MAI DAKI (2) Hausa Novels By Hafsat Sodangi.docx

Author :  Hafsat C Sodangi Category :  KDP NOVELS

Chapter   1 / 5

1 to 3K   out of 13.9K words

MAI DAKI.... (2)

NA

HAJ. HAFSAT C. SODANGI

(Mrs. Yunus Abdullahi Dabai)

1

SADAUKARWA

Sadaukarwar littafin ta Iyayena ce,

Alhaji Chindo Muhammad Sodangi da

Hajiya Fatima Musa Sodangi, Ubangj

ya saka muku da alheri ya kuma kara

muku lafiya amin.

TUKUICI

Tukuicin littafin naki ne;

Khadija Chindo Sodangi (Mrs Nasiru

Idiris)

JINJINA

Jinjinar littafin taki ce Amarya ba kya

laifi (Maman Umar) Zuhuriyya Ibrahim

(Mrs Lawal Chindo Sodangi), Ubangiji

ya raya Umar da Imani.

FATAN ALHERI GARE KU

Fatima Abdulkadir Kazaure

Hafsat Iliyasu Unguwar Rimi

3

Khadija Usman Nasarawa

Nafisatu Ibrahim Muhammad

Fatima Ahmad Shehu Kaduna

Maryam Muhammad Gusau, Zamfara

Umaima Abubakar Umar

Maijidda Uba Magaji

Na gode, Ubangiji ya saka da alheri

amin.

KUNA RAINA

Hajiya Maryam (Mami) Dan Hassan

Hajiya Jamila Ibrahim Na-Bature

Hajiya A' isha Balarabe (Jazan)

Ubangiji ya bar zumunci amin.

4

Littattafan SODANGI:

Uwar Miji

Naga Ta Kaina

Rabon Kwado...

Cikar Alkawari

Wayyo Duniya

Yi wa Wani...

Abu Naka...

Mata Ma su Duniya

Nufin Allah

Kifi Na Ganinka...

Daga Kin Gaskiya..

Da Kamar Wuya...

Mai Uwa..

Duk Daya...

Mata Da Kicin Dinsu

Wacece Ni?

Wata Fuskar...

Mijin Ta ce

Garin Banza..

Ga ni Gare ka

5

Biyan Bukatar Rai

Shamaki

Hattara

Mata Masu Duniya

Kyautataa

Ayi Dai Mu Gani...

Tabbataccen Al'amari

In Kunne Yaji..

Halin Rayuwa

Mai Daki..

Littattafan ba sa nufin yi da wani ko

habaici ga kowa sai dai an rubuta su ne

don fadakarwa da nishadantarwa, ana

neman afuwa ga duk wanda yaga wani abu

yayi kamar 'abinda ya shafe shi, ba da shi

ake ba dace ne kawai.

6

MAI DAKI...2

W ahala dai irin wacce nayi ta ranar

ta wuce a zauna fada. Babu wani

na makwabta da zan tuntuba don ba ma

zan iya mikewa ba balle na ka1 ga zuwa

wani wuri.

Na kai awa biyu kafin ciwon ya sake ni,

na kokarta na ja jikina na hau kan

doguwar kujera na kwanta.

Wasu hawaye ma su dumi suna bin

kuncina. Ban kai mintina goma a haka ba

sai ga shi ya shigo ko kallonshi ban yi ba

balle nayi mishi sannu.

4Ya ya akwai matsala ne? ban ce mishi

komai ba, kukana kawai nake yi.

Ganin haka yasa shi ya ajiye ledar da ya

zo da ita ya wuce ni ya shiga dakinshi. Bai

fito ba haka nan nima ban tashi don yin

sallar Magriba da Isha'i da ban yi ba har

wajen karfe goma na dare.

Ya fito falon yana kalloa "Na tambaye

ki ko kina da matsala ne kin yi mun shiru,

7

amma kin zauna kina kuka wai ke wane

irin hali ne da ke ne?"

Ya kalli ledar abincin da ya ajiye a kasa

yayi tsaki. "Idan ba za ki ci abincin nan ba

wuce kije ki kwanta.

Na mike a hankali tare da rike gefen

cikina da ke mun wani irin ciwo na lallaba

a hankali na hau kan gadona na kwanta.

Wata kila yanayina da ya gani ne yasa

shi biyo ni dakin. Hauwa'u menene

damuwarki? Ina kuka na ce "Umma nake

so ka kira mun. 99 Ya ce, "Umma kuma? A

wane dalilin zan yi hakan?

Na ce, Ba ni da lafiya ne. nayi mishi

bayanin abinda ya faru da baya nan da

kuma ciwon da gefen cikina yake yi mun.

Fita yayi zuwa dakinshi ya dauko

mukulli ya sa hannu ya dauke ni zuwa

wurin motar shi, muka tafi asibiti.

Likita na duba ni ya ce haihuwa ce, duk

da akwai sauran kusan sati uku kafin

(E.d.d) dina ya cika. Nakuda kamar za a yi

8

kamar ba za a yi ba shiru ka ke ji kamar an

shuka dusa.

Har gari ya waye ya leko dakin yana

shaida mun zai je kiran Umma, don shi ma

ya je ya shirya yayi wanka na ce To.

Umma ce tazo ta tsaya a asibitin. Da

kyar da taimakon Allah da na Likitoci na

haihu wajen karfe uku na rana na samu

santalelen yaro, jajir da shi.

Ba mu dawo gida ba sai washegari

saboda hutu da suka ce na samu da kuma

dalilin zubar jinin da nayi

Umma ta nemi Ishak ya bar ni na koma

gida don yin jego bai yarda ba, don haka

dakina aka mayar da ni.

Mutanen unguwar mu sun zo mun

barka ba kadan ba, har ma da wadanda

ban sani ba. Sanin halin Ishak da nayi ne

yasa da aka fara maganar kawo mai yi

mun wanka na ce su bari a tuntube shi

tukunna.

9

Ilai kuwa sai cewa yayi Yayarshi ce

zata zo. Bayan kwana biyu kuwa sai gata

ta iso.

Mata mai saukin kai ni kuma nayi sabo

da ita ne ta yawan wayar da suke yi da

Ishak ta ce a bani mu gaisa.

Suna sosai aka yi ta bangarena iyayena

da 'yan uwana sun yi mun irin nasu

kokarin, sun kuma yi mun gata ta wajen

zuwa dubani da jariri.

Haka nan yan uwan lshak suma sun zo

ba kadan ba. Don haka bikin suna mai

gamsarwa sosai aka yi. Yaro kuma yaci

sunan Baban Ishak wato Abdullahi, amma

an yi mishi lakani da Abulkhairi.

Abinci kala-kala aka yi ta kawowa da

aka yi odar su babu kuma wanda zai ce bai

gamsu ba. Yaya ce da kanta ta tashi

washegarin sunan tunda asuba ta fara aikin

tsabtace gidan.

Kafin takwas na safiya kuwa tamfar ma

ba a yi komai a cikin shi ba.

10

Mu kuwa tuni mun yi wanka daga ni

har jarii Abulkhairi. Ta shigo har cikin

dakin da nake zaune ta fara karyawa muna

dan hira tana tambayata "Kin ga kayan

naku kuwa?

Na dan yi murmushi. Ta ce Hauwa'uu

kenan, hala ke ba kya halin naku ne na

zamani? Na ce, Yaya meye halin

zamani?

Ta ce, Rashin kunya mana wai ku nan

a dole kun waye? Yaya ce da kanta ta

ware mun kayan da Ishak yayi mana.

Kaya ne sosai ba wai masu dumbin

yawa ba, amma dai masu daraja ne kwarai

baran ma na jaririn wanda tamfar ba a

kasar nan aka yi sayayyar ba.

Ta bangaren gidanmu ma babu laifi ga

kuma alherin da na samu wurin mutane,

Momin Hindu ma ta yi wa Abulkhairi

sayayya ma kyau.

Zaman da nake yi da Yaya ba karamin

dadi yake yi mun ba, don kuwa 'tuni na

11

manta da irin zaman Kadaicin da na ke yi

da Ishak.

Duk da dai yanzu shima ya daina yin

dare Sannan duk da jarirantakar Baba

tunda shi abinda yake kiranshi kenan, yana

daukanshi ya kwanta da shi a dakinshi.

Ko kuma idan ya ji shi yana kuka ko

wani rikici za ka ga yana zaryar tambayar

abinda ke damunshi ko da dai ba dani yake

yi ba, hakan yana yi mun dadi a raina.

Da sassafe Yaya take juye mun ruwan

wanka wanda nake yi da tawul kafin na

gama na fito kuwa ta yi wa Abulkhairi.

Muna gama karyawa zata fara shirin

dora mana abincin rana idan kuwa ta gama

aikace-aikacenta to zama muke yi muna

kallon mu muna kuma hira.

Ga ta da kirki da raha da kuma saukin

kai, abin ya kan daure mun kai har nake

tunanin a raina tamfar ba ciki daya suka

fito da Ishak ba.

12

Shi ma idan ya dawo don kuwa yanzu

baya dadewa saboda yana zama hira da

Yayarshi, to sai ya kai karfe goma basu

kwanta ba suna hirar yan uwa da kumna

wasu al'amuransu can.

Zaman jegon da nayi mai cike da

nutsuwa da kwanciyar hankali shi ne yasa

kafin muyi kwanaki arba'in mun yi

bumbum gwanin sha'awa.

Babu abinda a yanzu nake tunawa

hankalina ya tashi irin na tuna watarana

dole Yaya ta tafi, hakan ne yasa muna hira

nayi nufin gwada yi mata tayin zama.

Ta kalle ni tayi murmushi ta ce, "Haba

Hauwa'u, koda ba ni da miji ai akwai

harkoki da nake yi a can na sana'o'i, ga

kuma yara."

Na ce, Yaya ai sun girma. Ta ce, Eh to

sun girma amma Rukayya fa? Na ce

wacece Rukayya? Ta ce, "A'a ba ki san

Rukayyar ba kuma yau? Yarinyar Isiyaku

mana.

13

Abin kawai sai ya dibibice mun har na

rasa waye ma Isiyaku. Ita kuwa maganarta

ta ci gaba da yi wacce ko fahimta bana yi

saboda ganewan da nayi Ishak take nufi.

Ai tun da uwarta ta dawo da ita tana

shan nono watanninta goma ta ajiyeta tare

da dan uwanta sai kawai naje na debo su

na zo nake rike da su.

Ba karamar dauriya nayi ba lokacin da

na cewa Yaya to amma Yaya ita me yasa

tayi hakan?

Ta ce, To halin su na yara mana daga

ita har shi din wanda rashin hakuri yasa

suka yi rabuwar da bata dace ba.

Ai shi Isiyaku ma naga ya canza gaba

daya yanzu kamar ba shi ba, duk wasu

abubuwan da yake yi a da can ya daina su.

Don ko matar da ya sake aura bayan

uwar su Rukayya ai bata zauna ba don ita

kam ma ai bata haihu da shi ba.

Ke dai kiyi hakuri da abin da za kigani

Wanda ba zai yi miki dadi ba, don shi

14

aure ba ka samun shi yadda kayi zaton

shi."

Maganar da Y aya tayi ya haifar mun da

wani abu a cikin raina mai ciwon gaske.

Bai taba gaya mun zancen auren da yayi

har guda biyu ba da kuma 'ya'ya.

Menene nufinshi nayin hakan? Yana

tunanin wataran ba zan sani ba ne ko kuwa

nima bal shirya zama da ni zuwa ranar da

zan sani ba ne?

Abinda ya tsaya mun a rai kenan. Babu

wata mata da zata iya zama da Ishak idan

har ba hakurinta ne ya kai inda ya kai ba.

Mace maras hakuri kuwa to babu inda

aurenta zai kai da Ishak. Babu ko tantama

abubuwan da yake yi ne sura ga ba za su

lamunta ba.

Kenan halin shi ne ba kuma zai daina

ba.Tunda ai an ce hali zanen dutse.

Taimako daya zan yiwa kaina shine na

tsaya tsayin daka na ga na koma

15



Makaranta kamar yadda tun farko va

alkawarta.

Gaba daya hirar ta daina mun dadi don

haka sallama nayi wa Yaya na shiga daki

na kwanta ba don nayi barci ba.

Don kuwa wane ni! Ina jin dawowarshi

ko motsawa ban yi ba ballantana naje yi

mishi sannu. Yau sun kai sha daya suna

hirarsu ina jinsu.

Sai a yanzu ne na gane ai dama can idan

suna irin wadannan hirarrakin suna yawan

ambaton sunan Rukayya da Anas da alama

shi ne babban. Ban san lokacin da barci ya

dauke ni ba.

Da safe kuwa da na tashi bin Ishak da

kallo na rinka yi ina kara jinjina hali irin

nashi.

Shiri sosai muka wayi gari yau muna yi

saboda gobe ne zamu yi fitan arba'in.

Yaya ce da kanta ta bada lissafin abinda za

a siyo mata na yin sadaka.

16

Tayi



funkasau



da



fanke.



Ta



bi

makwabta



gaba



daya



ta



rarraba



nima



ta

bayar



da



na



gidanmu



aka



kai.

Washegari



kuwa



ta



kama



Asabar

kwalliya



sosai



nayi



ta



burgewa



da



nufin

Zuwa



gidanmu



sai



Yaya



ta



ce



a'a



ba



haka

ake



yi



ba



nabi



makwabtana



mu



gaisa

saboda



hidimar



da



suka



yi



suma



suji



dadi.

Ina



kallon



Ishak



in



ba



don



ban



taba



jin

yayi



musu



da



Yaya



na



tabbata



da



ya



hana,

don



kuwa



tana



fada



naga



yanayin

fuskarshi



ta



canza.

Yana



zaune



rike



da



Abulkhairi



a

hannunshi



wanda



ya



zama



tamfar



dan



wata

uku



ba



shi



da



niyyar



miko



mun



shi,



ni

kuma



ban



ce



ba



ni



shi



ba,



na



gaji



da



jira



na

kama



hanyar



fita



tare



da



yi



ma



Yaya



sai



na

dawo.

Ta



ce,Yau



ji



mun



yarinya



za



ki



tafi



ne

ki



bar



yaron



a



gida



ki



kai



musu



kanki?



Na

dawo



da



baya



ta



kalle



shi.



17

"To kai kuma bata shi mana. Ya miko

mun yaron na kara gyara mishi ruhuwa na

juya zan fita ya ce Ke zo nan. Na dawo

na ce, "Ga ni."

"Tafi ki cire gyalen nan ki dauko hijab

na ce, "To". Har da na dauko hijabin ma

abin bai yi mishi ba sai da ya ce na goya

yaron duk kuwa da shi ma yasan a iyakar

unguwarmu zan tsaya, ban ki ba nayi

yadda yace.

Gidansu Hindu na fara shiga muma

sosai Momi tayi yadda dama can take yi

mun. Tasa hannu ta karbi Abulkhairi tana

rike dashi tana yaba yaron.

Ni dai duk kunyar Momi ta baibaye m,

ko nuna mun alamar ta san abin da Ishak

ya yi musu bata yi.

Na ce, Momi ina Hindu? Ta ce, Tana

wanka yanzu.zata fito. Muna zaune kuwa

sai gata, tsalle tayi ta rungume ni Maman

Abulkhairi!

18

Na ture ta na ce, Ban son wulakanci,

Momi ta ce, A to gaya mata dai mara

kunya. Ta karbi yaron ta zuba mishi ido

can ta ce, Gaskiya Momi mu ma ta karo

mana baby dubi yaron nan kamar na sace.

Hindu ce ta ce, na jirata ta shirya ta raka

ni gidajen da za ni, har cikin raina hakan

yayi mun dadi, don kuwa wasu da yawa

ban ma san su ba.

Muka fito daga dakin Momi ta miko

mun leda mai shake da turaruka na dakin

da na jiki da kuma magunguna ta ce Hindu

ta rike mun.

Godiya sosai nayi mata muka fito, mun

fito kofar gida kenan sai kawai muka yi

ido hudu da Ishak yana tsaye a kofar

gidanmu ya zuba hannayea aljihun

wandon jeans din da yake sanye da shi.

Kamar yadda na dake haka Hindu ma

muka wuce muka shiga wani gidan.

19

Alheri sosai 'yan unguwar mu suka yi

mun na kuma kudura a raina ba zan sake

zama ba na mu'amalla da su ba.

A kofar gida Hindu ta tsaya ta miko

mun Abulkhairi alamar ba za ta shiga

gidanmu ba.

Ni ma ban ce ta shiga ba, nayi mata

godiya na kawo alheri cikin wanda na

samu na bata ta ki karba nayi rantsuwa na

ce ai sai ta karba, hakan ne yasa ta karba.

Na shigo gida Ishak yana zaune a kan

kujera one sitter Yaya bata dakin alamar

tana kicin ko ta shiga bandaki.

Ban ce mishi komai ba nayi wucewata

daki. Na ajiye kayan da ke hannuna na

kwance goyon Abulkhairi na ajiye shi a

kan gado kenan na juyo na ganshi tsaye a

kaina.

Yanayin shi yasa ni ja da baya. "Ban ce

miki bana so kina mu'amalla da wadannan

mutanen ba iye? Keta dokata da ki ka yi

20

bata ishe ki ba shi ne ki ka je ki ka bata

dana tana goyawa?"

Bude baki nayi da nufin yin magana

kawai Ishak ya dauke ni da marin da sai

da na kifa a kan dressing mirrow

Ihuna da Yaya taji ne yasa ta tahowa da

sauri. Ta kama salati ganin da tayi har

bakina ya fashe, kuka nake yi sosai itama

Yayan haka tana cewa.

"Ashe baka bari ba Isiyaku, to yaushe

kuma? lye na ce maka sai yaushe kenan?

Wannan yarınya menene aibunta'?

Ya tsaya zai fara yi mata bayani ta

dakatar dashi ta ce, Bana son ji. Na kuma

fahimci zamana a gidanka ne ya isheka

dama kuma nayi abinda ya kawo ni

magana ta kare."

Wucewa Ishak ya yi ya fita ni kuma

naje na wanke bakina da ke ta fitar da jini

saboda buguwar da nayi kan madubi

hakan har idona na gefen d na fadi ya tara

jini.

21

Ita kuwa har yanzu Yaya kuka take yi

saboda cin zali yarinya na jego? Wane irin

hali ne wannan?

Har da rokon Yaya da na zauna nayi ta

yi bata fasa shirin ta ba. Ta rantse akan

gobe zata tafi. Ba dukana da Ishak yayi ba

ne damuwata, tafiyar Yaya ne.

Don kuwa nasan tana barin gidan zamu

koma zamanmu na baya. Na durkusa a

gabanta na ce "Yaya don Allah kiyi hakuri

ki zauna ko sati biyu ki kara kin ji?"

Ta zuba mun ido. Zuwa can ta ce

"Aiya! Abinda dan uwana yayi miki bai

6ata miki rai ba, don na dan faranta mata

sai na ce eh Yaya."

Ta ce, Ikon Allah kenan yanayin wanda

yafi haka. Kin ga kuwa ba zan tsaya sai an

yi kafin na tafi ba ko? Babu yadda na iya

da ita don haka na shiga daki na dauko

1 / 5