Ajmal Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Jb Category :  Complete Novels

Chapter   5 / 7

12K to 15K   out of 20.6K words

baki yana ganin riritawar da Ammi ke yiwa Nisha ita kuma sai wani nukewa take shi har kullum mamikin shakowarsu ga yarinyar yake sai wani shagwab'a mata suke suna shishshige mata kamar tafi kowa.

Ajmal shima d'ago mata gaisuwan yayi face dinsa asake ba tare da ya daure ta kamar yanda ya saba ba, cike da fara'a Ammi ta amsa tana mai tambayarshi.

"Tafiyar ne ta tashi duk da ma naga kamar kunaso ku makara ".

Ammi ta fadi tana duba time jikin bangon parlourn

"yanzu zamuwuce insha allah Daddy fa ?".

Ajmal ya fadi gamida tambayar Daddy

"Kyale Daddy da Hajiya duk zansanar su tafiyar ku insha Allah kai dai ka tabbatar kayi kiranmu bayan isaku ".

Gyad'a mata kai Ajmal yayi kafin suka fito Ammi har bakin mota tarakasu tana rungume da Nisha wacce idanuta sukayi rau rau duk sun ciko da k'wallah Ajmal bude mota yayi yashige gidan baya kasancewar ba shi zaiyi driving ba

Gaga nan Ammi ta kutsa Nisha itama tana shimusu albarka tare da fatan alkhari gamida bawa ajmal amanar Nisha ya kula da ita sosai daga nan drive yayiwa motar key mai gadi ya bude gate daga nan suka fice Ammi sai da taga kurewar motarsu yabar compound din gidan kafin ta juya ta koma ciki cikin yanayi na Nisha di farin ciki.

Tunda suka bar gida Nisha idanunta ke ta ambaliyan ruwan hawaye sai kauda kai gefe take shikuwa Ajmal kaman wanda bai lura da yanayinta ba sai faman waya yake ya kashe wanna ya dauki wannan daga bisani ma sai kashe wayoyin yayi gaba daya ya mai do idanunsa ga Nisha wacce ta takure can kusa da door din motar sai faman sharan kwallah take gamida tunanin wacce duniyar Ajmal ya nufa da ita.

Hanu Ajmal ya kai ya fisgo Nisha ya matsota jikinsa ba tare da wani tirjiya ba sai da d'a narkewa tayi because dama neman mai lallabinta take

"Kukan mekike?".

Lamo Nisha tayi tana sauke ajiyar zuciya a hankali ba tare da ta iyace dashi komai ba

"Tafiya danine ba kyaso? kinfiso na barki acan heelah ta yankaki? Ajmal ya kuma tamaya cikin wata kasalaiyar murya , aikuwa cikin hanzari Nisha ta shiga girgiza masa kai alamar aa , murmushin gefen baki ya sake kafin yasa hanu ya janyo mata tissue paper ya mike mata yana fadi

"Share wannan hawayen banason sake ganinsu amanarki akabani bazan wani abu ya bata miki ba but idan tanine bakin kita zubaddasu ba har mu isa ".

D'agowa Nisha tayi suka hada ido da ajmal jin batun da yake gaba daya ta kai ci ya lallubeta da harta suma jin dad'i ajma yana lallabarta yana mata magana cikin sanyin murya mai dadi ashe ba lallashi bane bakar magana zai fada mata Nisha janye jiki tayi ta matsa gefe ta cigaba da share hawayen face dinta sai faman tsuke lips take saboda da takaici.

shikuwa ajmal cikin rashin damuwa ya kauda kai gefe ya cigaba da sabgar gabansa, bawani dadewa hanya ta kawosu airport suna suwa wasu security's guda hudu manya majiya karfi madaka dukan katu suka rufa masa baya biyu gaba biyu baya tare da briefcase din kayansu, Nisha gata cikin jirgi ba zato ba tsammani ko a mafarki masha allah cikin jirgin kamar kana parlour.

cikin jirgin manyan mutuanene dattawa wasu da matansu wasu da kuma single suke duka cikin jirgin bai wuce mutum gomaba tunda Ajmal ya shigo suka zauna sai bashi gaisuwan bargirma suke duk da kasancewa sun girmemishi wasu daga cikima sun haifeshi but Allah ya bashi girma ya dauka kashi suma kuma suna darajashi kasan cewasa babban mutum a idon duniya.

_ 8:30_

flight dinsu ajmal ya daga izuwa kasar Indonesia tsawon wasu awowi flight dinsu yayi landing Bali island Indonesia, wasu mayun had'add'un motocine jeri guda tare da security's na musamman kowannensu ya shiga motar d'aid'ai tare da abokin tafiyarshi daga nan aka sake d'aukan hanya Nisha yawo kamar zai d'iga tsabar kallo ta sake baki tana kallon yanayin yankin guri gwanin sha'awa da burgewa batasan kallo yana gaba ba Ajmal duk yana kula da yanayinta d'an Nisha komawa Ajmal tayi kamar d'an kauye ya shigo burni.

compound din wani katutuwar hotel dan ubansu na isasun mutane wayanda suka driver's sukayi parking sukayi kowa yafito suka nufi cikin kyakykyawan hotel din Nisha daga nan taga kowa ya kama hanyarshi duk inda a

Ajmal ya sanya k'afafuwansa na Nisha na biye dashi haka zalika yana rike da hand dinta k'am , daganan suka hawara security biyu na tare da su da briefcase dinsu sai da suka zo daidai lipter daga nan security din suka dagata ajmal ya danna hawa na 5 kofa ta bude ajmal ya sanya kafa Nisha sai k'arewa cikin abun kallo take sai ji tayi Ajmal ya janyo hanunta ciki kofa ta rufe kirif .

suna isuwa hawana 5 kofa ta bude sai ga wasu mutane biyu again cikin girmamawa suka shiga taimaka musu da briefcase dinsu dagan ajmal ya shige gaba tare da Nisha su kuma suna take musu baya harsu ka kariso wani door gurin shiru ko giftanwan mutum babu kai kace ba masu rayuwa gurin, daya daga cikine ya sanya key ya bude door din daga nan ya mikawa Ajmal key din hanu biyu daga bisani Ajmal ya amsa suka karisa shigar musu da kayan kafin suka fice gamida barin arean gurin gaba daya.

daga nan ajmal ya ja hanun Nisha ya wurga ta ciki ya maida door ya rufe, Ajmal kallo daya yayiwa Nisha ya kauda kai duk tayi wujiga wujiga da ita idanuta duk sun k'ank'ace alamar gajiya duk ya bayyana ga jikinta, shi dinma a gajiye yake dan haka sai karisawa cikin bedroom yayi domin yayi wanka yaji dadin jikinsa.

Nisha gurin tabi da kallo tana karewa ko ina kallo hotel tamkar cikin gidanka kake parlour mai kyau mai na ciki fari tas dashi gwani shaawa, ga kitchen dining area ga room har biyu masha Allah guri yayi matukar kayatuwa, .

Ajmal haryayi wanka ya shirya yafito cikin wani lallausan t shirt mai gajeren hannu gamida gajeren wandon jeans yanda ya bar Nisha haka yazo yataddata tsaye kamar ta hadiyi tabarya bata samu halin zama ba .

Ajmal

story and writing

by

oum amreesh

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v

馃挭 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*馃挭 鉁嶏笍

(J.W.A)

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan 茩asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau茩i_.鉁忥笍

_*TAKUN KARSHE*_

book 3

page1锔忊儯0锔忊儯2锔忊儯

________ "Tsayuwar mai kike anan go and take the shower"

ajmal ya fadin time din da yakariso ya nemi sofa ya daura daya kan daya yana binta da kallo , a sukwane Nisha ta ja dan karamin trolley din da Ajmal ya sunkuto mata ba tare da ta tantace maike cikin ba , tanufi daya daga cikin bedroom din parlourn Ajmla da rakiyan idanu ya bi bayan Nisha har tashige bedroom din ta maida ta rufe.

Nisha bedroom din tabi da kallo komai fine gefe ta jingina trolley dinta ta matsa bakin lallausan bed din ta zauna tana sauke wani nan nauyan ajiyar zuciya kafin tasa hanu ta warware rolling din mayafin kanta daga nan ta zame duguwar rigar jikinta tanufi bedroom, Nisha ruwa mai dumi ta sakarwa kanta ta tsaftace jikinta kafin ta fito jikinta sanye da bathtub pink color ko gwaiwarta bai gama karisawa ba saman kanta nannade da towel because ruwan dake suman kanta ya tsantsame jikin towel din daga nan ta nufo tsakiyar bedroom tana wutsil wutsil da idanu.

Trolley kayanta ta janyo ta zuge zip din first phone dinta ta suma cin karo da shi ciki wanda Ajmal ya kutsa mata ciki kwata kwata tama mance da batun wayanta, daga nan ta sanya hanu ta zaro phone din ta ajiye gefe kafin tashiga duba kayan dake ciki gamida lalub'a kayanda zatasa amma abun takaicin babu wani kayan kirkin da zata iya sanyawa ta sitirta jikinta nan tashigayin d'aid'ai da kayan tana budewa because kowane cikin ledersa yake alike sai yanzu taki jin haushi da ta kaicin kanta da bata tsaya ta kimtsa kayanta ba tunda tafiyar tazama wajibi gare ta amma ta tsaya kunci da taurin kai gashi Ajmal ya mata gaban kansa ya san k'wamo mata jaka batare da yasan maike cikin trolley din ba .

Gefe Nisha ta zauna bakin bed tana huci ta ranta gaba ki daya ya jagule sai tura tsukeken lips dinta gaba take, da tunanin ya zatayi dan dai ita duk cikin kayanda tagani bataga wanda zata iya sauwa ta zauna da shi ba, turo door Ajmal yayi ya shigo cikin bedroom din kansa tsaye ya dubeta yana fadin

"what you are doing for? kin barni a parlour ina jiranki"

Nisha ba ta iya boye bacin ranta ba sai da d'a sake turo baki da tayi kafin tashiga fadin

"wadannan kayan cikin trolley din ba wanda zan iya sanyawa ciki "

"because of what? "

Ajmal ya tambaya yana mai karisowa tsakiyar d'akin yana kallonta gamida duban kayan trolly din da tayi d'aid'ai da su saman bed din duk kananun kayane sleeping dress dana hutawa, Nisha bata iya bashi amsa ba sai faman kunci take d'aker ta iya ba shi amsa da cewa

"Ni sunyimin kananu"

"so what ? kisa haka koyayane kifito ina jiranki "

Yana fadin haka ya juya ya fice ya bar Nisha gurin ta kaici kamar ta diga kwallah gaba daya haushin kanta take ji , ba yanda ta iya haka tashiga lalub'a mai dan dama cikin kayan wanda zata iya sanyawa ta fita, wani t shirt mai dogon hanu milk colour ta janyo tare da wando mai laushi da sulbi maroon da rintsi rintsin ido ta gefen duk da kasancewar wandon gajerene bai karisa gwaiwarta ba haka Nisha ta sanya ta tufke suman kanta a tsakiyar kanta tafito tas irin kyakykyawan Indian girl din nan.

A sukwane Nisha ta nufi door ta bude ta fice ta nufo parlour inda ta tadda ajmal zaune da kayataccen tray din abinci gabansa saman table wanda ganin fitowarta yasa ajmal dago kai ya kai kallonshi ga Nisha wacce take ta faman jan kafa yayin karisowa sai wani kauda kai gefe take a kunyace gamida hade kafafunta yayin tafiyar gaba daya wandon yayi masifar kamata tamau.

Wani ajiyar zuciya ajmal yasauke kafin yakauda idanunsa daga kallon Nisha gamida karewa halittar hips dinta kallo wanda yanda ya fidda shape gashi masha Allah gwanin shaawa da burgewa, Nisha daga gefe ta zauna gamida ta kurewa tayi kasa da kai tana murza ya tsun hanunta gaba daya kunya yarufeta ganinta zaune gaban ajmal da gajeren wando cinyoyinta duk a waje bugu da kari yanda wando yayi fitting dinta duk suran jikinta kusan a baiyane yake.

"Kariso nan "

Ajmal ya fadi yana kallota ba tare da ya dauke idanu daga gareta ba harta tasu ta kariso inda yake zaune taimasa tsaye bisa kansa kafin ajmal ya janyo hand dinta ya yazaunar da ita sannan ya matsar da kyakkyawan tray din abincin gabanta yana fadin

"Eat"

Yana fadin haka ya mike ba tare da ya kara bin ta kantaba ya fice daga parlourn Nisha sai bin bayanshi tayi darakiyan idanu kafin taja wani goron numfashi daga bisani ta mai da. kallonta ga jerin da launukan abincin dake saman table din , duk da tana jinyowa because ko acikin jirgi bata iya cin abinci da aka kawo musu sosai ba bai wuce one spoon zuwa two spoon ba but wannan launukan abincin nasu bata zatun zai samu gurbi bisa cikin ta Nisha sai ya tsina face take kamar mai shirin kuka tana bin table din da kallo.

Ba tare da tabi takan abincin ba tamike tanu bedroom ta nemi saman bed ta kwanta gamida dunk'ulewa guri guda gaba daya yanzu a takure take, ta dau tsawon lokaci a haka har ta suma g'yang'yad'awa saboda gajiyan da ya taru mata idanunta sai faman lumshewa suke ba shiri sai bacci mai nauyine ya dauke ta.

Nigeria

Heelah bacci mai nayau ne ya dauke ta bayan da taci kuka ta k'oshi , ita ce bata samu farkawa ba sai guraren 8:30 na safe kafin tanufi bathroom tayi wanka gamida alwala ta fito ta nemi yar duguwar gown mara nauyi ta sanya tare da hijab daga nan ta tada sallah bawani sabon abu bane gurin heelah yin sallah akurarren time , lokacin da take gidansuma wani sa'in sai 9 zuwa goma take tashi tayi sallahn asuba balle kuma uwa uba da take school hawan kawara take ma sallah wani lokacin ma sai yazo ya shige ba tare da tayi shiba because lokacin tana tsakiyar sharholiyarta.

Abinka da sallahn heelah shape shape ta idar hijab din jikinta ta zame ta dauki mayafi ta sanya saman kanta ta fito tanufi bedroom din ajmal, kanta tsaye ta tura door ta shiga but sai ganin bedroom din tayi wayam ba kowa cikin dan haka sai ta karisa bathroom da tunanin ko yana ciki nocking daya zuwa biyu taji shiru don haka sai ta murda handle gamida kutsa kai but baya ciki, downstairs heelah ta nufa ta iso parlor nan ma dai samma kal dan haka sai ta sake uban kwafa tana girgiza kai tana fadin

"yanzu maybe duk nemansa da nake bai wuce yana bedroom din waccer shashar algungumar ba"

Dan dai tasan Ajmal bai cika fitan sassafe haka ba inba wani uzurin ba zama tayi bisa parlourn tana kada kaf'afu tana jin wani takaici da bakin ciki yana tushe mata makoshi ga kuma zafin kishin da yake di banta ita tarasa mai Ajmal ya hango jikin yariyar da har yaji ya rabeta da yawa haka tana cikin wannan yanayin Baraka ta turo door bakin ta dauke da sallama ta karisa shigowa, hango Heelah da Baraka tayi saman sofa ta wani hakince tana girgiza rai bace yasa Baraka ta sakin wani murmshin zuci aranta tana

fadin

"shasha"

Afili kuwa sai dagowa heelah gaisuwa tayi but bata amsa mata ba sai faman wurga mata harara take daga nesa idanunta kamar zasu fado murmushin gefen baki Baraka tayi kanta tsaye tanufi door din Nisha tana kokarin murda handle zata shiga

"Hee madam waya baki izinin shiga Private room dinmu kai tsaye kin wani shigowa mutane kaitsaye ba excuse still yanzu kina kokarin kutsa kai ciki waya baki wannan karfin guwar haka ?".

Heelah ta Fadi cikin tsawa da rashin kunya tana daga murya kai kace da sa'anta take magana.

" Afuwan Hajia ganin nayi ba kowa cikin d'akin shiyasa kaina tsaye zan shiga na dauko tray din da na kawowa Hajia Nisha dinner jiya naje na wanke su"

"Mai kike nufi da ba kowa ciki?".

Heelah ta tambaya gamida sassauto da muryanta kasa

"Eh dake yau suka yi tafiya da mai gidan nata shiyasa".

"Tafiya ! tafiya fa kikace zuwa ina kenan?".

Heelah ta kuma tambaya tana zare idanu cikin mamaki

"Eh to shine ban sani ba amma kya iya kiran mai gidan naki ki tambaya hala basu miki sallamaba".

Baraka ta bata amsa gamida tambayar heelah tana washe baki

Wani irin yuuuu cikin kan Heelah gamida k'wak'walwarta keyi yana juya mata sai dafa bango tayi ta jingina jin tana neman faduwa wani irin huci heelah keyi kamar wacce tayi tsare

"Lapia kuwa"



Baraka ta tambaya cikin damuwa duk da cikin zuciyar ta fes yake

"Ba abunda ya shafeki bane".

Heelah ta fadi cikin wata iriyar murya kafin Barka taga Heelah ta zame jiki da sauri tabar gurin tanufi upstairs a hanzarce, tintsirewa da dariya baraka tayi hartana tafa hannaye kafin ta kutsa Kai cikin bedroom din Nisha ta dauki abunda tazo dauka ta fito ta fice daga side din gaba daya........

Bali island Indonesia 7:30 na dare

Nisha ta bude idanu gamida sakkowa daga lafiyayyen bed din da take kwance, ta nufi bathroom ta wanko face dinta duk da bawai baccinne ya isheta ba mafarkin da tayi da kuma tsoron da ke tare da ita yasa baccin yayanke mata, ko da ta fito daga bathroom tana ta faman goge ruwan face dinta da dan karamin towel din dake hanunta nan idanunta suka ci karo da wasu manyan leder shopping da ke ajiye saman table.

Duk da takawowa ranta cewa ko Ajmal ne ya shigo ya ajiye ya fice dan haka sai ta shiga karisawa zuwa ga table din a kokarinta na taba leder da nufin budewa taga abunda ke ciki sai motsin bude door taji wanda yasa ta dakata daga abunda take kokarin yi tashi zubawa door din ido.

Ajmal ne ya shigo cikin bedroom, Nisha sai mis mis take da ido ganin yanda Ajmal ya nufo ta direct, hanu Ajmal ya kai ya sunkuci Nisha kamar wata baby ba tare da yace da ita komai ba ita kuwa sai faman zare ido take kamar tayiwa sarki karya, fito da ita yayi suka nufo parlour kafin ya direta saman sofa shima ya zauna suka jero da juna kafin Ajmal ya janyo table din abinci gabansu ya shiga bude kowani plate din dake gurin time din ansake chanzo wani delicious din.

Nisha tana ganin Ajmal ya dauki fork ya dibo hadin had'add'en salad na mussaman ya dangana ga bakin Nisha.

"Oya open your mouth"

Ajmal ya fadi yana had'e gira, domin ya fahimci in ya kyaleta

5 / 7