Author : Aisha Jb Category : Complete Novels
jijjigawa yana fad'in ta nitsu ba shiri Nisha ta nitsu gamida saurin kifa goshinta ga saman kirjinsa kirjinta sai faman bugu yake sauri sauri Ajmal hanu ya aza bisa saman bayan Nisha cikin murya mai kama da rada yana fadin
"Listen to me "
Sai da Ajmal ya tabbatar Nisha ta nitsu sannan ya cigaba da fadi'n
"By now kin kasance amana a gareni so bazanso na bata miki ko na saki cikin wani damuwan kasan cewarmu nan baya nufin na kyaleki ki kadaice ke kadai guri guda ba tare da kasan cewata gurin ba, because yanzu karkashin kulawata kike dole na kula da duk wani situation nake "
Nisha dai shiru tayi tana sauraren Ajmal yayinda yake maganar mai kamada wa'azi ko nasiha, tare da mamakin yanda yake maganan cikin tattausan lafazi wanda yasa zuciyar Nisha yin sanyi da karaya yau Ajmal ne ke rungume da ita yana shafa bayanta cikin kulawa gamida sanyin murya to ko mai ya kawo sauyin cikin wannan lokacin?,.shirun Nisha bata ko motsa ba ballai ta tamka batunsa yasa Ajmal dagota yana fadi'n
"Ko ba kijin mai nake cewa "
Ajmal ya tambaya yana dan jijjigata , cikin sarkewar murya tana g'yada kai Nisha tace
"Ina..ji "
Sai jinjina kai Ajmal yayi gamida kokarin gyarawa Nisha kwance bisa jikinsa gamida janyo musu blanket yarufe su Nisha ko gaba ki d'aya ta takura kunya duk ta gama isarta yau ita ke jikin Ajmal a rungume cikin blanket suna shirin bacci tare abun kamar mafarki, shikuwa Ajmal ko ajikinsa sai lumshe idanu yayi yana fidda sassanyar ajiyar zuciya.
Jin k'aran ringing din phone d'in Ajmal ne yasa gaba ki daya hankulansu ya dawo gurin side din da phone din Ajmal yake , Ajmal da ya lumshe idanu sai budewa yayi ya wurga yan idanunsa saman bedside inda phone d'insa keta haske yana ruri, dayan hanunsa ya kai ya janyo wayar ya kai idanunsa ga screen phone din wanda time d'aya ya had'e rai gamida had'e gira ganin Heelah ke kiransa wacce tun dirowarsu kasar ta addabeshi da kira, kira kan kira yana katsewa ga kuma test massage rututu wanda baima samu halin bi ya karanta ba ballai yasan abunda ke kunshe ga test massages yanzun ma wata yar guntuwar tsiki yaja gamida kashe wayar gaba d'aya ya maida ita ya ajiye gamida lumshe idanu yana rungume da Nisha jikinsa.
A wannan dare duk wani motsin Nisha jikin Ajmal zatayi shi tun tuna jin abundai wani iri haka tana takure hardai ta sake jiki bashi bacci barawo yayi awun gaba da ita bazato ba tsammanin bacci mai nauyi Nisha ta shigayi zamu iya cewa batama san wata duniyar ta lulaba because baccin yau na da banne kuma na musamman ne .
Washe gare karfe 6 Nisha ta shiga motsa yan idanunta tana neman farkawa bude idanun da zatayi saiwani kyakykyawan hasken rana ta ga ya baiyana ya hasko gari yayi haske alamar gare ya waye jiki ba kwari Nisha ta mike zaune saman bed tana ajiye wani dogon hamma gamida mika tana salati kafin ta lumshe idanu jin daddad'an kamshe tureren Ajmal da tun jiya ya hana hancinta hutawa gurin shakar k'amshinsa.
Jin kamshensa ne ya kara mai da ta tunanin ta ta mance yau da oganta suka kasan ce guri guda but koda ta juya ban garan da ya kwanta wayam yake baya nan alamar ya fice sai kamshin turaren jikinsa da ya kasa gushewa kai kace haryanzu yana kwance gurin ,.
Jiki a sanyaye Nisha ta tazamo daga saman bed din ta mike ta nufi bathroom, kasan cewar Nisha ta ga lamar daukewar period d'in nata gaba daya yasa bawani jinkiri ta yi niyya ta shiga tsarkake jikinta daga bisani tayi wanka ta tsaftace jikinta kafin ta fito ta kimtsa jikinta daga nan ta matsa wardrobe ta shiga janyo wata white t shirt mai gajeren hanu da wata straight skirt coffee brown mai taushi da sulbi ta sanya jikinta daga nan ta kuma janyo hijab ta shinfida sallaya ta tada sallah.
Koda ta idar ta da d'ai bisa saman sallayan tana addu'oi gamida lazumi kafin ta mike ta ninke sallayen ta kuma cire hijab din tanemi hula ta sanya bisa saman kanta ta nufi parlour, zuwanta parlourn shiru yake ba kowa sai TV da aka kunna yanataa faman aiki cikin parlourn.
Guri Nisha ta nema ta zauna daga gefe tana mai cigaba da kallon TV but sam hankalin ya baya ga kallon yana can wani wajan tana karanta wasikar jaki tsawon lokaci tana zaune gurin but shiru ka keji ba Ajmal ba alamar shi, ganin haka yasa Nisha mikewa cikin sanyin jiki tanufi bedroom d'in domin dabawa taga ko lapiyar rashin fitowarsa because ta dad'ai zaune parlour but bataji motsin fitowar shi ba .
Koda ta shigo cikin bedroom din nasa still dai baya ciki sai ma shaidar da yabata nacewa baya nan ya fice saka makon jallabiyar sa da ta hango saman bed wanda ya cire, dan haka sai juyawa tayi ta koma parlour ta zauna tare da tunanin ina Ajmal ya je bai tasheta ballai ya sanar da ita ba gashi tsawon lokaci babu shi babu alamar shi, jikin knocking daga bakin door yasa ta dan mike a hankali ta isa ga door din ta murd'a handle din door din ta wangale door din Tana zazzare idanu.
Wasu kyawawan matasan yan mata ne kallo daya zaka musu kasan ma aikatan cikin hotel din ne suna sanye cikin uniform din kowacce hannayenta dauke da kyawawan bedsheet da alamun sunzo gyara musu muhallinsu ne dan haka ba shiri Nisha ta basu hanya suka shigo sai faman jijina mata kai suke alamar ban girma Nisha kuwa sai daga musu hannu tayi tana because daga ita harsu bamai jin yaren kowa daga nan Nisha sai maida door din tayi ta rufe ta koma inda take ta zauna.
_______Nisha tana daga zauna ma aikatan yan matan nan suka g'yara komai suka wanke suka goge suka kuma share komai yafito kyal kyal duk da dama can ba abunda ya baci koyayi dotti but komai ka kidane ko bai baciba za akuma gyarawa ko ajanza masa tsari, saida suka kimtsa komai kafin suka sa kai suka fice, ba jimawa da fitarsu Nisha na daga zaune ta sake jin karan knocking cikin ga jiyawa ta kuma mikewa ta isa ga door din ta bude .
Har'ila yaude wani ma aikacin nasune tafe da kyakykyawan tray d'in breakfast bisa hanunsa cikin girmamawa shima cikin dukar dakai irin na girmamawa ya mika mata tray din abincin Nisha tasa hanu ta karba kafin ya juya ya koma inda ya fito itama Nisha tarufo door ta dawo ta dare tray din bisa table, Nisha zuciyar ta duk ta da gule gaba ta takura tarasa mai sa Ajmal ya daukota ya kawo ta nan ya fita yabarta ita daya bayan shiyace ba zai dinga barinta ita kadai tana kasan cewa ba gaba daya sai takejin badadi a ranta.
A taikaice dai wunin yau ita kadai tayi shi Ajmal ko lekota baiyiba still koma bai kirata ba ta ban garan Nisha abun duk ya daga mata akwatin hankali da tunanin ina Ajmal ya je haka tunsafe gashi harana tana shirin fad'uwa tsoro duk ya da bai bayeta wannan shine kulawar da yace zai bata ya rabota da kasarta ya kawota kasar mutane ya ajiyeta yayi tafiyar sa Nisha abun duk ya dameta ko abin takasa zama taci yanda aka kawo mata breakfast fadi'n haka a ka dawo aka dauka ko tabawa batayi ba hatta lunch din ma ba ta taba ballai taci karshema bedroom ta shiga ta takura kanta ciki ta shiga aikin kuka da baya bata wahala..
Guraren karfe 8:30 na dare
Ajmal ne ya turo door kansa tsaye ya shigo parlourn yana sanye cikin wani black suit yayi matukar kyau dashi but daga yanayin yanda yashigo zaka fahimci amatukar gajiye yake sosai direct bedroom d'insa ya nufa ya cire suit din jikinsa ya fad'a bathroom wanka yayi sosai daga bisani ya fito ya kimtsa jikinsa daga nan ya kuma shirya kansa cikin wasu kyawawan kananun kaya blue shirt mai gajeren hanu mai laushi da taushi sai white jeans gajere zuwa gwiwansa daga nan ya fito ya nufi bedroom din Nisha.
Ko da Ajmal ya tura door ya kutsa kai ya shiga daga bakin door din bathroom ya hangi Nisha ta fito tana daure da towel bisa k'irjinta da alamar daga wanka ta fito, Nisha kallo daya tayiwa Ajmal dake can bakin door yana aika mata da kallo ta dauke idanu ta maida kanta kasa yayinda ta shiga takowa ta karisa bakin bed ta dauki kayanta dake shirin sawa ta juya tana shirin komawa cikin bathroom.
Ta ku d'aya zuwa biyu Ajmal ya sha gaban Nisha ya tsaya yana aika mata da wani kallo but sai ya ga Nisha tayi gefe da nufin kauce masa kanta kasa , Ajmal kuma tare ta yayi ya kuma tsayawa gabanta ya wani had'e rai ya bata face still gefe Nisha ta karayi ta kauce masa ranta a had'e sai faman bata fiska take tana tura baki hakan yasa Ajmal ya janyo hanunta ya fisgota jikinsa still dai Nisha bata dago sun had'a ido da Ajmal ba .
Hanu Ajmal ya kai ya dago habar Nisha time din wasu sirarun hawaye datake ta faman boyesu tun time din shigowar sa suka hada ido sai yanzu suka shiga gangarowa ta gefen idanunta kamar ana turosu daya nabin d'aya shaa kasancewar Nisha mai dilar k'wallah cid'aka Ajmal yad'ago Nisha suka karisa bakin bed suka zauna Nisha sai faman ajiyar zuciyar take , Ajmal lallausan farin hand d'insa ya sanya ya shiga goge hawayen dake malale bisa kuncin Nisha yana fad'in.
"Bana ce karna sake ganin wa dannan hawayen ba? mai ya kawosu yanzun?"
Wannan tambayar da Ajmal yayiwa Nisha sai tsokano ta yayi ta fashe masa da kuka harda yar shashsheka, Ajmal har cikin heart d'insa yake jin kukan Nisha baisan kukan mai take ba but tun shigowar sa ya fahimci halin da take ciki yasan daga cikin bai wuce makone da kad'aicin barinta zama ita kad'ai ba , Ajmal jinginta yayi jikinsa yana shafo suman kwanta wanda ke kwance luf.
" Banason wannan kukan stop it "
Nisha sai narkewa tayi jikinsa tana jan hanci gamida ajiyar zuciya tana goge hawayen face d'inta sam ba taso kuka ya kwace mata ba to amma kukan yaci karfinta ne ba k'aramin ta kaicin Ajmal take kulace dashi yau but ta kasa yi masa uzuri duk da ba ta san uzurin nasan ba , Ajmal riga da skirt din da ke hanun Nisha ya amsa ya nufi wardrobe ya maida shi ciki daga bisani Nisha ta ga Ajmal ya dauko mata wani sleeping dress wata yar shilan shalan din riga mai hanun vest tsayin rigar bai wuce cibiya ba tare da wani gajeren wando shima dai bai wuce iyaka cinya ba mai santsi sai duguwar rigar da za adaura sama mai bud'edd'en gaba tare da madaurin da mutum zai daure saman waist d'insa .
Sleeping dress din yayi kyau sosai white color mai d'igo d'igon baki jikin kayan, Ajmal ya dawo ya ajiye mata saman cinyarta yana fad'in
"Ki sanya wa d'annan"
Nisha sleeping dress din ta bi da kallo kafin ta kuma maida kallonta ga Ajmal wanda tuni ya juya baya ya nufi hanyar fita, to ita yanzu mai zatayi da wannan sleeping dress din da Ajmal ya ajiye mata yake nema da ta sanya ita sam bazata iya sanya suba koda a ce ita kad'ai ce ballai da tasan tare da Ajmal zata kasance anyama kuwa Ajmal qalau yake rana d'aya ya dauko wa dannan yan iskan kayan ya ce ta sanya .
Ba da d'aiwa Ajmal ya dawo cikin bedroom d'in hanusa dauke da tray d'in abinci ko da ya dawo yanda ya barta haka ya dawo ya taddata zaune bisa bakin bed tana ta faman juya kayan da ya ajiye mata yace ta sanya, wani sassanyar iska Ajmal ya furzar cikin bakin sa yana mai ta kaicin rashin jin magana irin na yariyar is too young but ta cika taurin kai da yawa simple
Instructions but sai ka ta surutu kana na na tawa .
Saman table Ajmal ya dire tray d'in kafin ya nufo inda Nisha take zaune ya tsaya bisa kanta yayinda hand d'insa ke zube cikin aljuhunsa yana kallonta kafin yace
"Ko kina da bukatan taimako ne gurin sa kayan ?"
, Nisha da kanta ke kasa sai dan d'ago kai tayi suka had'a ido da Ajmal wanda ya tsare ta da ido yana tambayar ta , sauke idanunta kasa tayi tana girgiza kai kafin tace
" Ni ba zan iya sa wa d'annan ba "
Nisha ta fad'i tana ya motsa face kaman mai shirin kuka sai faman turo baki take
"Nikuma su nake da bukatan kisa"
Ajmal ya bata amsa a takaice yana wani bata fiska
Nisha mis mis tayi da idanu ranta babu dad'i tamike ita dai taga ta kanta kayan sawa ma sai anyiwa mutum dole zame jiki Nisha tayi da niyar barin gurin ba tare da ta dauki kayan ba ganin haka yasa Ajmal ya janyo hanunta ya fisgota da karfi wanda sai da yan hanjin cikinta suka kada tsabar tsoro ,
"Where are you going for".
Cikin sarkewar murya Nisha tace
"Kayi hakuri dan Allah wannan kayan sunyi min kadan na sasu bazan iya...."
Kafin ta kaiga karishe maganar ta sai gani tayi Ajmal ya daura hanusa bisa kirjinta d'aid'ai madaurin towel d'inta because ya fahimci komai sai tayi masa musu kafin tayi ita kuwa Nisha jin Ajmal na kokarin zame mata towel yasa ta fiddo idanu waje tana zazzare idanu gamida sanya hanu ta dafe nashi da kokarin hanashi abunda yake but sai gani tayi ya sanya hanu biyu yana kokarin bude towel din gaba d'aya da iyaka k'arfinsa jikinta harya suma baiyyana ganin haka yasa Nisha d'urk'ushewa da iyaka karfinta ta kife gurin tana fidda wani walallain numfashi cikin tsoro da takaici ganin karfin hali irin na Ajmal gurin tilastata ga abunda bata da ra'ayi.
Shima biyota kasan Ajmal yayi ya d'urk'uso yana hararo ta wanda ta kifa kai kasa a kunyace a tana fidda wahalallen numfashi
"Zaki sa d'in ko na sanya miki da kaina?"
Da sauri Nisha ta kuma mikewa tana girgiza kai kafin ta kuma tattaro towel d'inta da yakusa barin jikinta ta mike gamida janyo sleeping dress d'in tanufi bathroom da gudu ta mai da door ta rufe
"Better "
Ajmal ya furta a hankali time d'in da ya mike shima ya nufi sofa ya zauna da tunanin yanda zai sanya turin kan Nisha izuwa laushi da kuma wannan kunyar karyan duk saiya yakice ma ta su