Ajmal Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Jb Category :  Complete Novels

Chapter   4 / 7

9K to 12K   out of 20.6K words

zuciyarta bisa k'irjinta sauri sauri k'arfi k'arfi , Nisha jinta jikinsa yasa ta shiga zamewa a hanzarce wanda shima Ajmal ya jinye jiki daga nata yayi baya yana kallonta.

Nisha guri taga Ajmal ya nema daga bikin bed din ya zauna yana worgo mata da idanusa wanda suke kamar touch saboda haskensu kafin taji yana fadi'n

"Come and seat here". yaimata nuna da gefensa Nisha dake tsaye tana kallon jin abunda ya fad'i da kuma gefensa da ya mata alamar ta zo ta zauna yasa ba tare da wani musu ko tunanin ba ta nufi inda yake kai sunkuye tana murza yan yatsun hanunta tana wasa dasu.

Ajmal zuba mata idanu yayi gamida karewa kyakykyawan halittar suran jikinta kallo wanda yake mantar dashi tunanin da shagala da kallonta ba tare da so ko ya shiryawa hakan ba.

Nisha gunda Ajmal ya nuna mata nan ta zauna ta duk'ar da kai ba tare da ta d'ago ta kalleshi ba , Ajmal hanu ya kai ya kamo hab'arta gamida juyo da face d'inta yana fadi'n

"Look at me " da k'yar Nisha ta iya d'ago idanu ta sanya cikin na shi duk da kallonsa sunyiwa idanunta nauyi but haka ta daura nata idanun cikin nasa tunda ya bukaci hakan, junansu suka k'urawa idanu ba wanda yake iya k'yaftawa Nisha ba k'aramin dama ta samu na tsatso kyawun ajmal ba gurin kallon shi gashi dai na mijine shi tsayayye Kuma dararre but wasu halittar sa tamkar na mace.

Wato Allah ya bawa Ajmal halittar suma mai tsayi ko kan wata ya macen albarka, ga kuma kyakykyawan eyelashes dugaye da wata macen ma ba za asame ta da shiba ga kwantaccen gira da suka kusan hadewa da junansu kuma cikako gwanin sha'awa.

bugu da kari dugun hancinsa siriri kamar shi ya dasawa kansa idan ka karisa sakkowa kasa gurin lips d'insa mai kyau da jan hankali jajir dashi kai kace janbaki ya shafa ga kuma kyakykyawan saje baki wuluk da ya mamaye gefen face d'insa zuwa habansa sai shining yake yana walkiya.

"Hi wani irin kallone wannan cinye ni zakiyi?".

Ajmal ya fad'i time din da ya d'age idanu daga face d'in Nisha Ganin wani kallon kwakwaf da takewa face d'insa

Tura baki Nisha tayi jin wata tambayar da Ajmal keyi bayan shi yace ta kalleshi ita kuma ta tsinci kanta da yi masa kallon kwakwa, Ajmal bakin Nisha ya bi da kallo wanda ta turo shi gaba gamida kauda kanta gefe.

Ajmal hanu yakai ya janyo lips d'in Nisha da d'an k'arfi wanda yasa Nisha zaro ido gamida kama hand d'insa tana kokarin janye hanunsa ganin yanda ya janyo mata lips kamar zai cire mata leb'e

"Ba kya jin magana da alamun kin soma ranani". Ajmal ya fad'i yana jijjiga lips d'in yana kallonta gamida watsa mata harara, girgiza masa kai Nisha ta shigayi tana rike da hand d'insa ita sam ta mance tura baki ya zaman mata jiki especially shi da yake kunnata take jin haushi .

Ajmal mirginuta jikinsa yayi saman cinyarsa zaune kafin ta ankara ya janye towel d'in dake jikinta, baki na bari Nisha ta bude baki danu fi bashi hakuri amma sai ji tayi kirif ya rufe bakinta da nasa yayinda ya tura harshensa cikin nata ya janyo nata harshen ya suma sucking cikin mugunta kamar zai cire mata harshe.

Cikin azaba Nisha ta shiga janye kanta gamida zamewa amma ya rike ta gam, yayinda da ya kai d'ayan hannusa ya cafke dukiyar fulaninta ya shiga matsawa da k'arfi wanda ba dan rufe mata baki da yayi ba da kuwan ihunta sai ratsa bedroom din.

Kukan wahala Nisha ta shiga jerowa jin yanda Ajmal ke matsa Brest d'inta cikin horo duka biyu azaba goma da ashirin ga harshenta shima Ajmal kamar zai cire mata , Ajmal sai da yai mata muguntarsa san ransa kafin ya kyaleta because baya so yayi nisa Nisha a hanzarce tazame daga jikinsa ta fad'a bed gamida g'yara towel d'in jikinta wanda yazo daidai maranta yana shirin fad'uwa Allah yaso da d'an kanfai jikinta.

Kuka wui wui Nisha keyi kasa kasa tana shashsheka ganin muguntar da Ajmal yai mata duk da batayi mamaki ba dan tasan dama ya gama tsanar ta abu bai kai abu bama zaice ya kai yayi mata horo.

Ajmal mikewa yayi yana jin kukanta har cikin kokon ranshi but sai dannewa yayi gamida sanya hanunsa cikin aljuhunsa ya zaro rafan dala ya cilla mata saman bed din yana fadi'n

"Amshi wannan ladan hidamar da kika yimin a baya because kar tafiya tayi tafiya kimin gori kinyi da wainiya dani dan haka ga ladan aikin ki nasan kinaso kuma zaki bukata".

Ajmal na gama fadi'n haka Harya juya zai fice sai kuma ya jaa ya tsaya gamida zura hanu cikin aljuhunsa yana fadi'n

"Am zaki tashi daga nan zuwa gobe ki had'a kayanki duk wani abunda kike da bukata kusa dake because gobe around 8:30 fligh din mu zai tashi so banaso bata lokaci ki zama ready Ajmal yayi magana cikin dad'in rai tamkar bashi ya gama aikin mugunta ba yanzu, ba tare da ya kuma biyawa ta kanta ba ya nufi inda ya ajiye hularsa ya dauka daga nan ya sa kai ya fice

Nisha tunda Ajmal ya suma maganan had'a kaya da maganar jirgi Cak Nisha ta tsaya da kukan jin wata sabon salon kuma da ya b'ullo da shi

Ajmal

story and writing

by

Oum amreesh

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v

馃挭 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*馃挭 鉁嶏笍

(J.W.A)

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan 茩asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau茩i_.鉁忥笍

book 3

*_TAKUN KARSHE*_

page 100

__________ Wato muguntar da yake mata a nan bai gamshesa ba sai ya dan gana da ita wani gurin inda babu idon kuwa ballai ashaida kukanta da kuma halinda take ciki dan haka ta k'udiwa ranta ba inda zata bishi sutafi sai dai ayi wacce za ayi.

gefe guda kuma ta koma ta bi dallan da Ajmal ya wurga mata gefenta ko wace uwar zatayi da wannan kudin oho duk wani salon neman magana Ajmal ya sani to ko sadakin ta da Ammi ta bata kin karba tayi saboda bata san mai zata farayi da wannan kudin ba dan haka tabawa ammi wuka da nama ayi duk abunda ya dace da ballai wannan kudin da batasan yawan adadinsa ba tunda ba tamu bace.

Nisha ko ta kan kudin bata bi ba ta zamo daga saman bed din ta nufi bathroom ta wanko face dinta kafin ta nemi dugowar night gown dinta mara nauyi yar shalan shalan ta sanya kafin ta matsa ta haye saman bed din ta kwanta cikin k'unar zuci gamida takaicin abinda Ajmal yayi mata gaba daya Brest dinta sai wani irin rad'ad'i suke suna zogi uwaba harshenta da ajmal yari ke mata kamar zaicire rintsa idanu tayi wasu sabbin hawaye Suka suma wanke mata face

"Allah ya isa sai Allah yasa kamin ".

Nisha ta fad'i afili kamar suna tare kafin ta kuma fashewa da kuka kasa kasa tana nitsa face dinta cikin pillow sai da tayi kukan ya isheta kafin bacci b'arawo ya saceta..

Ajmal koda ya fito da nufin haurawa upstairs ya nufi bedroom dinsa time Heelah itama ke ta fe ta nufo downstairs sai faman mika take gamida dogon hamma because tayi jiransa harta gaji, kallo daya Ajmal yayi mata ya kauda kai kamar bai ganta ba ya ratsa gefenta ya shige abunsa , Heelah da rakiyan idanu tabi bayansa gamida tab'e baki kafin ta iya karisa takowa tadawo tsakiyar parlourn ta tsaya tana jin wani sabon haushi da takaicin Nisha da ke k'ara lullub'e zuciyarta .

Ajmal na shiga bedroom dinsa cire kayan jikinsa yayi ya fad'a bathroom wanka yayi kafin ya fito ya kimtsa jikinsa ya shirya cikin kyakykyawan jallabiyarsa kafin ya nemi saman katafaran lallausan bed dinsa ya kwanta yana mai lumshe idanu gamida saukar da ajiyar zuciya a hankai.

Turo door din da akayine yasa Ajmal waro manyan sexy eyes d'insa gamida maido da kansa da idanunsa ga door din ganin Heelah ce dauke da tray bisa hanunta sai kauda kai yayi gamida mai da idanunsa ya kuma rufewa sai wani faman had'e gira yake yana had'e fiska .

Heelah can saman table ta nufa da d'an madaidaicin tray din kafin ta dawo gefe da shi ta zauna tana kallon kyakykyawan face dinsa hanunta dauke da cup din coffee ta na fad'in

"Ga coffee kashaa nasan kanada bukata" .

" Bana bukata ".

Ajmal ya fad'i a takaice ba tare da ya bude idanunsa ya kalleta ba, cike da rashin jin dad'i Heelah ta sauke cup din coffee kasa tana fadin

"Nasani bakaji dad'in ganinaba sam bakaso na dawo na katse muku jin dad'in ku ba, ".

Heelah ta fadi cikin sanyin murya tana sunnar dakai kasa gamida matsar k'wallar bakin ciki da ta kaici kafin ta cigaba da fad'in

"Nina rasa maisa ko shaawar had'a idanu da ni bakason yi ballai ka kalleni ka tsaneni bakasona k'wata k'wata maiye laifina?" Nifa 'yar uwar kace bayan mata a gare ka kuma uwa ga d'anka Aheel".

Heelah ta kuma fadi cikin face din tausayi

"Hold down please banason damuwa da wadan surutain naki I'm tired ni ban tsaneki ba but bazan soki ba ko nan gaba".

"Daga haka Ajmal ya juya mata baya yana mai g' yara kwanciyarsa still ba tare da bud'e ya kalle ta ba

Zuciyar heelah kaman ta bashe nan da nan ta suma Sharan hawaye gamida da mikewa tanufi tray din da ta shigo da shi ta ajiye cup din coffee ciki wanda tuni ya suma hucewa ta kwashi tray tayi gaba tare da k'ud'irawa ranta cewa tunda Ajmal ya fitu kiri kiri ya fad'i mata bazai taba sonta ba to daga shi har Nisha sai tasa sunyi bakin ciki a rayuwa zuciyarsu ta k'untata kamar yanda suka k'untata mata nata ayanzu..

washe gari karfe 7: Ajmal fitowan shi daga wanka kenan sanye cikin kyakykyawan bathtub hanunsa rike da wani karamin towel yana mammatse suman kansa yana tsantsame ruwan dake suman, turo door din da akayine ana kokarin shigowa wanda a tunanisa heelah ce because ita kadai yake thetunanin zata iya ziyartarsa gamida ta kurasa a wannan lokacin but jin muryan Nisha da sallamanta sai ya kawar masa da tunaninsa.

Nisha ganin shi da tayi haka sai taji nauyin karisawa ciki ta tsaya tana zare idanu ita bata shiga ba ita bata koma ba,

"come in ".

Ajmal ya fadi gamida mamakin meya kawota da sassafen nan, Nisha hannayenta zube cikin duguwar hijab dinta jikin ba kwari tashiga jan jiki ta gamida karisawa tsakiyar dakin kafin ta durkusa saman lallausa carpet din cike da ladabi ta shiga gaishesa

"ina kwana".

"lapia ".

Ajmal ya amsa mata still idanunsa na kanta

"antashi". Nisha takuma fadi

"I'm fine".

Ajma ya kuma amsawa cikin kosawa da gaisuwan nata gamida dauke kai ya shiga kallon kansa jikin mirror ya cigaba da abunda yake

"what's your problem".

Ajmal ya tambaya ba tare da ya kallo taba, a hankali Nisha tazaro hanunta dake ta faman rawa cikin hijab tafidda kudin da ajmal ya bata bisa hanunta daga bisani ta daura masa kudin bisa table tana fadin

"Ga kudin ka bani da bukatarsu it means bansan mai zanyi dasu ba kuma dan Allah ni ka kyaleni anan bani da bukatar zuwa ko ina please..".

Nisha ba takai ga karisa maganar ba wani juyawo da ajmal yayi ya watsa mata wani kallo yasa ta hadiye sauran batun nata tashiga zare masa idanu

"Are you mad ".

Ajmal ya fadi a tsawace cikin kakkausan murya yana ta kowa inda Nisha take wanda yasa yan hanjin Nisha kadawa ta mike a zabure tana fidda idanu waje ta suma kokarin baya da nufin barin bedroom din cikin hanzari datsoro, aikuwa taku daya zuwa biyu kafin ta ankare ya fizgota cikin zafin nama yana fadin

"you are very stupid 馃槨 "

Ajmal ya fad'i rai a matukar b'ace ganin tsaurin ido irin na yarinyar gamida taurin kai dayi masa musu cikin lamuransa tana kokarin jayayya dashi

Hakuri Nisha ta shiga bashi cikin tsoro gamida jin zafin rikon da yayi mata yariko hannayen duka biyu ya had'e su bayanta yana jijjigata yana cigaba da magana

"kinada taurin kai bakya jin magana saina ta surutu ".

Ajmal ya fad'i time din da ya kai hannunsa jikin kunnenta ya jaa da d'an karfi wanda yasa Nisha ta saki wani kara mara sauti tana fad'in

"Dan Allah kayi hakuri na tuba ".

cikin magiya da marairai cewa da kyar ajmal ya kyaleta yaja baya Yana hararo Nisha da ta ja baya itama tana muzurai gamida fidda idanu waje

" This is the first and last da zaki karayimin musu ga duk wani batuna dan gane da ke ".

Ajmal yafi ya na kuma watsa mata wani banzan kallo, jiki na rawa ta shiga gyada masa kai alamar gamsu kafin cikin hanzari ta nufi hanyar fita , ajmal ya kuma dakamata wani uban tsawa ya dakatar da ita a tsawace yana mai umartarta data dauke masa wannan kudin ta fice masa daga bedroom dinsa aikuwa kafin ya gama rufe bakinsa daga maganar da yake Nisha ta nufi inda ta ajiye masa kudin ta fice da sauri har tana yar tuntub'e.

Guraren 7:20 Ajmal ya kimtsa ya gama shiryawa tsaf cikin kyakykyawan kananun kaya black t shirt mai dugun hanu mai mab'allai a tsakiya gamida dugun wandon jeans milk colour mai taushi da sulb'i saman kansa dauke da kyakykyawa p-cap yayi kyau har ya gaji .

phone's dinsa kawai ya dauka ya nufo downstairs, koda ya kariso sofa ya nema ya zauna gamida daura daya bisa daya ya shiga ya shiga danna phone dinsa...

Nisha ce tafito cikin kyakykyan shirinta duguwan rigar abaya ash colour mai rintsin baki baki rigan tayi matukar kyau da kayatarwa sai farin mayafi da tayi Rolling saman kanta ta fito kamar wata kyakykyawar balarabia, tayi matukar kamar asaceta a gudu.

Nisha idanunta ne ya sauka cikin na Ajmal dake zaune bisa parlourn sai da taji k'irjinta ya d'an harba , shikuwa AJmal yana daga zaune yake wurginta da kallon up and down

Ajmal

story and writing

by

Oum amreesh

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v

馃挭 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*馃挭 鉁嶏笍

(J.W.A)

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan 茩asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau茩i_.鉁忥笍

*_ TAKUN KARSHE_*

book 3

page 1锔忊儯0锔忊儯1锔忊儯

______. Nisha shafo gefen wuyanta ta shigayin fiki fiki da idanu da tasan Ajmal na parlourn da ba abunda zasa ta fito yanzun because dama yunwane ya korota daga ciki ta fito neman abunda zata sanyawa cikinta saboda yau ta tashi da wuri kuma takasa komawa bacci dan haka sai taji cikinta a fafake yunwa ta tusota gaba.

Ajmal ganin Nisha tsaye can ita bata kariso ba kuma ba ta komaba yasa ajmal yimata kiranye da hannayensa alamar ta kariso wanda yasa Nisha ta daga k'afafu ta shiga karisawa tsakiyar parlour gamida samun guri gefe ta tsaya kanta kasa

"ke!"

Ajmal ya fad' i cikin cold voice mara sauti wanda yasa Nisha dago rinannun idanunta wadanda suka kumburu alamar taci kuka harta godewa Allah

Ajmal ba k'aramin tausayin yariyar ne yake d'ibansa ba but wani lokacin tauri kanta ke jawo mata wahala gunsa, sam bata jin magana tafiye tirjiya sai da ya kare mata kallo na wasu ayan mintuna kafin ya kauda kai yana fad'in

"coffee zaki kawo min ".

Aikin kenan Ajmal mayen coffee ne na gidan gaba sai yasha coffee sau biyu a yini safe da dare , ba musu Nisha ta nufi kitchen kyakykyawan coffee ta dauko ta koma dining area tashiga hado Masa zazzafan coffee kafin ta dawo ta mika masa cikin ladabi gamida kulawa shikuwa ya amsa ya rike bisa hanunsa ba tare da ya kalleta ba Nisha harta suma jan k'afa da niyar barin gurin sai tsin kayan muryan Ajmal tayi ya dakatar da ita ya na fadin

" wait! "

Nisha tsayawa tayi tana jiran taji yace wani abun but sai taji shiru yana ta faman latsa waya yana k'urb'an coffee ba tare da ya kalleta ko yace wani abinba, Ajmal sai da ya shanye coffee tas kafin ya mike tsawonsa ya tako inda take tsaye dab da ita har numfashinsu na koran najuna wanda yasa cikin Nisha tsurewa ta shiga zare masa idanu tana kallonsa sai da Ajmal ya huro mata sassanyan iskan bakinsa ya hure mata y'an idanun daga kallonsa da take tana zare masa manyan idanuta kamar wacce taga dodo sanan yace

"Dai na kallona haka ki dinga rage power idanunki yayin hada ido dani".

Nisha sunkuyar da kai tayi gamida rintsa idanu daga nan sai ji tayi a

Ajmal ya janyo hanunta fuuu suka kama hanyar fita daga parlourn, koda suka fito daga side dinsu Ajmal yana rike da hand din Nisha bai sake ba harta ga yanufi side din su Ammi nan ma sai da suka dan gana izuwa tsakiyar parlourn kafin ya raba hannayensu time din Ammi ta fito daga kitchen wanda ganin tsayuwar su Nisha da Ajmal cikin parlourn yasa ta saki murmushin farin ciki ganin Nisha wadda take ji kamar tayi sati bata ganta ba, itama Nisha murmushin ta sake sai faman sunnar da kai kasa take koda karisowar Ammi Nisha ta shiga dago mata gaisuwa gamida rusnawa Ammi ta amsa tana mai saurin d'ago Nisha daga dukawar da tayi wanda yasa ammi fadin

"kyakykyawar yata mike munyi kewar ki sosai ba kad'an ba duk da kina kusa damu munajin numfashinki"

Ammi tafadi tana yar murmushin farin ciki gamida jawo Nisha jikinta wacce take ta murmusawa ba tare da ta ce komai ba daga nan Ammi ta maida kallonta ga ajmal wanda yasa ki

4 / 7