Author : Hafsat C Sodangi Category : KDP NOVELS
tare da na yi wani kuzari ba.
Shi kenan ta faru ta kare wai an yi wa
mai dami daya sata. Aurena ya mutu a kan
karatuna gashikuma karatun yana nema ya gagara.
In ba wani ikon Allah ba. Dare ya yi
nisa bacci ya ce bai san idona ba sai juyi
nake yi a kan 'yar katifar tawa.
Zamana da Ishak ya rinka dawo mun a
raina rashin yanci na walawa da
mu'amalla da fargaba a kowanne lokaci.
Kamar ba aure ba. In ban da ma zuciya
banga abinda zai sa har sakin da yayi mun
ya daga mun hankali ba.
Matsalar daya ce, Babana da yaja ya
tsaya akan ba zan koma Makaranta ba.
65
Ba dai a gianshi ba. Idan na auri wani
mijin yaga zai bar ni na koma Makaranta
to wannan a tsakanın mu.
Haka kawai naji zuciyata tana bani
shawarar zuwa birnin kudu nayi Azumin
Ramadan a can.
Don haka tun kafin Babana ya fita na
sanar da shi, na kuma yi sa'a bai hana ni
ba.
Ya ce,"Yaushe ki ke son tafiya? Na
ce, "Ko zuwa nan da kwanaki uku." Ya ce,
To." Ya shiga daki ya fito ya ce, To ungo
rike kiyi kudin mota sai kiyi manejin su.
Na ce, Lah, Baba ai fna da kudi, ya ce
eh karbi dai ki kara. Nayi godiya. Umma
ta shiga kokarin hada mun kayan tsaraba
irin su omo, sabulun wanka, sabulun
wanki, sugar, maggi da dai sauransu tunda
Su karkara ne.
Shiryawa nayi don zuwa kasuwa saboda
SIyayyar da zan yi na tafiya.
66
Kwalliya sosai nayi ban kuma san
dalilina na yin hakan ba. Doguwar riga na
saka mai fadi sai dai girmanta yabi jikina
saboda santsi da laushinta.
Hannunta shima mai matukar fadi ne
amma ya tsinke a daidai wuyar hannun.
Rigar ribi biyu ce samanta bulu ce mai
shara-shara da ake iya ganin na kasanta
wanda yake ja.
Sai adon da aka yi ana saman shima da
jan zare da kuma hannun rigar.
Na dauka jan gyale na yane kaina dashi
na saka jan takalmi da kuma karamar jaka
itama jar kala.
Na kalli kaina a madubi na tuna ranar
da Ishak ya kawo mun rigar da kuma uban
tashin hankalin da na gani a ranar.
A dalilin bakin da ya dawo ya same ni
da su wadanda suka zo daga Birnin Kudu,
kannen Babana.
Nayi saurn kawar da tunanin lshak daga
cikin raina, don gudun samun matsala, na
67
kamo hanyar fita a dakin, a zuciyata ina
addu'ar samun miji mai hali sabanin na
shi, wanda zan yi mu'amalla ta kwanciyar
hankali da shi cikin farin ciki da jin dadi.
Shi yasa kuma a yanzu ko kadan na
daina jin haushin irin sakin da Ishak ya
yimun, fatana kuma shi ne ya zamo mun
alheri.
Na fito tsakar gida Umma tana bina da
kallo. Zuwa can ta ceYanzu nan wannan
kwalliyar duk ta zuwa kasuwan ce?
Nayi murmushina ce Ta yi yawa ne
Umma?
Ta ce, "A'a je ki Allah ya tsare." Na ce,
Amin. Ina Tasi'u ya raka ni? ta ce, "Na
aike su gidan Mama Tambaya su bi min
bashina, amma sun kusa daowa ma."
Na ce, "To bari na gani ko zan gansu a
waje.
Tun ranar da na dawo gidanmu da
takardar sakin aurena ban kara leka koda
68
kofar gida ba ne ballantana nasa kafata na
fita.
Hakan ne yasa ni tsayuwa a kofar gidan
ina bin layin da kallo, ina kuma wasu yan
tunane-tunane a raina.
Na irin yadda unguwar ta canza gaba
daya tun daga lokacin aurena shekaru
hudu da suka wuce zuwa yau dinnan.
Karab! Sai kawai muka yi ido hudu da
Abdussamad wanda daga ganin irin kallon
da yake yi mun na gane ya dade yana
kallona bá tare da na ganshi ba.
Sauri nayi na sunkuyar da kaina ga
barin kallonshi, sai dai hakan bai hana ni
ganin canjin da ya samu ba.
Ya kara tsawo yayi haske sosai sannan
yayi 'yar kiba daidai ba mai yawa ba.
Wacce ta sanya shi ya yi kwarjini, ba
kadan ba. In da da hali to da na fasa. fitan
da nayi niyya.
69
Sai dai zai yi mun wata fassara haka
nan dole na gayawa Umma abinda ya hana
ni fita tunda har mun yi sallama.
Wuce shi nayi, nayi tafiyata bayan nayi
iyakacin kokari na ganin tsananin kallon
da yake yi mun bai harde ni na fadi ba.
Tafiya nake yi ina tunani a raina nasan
Abdussamad ya ji maganar mutuwar
aurena.
Don kuwa a unguwarmu kaf babu
wanda bai ji ba. Wani babban shagon saida
kaya na shiga saboda daukan hankalina da
shagon yayı.
Rabon da wani abu ya kawo ni kasuwa
tun kafin aurena da Ishak, don kuwa shi
baya ba ni kudin komai kawowa yake yi.
Wani dan saurayi ne ya karaso inda
nake tsaye saboda girman shagon yasa na
kasa fahimtar inda zan dosa.
Barka da zuwa Hajiya, me ki ke so?
Lokacin ne na fara kallon yadda aka
kakkasa shagon gefen takalma da
70
jakunkuna daban, haka na leshi haka na
atamfa, haka na material da kuma shadda.
Na dawo da kallona ga yaron saboda
kada na bata mishi lokaci, duk da akwai
masu sayar da kaya a shagon irin shi masu
yawa na ce atamfa.
Ya ce, "Babba ko karama?" na ce,
"Kanana za ka bani guda hudu." Ya ce,
To ga wuri zauna bari naje na kawo
miki."
Na zauna a kan kujerar da ya bani ina
kallon mu'amallar kasuwanci yadda take
tafiya a shagon da irin mutanen da suke
shiga suke fita.
Yaron ya dawo rike da atamfofi guda
hudu na duba na ce, "Sun yi." Na mika
mishi wata na ce ya karo mun irinta guda
daya.
A raina kuma ina tunanin wadanda zan
baiwa. Kakata Baba Ladi da kishiyoyinta
guda biyu, sai matan Yayun Babana biyu.
71
Sai kuma kanwar Babana. Ya dawo na
tambaye shi kudin ya fada, nasa hannu a
cikin jakata na mika mishi yayi godiya
yana saka mun a babbar jakar su ta shagon
mai dauke da suna da adireshin shagon.
Yana kuma tambayata ko za ki duba
gefen mu na takalma ne? kamar naki sai
kuma na bishi ina dubawa.
Wani takalmi yayi matukar daukan hankalina, na dauke shi ina dubawa na
tambaye shi kudin ya fada mun.
Na mayar na ajiye yana gaya mun ai da
kin dauüka Hajiya "zai matukar yi miki
kyau, saukinshi na fada miki, in kin duba
da kyau. za ki gane asalin takalmi ne dan
Italy.
Na ce, Eh na sani wani lokaci nazo na
saya amma ba yau ba."
Na fito daga shagon don ci gaba da
Siyan abubuwan da nake bukata na káina.
"Hajiya! Hajiya!! "
72
Nayi maza na waiwaya saboda wani
mutum da yayi mun alama da cewa ana
kirana.
Yaron da nayi sayayya a shagonsu ne
"Lafiya? na tambaye shi. "Ki zo in ji
Maigidana."
Na. ce, Maigidanka kuma?" ya ce, Eh.
gabana ne ya y1 mummunan faduwa.
Na ce, Ina ce na baka kudinka? Na
tambaye shi saboda tunanin da yazo mun
raina.
Ya ce, Eh ban san dai dalilin kiran naki
ba, ki dai taimaka din kizo tunda kin gani
nima dan aike ne."
Juyowa nayi na biyo bayan yaron nan
zuwa shagon su.
Mutumin yana zaune a can wani
kebantaccen wuri da aka tanada a shagon,
amma daga wurin kana iya ganin duk wani
abinda ake yi a cikin shagon.
Kammalallen mutum mai kwarjini mai
matsakaicin hasken fata da tsawo. Kamalar
73
shi ce tasa na dan rusuna a lokacin da zan
gaishe shi.
"Lafiya yanmata, kiyi hakuri fa naga
kamar kin dan damu ina fata ban takura ki
ba ko?"
A lokacin ne naji na dan sake saboda
tunane-tunanen da nake tayi a zuciyata, na
game da kiran Wata alfarma nake nema
kiyi mun."
Na ce, Kamar ta me fa? ya ce Lambar
wayarki za ki taimaka ki bani.
Nayi shiru saboda yadda abin ya yi mun
wani iri. Don Allah. Lafuzzan shi da ya yi
amfani da su suka hana ni bijirewa bukatar
tashi.
Don kuwa ban san mu'amalla ta roko a
tsakanin mace da namiji ba.
Yayi godiya na juyo na wuce, yaron
nan yana ta harkokinshi ya ce sai anjima
Hajiya, na ce Yauwa.
Ban wani dade a kasuwar ba na gama
siyayyata na kamo hanyar dawowa gida.
74
Sabanin dazu da Abdussamad yake
tsaye a kofar gidansu a yanzu tsaye yake a
kofar namu gidan, hannayenshi duka
biyun zube cikin aljihunshi.
Babu yadda zan yi na shiga gidan ba
tare da ya katdce hanya ba. Ban san me zan
ce mishi ba, hakanne yasa naja na tsaya
don ya fahimci ina da bukatar shi din ya
kauce mun a hanya.
Ban ga alamar yana da niyyar yin hakan
ba, na daga ido na kalle shi shima ni yake
kallo kuri kamar bai taba ganina ba.
Ban ce mishi komai ba amma sai nayi
nufin rabawa ta gefe na wuce. Ya sake
tarewa.
Hakan yasa na fahimei neman magana
yake yi, don haka na juya kallona ga wasu
yara can gaba da mu da ke guje-guje suna
wasan ojiyo jiyo.
Dama nasan wata rana zata zo, ranar
da zan fuskance ki gani ga ki don na gaya
75
miki cewa a wancan lokacin zabin da ki ka
yin kuskure babba ki ka tabka.
To gashi ko lokaci mai tsawo ashe ba za
a yi ba ranar zata zo. Mata irinku masu
kwadayi da kallon kyalkyalin mota a mafi
akasarin lokuta abin da ke faruwa da su
kenan.
Ba zan mance bakin cikin da ki ka sa ni
ba, bakin cikin da da kyar na samu ya bar
ni, bakin cikin da ya yi mun sanadin
abubuwa masu yawa.
To amma na gode Allah ko ba komai
kema yanzu gashi nan kin gani ya gama
cin amfaninki ya kore ki ya mayar da ke
tokumbo 'yar kwatano."
Ganin da nayi Abdussamad ba shi da
niyyar tsayawa da maganganun banzan da
yake ta jero mun yasa ni dakatar da shi
cikin sauri.
Na ce, Kayi kuskure da ka dauka
tokumbo bata da daraja, don kuwa akwai
wata tokumbon da ta fi sabuwa daraja.
76
Misali, Tokumbon mota kirar America
da kuma Tokumbon mota kirar China kaga
kamar yadda kwarin su ba ya zama daya
haka ko da suke na hannu farashinsu ba
daya ba ne.
Kuma ka godewa Allah da ya taimake
ka ya rufa maka asiri da a lokacin ba ka
tunkare ni da wata magana ba.
Don kuwa da jinyar bakin cikin da kayi
ka warke da kyar da har yanzu kana yi
bata kare ba, don kuwa babu abinda zan yi
da kai ko a da can ballantana a yanzu da
aka yi iska asirin kaza ya budu."
Naja mishi wani dan banzan tsaki
sannan na ce Da ka ke cewa naga mota
nabi kyalkyali kudi banza ne?
Kaima kayi mana kaga kenan har a
yanzu kai din ba tsarata ba ne. Na raba ta
gefenshi na wuce na shiga zauren
gidanmu.
77
Na dan tsaya sai da na dan ji nutsuwa
saboda barin da jikina yake yi sannan na
shiga gida.
Ban so haka ya shiga tsakanina da
Abdussamad ba, amma ko ma dai menene
shi ya fara.
Sammako nayi don kuwa karfe goma na
safiya na isa tasha tare da rakiyar Yaya
Auwalu.
Karfe uku daidai kuwa muna tasha.
Sammani shi ne yaron wan Babana da
yazo daukana a tasha.
Saboda dama tun da motarmu ta tashi a
tasha nayi waya na sanar da su zuwana.
Saurayi ne da zai kai shekaru ashirin ko
zuwa da biyu. Ba karamar karba na samu
ba daga wurin Kakata Baba Ladi da sauran
kishiyoyinta ba.
Baba Jummai da Baba Iya da kuma
sauran matan gidan baki daya.
78
Babana mutum ne mai dangi, don kuwa
maza ne da su sOsai haka nan yawancinsu
daga mai mata b1yu sai mai uku ko hudu.
Da wuya matuka kaga mai mata daya
sai dai ko yaro. Haka nan 'ya'ya ne da su
masu dumbin yawa.
Wasu daga cikinsu suna zaune ne a
cikin gidan da iyalinsu, yayin da wasu da
suka sanmu hali sun yi nasu a waje sun tare.
Don haka gidan su Babana babban gida
ne na gandu.
Kakata Baba Ladi ita ce mata ta biyu a
wurin mijinta, Dattijuwa ce da a kalla ta
doshi shekaru tamanin a duniya, amma
saboda irin kirar karfi da Allah ya yi mata
har yanzu din nan da karfinta.
Uwargidanta ta dade da rasuwa, haka
nan ma Maigidan gaba daya don kuwa mu
ba mu ma san shi ba.
Kafin nayi wanka na ce zan rama
sallolina da aka biyo ni tuni kwanukan
79
abinci sun kusa cika tsakiyar dakin Baba
Ladi.
Na idar da sallah itama tana miko mun
furar da ta dama mun da hannunta, tana
cewa "Fara shan wannan ki warware yan
hanjinki tukunna."
Na ce, To. Ina shan furata tana
tambayata labarin Ummana da 'yan uwana
ina gaya mata.
Ta ce, Ikon Allah! Ashe ke kuma
wannan aure naki haka ya kasance? Na ce,
Eh Baba Ladi ki taya ni da addu'a hakan
ya zamo mun alheri.
Ta ce, To amin hakan ne kam yafi
amma wai! Alamar tana jinjina abin
mutuwar aure ai ba karamin al'amari ba
ne.
To shi ina dan naki yake? Na ce, Ya
karbe shi. Ta fara zata yi magana na ce
Baba Ladi bar maganar Ishak bana so.
80
Ta kalle ni ta ce, To na bari 'yar, nan,
maganar dai kam babu dadi. Na ce, Yauwa
ashe kin gane kenan.
Na jawo kwanon kwadon zogalen da na
gani ya bani sha'awa saboda wadatar kuli-
kuli da su tumatur a ciki na fara ci.
Ta ce, "To ba kin gama idda ba har
yanzu ba ki fara zawarwa ba ne? na ce, Na
fara to ina suke? Na ce suna nan.
Na mike na fito saboda a yanzu babu
abinda na tsana irin naji ana kirana
bazawara.
Da alama hirarmu da Baba Ladi ba za ta
rinka yin tsawo ba.
Dakin Baba Jummai na shiga duk da
mutanen gidan sun zo mun gaisa nayi
nufin kuma na zaga su gaba dayansu.
Baba Jummai jika take yi da ni sosai.
Ta kalle ni tana balla goronta ta cc, To ke
kin je in kashe aurenki, ga 1azan naki duk
sun kare sai kawai kiyi zamanki a nan
muyi ta lallabawa.
81
Nayi dariya na ce mata, Kada ki damu,
kwanan nan zan ballo miki wani darjeje ki
sha gara har ki ture.
Ta ce, Wayyo yan nan gamu nan dai.
Daga nan dakin ta hudunsu na shiga Baba
Iyalele kafin na gama zaga gidan Magriba
tayi.
Don haka daga nan alwala nayi na wuce
dakin Baba Ladi don yin sallar Magriba.
Harkokina nake yi cikin walwala da
sakewa ga iyayena maza kowa ya fita
kasuwa ko gona ya dawo zaka ji ana ina
"Hauwa Kulu?
Kowa da irin tsabar da yake riko mun.
Da safe kuwa to zan yiwa Baba Ladi aikin
gyaran wurinta na tsabtace shi.
Na cika mata randunan ruwanta na
kuma wanke mata kayanta na sakawa.
Haka ma sauran abokan zaman nata.
Matan gidan kuwa zaka ji suna ina Kulu
take ta taya mu kaza...ina jin Baba Iya
82
rannan tana korafin basa barina ina hutawa
amma ni kam ko a jikina.
Sammani kuwa babu inda bai zaga dani
ba a cikin gari, gidajen yan uwa na waje
da kuma yan kananan kauyukan da yake
kai kwan kaji.
Kafin na cika sati biyu sai kawai aka
fara sallama wai ana kirana zance. Wasu
ko sunana ba su sani ba sai ka ji yaro ya
shigo wai ana sallama da bakuwa.
Haushi ya kama ni ba kadan ba, ban san
yadda aka yi naja wa dan aikan wani dan
banzan tsaki ba na ce, Je ka ka ce ba zan
zo ba, kada kuma su dame ni.
Baba Jummai ta rarumo muciyar tukin
tuwonsu ta nufo ni wai zata fasa mun kai.
Inna Hadiza matar kanin Babana ta ce,
Haba Baba, ai sai ki nakasata. 1Ta ce, To ba
shi kenan ba magana sai1 ta kare.
Ja'irar yarinya kowa yayi sallama ta yi
tsaki kin kaso auren naki ne ki zo ki zaune
wa mutaneki rinka jawo musu
83
maganganun mutane da ba a iyar musu sai
sun tanka?
Ina ce gayar gidan Malam Akawu
kwanaki da aurenta ya mutu washegarin da
ta gama lddarta aka daura mata aure da
mijin da ko ganinshi bata taba yi ba
saboda ta san darajar iyayenta.
To ki raba ni da wannan rashin
mutuncin da ki ke yi wa mutane, idan ba
so ki ke nasa iyayenki su nemo miki miji a
garin nan su aurar da ke ba.
Tsit nayi jikina a sanyaye kuma na
shiga daki na kwanta don nasan zata rina.
An kama azumin watan Ramadan ne
ranar Jumma'a saboda ganin watan da aka
yi a daren Alhamis.
Don haka wayewar garin sai ta zamo
daban. Yau aikin duk na azumi ne masu
surfe suna yi masu daka suna yi.
Nima ba a bar ni a baya ba, sai dai
sabanin yadda nayi zato ba a je ko ina ba
84
na ajiye tambayar saboda bororon da
hannuna ya fara yi sai na koma tankade.
Ranar da aka yi ukun azumi tashi nayi
da nufin yin abinda zan yi buda baki da shi
da kaina.
Alele da kuma soyayyiyar doya da
miyar kwai don kuwa su kunu kawai suke
yi sai abincin gida.
Baba dan Juma ne ya ba da kudin da
aka yi mun cefanen kayan da babu a gida.
Zama nayi nai abincina mai rai da lafiya
na bi 'yan tsofaffin na basu sannan nayi
alwala na zauna ina jiran a kira sallah.
Wayata ta fára kara kamar ba zan dauka
ba, saboda magana ma wahala take yi
mun.
Don kuwa ba karamin jin azumin nake
yi ba. Na yi sallama daidai na