KIDA A RUWA 3 BY BILLYN ABDUL

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 11

15K to 18K   out of 32K words

na zahiri da suka fito daga yankunan su a sanda suke mulki na shugabanci ko na wani office da suka riƙe.
Received at 12:22 PMReactions: Rasa wazai tunkara yay shawara yayi. Gashi kwanaki uku kacal suka bashi. Yau hatta office yaƙi fita da wuri har kusan sha ɗaya. Wani gefe na zuciyarsa keta kawo masa Zak-Shadow da Imran. Kuma tabbas yana jin gamsuwa da yaran. Dan wannan rikitaccen mulkin baya yiwuwa sai da ɓoyayyun mashawarta. Wlhy badan fidda Haysam da yayi ba da yace shi wannan mulki baiga amfaninsa ba, dan rikicin cikinsa da kitumurmura sun wuce tunanin mai tunani. Wanda ke waje shike kallon shugaban ƙasa a mai zartarwa sama da kowa. Amma a zahiri hotone kawai a kujerar mulki shugabancin ƙasar nan. Ainihin masu mulkar ƙasar suna gefe ne kawai suna busa sigari kalar wadda suke buƙata. Sai abinda suke so, sai abinda sukace dole za'ayi, idan kace zaka bijire su ƙasƙantar da kai a idon talakawan ƙasar a bayyane, a ɓoye su raunana lafiyarka da kuzarinka. Duk mai baka goyen baya su siyesa da kuɗi, idan yaƙi bi shima su ɓatar da shi ko su tsigesa a kusa da kai ɗin. Wannan itace zahirin ƙasar da talaka bai sani ba, wata shari'ar dai sai anje can kawai.
Wayarsa ya ɗauka da mutane masu muhimmanci ne kawai a ciki yay gajeren text ya tura. Daga haka ya miƙe domin shirin fita office.....

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Saƙon shugaban ƙasa ya shigo wayar Dada ne a dai-dai lokacin da motar su ke hawa kan babban titi bayan fitowarsu a cikin asibiti. Dabo ne ke driving ɗin, gefensa Imran. A baya Nimrah sai Dada dake ta aiki da laptop a kusa da ita. Tana lafe ne jikin ƙofa idanunta a lumshe, ji take kamar tai tsuntsuwa ta ganta a gida saboda ɗoki. Duk da dai akwai ajiyayyar damuwa dake danƙare da zuciyarta da brain ɗinta. Amma kamar yanda tai alƙawari zata bi komai a sannu kamar yanda ta fara. Dan a yau ta sake fahimtar gane ainahin Dada ba abune mai sauƙi ba. Dole ta dake, dole ta shirya, dole ta jajirce, dole ta ƙara wayo da taka tsantsan. Sai dai duk da haka maganar auren nan na ɗaga mata hankali. Tana son taji tabbaci a bakin Mammah da sauran Uncles ɗinta da Daddy Imran. Harga ALLAH indai da auren nan batama san yanda zata fassara shiga ukun da take ciki ba. Waye wannan miji? Tana son ta sanshi, ta ƙagara ta sanshi.
Duk halin da take ciki Dada na lure da ita. Dan yanda take yamutsa fuska, ta cije lips, ta matse idanu yasa shi fahimtar akwai abinda take tattaunawa da zuciyarta. Kuma ko minene yana da girma da rikitarwa a gareta. A lokacin da yake ajiye wayarsa dake tsakkiyarsu bayan kammala karanta saƙon Mr President sai yaga tasa hijjab ta share hawaye. Hakan ya sake tabbatar masa da zarginsa. Baiyi magana ba ya cigaba da aikinsa yana sauraren tattaunawar Imran da Dabo akan Ojo da suke ƙoƙarin gano inda yake yanzun...
Gidan Daddy Imran suka fara zuwa domin sauke shi. Nimrah nason shiga taga Ammie tana kuma zumuɗin zuwa taga Mammah. Sai kawai ta saka a ranta tunda weekend za'a shiga zasu zo ita da Ruky. Isowar su gate ɗin nasu gidan sai taji ƙaguwar a buɗe, dan badan Dada bane a motar da tuni ta ɓalle murfin ta shiga da gudu. Amma jikinta sai tsuma yake ta yanda har shi ma ya gane. Aiko Dabo na tsayar da motar ta buɗe ta fice dan haƙurinta yakai maƙura. Dada ya bita da kallo kawai, dan kamar ƙyatawar ido har taje ƙofar falo.
Kansa ya ɗan girgiza yana miƙama Dabo daya buɗe inda yake laptop ɗin daya rufe. Daga haka ya sakko ƙafafunsa ya fito gaba ɗaya. Sauran kayan Dabo ya tattauro, dai-dai kuma isowar maigadi da malam Buba dake noƙewa a baya wajen. Cikin girmamawa suka fara gaida Dadan. Dada ya janye idanunsa daga kallon da yay ma malam Buba na seconds, kafin ya amsa gaisuwar tasu. Suka ɗora da nuna farin cikin dawowar Nimrah, sunata ambaton godiyar ALLAH. Shi dai wajen yay ƙoƙarin bari. Amma sai maigadi ya miƙo masa abinda ke hannunsa yana faɗin, “Af naso na manta. Ranka ya daɗe dama ga saƙo yanzun nan babu jimawa wani ya kawo shi a baka. Dan zanje nakai ciki ne ma kuka iso na dakata buɗe muku ƙofa.”
Received at 12:22 PM
reacted with ❤ Idanu Dada ya ɗan zubama hannun maigadi, sai kuma ya miƙa hannu ya amsa batare da yace komai ba. Yana barin wajen Malam Buba ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi da har sai da maigadi ya kallesa. Kamar zai yi magana sai kuma yay shiru suka koma bakin gate. Sanda da ya shige ɗaki wufff tun buɗe gate da akai ya fito shima sum-sum yana leƙa hanyar sashen Mammah da har Dada ya shige....

Yanda Dada ya samu falon ya kacame da murnar ganin Nimrah sai yama tsaya kawai yana kallonsu. Dan Ruƙayya na rungume da ita tana kuka ana lallashinsu. Su duka biyun suna jikin Mammah. Mu'azz ma sai sharar hawaye akeyi na farin ciki. Shigowarsa tasa su Bilal dake zagaye da su maido hankalinsu kansa. Sai kuma duk suka zaburo cike da farin cikin ganinsa suma. Mammah kanta yau ta kasa dannewa kallonsa take farin cikinta a bayyane. Gwaggo Alawiyya tazo ta kama hannunsa tana faɗin, “Sannu kaji Haysam, ALLAH yay maka albarka. Maza zo ka zauna ansha fama kwana biyu”.
Murmushi kawai yayi yana kaiwa zaune. Ya gaida Mammah sannan su Gwaggo Khadijah. Suma su Ja'afar suka gaisheshi. Kafin wani lokaci Aunty Mimi ta kawo masa ruwa. Dan suma duk suna gidan daga asibiti suke duba Lailah. Mammah tasan duk yanda suke son jin yanda aka samo Nimrah bazai faɗa ba, dan haka ta tambayesa a shirya masa abinci ne. Miƙewa yay yana amsa mata da zai yi wanka tukunna. Ya ɗan kalli Nimrah da Ruƙayya ke bama abinci a baki itama yana bata ya wuce abinsa. Dai-dai Ammar na sakkowa daga kai kayansa ɗaki da Dabo ya kawo. Umarnin kawo masa coffee ya bashi yana wucewa...........✍️
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 09017242889


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

[16/02, 10:58 pm] null: KIƊA A RUWA 3

12

.........“Aunty wlhy Dada ya dawo”.
Zimbur Nabeeha ta tashi daga barcin da take yi tana kallon Rayhana mai maganar. Dan yanzu babu jimawa suka zo gidan ita da Amima. Iske Nabeeha na barci yasa sukai zamansu a falo suna kallo bayan sun saka mai aiki da suka zo da ita yanzun nan shiga kitchen ta musu abinci batare da ko matar gidan sun bari ta san da zuwanta ba. Momy ce tace su kawota kasancewar Nabeehar tayi mata complain a jiya game da aikin gidan. Tasan ragwantar Nabeeha sarai, ita kuma a wannan lokacin bata son a samu matsala kodan First Lady shiyyasa tai gaggawar samar mata da mai aikin, ko muce First Lady ta samar.
“Aunty badai can ɓangaren zakije ba?”.
“To mi kike so nayi Rayhana. Kin san dai mugayen can bazasu faɗa masa na dawo ba. Gara naje da kaina ya ganni.”
“Hu'umm da dai kin bari ya kawo kansa wlhy. Amma kije ai babu aji, bayan kin san shegiyar yarinyar nan tare suka dawo. Ƙilama babu wani saceta da akayi shiyya ɗauketa yaje yasha shagalins.....”
Kallon da Nabeeha ke mata ya hanata ƙarasa faɗa, sai kuma tace, “ALLAH ya baki haƙuri. Amma magana ta gaskiya yanzu fa ba da bace Aunty. Dole ne ki gyara wasu abubuwan musamman zumuɗin nan akansa.” tana gama faɗa ta fice a ɗakin. A ranta kuwa tana saƙa abinda ya daɗe a zuciyarta ne. Dan wannan karon tayi alwashin zatayi yaƙi domin kanta. Bazata iya haƙuri da ciwon dake ranta ba. Sai dai ayi ɗayan biyu. Kota samu, ko kuma kowa ya rasa...
Nabeeha kuwa ƙwafa tayi kawai. Ta nufi bathroom. Babu jimawa ta fito fuskarta jiƙe da ruwa alamar wankota tayi. Gaban mirror taje ta fara gyara fuskar da kayan kwalliya, sannan ta cire kayanta ta canja da wani arnen lass da yay masifar ƙyau ta saka turare sosai a jikinta. Koda ta fito daga Amima har Rayhana da kallo suka bita. Amima data saki baki na mamaki ta ce, “Aunty ina zuwa haka da rana tsaka?”.
“Sashen Mammah”.
Ta bata amsa a taƙaice tana ficewa abinta. Kallon juna sukai ita da Rayhana, Rayhana ta taɓe baki da faɗin, “Kin san bata da wayo sam.”
“To ALLAH ya ƙyauta wannan ai zubar da mutunci ne”. Cewar Amima...

()<>()<>()<>()<>()

Tunda Nabeeha ta shigo falon kowa ya saki baki yana kallonta. Mammah kam kallo ɗaya tai mata ta ɗauke kanta. Koda ta gaisheta ma a haka ta amsa hankalinta akan Nawal ɗin Aunty Mimi. Su Ma'aruff da suka zo wuya zasuyi magana Gwaggo Khadijah tai musu gargaɗi da idanu. Dole sukai shiru. Sarai Nabeeha ta lura da yanayinsu, amma ta danne dan a ganinta basu bane a gabanta. Idanunta akan Mu'azz ta tambayesa ina Dada yake.
Mu'azz ba komai ya sani game da lamarin Nabeeha ba. Duk da dai da wayonsa tabar gidan amma ba komai ya sani ba. Da hannu kawai ya nuna mata sama. Bakuwa ta sake magana ba, ba kuma kunyar kowa balle jin nauyi ta nufi stairscase ɗin tana taku ɗai-ɗai cike da gadara ita ga matar boss.
Aunty Ummi dake jin kamar ta amayo zuciyarta dan takaici taja hannun Aunty Mommy suka shige kitchen bayan tama Mimi signal da ido. Fakar idanun su Mammah tai itama tabi bayansu.
Basu wani jima ba suka fito, hannun Aunty Mimi da tray an haɗa kayan abinci akai. Cikin sa'a dai-dai nan Nimrah da Ruky da Biebah ke fitowa. Nimrah tayi wanka ta canja kayanta. Kuma wando ne fari daya kwanta a jikin nata da riga iya gwiwa Pakistan style na yadi mai taushi. Sai siririn gyale kalar yadin rigar. Babu wata kwalliya a fuskarta sai rosy lips data shafa daya saka lips ɗin taushi da santsi, yay pink sosai, ko daga nesa kake da ita zakaga hakan....
“Yauwa Nimrah zoki miƙama Dada abincinsa”. Aunty Mommy ta faɗa kai tsaye. Ɗagowa Mammah tai da sauri, ta buɗe baki zatai magana Gwaggo Alawiyya ta katseta da faɗin, “Dama yanzu zan yi magana kuwa. Amsa kinji ƴar albarka. Ruƙayya ke kuma zo nan na sakaki aiki”.
Haɗa ido Mammah da Gwaggo Khadijah sukai, Mammah tayi yanayin kai ƙara gareta, amma sai Gwaggo Khadijahn ma tai mata murmushi alamar tana goyon bayan abinda ƴan ta kife ɗin ƴaƴanta ke shirin yi. Kanta ta girgiza kawai tana kallon su Ma'aruff, a mamakinta suma duk sun washe fuskoki ba kamar yanda suka ciskule ba tun shigowar Nabeeha.
Received at 12:22 PM
reacted with ❤ Nimrah dai da ba sanin abinda ya faru sukai ba tuni ta shagwaɓe fuska zata fara langare. Aunty Ummi ta balla mata harara dole tazo ta amshi tray ɗin. Wucewa tai tana ɗan tuttura baki, dan harga ALLAH tana son yin ɗan nesa da shi har sai taji amsar tambayiyinta akan batun nan ɗaya tak daya zame mata ƙayar kifi a maƙoshi....

A wannan lokacin da Nabeeha tuni ta iso ƙofar ɗakin na Dada bayan ta hauro taci karo da Afeef dake fitowa a ɗakinsu shi da Mu'azz ta tambayesa ya nuna mata. Knocking tayi a hankali, sai dai shiru babu motsi balle ta samu amsa. Sanin halinsa yasa ta sake yi har sau biyu, daga nan ta buɗe Kofar kawai ta shiga dan ta kasa daurewa. Da wani irin ƙamshi ta fara cin karo, dan ƙamshin turaren wutar SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. na Maman Abdull ya gama kama lungu da saƙo na sashen Mammah. Sai da ta lumshe idanu ta buɗe tana sauke ajiyar zuciya kafin ta ƙarasa shiga ɗakin. Ko ina fes a gyare, babu tarkace kamar yanda ta sanshi mutum mara son hayaniya. Jin motsi a bayi yasata zama a bakin gadon tana murmushi, babu abinda take hangowa sai yanda zaiyi mamakin ganinta da farin ciki. Ta sake gyara zamanta da ƙyau. A dai-dai lokacin kuma Nimrah data iso itama tai knocking ƙofar. Sai dai jin shiru da sanin halinsa na in ba shi yaso ba bazai tanka ba yasata murɗa handle ɗin ƙofar kawai ta tura ta shiga da sallama.
Wani kalar zubo mata idanu Nabeeha da zuciyarta tai zallo cikin ƙirjinta tayi. Ta buɗe baki zatai magana tana ƙoƙarin miƙewa kawai aka buɗe ƙofar bathroom. Dada da bai san dasu ba su duka biyun ya ɗan yi tsaii yana kallonsu.
Nimrah kam jitai ƙirjinta ya buga, a lokaci guda tai saurin duƙar da kanta. Gaba ɗaya ji take ta daburce, a hakan ma ALLAH ya sota bathrobe ce a jikinsa ba towel ba. Sai dai kuma abinda bata taɓa gani bane daga garesa dole ta rikice. Dan bathrobe ɗin ma dai kaɗan ta wuce gwiwarsa.
Har cikin ransa bai ji daɗi ba shima. Idan Nabeeha ta ganshi a haka normal ne ai, amma Nimrah ina, da sauran lokaci. Jallabiya ya ɗauka batare da yayi magana ba ya juya cikin bayin. Babu jimawa ya sake fitowa da ita a jiki. Abinda ya bashi mamaki har lokacin Nimrah na'a inda ya barta. Kanta a ƙasa ga kaya a hannu kamar wadda aka dasa. Yayinda Nabeeha ke mata wani mugun kallo sai dai itama bata iya tayi magana ba saboda wani curarren abu daya dunƙule mata ƙirji ko numfashi bata fitarwa da ƙyau. Zuciyarta tsara mata take taje ta fisgi tray ɗin abincin ta kife mata shi a jiki, sannan ta kamata da shegen duka har sai ta daina numfashi. Kai itafa da tana da dama ko macen sauro bazata sauka mata a jikin miji ba..
Tana can tunanin ya kwasheta kawai sai hango Dada tayi a gaban Nimrah. Itama Nimrahn daba sanin isowarsa tai ba jin an riƙo tray ɗin hannunta ta ɗago da sauri alamar dawowa hayyaci, dan ya fahimci tsayuwar da tayi tunani ta tafi mai zurfi.
“Kina lafiya?”.
Ya faɗa cikin zurfin lafazi daya sakata jin wani sanyi ya dira tsakkiyar kanta yana bin jijiyoyin jikinta yana sauka har ƙafafunta. Slowly ta ɗago idanun da suka kaɗe sosai da ja a ciki, kasancewar shima ita yake kallo sai suka shige cikin nasan har sai da yaji wani dummmm a ƙirjinsa. Dai-dai lokacin Nabeeha ta matso kusa da shi, cike da salon daya ƙona ran Nimrah kawai ta rungume shi ta baya tana kwantar da kanta a faffaɗan bayan nasa. Cike da shagwaɓar iskanci ta furta, “I miss you baby”.
Gefe Nimrah tai da fuskarta tana lumshe idanunta da suka cika da ƙwalla. Dan wani suka da ƙirjinta yayi zata iya rantsewa tunda tasan kanta bata taɓa jin irinsa ba. Gaba ɗaya taji duniyar ta mata ƙunci, wani irin tsanar Nabeeha da haushin Dadan suka zagaye ƙirjinta batare data san dalili ba. Bata motsa ba a wajen da take balle nuna alamar zata fita tabar ɗakin kamar yanda ta fahimci Nabeeha naso, sai ma ji tai a ranta saita baƙanta mata rai itama, sannan wlhy bazata bar ɗakin nan ba yau sai da su zauna su ukun, in banda iskanci da ballagazanci miye na wani rungumeshi a gabanta, ai ko ba komai shi uba ne, yakamata itama ta mutunta kanta a gabansu dan su bata irin darajar da suke bashi koda bata da ita
Received at 12:22 PMa zahiri kamar shi. Amma tunda tace ita ta iya yanzu zata nuna mata shege ma da ubansa ba aruwa ake shawosa ba. ALLAH saita gogema matar nan hadda yanzun nan. Idan ita mijinta ne ai suma Babansu ne.........✍️

Tofa Madam Nimrah mutum da matarsa. Tunda kin yarda ita mijinta ne ku babanku ne basai ki fita ki barsu su jiƙa kansu ba🥱. Anya kuwa kikaji shine mijin ba akwai yaƙi ba? To bari muga ya wasan zai kaya a yanzu💃💃🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️☺️.
Received at 12:22 PM
[16/02, 10:58 pm] null: KIƊA A RUWA 3

13

.........Dada shi kansa jiyay wata kunya mai tsananin ta rufeshi. Haba shi girma abin a riƙe ne ai. Baiyi ma Nabeeha magana ba amma ya zame jikinsa daga nata, yana nufar kan center table ya ajiye tray ɗin abincin. Yazo ya sake raɓasu ya wuce gaban mirror, wayarsa ya ɗauka ya sake gittasu dai again ya koma kan sofa ya zauna.
Nimrah dake ƙoƙarin controling ɗin kanta ta kalli ƙafafun Nabeeha dake tsaye itama kamar an dasata, da alama abinda yay ɗin ya ɓata mata rai ne ko wani abu oho mata. Kawai sai taji murmushi na neman kufce mata

6 / 11