KIDA A RUWA 3 BY BILLYN ABDUL

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   11 / 11

30K to 32K   out of 32K words

rayuwata da zuri'ata ba dan ALLAH ya tattara yaransa su koma. Wai ki duba video cikin yaran nan wani ya ɗauka na Muhammad da Nimrah, shine yazo yana zancen banza akan hakan. Wai Muhammad na neman Nimrah...” babu wanda bai razana ba a falon, Mammah ta cigaba da faɗin, “To bari kaji kai da masu ɗaukar Videon ko zaku dawo cikin hankalinku. Nimrah MATAR Muhammad ce. An ɗaura musu AURE tun tana da shekara bakwai. Sai ka sake wani shirin”.
Received at 12:31 PM
reacted with ❤ Wani irin duka kan Nimrah yayi tamkar an saki irin tsawar nan mai girgiza gari a cikin tsakiyar ruwan da ke sauka da manya-manyan ƙanƙara. Kalaman Mammah suka wani irin sake maimaita kansu a cikin illahirin duk wata ƙofa dake amsa suna ƙofa a cikin jikinta. (Nimrah MATAR Muhammad ce. An ɗaura musu AURE tun tana da shekara bakwai). Ai sai kawai tayi luuuuu zata zube. Da wani irin ihu su Ruƙayya da sukai sumar tsaye dan suma kalmar ta dake su da girgiza su suka zabure kanta. Sai kuma suka tsaya cakk sakamakon ganin Dada da babu wanda zaice ga sanda ya shigo falon, da ga gefensa Daddy Imran ne. Nimrah da ta tafi zata zube ya tare da jikinsa. Yana tsaye ne ƙyam akan ƙafafunsa, hannunsa ɗaya tallefe da bayanta saboda tareta da yayi, ɗayan na cikin aljihu. Sai dai idanunsa da sukai masifar juyewa da wani irin hargitsatstsen yanayi tsaye suke ƙyam akan Uncle Tasi'u da shima ya juyo wajen kamar su Mammah saboda ihun Mu'azz da Ruƙayya...
Tuni Hanoon da Afeef da Dayyan dake laɓe sun fito suma. Ganin Dada da basuyi zato ba tunda sun san tun jiya baya gidan tuni ya firgitasu. Dan Afeef ya jiƙe sharaf da zufa ga icayi na neman kufce mas a wando.........✍️

Afeef tsuntsun da yaja ruwa ba shi ruwa ke doka ba🤣. Ka ragema su Mammah aiki 🥱🚶👌..........A hankali Daddy Imran da shima ke kallon Uncle Tasi'u cike da ɗunbin mamaki dan duk abinda Mammah ta faɗa a kunensu ne. Shigowar su Nimrah babu jimawa suka shigo. Hakan ta faru ne kuma saboda su ta gaba suka shigo, su Nimrah kuwa daga sashen su Ma'aruff ta kofar baya suka shigo. Dan haka basu san da zuwansu gidan ba.
Idanun nasa da shima suka kaɗe ya janye daga kan Uncle Tasi'u ya maida kan Dada. Yasan waye Zakinsa, dan haka ya ɗan sauke numfashi da kai hannu ya akan kafaɗarsa ya ɗan bubbuga alamar lallashi. A hankali kuwa Dada ya juyo ya zuba masa idanun nasa, sai kuma ya lumshe su ya sake buɗewa. Batare da yace ma kowa uffan ba dai-dai Uncle Tasi'u da jikinsa ke rawa na zaburowa da nufin zuwa inda yake lips ɗinsa na motsi alamar magana zai masa kawai Dada ya ɗaga Nimrah dake a sume cak yau wucewarsa.
Ai ba Mammah data san halin kayanta ba hatta su Gwaggo Khadijah sai da suka ɗan waro idanu waje. Dan asalin manna wulaƙanci gangariya da babu gauraye Dadan yay ma Uncle Tasi'un. Imran ya duƙar da kai yana danne murmushin dake neman suɓuce masa da ƙyar. Sai kuma ya ɗan sake ɗagowa ya kalla Dadan dake haura staircase da wani irin salon ainahin jarumai. Sai ka rantse ba mutum ya ɗauka ba, dan babu alamar yana jin nauyinta duk da tana a sume ne....
Da wani irin sauri itama Nabeeha ta dafe kanta dake sara mata, sai kuma tai ƙoƙarin riƙo Ruky dake kusa da ita. Da sauri Ruƙayya ta juyo, hakama kowa na falon da sai yanzu suma suka farga da ita. Ashe itama komai a kunnen nata ya faru, dan su Amima na balcony na sashenta motar su Dada ta shigo, shine Rayhana ta kirata a waya ta sanar mata. Sai ko gata ta fito da hanzari, sanda take fitowa su kuma har sun kusa sashen Mammah. Sun shigo kenan itama ta afko amma taja ta tsaya ganin abinda ke faruwa alamar babu lafiya saboda ganin Mammah na kuka. Sai kuma ga bayani taji kamar yanda kowa ya ji. Zuciyarta na neman tarwatsewa duk da tasan wannan amma sai taji kamar ita Mammah ke ma bitar tunatarwar mijin Haysam mijin Ninrah ne ƴar cikinta da da'ace tana zuwa gidan ta samu ciki zata haifi kamar Mu'azz ne. Dai-dai ta ɗago zata kalla Dada dake gabanta kaɗan kawai taga ya matsa da wani irin zafin nama ya taro wadda keta gabansa kaɗan Da sai da ta faɗa jikinsa sannan taga fuskar Nimrah. Sai kawai taji numfashinta ya ɗauke komai ya tsaya mata cak, shine bata dawo a hayyacinta ba sai yanzu, duk da yanzun ma a wani yanayi ne saboda ganin abinda Dadan ya aikata kuma ko'a jikinsa ya ɗauki ƴar yarinya a hannu a gaban kowa ya haura sama inda kowa yasan ɗakinsa zai kaita.....
___

A dai-dai kuma wannan lokacin cikin hikimar UBANGIJI wani al'amari mai girgiza ƙasar da al'ummar cikinta, dama ɓoyayyun munafukai yay amsa kuwwa. Domin kuwa bayani ne mai girma, mai tsauri, daban al'ajabi ya fita daga fadar shubagaban ƙasa akan sunayen waɗanda aka bama muƙamai masu daraja da kima da zasuyi aiki a wannan gwamnatin tasa.
Akwai manyan ministoci guda takwas da sunansu ya fara fita, sai babban sakatare. Sai NATIONAL SECURITY ADVISOR (NSA) . da CHEF OF STAFF. Ba muƙaman ne suka girgiza ƙasar ba, sunayen mutanen da aka bama muƙaman biyun ƙarshe ne. Mr. Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi is appointed as the (Chief of Staff to the President). & Mr. Imran Abbas is appointed as the National Security Advisor (NSA).

Gan-gan-gan-gan. Wannan fa shine ainahin tashin bomb mai kai goma sha biyu. Shugaban ƙasa kuma na kammala bada umarnin sanarwar dan tun jiya ya rattaɓa hannu a gidansa yau ya ƙaddamar a yanzu kuma ƙarfe huɗu na yamma. Yana badawa kuma yay shigewarsa gida. Gashi yau juma'a ce, za'a shiga hutun weekend.
Wannan fa shine (Tarwatsa wara wari jikan Tafida!, rai ya daɗe rai yayi ma alfarma. Kaga mazan aiki sun zo. Ya cika sittin mai ban mamaki🔥....) Aba Nasiru Sarkin waƙa shawara ya yoma shugaban ƙasa Yusuf Shu'aibu Tafida irin wannan waƙar sak ta sarkin Kano shima. (Kai ku bamu kiɗan janaral a sama. Masu gudu su gudu, sai Baba Tafida, sai Baba Tafida. Bana dai janar shine a sama... Amma a KIDA A RUWA..... Masu gudu su gudu.
Received at 12:31 PMKu faɗama shaggun can su ware💃💃🥱😂🤣).

Tabbas Janar ma KIDA A RUWA ne MAI TADA HANKALIN DODONNI

Jama'a to ALLAH ya taroni🥺, sanyi fa ya kankama sai kun haɗa da haƙuri magana ta ALLAH. Yo irin wannan waƙoƙi haka kamar babana ne Janar ɗin🥱😎🥶🧑‍🦯.

•••••••••••••••••

“Amma kai Mole wawa ne, jaki ma dabbul arab. Shine sai yanzu kake gaya min?”.
Wani irin tafasa zuciyar Malam Buba ta shiga yi a cikin ƙirjinsa. Ya kalla Dagger da idanunsa da suka kaɗe jazur saboda yanda kalamansa sukai masa zafi matuƙa. Amma sai ya danne a kan harshe ya furta. “Oga ya kake so nayi?. Tun jiya da Uwa ta faɗa min fa na baro gidan nake nemanka. Yanzu haka kalla jakkata anan na gama yanke binka sansani idan har ban sameka na ƙarshen nan ba. Sai kuma nayi sa'a kaga saƙona kazo.”
Gaba ɗaya Dagger ji yake kamar kansa zai tarwatse dan tashin hankali. Ya dunƙule hannu da masifar ƙarfi ya daki bangon ɗakin Malam Buba yana wani irin ƙaraji daya saka Malam Buba zaro idanu yana kallon ƙofa. Duk da saida ya rufe windows da ƙofar tunda Dagger ya shigo yana tsoron wani yaji ihunsa a gida... “Oga kayi a hankali mana kada wani yaji. A ganina ba rikita kai bane mafita. Tunanin abinda ya dace. Kasan dai tunda Uwa tace taga hoton nan mutumin nan bazai ƙyale mu ba. Dole zai fara bincike akanmu......”
“Shiyyasa nace kai wawa ne Mole. Idan kai jaki ne shi ba irinka bane ai. A zatonka zai mance da fuskata ne har ya zauna wani bincike a kaina? Kaima badan wannan gemu da sajen ɓadda kamar daka sanya ba da wannan fentin da kake ma kanka an gaya maka bazai gane ka ba ne tun a ranar farko? Ko a yanzu na fara tantamar guy ɗin nan bai gane ka ba, ya barka ne kawai a cikin takunsa.”
Tsuttt fitsarin tashin hankali ya zubo jikin Mole. Jikinsa na karkarwa ya ce, “Amma Oga miyyasa baka taɓa faɗa min haka ba?”.
Wata muguwar Harara Dagger ya zuba masa kawai, batare da yace komai ba ya hankaɗesa ya buɗe ƙofar ɗakin ya fice abinsa. Ai gaba ɗaya sai Mole ya sake jin gudawa ma na neman zubo masa ba fitsari ba. Tuni ya zabura ya ɗauki jakarsa da dama ya haɗa komai nashi yabi bayan Dagger. Yana fitowa ya samu har ya shiga mota. Ai shima sai kawai ya buɗe ya shige wufff kusa da shi. Ko kallonsa Dagger baiyi ba ya tada motar yabar ƙofar gidan a guje.....

<<<<<<%>>>>>>

“Tabbas Oga magana ta tabbata. Nimrah matarsa ce. Dan yanzun nan Mammah ta faɗa da bakinta a gabanmu. Sakamakon cikin baƙin yaran nan sun naɗi video sun turama babansu cewar Dada na nema Nimrah. Shi ne shi kuma ya ɗakko ƙafa ya taho, yanzu dai haka shi ya ɗauketa yayi ɗakinsa da ita. Nan kuma falon ya birkice ga matarsa nan uwargidansa ta yanke jiki ta faɗi tana abu kamar mai farfaɗiya ƙannenta sun ɗauketa zuwa sashen ta”.
“Hummm kice anzo dai-dai inda nake so?”.
“Anzo kuwa ƙwarai da gaske Sir!”.
“ALLAH yay miki albarka, sai ki kasance cikin shiri dan aiki ki gab yake da fa ƙarewa. Lokacin bayyanata yayi.”
“In sha ALLAHU Sir”.
Ta faɗa cikin ƙamewa da salute ɗinsa tamkar tana a gabansa ne. Shima daga can sai ya saki murmurshi da jinjina mata kansa tamkar yana a gaban nata ya ce, “Proud of you dear”.
“Thank you Sir! Proud of you too.”
Murmurshi kawai yay mata da har taji fitar sautinsa a cikin kunneta, daga haka ya yanke wayar, itama sai ta ajiye tana sauke ajiyar zuciya. Sai dai kuma cak numfashinta ya ɗauke sakamakon fitowar ƴar uwarta daga bayi da bata san da ita ba. Yanda take kallonta cikin ido ya sakata fahimtar duk taji wayar tata. A rikice ta zabura kanta, sai dai da sauri ta ɗaga mata hannu alamar karma tazo gareta. Dole ta tsaya cak suna kallon juna tamkar tsaiwar zakaru...........✍️

Tooooo barkanmu da juma'a. 🥱Dada ya shige da ƴar mutane marainiyar ALLAH ɗaki.

Ga shugaban ƙasa yayi bombing zukatan munafukai🔥😉🤏.

Ga Dagger da Mole a kwale-kwale😂🥱.

Ga Nabeeha uwargida mai capacity na farfaɗiya🥺🤕.

Ga Uncle Tasi'u da ƴaƴansa a lukutar masifa😱.

Ga ƴar leƙen asirin mai aiki a ƙaulani🥺🥶.

Kai wannan sati yazo da alheri🤭.
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 09017242889


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

11 / 11