɗaukan Marwa ta dawo hannuna ina bukatar wani a gefe tunda yanzu Yallaɓai ya zama namu ba nawa ba.
Ban taɓa tunanin zan samu jarumtar iya faɗa ma wani Yallaɓai ya ƙara aure ba. Amma sai da na yi wani tunani sai na ga gwara ni a fara ji a bakina ina da tabbacin in na bari Ma'u ta yaɗa mganar nan kamar gazawata ce shi ya sa da hanzari na shiga group ɗin gidanmu na yi mgana.
"Assalamu Alaikum fatan mun tashi lafiya? Ya iyalai ya yarorin mu? Daman zan sanar da ku jiya an ɗaura ma Yallaɓai aure da yar'uwan sa Gimbiya(Saudatu) a garin Rano."
Na yi rubutu ya fi sau biyar ina gogewa kafin na yi dauriyan turawa ina gama turawa ya yi tickig ya ta fi na yi saurin kashe data na koma na jingina da jikin kujera ina maida numfashi.
Mintina goma tsakani kawai na ji wayata da ke hannuna ta na vibration ina dubawa sai na ga Yaya Balki amma har ta katse ban ɗauka ba ta na katsewa kiran Rahila na shigo min itama nata na gamawa sai na ga na Amina.
Mirmishi kawai na yi na san suna so su ce min ne da gaske ne Sadiya?
Da gaske ne Sadiya? Nima tambayar da na ke yi ma kaina kenan shin wai da gaske ne Yallaɓai ya ƙara aure Sadiya? Amma har yanzu na kasa samun zuciyar da za ta ƙaryata wannan auran na Yallaɓai.
Wai daman haka kishi ya ke! In ko haka ya ke to tabbas Kishi ya na da ɗaci sannan na yi imani ga Allah ko ɗacin rashin wani makusancinka bai kai kishi ɗaci da maƙaƙi ba
Na daɗe ina kwatanta yanayin zafin shi. A yadda na ke kwatatanshi ban taɓa hasso shi a yadda na ji sa ba. Tabbas kishi kummallon mata na ƙara jinjina ma duk wata mace da a ka yi mata kishiya saboda ƙishi akwai zafi akwai ƙuna akwai ɗaci da radaɗi. Raɗaɗin da in ba akan ka ya faru ba labari ba zai iya gamsar da kai ba.
*Janafty*
*04 Wed. December 2025*
*TKD*
02.
Haka suka yi ta kirana amma na kasa iya jarumtar ɗaukar wayarsu. Sai na ke jin kamar da na amsa wayarsu suka fara jefemin tambaya da cewa shin da gaske ne Yallaɓai ne ya ƙara aure ? Na tabbata rauni ne zai zo ya yi min rumfa ɗan jarumta da na samu ya ƙwace min na saka kuka shi ya sa na kasa iya ɗaga wayar ko ɗaya daga cikin su.
Yaya Balki sau biyu ta kirani Rahila ce wajen sau huɗu da ta ga ban ɗauka ba sai ta haƙura amma ban da Amina da saboda na cin kiranta sai da na ɗaga wayarta.
Tun kafin na yi mgana na ji karaɗinta a cikin kunnina sai da na runtse ido.
"Ya Sadiya wai wani Yallaɓan kike nufi ya ƙara aure?
Haka ta faɗa cikin sauri kamar ta na jira. Daman na san za a rina wai an saci zanin makauciya. Mirmishin yaƙe na yi kamar ta na gabana Amina ce ƴar'uwan da muka haɗa uwa ɗaya ita ce zan je gidanta na kwanta mata ina kuka ta lallasheni amma sai dai kash ta yi min nisa.
"Wai dai Yallaɓan na ki babansu Jidda kike nufin jiya aka ɗaura ma aure?
Haka ta sake faɗa jin na yi shuru. Cikin sanyin murya na ce" Shi fa Amina. Ai yanzu Yallaɓai ya zama namu mu biyu, ya tashi daga Yallaɓai na ni kaɗai"
Na ƙarishe faɗa kamar zan fashe da kuka domin ina mganar ina jin wannan abun da ya tokaremin a kirjina ya na motsawa ina jin wani irin zafi a ƙasan zuciyata zafin da a kan jin in an yi maka wani gagarumin rashi mai zafi ko ka rasa wani abu naka mai muhimmaci. To irin wannan zafin da raɗaɗin na ke ji ya na taso min daga ƙasan zuciyata.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un na shiga uku ni Amina Yallaɓai dai ya ƙara aure Ya Sadiya"
"E."
Na bata amsa a takaice jin ta ƙara jero wani salatin ya sa na yi saurin cewa" Ke miye na wani salati! Shirka ne? Umarnin Allah ne fa."
Daga can bangaren Amina ta sauke numfashi har ina jin hucin sa daga cikin wayar cikin ƙaramin sauti da wani abu a muryanta ta ce" Uhm ni mamaki ne ya ishe ni. Wallahi na kasa yarda"
"Uhmm."
Na samu kaina da cewa kawai. Nima ɗin in zan ji kamar karya ne sai kuma na ji wani shashi na zuciyata na gasgata lamarin.
"To wai ya aka yi ne aure kwatsam ba sanarwa? Sai kawai mu ji an riga an ɗaura aure Ya Sadiya.?
Takaici ya ƙara kamani sai kawai na gyaɗa kai kamar tana ganina kafin na ce" E nima kwatsam na ji Amina."
"Kai jama'a har yanzu na kasa yarda Ya Sadiya."
"Ki yarda Amina. Da gaske ne Yallaɓai kam ya ƙara aure."
Sai ta yi shuru nima sai na yi shuru kafin can ta ce" Allah ya kyauta. To wacece ya aura ɗin?
"Ƴar'uwansa ne. Ɗiyar marigayi Tafidan Rano ne. Mijinta ya rasu wattanin baya."
Amina ta jinjina kafin ta yi fatan alheri daga karshe ta ce" Ki yi hakuri ya Sadiya ki kauda kai. Na tabbata duk wacce Yallaɓai zai auro wallahi a bayan ki ne."
Uhm kawai na ce ban yi mgana ba. To wani baya kuma, ai an gama mgana tunda an raba mijin gabaɗaya shike nan kuma.
Muna cikin waya Rahila na ta ƙara kirana ina katse na Amina na ɗauki wayarta itama tambayar ta farko shi ne wai wani Yallaɓan ne ya ƙara aure?
Kai tsaye na ce mata" Wani Yallaɓan kika sani? Abban su Jidda ba."
"Kai Sadiya fa."
Sai kawai na yi mata dariya kafin na ce" Wai me ya sa kuke tamtama?wallahi tallahi da gaske na ke yi."
Rahila ta jim kafin ta ce" Danƙari! Aure kuma bagatatan Sadiya? Yar wacece a Rano ya aura?
Itama bayanin Gimbiya na yi mata da sauri ta ce" Gimbiya? Haba na gane ta ita ce ya aura ɗin? Sai na ɗaga mata kai kamar tana ganina fatan alheri ta yi kafin ta ce" Sadiya an shiga wata ƙwaryan sai kin ninka haƙurin ki. Duk da ta bangaren miji ba ni da haufi a kan ki in sha Allahu ba macen da za ta kama kafarki. Allah ya zaunar da ku lafiya."
"Amin"
Na amsa mata da Amin sai ta ce" Yaushe ne tariyan! Ko har an taren ne?
Kai na fara girgizawa kafin na ce" A'a.."
"To sai yaushe?
"Ban sani ba Rahila."
Haka na faɗa kai tsaye domin da gaske ɗin ban sani ba fahimtar yanayin da na ke ciki yasa ta yi min sallama kawai amma ni a muryanta sai na ji kamar tausayina ta ke yi. Tabbas ni abar tausayi ce domin ya kamata a riƙa sara ma duk wata macen da aka yo ma kishiya saboda zafin abin ba wanda zai iya kwatanta yanayin shi sai ya faru a kanka. Sannan duk macen da ta shanye ya ci a kira ta jaruma ko sarauniya kuma a yabe ta a jinjinta domin ta yi matukar namijin ƙoƙarin da ba kowa ne zai iya yi ba.
Muna cikin waya da Yaya Balki ne Yallaɓai ya fito falon. Ganin shi ya sa sai na ce zan kirata zuwa anjuma a lokacin n nasiha kawai ta ke yi min tana nuna min na ƙara hakuri domin zan ci riban hakuri tunda ai ita an yi mata tana ta bani misali da kanta da ba ta da haƙki ga shi matar ma ta fita sun rabu da mijin kuma da ƴaƴa biyu a tsakaninsu.
Kamar Yallabai ya fahimci wayar da na ke yi saboda sai da ya kalleni kafin ya ce" Wannan doguwar wayar fa?
Ina mikewa na ce" Ya Balki ce muna wata mgana ne."
"Ok. Na ga Tiolet ba ruwan zafi. Kin saka a heater ne.?
Ban yi masa mgana ba na dai gyaɗa masa kai na yi wuce gaba ya biyo bayana a cikin tiolet ɗin daman na ke saka heater ɗin ni na je na jona masa sai ya ce na haɗa masa abin karya in ya yi wanka zai fita akwai mutanen da zai gani a office ne sai na amsa masa.
Daga Tiolet na ja birki a kitchen ƙwai kawai na sake soya masa. Na kwasa na kai dining daman akwai ruwan tea a fulas sannan ga kayan tea ɗin da buredi. A niyyata na yi tafiyata falon yara na zauna amma sai na danne zuciyata na zauna a saman kujeran dining ina jiransa na tsawon lokaci ina zaune ne amma ina tunanin Mama. A raina na ce da uwata na raye yau da wajenta zan yini in sha kukana ta lallashe ni sai dai ina ba ta a raye.
"Allah ya jadadda rahama a kabarin Mama da Hajiya."
Na faɗa a fili ina jin ƙwalla na taruwa a ƙwarmin idanuwana sai dai na yi ƙoƙarin maida ƙwallar da ta taho min
Ina nan zaune ƙamshin turaren Yallaɓai ya fara min maraba a ƙofifin hancina sai ga shi ya bayyana a cikin falon cikin shigar Shadda mai ruwan toka sabuwa ce sau ɗaya Yallaɓai ya taɓa sakata da wancan sallar azumin ya ɗinka ta ɗinki ba tazarce ba ne half jamba ce irin na matasan samarin zamani. A lokacin Yallaɓai masifa ya yi ta ma telan shi wai shi tazarce ya ce bai ce ya yi masa ƙaramar riga ba. Ni na yi ta tausan shi na ce ya yi haƙuri tunda an riga an ɗinka. Daƙyar ya haƙura amma bai ƙara saka kayan ba. Kuma kayan suna yi masa kyau matuƙa amma saboda ba haka ya so ɗinkin ba sai kayan su ka fita daga ranshi. Na sha ce masa ya saka kayan suna yi masa kyau sai ya ce min shi ba zai saka ba saboda ɗinkin su ɗan kama masa jiki shi dai kawai basu yi masa kyau ba. Da na gaji da yi masa magiyan ya saka nima sai na haƙura na ƙyaleshi har na manta da kayan a tunanina ma ya kyautar ne ashe suna nan sai yau ya ɗauko su ya saka saboda ya na ANGO.'
"Ango.".
Haka na maimaita a cikin raina ina jin kamar ƙirjina na ɗagowa saboda yanayin da na ke ciki.
Kallonsa na ke yi da dukkan zuciyata. Haƙika duk macen da ta samun daman auren Yallaɓai ta gama dacewa domin shi ɗin mai kyau ne kuma ɗan gayu ne ɗan ƙwalisa da ya haɗa komai na matakin rayuwa.
Ya yi min wani irin kyau a idona. Sai wata zuciyar ke faɗa min wannan adon duk ba na ki ba ne Sadiya tun yaushe kike son ya saka kayan yaƙi? Sai yau tun da zai je ya ga Gimbiya.
Tuni na ji taɓon da ke zuciyata ya taso. na ma fara ganin hazo hazo ne saboda tuƙuƙin da ke muƙurƙusan zuciyata.
Har gabana ya tako ya na wani tashin kamshi. Kafarsa na kallah sai na ga takalminsa da ya ke ji da shi a cikin jerin takalmansa ya saka sai na ɗago ina kallon hulan kansa itama mai tsadan ciki ne ya ɗauko ya saka. Lalle Yallaɓai kallonsa kawai na ke yi na ma kasa mgana ina ƙoƙarin danne abin da ke taso min daga ƙasan raina.
"Kallon fa?
Ya faɗa bayan ya ɗan buga min agogon hannun shi a saman kaina kaɗan. Sai na ƙara kallon shi a baya in Yallaɓai ya yi kwalliya ya yi kyau in zai fita har wani alfahari na ke yi amma yau kam sai na ga ina ganin duhun shi domin zuciyata na raya min ne wajen Gimbiya zai je kuma ina da tabbacin domin ita ya yi wannan gayun.
"Ko na yi miki kyau ne Madam"
Ya faɗa ya na mai miko min hannun shi lokaci ɗaya da agogon fatan da ke hannun shi.
Na fahimci nufinshi kamar na ce ya je da shi sai Amaryansa Gimbiya ta ɗora masa sai kuma na fasa na saka hannu na karɓa ina saka masa lokaci ɗaya ina faɗin" Yau kuma kayan da ba a so ne aka saka?
Na faɗa bayan na gama ɗaura masa agogon na mike ina ja masa kujeran zama.
"Wallahi yau kawai na gansu ƙasan kaya. Na ɗauko su ne ban ma san za su shige ni ba ina ko sakawa sai na ga sun yi min kawai sai na bar su."
Ya faɗa ya na mai zama a kan kujeran da na ja masa.
"Uhmm."
Na faɗa ina tura masa farantin ƙwai a gaban shi. Ruwan tea ɗin ma na zuba masa a wani Mug na tura masa gabanshi sannan na koma na zauna.
"Kin siya wankan ne?
Uhm!
Ni fa kwata kwata kalamansa sun daina wani burgeni. Shi ya sa na yi masa ba kan, ina kallonsa a ɗage bai sani ba ya fara karyawa ya na min hira sama sama ina amsa shi, sai da ya ce min ƙila gobe ya shiga kaduna.
Sai kawai na gyaɗa kai kafin na ce" Allah ya kaimu."
Ya amsa da Amin na ga alaman yau ya ɗan saki jikinsa ba kamar jiya ba. Ya na cikin karyawa na ji buga get na san Saude ne sai na mike na ce masa bari na je na buɗe ina jin Saude ce illau ko ita ce tare muka dawo falon ta rankwafa ta na gaishe da Yallaɓai ya amsa mata har ya na tambayan mamanta ta ce duk suna nan lafiya.
"Sai yaushe za ku koma makaranta ne?
Na faɗa ina komawa in da na tashi na zauna.
"Ranar monday."
Sai na gyaɗa kai ban yi magana ba ita kuma sai ta shige ciki ta bar ni da Yallaɓai ya na karyawa har sai da ya gama ana ta ma kiransa a waya ya ce min Musbahu ne, ni ya tura na koma bedroom na ɗauko masa key ɗin mota har ga Allah na so na duje ne na ki masa rakiya amma ya manne min dole na yi masa rakiya kamar yadda na saba amma na kasa iya ɗaga masa hannu kamar yadda na saba sai na ke ganin kamar in na ɗaga masa hannu na cucu kaina wata fa zai je gani? Watan ma wacce ya raba min kanshi da ita shi dai ya ɗaga min hannu na yi masa ya ƙe ya na fita da motar na shige ciki na rufo kofar, Ina jin sa ya rufe get ɗin sannan ya koma motarsa ya fice.
Ina komawa cikin gida na ga Saude a kitchen ta fara haɗa wanke wanke kallonta na yi kafin na ce" Kin karya ne? Sai ta gyaɗa min kai ni kuma kawai sai na bi kofar da za ta maidani cikin bedroom ɗina wayata a hannuna ina faɗin" In dai kina jin yunwa akwai ruwan zafi ki sha tea kin ji ko?
Sai ta gyaɗa min kai ni kuma na wuce ɗaki na koma kawai na kwanta waya a hannuna na kasa buɗe data saboda ba na son na ga wani abu da zai ɓata min rai shi yasa na ƙi taɓa wayar ma.
Ina nan kwance a kan gado ina ta faman juye juye daga kudu zuwa arewa. Gabaɗaya zuciyata ba daɗi har hasaso Yallaɓai na ke yi ya na can shi da Gimbiya suna hira suna dariya. Kai kishi bala'i ne na kasa sukuni kamar zan haukace fa, in na runtse ido Yallabai na ke gani da Gimbiya sheɗan su kawai ya ke nuna min gabaɗaya na kasa sukuni kamar zan mutu haka na ji saboda zafin da zuciyata ke yi, ina cikin wannan halin Marwa ta zo zuwanta ne ya tsamo ni daga haukacewa na fara sumbatu saboda kishi.
Marwa ta daɗe ita ta yi mini girki sai mangariba ta tafi Saude daman tun wajen azahar bayan ta gama aikinta ta tafi. Itama na ɗibar mata cake da yawa na ce ta je gida su ci da ƙannenta.
Na yi na yi Marwa ta kwana ta ce min ba ta tambayi Babanta ba na ce zan kira waya ta ce a'a za ta dawo gobe in ta zo ɗaukan kayanta.
Ina hararanta na ce" Marwa tawaye za ki yi min?
Ta na dariya ta ce" Umma can gida ya fi kusa da asibitin da zan yi pratical ne amma zan dinga zuwa Allah kuwa."
"Ki dawo nan mana sai Yallaɓai ya rika kai ki in zai fita office."
Sai da na faɗa sai kuma na kwaɓi kaina daga jiya Yallabai ya tashi daga wannan wanda na sani yanzu namu ne ni da wata ba ni da wannan ikon a kan shi kamar baya. Hakanan na ba ta 1k muka yi sallama na ce ta gaida Ya Aina. Sannan na ɗibar mata na ta cake ɗin har da kazan jiya na ce na Anniversy ne. Ni daman kazan ko a bakina saboda gani na ke yi kamar kazar angwancin Yallaɓai ne saboda ya ƙure ni. Sauran na bar ma su Jidda amma ni na haramta ma kaina cin kazan nan.
Bayan tafiyarta na idar da sallar mangariba Ya Ainan ma ta kira wayata ta na faɗa min Ya Balki ta gaya mata wani labari wai Babansu jidda ya kara aure sai na tabbatar mata ita kanta ta jinjina har sai da ta ce min" Sadiya kishi akwai zafi sai kin daure."
A raina na ce" Tabbas kishi akwai ɗaci ba ma zafi ba."
"Yaushe ne tarewar? A ina za ta zauna ita matar Balki ta ce min wai yar nan Rano ce ko?
Sai na amsa mata kafin na ce" Ban san in da za ta zauna ba."
"Ko nan gidan zai haɗe ku?
A firgice na ce" Wani gidan Ya Aina?
Ganin yadda na zabura ne ya sa ta yi dariya kafin ta ce" Nam ma Sadiya."
Yaƙe