MAI DAKI (2) Hausa Novels By Hafsat Sodangi.docx

Author :  Hafsat C Sodangi Category :  KDP NOVELS

Chapter   2 / 5

3K to 6K   out of 13.9K words

/>
turamen zannuwa masu kyau sosai na bata

guda biyu.

22

Na hada da kayayyakin su turare

sabulu da omo da hijabai tare da kudi ma

dan auki na ce, Yaya to ga wannan tunda

ban san haka tafiyar taki zata zo mana ba.

Ta ce, na gode miki Hauwa'u ki kuma

yi ta hakuri kin gane ko? Na ce, eh. Na

dauko Naira dubu biyu na ce mata wannan

ki siya ma Rukayya sweet a hanya ki ce

mata in ji ni.

Tayi murmushi abinda yasa na fahimci

hakan yayi mata dadi ba kadan ba. Ta ce,

zan gaya mata.

Kicin na wuce don nayi girkin dare, don

ba zan jira sai Yaya ta tafi ba, 1tama tana

shirin kayanta.

Da daddare ina daki ina jin su da Ishak

fama yake yi da ita. Amma ko sauraronshi

bata yi, wasu irin maganganu take yi mishi

masu zafin gaske.

Hakuriyake bata amma bata

sauraronshi. Kayi kokari itama ka koreta

sai kuma ka san nayi. Amma ina tabbatar

23

maka zuwa gidanka na daina yi, idan har

ba taitayinka ka shiga ka kama kanka ba,

Ni dai bacci ya dauke ni ni na sake

farkawa na jiyo su na gyara kwanciyata

ban bude ido ba sai da aka yi kiran sallah.

Yaya na samu har tayi wanka ta gama

shiri cikin sauri na ajiye mata tunda ni har

yanzu sallah ta bata daidaita ba.

Wani lokaci ina ganin alama. Ta ce, kai

ni Hauwa'u wani kari zan yi, na ce yi

hakuri Yaya ki karya, ta ce to.

Ina zaune a gefen ta ina shayar da

Abulkhairi ta kalle ni, "Hauwa'u. Na ce,

Na'am Yaya. Kada kijewa iyayenki a

haka da wannan idon ki bari sai ya

washe." Na ce, To.

Tafiya Yaya tayi bata dauki ko

kwandalar da lshak ya bata ba. Duk kuma

alama ne na tsananin fushin da tayi da shi.

Gidan yayi mun wani iri don dama-

dama Abulkhairi yana rage mun 'yar

24

damuwa. Wunin ranar kuma Ishak bai

leka ko ma ba.

Na gama abincin rana na dauko na

kawo mishi dakinshi ya ce, kai mun falo

gani nan zuwa.

Bai fito ba sai da ya yi wanka yayi

sallah ya gama cin abincin shi ya shigo

dakin ya same ni ina bai wa Abulkhairi

nono.

Ya zauna a gefen gadon yana kallonmu.

Na gama ba shi nono na mika mishi shi ya

karbe shi. Yana dan mishi 'yan wasanni.

A raina na ce Ya iya wasa da danshi

kuma kana ganin irin yadda yake tafiyar

da yaron zaka gane yana da muhimmanci a

wurinshi.

Da ni ne kawai ko kuma na ce da

matanshi bai iya mu'amalla ba. Ya dago

kanshi ya kalle ni muka hada ido kadaran-

kadahan fuskarshi.

Na sunkuyar da kaina. "Me yasa idan

na ce miki bana son abu ba kya bari?

25

Kinga abinda hakan yaja mun Yaya ta tafi

tana fushi da ni abin da bai taba faruwa ba.

To kada kiyi tunanin hakan zai sa na

sassauta daga kan ra'ayina na bana son

mu'amallarki da ita.

Nayi shiru zuwa wani dan lokaci na ce,

To amma menene dalilinka na hana ni

mu'amalla da mutane da ka ke yi?

A ciki har da yan uwana? Kana ganin

idan kayi mun hakan kayi mun adalc1?

Kada ka manta kafin aurena dą kai ina da

kyakkyawar m:'amalla tsakanina da 'yan

uwana a yanzu ko inda suke ba ka barina

naje?

"Ba hana ki mu' amalla da su nake yi

ba. A yanzu kin yi kuruciya, ki fahimci

abubuwan da nake kokarin fahimtar da ke,

don haka ba zan Zauna yin wannan

bayánin ba a yanzu."

Ya dauki Abulkhairi ya fita da shi. Na

bishi da ido har ya gama fita a dakin nayi

ajiyar Zuciya a hankali,

27

Ban je gida ba sai bayan sati guda cif da

tafiyar Yaya. Ina zaune a gaban Ummana

farin cikinta bai misaltuwa. Su Tasi'u

kuwa sai kokarin a ba su Abulkhair su

dauke su.

Umma ta hana har Yaya Auwalu ma ya

baro kasuwarshi da wurwuri da nayi mishi

waya na gaya mishi muna gida.

Shi ma Ishak bai zo daukata ba har

Babana ya dawo daga aikinshi ya same

mu. Muka hadu muna ta hira gwanin dadi.

Ishak bai zo ba sai karfe shida na

yamma, kirana yayi a waya ya sanar dani

isowarshi ban kuma nemi ya shigo ba don

nasan ko na nema ba samu zan yi ba.

Na shiga daki muna sallama da Umma

na ce, Ni Umma kina ganin za ki iya yin

wata sana'a kuwa ta cikin gida'?

Ta ce, Eh to me zai hana sai na gwada

na gani. Hannu nasa a cikin Jakata na ciro

mata kudin da na tanada wanda na tara a

lokacin bikin sunan Abulkhairi.

27

Na mika mata gaba daya na ce, Ga su

nan ki gwada muga abinda Allah zai yi. Ta

ce, Ke ko a ina ki ka samu kudi haka?

Ban tsaya yi mata wani bayani ba goya

Abulkhairi kawai nayi na fito muka tafi.

Abubuwan Ishak sun dan ragu,

musamman da yake ya kan dawo gida a

yanzu da dan wuri ko don Abulkhairi.

Sai dai duk da haka ranar da abin nashi

ya motsa sai ya kai sha daya na dare.

Kullum naga yanda Ishak yake tafiyar da

yaron mamakinshi yana kama ni.

Menene hujjarshi na har a yanzu da na

fara haihuwa da shi bai yi tunanin ya gaya

mun komai game da labarin 'ya'yanshi ba?

Wani lokaci sai naji kamar nayi mishi

magana amma sai naga to ma menene na

hanzari ne bari dai na kyale shi naga

iyakacin gudun ruwanshi.

Yau kuwa da ya dawo aiki da wuri

zaune muke duka a falon yayin da

28

Abulkhairi yake kwance kan Cinyarshi

yana barci.

Ya dauko wayar shi ya daddanna ya

fara magana na kuma gane da Yaya ne don

haka na nemi ya bani wayar na gaisheta.

Muna gaisawa ina tambayarta abubuwa

da gangan na ce Yaya ya su Rukayya? Ina

ganin irin kallon da Ishak ya watso mun

wanda ban san ma'anar shi ba.

Yaya ta ce, Tana nan lafiya gata nan ma

a kusa da ni na ce bata mu gaisa, yarinyar

ta fara gaishe ni cikin muryarta mai sany

ta ce mun, Ina Baba karami?

Nayi murmushi na kuma san Yaya ce ta

sa ta ta tambaya. Na ce Baba karami yana

nan lafiya Rukayya, to ai ba ki tambayi

Baba babba ba?

Ta ce, To ina Baba babba? Na ce gashi

nan bari na baki ku gaisa. Na mika mishi

wayar har yanzu kallona yake yi.

Ban zauna ba' wuce shi nayi na shiga

daki na zauna. Sai dai a madadin naji

29

dadin abinda nayin wani gululun bakin

ciki ne ya tokare mun kirii.

Ishak ya raina ni yana yi mun wani

gani-gani to amma babu laifi.

Da kanshi ya shigo dakin yazo ya

gyarawa Abulkhairi wurin kwanciya, ya ce

zan samu wuri kuwa a nan? Na ce me zai

hana idan kana bukata na gyara yanayin

kwanciyata shima ya kwanta yana

fuskantata.

Juyawa nayi na fuskanci bango da nufin

na kaucewa kallonshi nayi bacci sai dai

abin ya gagara.

An kai kamar awa daya bayan nan sa1

naji ya kira sunana ban amsa ba har ya

sake tare da dan daga murya.

Na amsa ya cé, juyo muyi magana. Na

juyo ina fuskantarshi. Ba tun yau ba naso

na zaunar da ke don muyi wasu yan

maganganu sai dai ban samu lokaci ba.

Nasan babu mamaki kin ji wadansu

maganganu daga wurin Yaya. Na ce kamar

30

Don kuwa yadinan shadda bandir biyu

ya saya da atamfofi da kuma wasu

kananan abubuwan amfani iri-iri.

Nima koda nake da kayan amfani ya

karo mun da kuma Abulkhairi da yake na

fara bashi abincin gongoni.

Muna zaune a falo ana gobe zai tafi rike

yake da abokiyar hirar tashi Jarida na ce ni

haka zamu zauna ne a gidan nan idan ka

tafi dagani sai Abulkhairi?

Ya duake Jaridar a fuskarshi ya kalle ni

Ban gane ba? Na sake maimaita mishi

tambayar ya ce, Eh to menene?

Na ce, Ba zan iya ba ne ina jin tsoro.

Kuma nayi tunanin kai da kanka zaka

fahimci hakan ba tare da nayi maka

magana ba.

Sai naga ba ka yi ma wannan tunanin

ba. Kuma ai ya kamata ka fahimta. da

kanka cewa ko ba na tsoron zaman ni

kadai ma ai ba1 yi tsari ka tafi ka bar ni

33



daga ni sai yaro mai watanni biyar a cikin

gida irin wannan ba.

Ko mutanen gari ne suka fahimci baka

nan ai.. To naji ya isa haka. Na ja bakina

nayi shiru shima ya ci gaba da karatunshi.

Abulkhairi yayi bacci na mike na shiga

daki na shimfide shi na fito falon na sake

zama lokacin ne ya kalle ni.

To menene ra'ayinki na ce ni bani da

wani ra'ayi idan a kan wannan ne. tunani

yazo mun a cikin raina.

Mutumin da bai yarda da mu'amallar

matarshi da kowa ba ba shi da kyakkyawar

mu'amalla ko kankani da makwabtanshi

balle da mutanen waje.

Ban taba ganin mutum irin Ishak ba.

Naja bakina nayi shiru ni dai kawai nasan

ba zai tafi ya bar ni a gida ni kadai sai

Abulkhairi ba.

Na sake tashi don zuwa kwanciya tunda

dare ya soma yi na kwanta har na fara

34

bacci sai naji yana tashina na bude ido ki

shirya kayanki mu tafi tare, na ce to.

Kayan Abulkhairi nafi diba tunda shi

yaro ne sai na dauki nawa guda hudu ban

da na jikina.

Sai 'yan tarkacen amfani, tunda dai ya

ce kwana uku zai yi. Tafiya sosai muka yi

don kuwa cikin awowi hudu sai ga mu a

Kaduna gidan Yaya.

Murna sosai tayi tana rike da

Abulkhairi da itama take cewa Baba tana

ta shafa shi tare da yaba girmanshi ta ce,

Ikon Allah! Wato yaron nan da magajinshi

ya ke kama?

Ishak ya dan yi murmushi ya ce, Nima

lokaci-lokaci sai naga kamar hakan. ta ce,

Ai babu ko wai a ciki, to Allah yasa ka

gaji halinshi.

Ta kalle ni yau ga Hauwa'u a gidan

Yaya, nayi murmushi muka sake gaisawa

na ce, Yaya ban ga yara ba ta ce eh sun tafi

35

Makaranta. Tafiyar taku babu sanarwa

babu komai?

Ya ce, Eh ban sa rän yinta ba a yanzu

nima, ta dauro ne kawai tunda kin ga

hutun kwanaki uku kawai na dauko duk da

kwanakin sati sai su zama biyar.

Ta ce, Eh hakan yayi kyau zaka wuce

Kaciya kenan? Ya ce, Eh su Abulkhairi za

su gida kenan. Ya ce, A'a su a nan zan bar

Su.

Ta ce, Saboda me? Bai bata amsa ba sai

dai daga ni har ita bin shi da ido muka yi.

Hajiya Baba kamar yadda naji yaron

suna kiranta mata ce mai matukar

mu'amalla da mutane sabanin kanin nata.

Tun da muka shiga gida kafar yara bata

dauke ba haka nan babu abinda bata

siyarwa na amfanin gida.

Don haka tana da rufin asirinta daidai

ita, don kuwa kaninta a tsaye yake akan

al 'amuranta tunda gidan da take ciki ma a

36

yanzu nashi ne, shi ne kuma ya biya mata

ta sauke farali.

Su Rukayya ba su dawo ba sai wajen

karfe biyu da rabi. Na bi yarinyar da kallo

lokacin da ta durkusa tana gaishe ni

Ba za ta fi shekaru shida ba, ya yanta

kuma takwas ta juya tana gaida Babanta ya

miko mata hannu alamar ta karasa inda

yake ta kwanta a jikinshi yana mata 'yan

tambayoyi.

Sai da ta gama ba shi amsa ya ce, To ba.

ki tambayi kaninki ba gashi can je ki ki

dauke shi, ta taho inda nake zaune tasa

hannu ta dauki Abulkhairi da ke zaune

yana wasa.

Duk da sanin da nayi ba wani iyawa

zata yi da shi ba, ban hanata ba. Ishak ne

dai da yaga zata tima shi a kasa ya zabura

ya karbe shi.

Sosai na sake da yarinyar saboda

yanayinta na nutsuwa don kuwa tafi

37

wanta, tana yawan zuwa inda nake saboda

Abulkhairi, ba na kuma hanata daukanshi.

Washegari da sassafe Ishak ya wuce

garinsu na sake a gidan Yaya sosai har

kicin tare muke shiga ina kuma tayata

sayar da kayanta.

Muna cin abincin rana take tambayata

ni Hauwa'u ya mijin naki dai komai lafiya

ko?

Na ce lafiya kalau Yaya. Babu wata

matsala? Na ce ko kadan. Ta ce, To ai shi

kenan tunda kin fadi haka, alama ne na ke

din mata ce mai hakuri to sai ki kara a kan

na da.

Bakunta mai matukar dadi muka yi har

Ishak ya dawo washegari na roke shi ya

kai ni na yi wa yara siyayya bai ki ba.

Siyayya sosai nayi musu dangin kayan

sakawa kayan wasa da kuma na kwalama.

Murna sosai Rukayya ta rinka yi sannan

na ce muje studio aka yi mata hoto da

Abulkhairi wait and take.

38

Na bata nata nima na dauki kwafi daya,

hoton yayi matukar kyau hakan ne yas

Ishak cewa a wanke musu baba, duk da

dai ba tsayawa karba zamu yi ba a baiwa

Yaya.

Ni kaina bakuntar tayi mun kadan,

amma haka muka taho gida washegari

muka bar su cikin kewa Rukayya kuwa

tana ta kukan a bar mata Abulkhairinta.

A yanzu da Abulkhairi yayi wayo kuma

nake ganin canji daga wurin Ishak alamar

ya dan fara sassautowa daga tsamin

halinshi, sai nake ta kwadayin komawata

Makaranta.

Tun da dai yaron yay1 wayo a watanni

goman da yayi ne a duniya yake gudunshi

ko ina.

Samun Ishak nayi cikin dabara na yi

mishi maganar Makarantata tun da ni dai

babban burina kenan. Na ce, Don Allah ka

bar ni na koma ko ba ka yarda nayi aiki ba

ni bani da matsala.

39

Amma burina dai yin karatun ne kawai

zai amfane mu ba ki daya. Karatuna ba zai

taba zama maka mätsala ba.

Bai ce mun komai ba har na yi

maganganuna na gaji nayi shiru. Sai ma

gyara kwanciyar shi da ya yi ya juya baya.

A haka muka ci gaba da zama sana'ar

da Ummana ta fara yi sai ya bunkasa ba

kadan ba itama dai kayan gidan ne dangin

man gyada, maggi, kalanzir har da su

kuli-kuli.

Kai komai yanzu sayarwa take yi, kuma

sana'a ce mai albarka ta rufin asiri. Ba na

ko damuwa don ban bata kudi ba yanzu

tunda nasan bata rasawa.

nrbRasuwa aka yi a unguwarmu kuma

Ishak ne da kanshi yazo yake gaya mun,

na kuma roke shi ina son yi musu

ta'aziyya ya ce to.

Don haka da na gama ayyukana sai ma

rike hannun 'Abulkhairi muka fita na rufe

gidan.

40

A gidan ta'aziyyar naga Hindu da

Mominta muka fito tare don komawa gida

Hindu tana rike da hannun Abulkhairi tana

gaya mun ta samu admission a (Ahmadu

Bello University) da ke Zariya.

Murna sosai nayi mata ta ce ke dai

Maman Abulkhairi har yanzu shiru. Nayi

murmushi ban ce mata komai ba.

Muka yi sallama da Momi na mika

hannu zan karbi Abulkhairi ta ce, a'a bar

mun shi kawai zan turo Abubakar ya dawo

da shi.

Na ce to, ba don raina ya so ba sai don

kada suyi zaton wani abu sannan kuma shi

da ai ba a rowarshi.

Na dawo gida sai dai gaba daya

hankalina yana wurin Abulkhairi, har

karfe shida a yanzu da Ishek bai cika yin

dare ba ina tsoron ya dawo yaga danshi

baya gida ban san abinda zan ce mishi ya

fahimce ni ba.

41

Ina jin taba kofa na zabura na mike

cikin sauri na bude kofar, Abubakar ne

rike da Abulkhairi sai dai an makara, don

kuwa shima Ishak din gyaran parking yake

yi.

Jikina a sanyaye na fara kokarin rufe

kofar tunda shi ta cikin gareji zai biyo. Ina

shiga daki shima ya shigo.

Abulkhairi ya falla a guje ya tafi don yi1

mishi oyoyo din da ya saba. Yana

daukanshi ya shigar dashi cikin daki ya

kulle ya dawo.

Me na gaya miki a kan mutanen nan

iye? Na fara ja da baya saboda matsowar

da yake yi da kuma abinda na gani a

idonshi na tashin hankali.

Ni kuma a yanzu babu abinda nake

tsoro irin dukan Ishak, sai dai ban tsira ba.

Duka sosai ya lakada mun ya tara mun jini

a ido.

Kwana nayi ina kuka, haka nan

Abulkhairi duk da kin barin shi yazu

42

gurina da yayi ya shiga dakinshi da shi ya

rufe kofa.

Na fara gajiya da irin wadannan

abubuwan har gashi yaro ya fara fahimtar

wasu abubuwa ya tayaka kuka.

Da kyar na lallaba da asuba na shiga

bayangida na gaggasa jikina, har da

fuskata na dawo alwala nayi sallah.

Lokacin ne shima ya bude kofa ya fito

don zuwa Masallaci.

Har da gari ya waye bai bar Abulkhairi

yazo wajena ba, da kanshi ya ba shi abin

karyawa ya yi mishi wanka ya sa shi a

mota ya tafi da shi, ban san inda suka tafi

ba.

Ko girki ban iya yi ba sai tea da na

wuni sha saboda mummunan ciwon daa

jikina yake yi mun, ba su dawo ba sai

karfe hudu na yamma.

Yana sake Abulkhairi dakina ya nufo a

guje. Ina kwance gwalandin magana yana

43

tambayata wai Babanshi ne ya dake ni to

nayi hakuri kin ji Mama.

Ban ce mishi komai ba amma duk

kokarin hana hawayena zuba da nake yi

bai fasa gangarowa ba.

Ya shigo dakin ya rike hannun

Abulkhairi yaja shi suka sake fita, na ci

gaba da kukana.

Idan na bari Ishak yana yi mun irin

wannan dukan wanda jinýa take biyo

bayanshi anya zan kai labari kuwa?

Ya sake shigowa dakin rike da leda a

hannunshi ya zauna a kan stool din gaban

dressing mirrow yana ciro abubuwan cikin

ledar.

Robar abincin ne na take away sai

gasasshiyar kaza sai magunguna. Tashi

kici abinci.ban ce mishi komai ba, amma

ban iya daina kallonshi

2 / 5