KIDA A RUWA 3 BY BILLYN ABDUL

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   9 / 11

24K to 27K   out of 32K words

“Uhmmm”.
Ya faɗa a maƙoshi kawai yana binta da kallo harta shige. Ta turo ƙofar zata rufe suka haɗa ido. Da sauri ta ƙarasa rufewa tana jingina a jiki tare da runtse idanun tana sauke numfashi. Sai kuma ta zabura tana leƙensa ta jikin Door peephole na ƙofar. Yana tsaye har lokacin shima ya zubama ƙofar idanu da wani kalar kallo data kasa bama suna. Kusan mintuna biyu kafin taga ya furzar da iska yana barin wajen. Itama iskar ta furzar tana sauke ajiyar zuciya. Kafin ta bar wajen zuwa gaban gadon Ruky ta gyara ma bargo daya zazzame a jikinta. Sannan ta nufi bayi yin alwalar barci......

Jin hawowar Dada staircase ɗin ya saka Afeef komawa da sauri cikin ɗakinsu yana danne baki da hannu. Kafin ya tsaida video ɗin da yake recording a wayarsa.
Daga waje shima Dada tsai yay yana kallon ƙofar, sai kuma ya wuce abinsa ɗaki batare daya ce komai ba.

Hummm Afeef video kuma🤔?

_____

Yau da wuri ya shigo gidan. Dan gaba ɗaya baida nutsuwa. Ganin har dare yayi hakan na nufin kwanaki biyu suka rage masa da wannan daren game da umarnin ƴan jam'iyya. Zuwa yanzu ya yanke ma kansa hukuncin da zai fishshe shi ya kuma taimaki ƴan ƙasa da wani abun koda ba komai da komai ba. Dan itace kawai mafitar data rage masa. Yayi alƙawari ma UBANGIJI da talakawan ƙasa da sukai faɗi tashi akan zaɓensa da tunanin ya cancanta wajen kamanta musu abinda ya dace matsayin shugaba. Idan kuma har ya miƙa wuya ga wancan layin ya tabbatar waccan burin nasa da alƙawarin zai tashi a banza ne. Dan shi bai ci ba, ƴan ƙasar basu ci ba, tabbas wasu zasu ci da saka hannunsa. Kuma dole ya amsa tambayoyi akan hakan ranar sakamakon rarrabe ayyukan bayi.
ALLAH ne mai kare bawa akan komai. Amma yana buƙatar wani jajirtaccen mutum kusa da shi da zai dinga rarrabe masa gaskiya da saɓaninta tako wace fuskar data dace. Babu kuma wanda zai iya yin hakan sai mutum ɗaya tak. Mutum ɗayan da ya yarda da shi ɗari bisa ɗari a wannan duniyar. Sai dai fidda sunansa akan muƙamin da yake kallo wani sabon kalubale ne da dole sai ya jure, dan hatta ga shi mai sunan zai iya fuskantar tirjiya kodan sanin da yay masa akan ƙyamatar al'amarin mulki da siyasar ƙasar a bayyane. Dan hakama ya yanke bazai sanar ma kowa ba sai bayan ya ƙaddamar ya kuma zartar. Da wannan tunanin ya saki murmurshi, tare da ɗaukar wayarsa yay kiran ogansa na siyasa.
Bayan sunyi gaisuwa cikin mutunta juna kamar yanda suka saba. Kai tsaye ya furta, “Sir na amince da buƙatun jam'iyya, sai dai da sharaɗi guda ɗaya tak nima daga gare ni”.
Murmushi Oga yayi daga can, duk da yasan dama dole ne Janar ya amince ko yaƙi ko yaso. Kamar yanda ya saba cikin kwantar da kai ya ce, “Ina jinka General, kuma ni mai baka goyon bayane akan duk buƙatunka. Musamman a wannan gaɓar da ka faranta min ka saki wannan jayayyar da zata kawo ma kowa masalaha da kwanciyar hankali musamman ni da kuka saka a ysakkiya.”
Murmushin takaici shima Janar yayi, kafin ya gyara zama da faɗin, “Ta ɓangarena Chef of staff zai fito”.
Ɗifff numfashin Oga ya ɗauke kamar an daki kansa da guduma. Fin mintuna biyu kafin ya ja iska mai nauyi ya fesar. Bisa ga abinda zuciyarsa ta ayyana masa kawai ya ce, “Shike nan yanda kake so haka za'ayi, zan zauna da su, kuma nasan zasu amsa. Sai dai kayi ƙoƙari kaima ka cika musu alƙawarin su duka”.
“Oga! Ni indai akai min hakan na amince da komai game da muƙaman da wanda ma suke buƙatar a baiwa. Daga yau kuma yanzu nan ma chapter closed kawai”.
“Shike nan ka saurare ni, zuwa safiya in sha ALLAHU zaka ji dukkan bayani”.
Received at 12:22 PM “ALLAH ya kaimu Oga na gode sosai a gaida iyali, mu kwana lafiya”.
“Zasu ji. Amin”.
Kai Janar ya jinjina kamar yana a gabansa shima yay murmushi yana ajiye wayar. Jinsa yake sakayau kamar an sauke masa kaya bisa kai. Sai ma ya miƙe ya shiga bayi dan watsa ruwa a jikinsa. Amma murmushi ya kasa barin fuskarsa saboda hango ƙurar da zai tayar a wannan satin cikin ƙasar dan tako wane fanni bai hango sauƙin al'amarin ba, dole ai kare jini biri jini tsakanin maƙiyan ɓoye dana zahiri.........✍️
Received at 12:22 PM
Viewed 2 times
[16/02, 10:59 pm] null: KIƊA A RUWA 3

17

........Anan Gidan Mammah kam Nimrah ta tashi da ɗan dama-dama. Kasancewar ba makaranta suka koma ba suna gama aikin da duk suka san sunayi suka sake komawa barci. Sai wajen ƙarfe goma Mammah tasa Biebah tashinsu suyi kalaci.
Dada baya gidan, dan daga sallar asuba bai dawo ba. A waya ma ya kira Mammah suka gaisa babu jimawa, ya sanar mata yaje wani waje ne amma zai dawo nan kusa. Duk wani motsin Nimrah Mammah na hankalce da shi, ta kuma fahimci a sanyaye take tun jiya. Sannan bata yawan magana. Ganin yanda take kafe mazan gidan da idanu ɗaya bayan ɗaya a kaikaice yasa Mammah fahimtar batun auren da mutanen suka sanar mata ke damunta. Sannan tana son fahimtar waye mijin. Mammah tai ɗan ajiyar zuciya tana ɗauke kanta.
Sauran kuwa fahimtarsu daban data Mammah. Dan sunfi jingina batun kidnapping ɗin da akai mata ne da yanayin nata na shiru-shiru yau. Balle rashin lafiyar Imran ta basu tabbacin sai da akai gumurzu wajen samota, dan haka suka maida hankalinsu akan janta da labaran da zata saki jikinta. Alhamdullahi hakan kuma da suke yayi tasiri. Musamman da taji batun zuwa asibiti duba Lailah da babyn ta. Dama suna fitowa saida ta dangana da sashen Shariffa ta gano Nasir, yana mura ne ba'a son fitowa da shi shiyyasa ta haƙura ta barshi ta dawo.
Umarnin da Mammah ta bata na zuwa ta gyara ɗakin Dadan ya sakata miƙewa, dan a yanzu babu abinda tafi son buƙatar kusanci da shi kamar ɗakin Dada, ta fahimci dukkan abubuwan da take nema suna a ɗakin. Sai da taje ta tattara kayan sharar da duk abinda take buƙata sannan ta tafi. Bayi ta fara shiga domin gyarawa, sai ta samu underwers ɗinsa ajiye alamar zai wanke. Kunya taji ta kamata. Ta duƙar da kai kusan na mintuna uku tana shawarar ta wanke kota barsu a inda ta gani? Wankewar dai akwai ɗunbin kunya a ciki gaskiya, sannan idan ta bari ma tayi gyaran bayin dole zai san ta gani, idan ta tsallake bayin bata gyara ba bata ƙyauta ba, tunda daga shi har Mammah data sakata babu abin rainawarta a ciki.
Da ƙyar ta iya danne zuciyarta ta ɗibesu idanunta a rufe ta zuba cikin worshing machine, ta haɗa ruwan sabulu a ciki ta kunna. Gyaran bayin ta fara, sai da ta kammala tsaf ta dawo wajen worshing machine ɗin daya kashe kansa tun ɗazun ta fara cirosu. Nan ma idanu ta rufe sannan take matsesu ta sake canja ruwa. Sai da ta tabbatar sun mata yanda take so ta ɗauraye ta zuba a dryer ta busar. Sannan ta kwaso su ta fito. A kujera ta ajiye su ta fara gyaran ɗakin shima. Tayi har mopping ta saka turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Har zata tattare kayan sharar sai idanunta suka sauka akan underwers ɗin data wanke. Da kunya ta barsu a wajen yana shigowa ya gani, sai kawai taje ta kwashe ta nufi wadrobe da su dan gyara takai can ta ajiye salin alin. Sai da ta babbuɗe harta gano inda ake ajiyesu sannan tai ƙoƙarin ajiyesu gefe domin fara shiryasu a wajen. Babbar brown envelope dake wajen data ɗorasu ta faɗo, take hotuna dake ciki suka watse a ƙasa. Binsu tai da kallo, sai kuma ta kai duƙe da sauri ganin fuskar Dagger, ba fuskar tasa ce ta ɗauki hankalinta kawai ba ganin wanda suke tare, drivern su ne Malam Buba. Gabanta ya faɗi, tuna itace sanadin haɗa Dagger da malam Buba, ta kuma tabbatar ita Dagger ɗin yazo nema. Sauri-sauri ta kwashe hotunan duka tana kallo. Guda uku duk mutumin ne, ɗaya zai buɗe mota data kasance ta gidan ce ya waigo alamar tabbatar da babu mai kwallon sa, sai kuma dai-dai ya fito daga motar dai, wanda ya fara gani suna cikin motar ne ta gaba aka ɗauka kuma tabbas basu san anyi ba. Sauran hotunan bata gane komai ba, dan wasu mitanene daban.
Bata da zaɓin daya wuce kwashe hotunan Malam Buba da mutum nan da ko sunansa bata sani ba. Dan inta bari Dada ya gani komai na shirinta zai rushe. Gaba ɗaya ta miƙe tana ware iya nasu, sai dai cikin rashin sa'a ta ɗaga rigar jikinta zata saka cikin skirt aka buɗe ƙofar a bazata. Ba ƙaramin daburcewa tayi ba, musamman ganin mai shigowar. Shima da bai san da ita a ciki ba sai yay ɗan tsaii yana kallonta, dan kai tsaye ya gane a firgice take.
Received at 12:22 PM
reacted with ❤Waccan ranar da taga file ɗin nan ne yazo masa a rai. Ya sauke idanunsa ƙasa da take ƙoƙarin cusa abu a jiki. Farin abu ya gani, sai dai bai san minene ba, dan itama da sauri ta saki rigar ganin inda yake kallo.
Nimrah da illahirin jikinta ke tsuma ta aro jarumtar dole ta yafama kanta tana haɗiye yawu masu ƙauri. Cikin gyara yanayin ta ƙwarai da gaske ta ce, “Dada sannu da zuwa. Ina kwana?”. Bata jira amsarsa ba ta juya tana fara ɗaukar underwers ɗin nan.....
Dai-dai lokacin ya ƙaraso wajen, ya tsaya a bayanta gab har tanaji hucinsa. Idanu ta runtse tana karanto addu'ar duk da tazo mata a zuciya. Sai kawai ta fara cusa kayan inda ba'a nan ya dace ba. Hannunta ya riƙo, hakan ya sakata ƙara rumtse ido da cije lips da masifar ƙarfi, ta kuma runtse vest ɗinsa dake a hannunta daya riƙo da nashi.
“Mi kike yi anan?”.
Wani busashshen yawu ta haɗiye da ƙyar, har tana jin kamar yana yanka mata maƙoshi. Da ƙyar ta iya fisgo kalaman bashi amsa da.
“Ina gyara kayan wanki n...ne”.
Kayan hannunta ya kalla na sakanni, sai kuma ya ɗan ja baya daga jikinta. Har tana murnar ta tsira murnar ta koma ciki. Dan kuwa kafaɗunta ya dafa ya juyo da ita suna facing juna. Cikin golden voice ɗinsa dake fita da tsantsar gizago da zurfin iko ya ce, “Buɗe idanun ki”.
Jitai idanun ma sun cika da hawaye kafin ta buɗe. Tadai yi jarumtar haɗiyesu tana sake kame kanta. Koda ta buɗe ta kasa kallonsa gaba ɗaya, sai dai shi tana jin kaifin nashi har a cikin magudanar jininta. Bata san mi yake kallo ba a jikinta, gashi yaƙi yay magana. Ta takura matuƙa saboda kwarjininsa da yanda ya cika mata waje. Jinta take kamar a gaɓar ramin gacci mai matuƙar zurfi, gabanta kuma zaki dake a yunwace ya zuba mata idanu...
“Kayi haƙuri Dada”.
Kalmomin uku suka suɓuto daga cikin bakinta batare data shirya ba.
“Ba sai anyi laifi ake bada haƙuri ba?”.
Idanunta da suka cika da ƙwalla ta ɗago ta kallesa. Zata maida ta risinar ya dakatar da ita cikin umarni.
“Idan suka zubo sai kin kwashesu kin maida.”
Mar-mar ta shiga yi da idanun tana maida hawayen kuwa. Dai-dai yana kai hannu ya ɗaga t-shirt ɗin jikinta baƙa. Dan skirt ne light brown da bai kai mata har ƙasa ba, sai da ya wuce gwiwa sosai, sai baƙar t-shirt ta mata da hoton katon teddy bear a gaban. Sosai kayan sun mata ɗas. Hannu takai da sauri zata hana shi. Ya wani ɗago birkitattun idanunsa da suka sake juyewa saboda halin da yake ciki ya watsa mata. Tare da faɗin, “Zan karya hannun nan”.
Ai da sauri ta janye hannun nata, shi kuma ya ƙarasa ɗage rigar ya jawo hotunan data saƙe a cikin skirt. Maimakon sakin rigar sai ya tsaya yana kallon wani tawwadan ALLAH dake gefen cikin nata babba sosai. Itama jin shiru ta buɗe idanunta, motsin da tai ya saka shi farga shima, sai kawai ya sake rigar yana ƙara tsuke fuska. Hotunan ya fara kallo, guda uku ne, ya zubama fuskar Dagger ido sosai cike da nazari, dan akwai handkachiff a fuskar tashi, ita kanta tsantsar basirar da ALLAH ya bata ne yasa a gani ɗaya ta gane shi. Duk da dai a na cikin mota babu handkachiff ɗin, amma kuma bai fita ba kamar na wajen. Shima ana cikin motar kai tsaye ya gane shi, hakama Malam Buba. Ɗagowa yay yana kallon fuskarta.
“A ina kika gani?”.
Ai ko musu batai ba ta nuna masa envelope ɗin data danne da ƙafafu. Hannu kawai ya miƙa mata. Dole takai duƙe ta ɗakko ta miƙa masa. Ya kalla fuskarta sannan ya buɗe envelope ɗin ya ciro sauran hotunan. Mutane ne mabanbanta har guda shida, yanayin inda aka ɗauka hotunan yay mugun jan hankalinsa. Cikin envelope ɗin ya sake maida hannunsa, sai dai babu komai kuma...
“Waya baki?”.
“Dada wlhy anan na gani”.
Tai maganar tana nuna inda ta ɗauka. Jimm yay na tunani. Tuna da kansa ya ajiyesu jiya ya sashi ɗan furzar da iska. Sai kuma cikin sauke murya ya furta, “Little Shadow kina da hannun ɓarna. Bincike ko?”.
Received at 12:22 PM
Viewed 5 times “ALLAH ba bincike nayi ba Dada. Kawai zan saka kayan nan ne na gani.....”
“Shine kika buɗe tunda kin raina Dada”.
Idanu ta waro sosai da jin furicinsa na ƙarshe tana girgiza kainta. “Wlhy Dada ban raina ka ba, na tuba bazan sake ba”.
Yanda tai maganar hawaye na zubowa ga kunnuwa ta kama ya sashi tsayawa yana kallonta kawai. Dan sai kawai tai masa ƙyau a hakan, har wani babban al'amari na tsarga masa. Dole ya kauda idanun nasa da sauri yana haɗiye yawu. Sai kuma ya bar wajen da sassarfa yana faɗin, “ALLAH ya shirya min ke. Shige ki tafi”.
Ai kafin ma ya rufe baki ta kusa ƙofa, shima sai kawai ya kai zaune yana sake kallon hotunan. A ƙasan zuciyarsa kuwa tunanin yake waye yayo masa wannan aiken?. Hannu yakai ya riƙe goshinsa, sai kuma ya miƙe tsaye ya fara kai-kawo.
Dole yana buƙatar zuwa UNIT ZERO yanzu nan. Hotunan ya maida cikin envelope ɗin, a ya da ya shigo a haka ya sake fita..........✍️
Received at 12:22 PM
Viewed
[16/02, 10:59 pm] null: KIƊA A RUWA 3

18

........Lokacin da Dada ke fitowa babu wanda bai bishi da kallo ba a falon. Dan shi bai kalli kowa ba a cikinsu ya fice. Dama sun zagaye Nimrah ne da tambayar miya faru da ita. Dan yanda ya fito ba'a nutsuwarta ba. Duk da tana ta yaƙin danne kanta kuwa. Sai kuma ga Dada ya fito shima ba'a yanda ya shiga ba. Ko kallonsu baiyi ba kuma ya fice.
Ta tabbatar musu babu komai, badan sun yarda ba suka ƙyaleta saboda Mammah data girgiza musu kai alamar su barta. Sam Nimrah bata cikin nutsuwarta, burinta ta kira Dagger yanzun nan a waya. Sannan tayi magana da Malam Buba. Amma ta rasa ta yanda zata bar falon ma balle yin hakan....

>>>>>★<<<<<

Gudu sosai Dada ke zubawa a titi dan shi ke driving ɗin da kansa. Kusan lokaci guda suka isa da Imran. Kowa na kammala parking ko gaisawa basuyi ba suka nufi hanyar shiga ciki. Daddy Imran ya saka Password ɗin ƙofar, bayan ta gama turance-turancenta daya sakasu matsuwa ta buɗe.
Ko zama basu gama yi ba Dada ya miƙama Imran envelope ɗin. Shima da sauri-sauri ya fiddo hotunan ciki yana kallo ɗaya bayan ɗaya. Sai da ya kai har ƙarshe kafin ya ɗago yana kallon Dadan.
“Tabbas drivers ɗin da suka wuce da kayan can ne. Domin kuwa motocin ne, sannan jejin ne. Waye da wannan aikin?”.
“Wannan shine tambayata Imran.”
“Shi kuma wannan waye? Nagansa tare da Buba driver?”.
Maimakon amsawa miƙewa kawai Dada yayi zuwa ɗakin sirri. Dole Imran ya miƙe yabi bayansa. Anan ma sai da suka saka Password. Suna shiga Imran ya danna wani abu a jikin ƙofar bayan ta rufe, a take haske ya gauraye ko ina. Lallai wannan ɗaki ya tsaru, dole kuma a kira shi da ɗakin sirri. Wani ƙaton bakin allo dake liƙe da hotuna Dada ya nufa, kai tsaye ya ciro wani hoto a layi na biyu ya miƙama Imran.

9 / 11