Author : Hafsat C Sodangi Category : KDP NOVELS
ba.
Abulkhairi ya matso, "Mama tashi."
Yasa hannu yana girgiza ni ban motsa ba.
44
Ya fita ya dawo da robar swan ya kama
ni zai daga ni na fizge hannuna na koma
na sake kwanciya.
Shima fita yayi bai sake ce mun komai
ba. Na sake fashewa da wani sabon kukan,
babu irin tunanin da bai zo mun raina ba.
Ya zama dole na hemi mafita abinda
kawai zuciyata take kara jaddada mun
kenan.
A hankali sai na samu sauki na ci gaba
da hidimomina, sai dai idona har yanzu bai
washe ba. Zazzabi sosai ne ya kama
Abulkhairi wanda yasa Ishak ya sauke mu
a asibiti don ganin Likita.
Muna zaune muna bin layi a sashen
yara sai kawai naga Sadiya Tanimu cikin
mamaki na rike baki ina kare mata kallo
sanye take da fararen kaya na jinya wato
Nurse na ce, Sadiya kada dai ki ce mun kin
zama Nurse?
45
Ta ce, a'a haba ce miki aka yi abin babu
wuya, ina dai shirin zama wannan ita ce
shekarata ta farko.
Na ce, Au to koda dai naji. Ta ce, ai
shekara biyu kenan rabon da muga juna
kin tuna?
Sai lokacin ne na tuna zuwanta na
karshe wajena da abin da ya faru
tsakaninta da Ishak. Na dan yi murmushi
na ce haka ne fa ba mu sake haduwa ba.
Ta sunkuya daidai inda Abulkhairi yake
ta mika mishi hannu tare da cewa "Hi
handsome ya ka ke? Ya ce, Salamu
alaikum Babana yake cewa.
Ta ce, To ko kuwa ya ce, Eh to ce to ka
gani kenan akwai 'bambanci. Ta mike ta
gyara tsayuwarta ta ce, yaron ki ya mun
kyau gashi da wayo na ce baki yi aure ba?
Ta ce, Eh to muna kan hanya na ce to
Allah ya ba da na kwarai. Ta kara zuba
mun ido tana kallona ta ce, Kin san wani
abu ne?
46
Mijinki exacthy mijin Sister ta shi yasa
abinda ya yi mun bai bani haushi ba. Idan
ya tashi dukanta itama sai idonta ya bar
jini, na ce kai! Sadiya kenan baki da dama
ce miki nayi dukana yayi jini ya taru mun
a ido? Ni ciwon ido nayi.
Ta dan tabe baki kamar dai yadda ta
saba ta ce, Oho dai ni na gaya miki nasan
maza irin su. Abu daya za ki yi ki taimaki
kanki ki koma Makaranta shi kanshi
wataran idan aka ce ya buge ki ba zai fara
ba.
Shi yasa wani lokaci ma ko son tunanin
aure bana yi saboda irin wannan tauye
hakkin.
Ai ba haka aka ce ayi auren ba. Ban ce
wa Sadiya komai ba amma dai ina ganin
shawararta zan bi to ta ina? Ni dai nasan
ba karamin yaki za a yi da Ishak ya bar ni
na koma Makaranta ba.
Sai da muka gama ganin Likita sannan
na kira shi a waya yazo ya kai mu gida.
47
Muna zaune da dadare bayan mun gama
cin abinci na kwashe kanukan duk da
faduwar da gabana yake yi.
Ban fasa yi mishi maganar ba cikin
hanzari kuma ya dakatar da ni irna so in
tabbatar miki da komawarki Makaranta ba
zai taba yiwuwa ba.
Nayi shiru zuwa wani lokaci na ce kayi
hakuri ka gaya mun sharuddanka na yin
karatuna ba zan kaucewa dokarka ba, ka
ji?
Na tambaye shi ya mike ya zauna ya
zuba mun ido, Kina son yin karatu? Cikin
sauri ya ce, To ga zabi zan baki.
Sai kiyi wanda ki ka fi so, babu matsala
duka zan yi miki. Za ki zauna ne kiyi
zaman aure shi kadai ba tare da kin yi
karatu ba ko kuwa za ki bar zaman aurenki
ki koma karatu?
Gabana ya yi mummunan faduwa, na
dago kai na kalli Ishak da ya zuba mun ido
yana kallona.
48
Wacce irin tambaya ce wannan? Ishak yana nufin kenan idan har zan zauna da shi ba zan koma Makaranta ba, haka zan yi ta zama dashi da halayenshi?
Ya raba ni da "yan uwana, ya raba ni da kowa haka nan kankanin abu idan nayi ya rufe ni da duka tamfar an aiko shi.
Amma hakan bai ishe shi ba ya tsare ni da irin wadannan tambayoyin saboda rainin hankali.
Ina son aurena duk da irin abubuwan da nake fuskanta, to amma idan na zabi auren nashi ai zai ga kamar naji tsoro na kuma ba da kaina ban kuma san abinda zai biyo bayan hakan ba.
Haka nan shi idan ya matsu da auren ai sai ya bar ni na ci gaba da karatuna saboda nima na samu mafita kan matsalolina, kenan dama ce ta zo mun.
Ya ce, Ke fa nake jira. Wanne ki ka zaba? Na ce, "Karatu. Ya ce, "To babu laifi. Ya koma ya kwanta.
49
Na hau gado na kwanta a raina ina
tunanin babu mamaki nima nan da yan
watanni kadan na koma na ci gaba da
makarantata.
ldan na gama kuwa na tafi na zama
Nurse har yanzu ban canza buri ba. A haka
barci ya dauke ni.
Da sassafe na shiga dakin Ishak don na
gaishe shi ya gama amsawa na mike don
fara shirin abin karyawa.
Ya ce, Zo. Na dawo na sake zama
Ungo wannan. Na karba, takarda ce ina
jiran ya yi mun bayanin wanda zai zo ya
karba ko wani abu makamancin hakan.
Sai na ji ya ce, "Zabin ki ne nakaratu
don haka kije kiyi na sauwake miki." Bai
jira amsawata ba ya juya ya fita a daki.
Ina zaune a wurin kwakkwaran motsi
na kasa yi, sauwakewa saki kenan ko me?
Sai dai har a yanzu ban bude takardar
na ga abin da ke cikinta ba. Ya sake
shigowa dakin ya ganni a inda nake zaune
50
ya ce Kije "gida kiyi musu bayanin komai".
Na mike na dawo dakina na dauki hijab
da Jakata nasa hannu na dauki Abulkhairi
da har yanzu yake barci na saba shi a
kafadata na fito falo zan wuce ya ce, Zo
Hauwa'u.
Nadawo ya ce, "Sauke shi. Nayi
sokoko ina kallonshi ya sake cewa "Sauke
min shi. A lokacin da ki ka yi zabin da ki
ka yin ba ki kalle shi ba, yi kawai ki ka yi
ba tare da kin yi tunanin wasu abubuwa
masu grma za su biyo baya ba.
Abulkhairi dana ne ni ke da cikakken
iko a kanshi, don haka ajiye mun shi.
A hankali ya mike har inda nake yazo
syasa hannu ya dauke shi a kafadata ya
shimfide shi tare da dan jijjiga shi a
hankali ganin yana kokarin farkawa na
dawo gida cikin wani yanayi da baya
kwatantuwa.
51
Umma tana ganina ta ce "Lafiya ki ka
bugo irin wannan sammakon haka? Ina
yaron?"
Na ce, Yana tare da Babanshi. To lafiya
dai ko? Ta sake tambayata na ce, Eh Baba
nake son gani.
Ta ce, Ikon Allah, to ai yanzu ya tafi sai
dai ko ki yi sammakon zuwa da safe, ko
kuma ki dawo da yamma.
Neman wuri nayi na zauna ba tare da na
ce mata komai ba. Ta sake bina da kallo ta
tashi ta kawo mun abin karyawa ta ce, To
ga shi nan ki karya ko?"
Duk da ban ci komai ba na fito daga
gida ban ji wani alamar yunwa a tare da ni
ba.
Ina kallon Umma tana ta harkokinta da
yaran da suke zuwa siyan kaya da kuma su
Tasi'u. Itama ta Iura ta gane ba zan yi
magana ba ta rabu da ni.
52
Sai dai a duk lokacin da nayi nufin
kallon inda take sai naga itama ni take
kallo. Zuciyata tana ta kaiwa da komowa.
Ban taba tunanin zabin da nayin zai
zamo haka ba. To me Ishak yake nufi
kenan?
Babana bai dawo gida ba sai wajen
Karfe biyar na yamma, yadda dai ya saba
dawowa kenan. Yana ganina ya ce, "A'a
Hauwa'u ce yau a gidan? To ina abokin
nawa?
Na ce mishi Yana gida Baba. Na
durkusa na gaishe shi. Ban yi mishi wata
magana ba sai da ya ci abincin shi ya samu
nutsuwa sannan na mika mishi takardar da
Ishak ya bani wacce har a yanzu din nan
ban iya budeta naga abinda ke cikinta ba.
Cikin nutsuwa ya budeta ya fara
karantawa. Babana duk da yake Masinja a
Banki ya iya karatu da rubutu daidai
gwargwado.
53
Inna lillahi wa inna ilaihir-raji'un.
Abin da ya biyo bayan karatun nash1
kenan.
Yayi shiru na kusan mintina biyar
sannan ya ce, Ikon Allah! Me ki ka yi
mishi da zafi haka Hauwa'u da yayi nufin
yanke miki irin wannan hukunci mai
tsanani? Ba zai yi miki saki daya ko biyu
ba sai ya yi miki uku gaba daya."
Na dafe kirji da sauri na ce "Uku Baba?
Yau na shiga uku! Tuni na fashe da kuka.
Mikewa nayi cikin sauri da nufin fitowa
a gidan na koma gidan Ishak. Babana ya
ce Ina za ki je? Na ce, "Baba zan dauko
Abulkhairi ne. "
Ya ce, "Dawo kawai Hauwa'u, ba shi
ya karbe shi ba? Na ce, "Eh Baba ai cewa
ya yi nazo nay1 muku bayani ne kafin na
koma na karbe shi."
Ya ce, "A'a bar mishi danshi kawai kiyi
hakuri. Wata rana za ki ga kamar ba ayi
ba, ki daure ki zama Jaruma ki yawaita
54
addu'a, Ubangiji yayi miki zabin miji
nagari da zai zamo miki alheri fiye da
wannan da ku ka rabu."
Cikin sanyin jiki na koma dakin Umma
na hau kan shimfidar na sake zama. Ita
kuwa tana ta harkokinta na kokarin ganin
ta karasa abincin daren da take yi.
Ban taba sanin haka abin zai zamo ba,
yanzu duk wannan zaman da muka yi da
kuma hakurin da na rinka yi a haka auren
zai kare?
Lallai Ishak ya wuce sanina, don
kuwaban taba zaton zai yi mun hakan ba.
Ko da ya bani zabi kuma na dauka karkari
ya yi mun saki daya ne ba uku ringis ba.
Hakan ya yi ne don ya nuna mun dama
can ni ce na damu da zaman ba shi ba.
Auwalu ne da kanshi ya shiga dakina na
da ya tsaftace shi ya gyare shi tsaf ya sayo
sabuwar katifa waya takwas da zanin gado
da filo guda daya ya ajiye ya shimfida leda
55
a tsakar dakin don na dan ji dadin zama a
ciki.
Kwanaki biyun da nayi a gida ba masu
sauki ba ne ko kadan don kuwa kwtaa-
kwata bana barci.
Babu abin da yafi damuna irin kwace
Abulkhairi da Ishak yayi da dai a ce yayi
mun sakin ne sai ya bar ni na taho da dana
to da abin ya zamo mai dan sauki a
wurina.
Shi kenan shima yanzu nasan yana
Kaduna wurin Yaya tare da su Anas da
Rukayya.
Ina zaune ne a gida amma ko tsakar
gida ba fitowa nake yi ba ballantana naa
taya Umma wan1 aikin gida.
Idan har nasa kafata a waje to kuwa
wanka zan yi ko wani uzuri ko kuma
alwala.
Ko abinci Tasi'u ne ko kuma Sabi'u
suke kawo mun na kasa sakewa ko kadan
naji dadin zuciyata.
56
Itama Umma harkokinta take yi ba tare
da ta saurare ni ba don kuwa har a yau
dinnan bata ce mun komai a kan maganar
ba ballantana ta tambaye ni abinda ya hada
ni da Ishak yayi abinda yayin.
Ranar da na wayi gari kwanana bakwai
a gidan ranar ne dan aika ya yi sallama ya
dire mun akwatunana wadanda su ne kadai
abinda na mallaka a gidan Ishak.
Komai na same shi ne a can ya kuma
miko mun zungureriyar envelop ya ce in ji
Ishak din.
Na koma daki na zauna na bude wata
'yar gajeriyar wasika ce, ga abinda ya ce:
Hauwa 'u,
ts Ina fata kina nan lafiya?,
Ga kayanki a bayar a kawo miki, don
nasan kina da bukatarsu. Wannan kudin
kuma kiyi amfani da su wajen ganin kin
koma Makaranta tunda na gane hakan
yana da matukar muhimmanci a
57
rayuwarki, tunda ki ka zabe shi a kan
aurenmu.
Ina so ki.san zan zamo mai taimako
kwarai ta fannin karatun naki a duk sanda
ki ka bukaci nayi hakan.
Ina miki fatan alheri. Abulkhairi yana
gaida Mamanshi.
Na gode.
Na bude daya envelop din, rafa ce ta
dubu daddaya guda daya.
Na mayar a ajiye na fara duba kayana,
duk wani abu da na mallaka a idanshi ya
saka mun a cikin akwatuna set daya mai
shida.
Sai saitin Encholac guda daya mai uku.
Na jawo babbanalbum dina wanda
hotunan Abulkhairi ne kadai a ciki na
bude hotonshi na karshe na fara gani
wanda aka yi mishi shi a ranar da ya cika
shekaru biyu a duniya.
58
Nasa hannu na shafa fuskarshi da ke
murmushi a hoton ko sai yaushe zan sake
ganinshi, sai Allah.
Hawaye suka yi ta zubo mun. Ya zama
dolena wartsake na fuskanci al'amuran da
ke gabana.
Ba zai yiwu nayi ta zama cikin kunci
don kawai Ishak ya sake ni ba. Rayuwata
yanzu ne take farkon ganiyarta, tunda ko a
bana shekaru ashirin da daya ne da ni,
auren kuwa shekaru hudu.
Wartsakewa nayi na fito tsakar gida na
fara taya Umma hidimar gidan da kuma
harkokinta na saye da sayarwa.
Irin su bayar da abu idan an zo siye,
karbar kudi da kuma bayar da canji, muna
kuma yan hirarrakinmu.
Su Tasi'u ma ganin na dan soma
wartsakewa murna suka rinka y1. Bini-bini
Su zo su zauna a inda nake suna yi mun
magana.
59
Babana yana dawowa da yamma sai da
ya gama cin abinci sannan naje na same
shi.
Na sake gaishe shi sannan na kawo
mishi batun bukatata na son komawa
Makaranta, don ganin na ci gaba da
karatuna.
Shiru yayi yana kallona, kallon da yake
yi mun shi ne yasa ni ta kara shiga
taitayina tun kafin naji abinda zai ce.
Ke! Kina cikin hayyacinki kuwa?
Anya wani abu vai shiga kwakwalwarkii
ba?
Idan ma kin kaso aurenki ne don ki
koma Makaranta, to ki kwaan da sanin
hakan ba zai yiwu ba, shashashar yarinyar
kawai, wacce ta ke nema ta mayar da
kanta wata ir1.
Tun kafin ki gama Iddah har kin fara
kokarin neman abin yi saboda ke addinin
ba damuwa ki ka yi da shi ba ko? Tashi ki
bani guri na sha iska."
60
Idan na ce ban shiga mawuyacin hali ba
ma to nayi karya. Duniyar tayi mun wata
iri.
Nayi ta kokarin ganin na sake jikina
nayi hidimar gabana amma abin ya gagara.
Don kuwa ko na dan manta kuma na
dan lokaci ne sai naji kamar wani abu ya
muntsini zuciyata.
Ko da ba wani jin dadin zama da shak
nake yi ba sai na fahimci dakina shi ne
cikakken 'yancina.
Sai nake ganin kamar na rasa komai
babu Abulkhairi wanda a kullum kewarshi
take sanyanına rasa sukuni.
Tsananta wa kana aikace-aikace da
nayi sai yake debe mun kewar zaman
tunane-tunane wadanda ba za su amfane ni
da komai ba.
Kullum na idar da sallar asuba sai
kawai na fito tsakar gida na wanke ta kwal
na wanke mana bayan gida na ciccika
randunan ruwa.
61
Nayi wanke-wanke nayi wanki sannan
na dora abin karyawa.
Yaya Auwalu da kanshi sai da ya ce,
aikin ya yi yawa na rage. Murmushi kawai
nayi ban ce mishi komai ba.
Idan nayi wanka sai na dora mana
abincin rana nayi na dare, Umma kuwa
tana harkar kasuwancinta wanda kullum
kara bunkasa yake yi.
Yanzu gidan ba a rashi kamar da. Dan
albashin Babanmu da kuma sana ar Umma
wani karin rufin asiri ne a gare mu baki
daya.
Ga Yaya Auwalu da a yanzu saukin
abubuwan da ya samu na gida yasa yake
ajiye mana hatsi a maimakon kullum a yi
ta awo.
Don kuwa a yanzu shima oga ne na
kanshi duk da dai ba rabuwa yayi da
maigidan nashi ba.
Duk da hakan dan kankanin lokaci ne
kawai sai na zube nayi baki. Ganewan da
62
nayi in ba matukar hankali nayi ba zan
canza gaba daya yasa nayi tsaye don ganin
na kula da kaina ta wurin cima da kuma
gyaran jiki.
Iddahta ta cika ne ana gab da fara
Azumin watan Ramadana mai albarka, bai
fi saura sati uku ba.
Zuciyata sai kaiwa da komowa take yi
akan na sake samun Babana a kan
maganar Makarantata.
Babu mamaki a yanzu tunda na gama
Iddah ya yarda amma ina matukar jin tsoro
don kuwa wani abu makamancin wancan
bai taba faruwa tsakanina da shi ba.
Ina zaune a kan shimfidar tabarmar da
nayi a tsakar gida ina taya Umma kullin
gishiri.
Yayin da take gete tana lissafin kudin
cinikinta na ce Umma ko za ki taimake ni
ne ki B yi.siwa Babanmu maganar
Makarantata tunda a yanzu babu wani
nauyi a kaina.
63
Ta ce, "A wane dalili?"
Nayi shiru ina tunanin abinda zan fada
mata don gamsar da ita zamana a haka ba
shi da wani amfani."
Sai ta ce, "Kina so né na taimaka miki
ki bijirewa maganarshi? In yaso kenan
nima sai nasa ran wata rana zai kafa doka-
ki taimaka a karya dokar ko?
To ba zan iya ba. Babanku burinshi a
yanzu na ki samu miji ne kiyi wani auren,
ki zauna a dakinki cikin rufin asiri.
Yanzu da da ba daya ba ne. da da yake
burin ganin kin yi karatu to ya wuce.
Yanzu ke ba yarinya karama ba ce,
koda ba ki da yawan shekaru a kanki
yanzu kuwa burinshi bai wuce na ganin
kin zauna a dakinki kin nutsu kin samu
mijinki da zai kula da al'amuranki ya
kuma tausaya miki.
Ba wanda zai nemi wulakanta ki ko
tozarta ki ba, karatu ga budurwa ba dole ba
ne ballantana ga bazawara.
64
Wani irin faduwar gaba naji da Umma
ta kira ni Bazawara.
Nan da nan sai maganganun Umma
suka zamo tamfar fami a zuciyata, nayi
wunin ranar ba