Author : Aisha Maman Teddy Category : Taskar Novels
Murmushi oumman tayi bata ce mata komai ba ta cigabada da Zan caxbihan
ta,tana mawa Kansu Addu'a".
*******************
ADAMAWA
Gidan Alh. Abubakar barau ne,wanda Akafi sanin sa kuma ake kiransa da (Alh. Habu
Maloniya....)tun daga farkon sa har karshen sa mutane yayyame,yan Uwa da Abokan Arxiki
duka Ana cikin farin cikin Dawowar Alh. Abubakar maloniyan,bisa ga jinyan da yayi na tsawon
shekaru uku baya.....wanda alhmdllh a wannan Rana ne jirgin sa zai sauka gida Nigeria. Kowa
a familyn farin ciki yake matuka da Dawo wans,wannan shahararran Attajirin,da duk fadin
Nageria babu wanda baisan shi ba". Ko inah ne ya rikece,don har Hutu aka Saka,na babu aiki A
gaba daya kasar,na jimamin ranar da Diyar sa ta mutu tsawon shekaru uku Baya,wanda
wannan shine musabbabin kamuwar sa da ciwon Zuciya,da yadade yana jinya,a kasar China".
Wannan kuma Rana shine ranar da ta zagayo shekaru uku kenan da mutuwar diyar tasa". Gaba
daya fannin sadarwa ko inah amsa kuwa yake na Kara dadin ta'aziyar Yarinyan tasa Daya tilo
da yayi,da kuma farin cikin samuwar lafiyan sa". Duk girman gidan nasa,sai da ya kasance
babu masaka tsinke. Manyan mutane kusoshin gomnati da yan kasuwa,kowa Ya halitta gidan
Alh. Maloniya don Tarbansa,banda Wanda Suke a Airport suna Zaman jiran saukan sa". Omar"
Omar".... Cikin dajin Ba dadi da kuma fara fusata Omar din ya kalli Safwan da cewa" Ehemm
Oga Inajinka". Safwan ne ya sunkuyar da kansa kasa". Kawai sai Hawaye ya Fara bin kun
cinsa,wanda cikin sauri Omar yafara masa magana cike da Taushin murya da cewa" Haba
Safwan,yaushe ne kuma a watta rana,zakayi hakuri ka rungumi kaddara na Rashin Bul-bul a
Rayuwar ka??!. Tsawon shekaru uku ya kamata ka sani kayi hakuri kuma ka mance
dakomai,Addu'a Zakayi mata". Kai Hannun sa Safwan yayi gami da daukar Hankie yana Goge
hawayen kan fuskan sa,cikin Dauriya yace,Omar na dade da hakurin Rashin Little
bul-bul,Amma Zuciyata takasa Juremawa Rashin Ta kusa Dani". Da soyayyar Ta na taso,kuma
na girma,kuma dashi Zan mutu". Maryam da Sakkowanta kenan daga Step tana karakowa duk
maganar Sa ya sauka a kunnen ta,cike da Dauriya ta nufesa tana cewa" Yah Safwan na Tafi".
Kasa bata amsa yayi kawai sai dai daga mata kai". Omar ne yayi saurin cewa" Okay Maryam
sai mun karaso". Tom Allah ya kawoku lfy!!". Kan ya bata amsa tayi saurin ficewa daga
Dakin,Tana jin babu dad I,don tuni idon ta ya kawo ruwa". A cewanta itah da mijin ta,baya Nuna
mata kulawa da kauna,sai dai Kanwar sa matansa ta baya,wanda ta Dade da isah gidan
Gsky??!. Tuni hawaye ya jika fuskar ta,da Sauri ta shiga moto yayi da Driver ya rufo ta yana
zagayawa yana Jan ta don nufar gidan Alh. Abubakar Maloniya". Da fitan ta ne Omar ya kalli
Safwan yana cewa" Haba Safwan kayi hakuri ka ringa daure mawa Rashin bul-bul kodon
matarka,mata fa da kishi a kasansu,bazata ringa jin dadI ba". Nisawa Safwan yayi gami da tabe
baki,cike da Nuna ko ajikin sa,don shi a ko inah zai Nuna soyayyar Bul-bul,don baiki ya rabu da
kowa a kan ta ba,duk da ta Mutun,cike dajin ma zafin maganar Aminin nashi yace"Bai dameni
ba,Tun Kaminn na Auri Maryam,na fadeta cewa" Bazan sota kaman Nanah ba". Kuma bazan
hada soyayyar wata ya mace da itah ba,wannan alkawari ne nayi mata tun tana a Raye". Baki
sake Omar yake bin sa da kallo,Har Ya mike yana mayarda hularsa da cewa" Zamu iyah tafiya
don yanxu Daddy ya Sauka suna airport". Hmm babu magana Oamar ya mike hadi da ficewa
kowannen su moton sa ya hau hadi da nufan gidan Alh. maloniya". Zaune take Tasha Ado na
mata masuji da Aji,cikakkiyar mace wanda a shekaru zata kai Arba'in da biyar". Matace
dattijuwa maiji da Karfin dukiya ga Hutu,Wanda sanye take cikin Dinkin Shadda Yar galila mai
kyaun gaske". Wanda yake dauke da Launin Coffee brown". Hannun ta kam Tasha Jan lallae
wanda yake dauke da Awarwaron Gold. Fuskan nan babu wani make Powder sai lipglow
tasaka....amma abun ka ga farar fata tuni ta haskaka,hadi da haskaka Wurin". Daurin Ture kaga
tsiya tayi,yyn da tayi parking din kwantaccen Gashun ta mai tsantsi da sulbi ta kasa,daurin yayo
sama. Saman wuyan ta kam ta Zuma masa sarkar zinare,da sai walwali takeyi". Hajiya Latifah
kenan,mata kuma Uwar gida ta Wurin Alh. Abubakar Maloniya". Sunan mutanen ta na kyewaye
da itah ne,amma hankalin ta na kan Hoton diyar tata,da ta mutu shekaru uku baya,yarinya mai
shiga rai,wanda kallo daya nayi mata na fahimci baxata haura shekara Sha Bakwai a shekarun
ta na haihuwa ba".
Tom fah!!!!
Chakwakiyar nannadaddiya kenan..
Ko wacece wannan yarinyar Alh. Maloniya??.
Kuma wacece wannan yarinyar da shi kansa Safwan Abokin Omar ke mata irin wannan
Zababban son???...
Shikam Baba Jume wani irim mataccen Zuciya ne yake dashi haka,ace sai dai Makauniya da
Yar ka suje Maulah sinemo su baka,ka kuma am she kaci???
Muje xuwa
Domun samun Cigaban labarin Littafin Yar Maulah zaki turo katin #100 MTN,normal kenan.
Idan VIP da VTU ne #200
SPC kuma #300 Duka ta wannan number 08081202932.
Idan kuma Bank Account ne ta wannan
7782217014
Mohammed Hassana
Fcmb.
Sai kiyi screen shorting ki turo shaidar biyarki ta wannan Whatsaap numbern
08081202932.
Naji comment naku ina godiya Allah yabar kauna.
Ku tura zuwa wasu grps
Mmn teddy
[7/17, 12:38 PM] Maman Teddy: Typing.......
*Y'AR MAULAH*
Story and Written by:
Mmn teddyteddy
*Alheri writers asso.*
*A.W.A*
```K'ungiya daya tamkar da dubu,masu aiki da ilimin su.Alheri sai Dan Alheri```
______________________________________
5-6
"Karar motoci da Dana Mutanen da ya Karo yasakata fahimtan cewa" Alh.Abubakar maloniya
ya sauka". Wanda cike da isah da Aji ta mike,Sauran matan na bin da kirari,Uwar gida Ta
Alh.Maloniya. Tuni falon ya rikice da guda na Mata,Murmushi kawai take binsu dashi,wanda a
hakan ta nufi Farfajiyar gidan,yan Uwanta da ma'aikatan ta na Mara mata baya". Farfajiyar
gidan Babu masaka tsinke....domun ko ta koinah Mutane ne kye Bulbulowa". Wanda basu San
ma daga inda suke ba". Nufo Mai gidan Nata tayi,a yau duk wani Annuri ya bayyana a saman
fuskanta". Hayaniya ne ya karcame,yayin da Masu maulah da Maroka,suka Fara kirari da cewa"
Allahu Akbar....Uwar gida Rangida,mata Tauraruwa mai Haskawa ta wajen Alh. maloniya uban
B'ull...... Maganan Marokan ne ya datse,tuno da Abun dake faruwa,wurin kam duk yawan
biladam nan,tsit kakeji,sai dai saukar numfashi. Cike da Dakiya da sanin Famin dasuka Dago
masa,ya Fara Kitsawa hadi da nifan Bangaren shi". Wanda tuni idon Hjy. Latifah ya kawo
Ruwa". Kasa bin bayan mijin Nata tayi,kawai sai ta juya hadi da nufar Part din ta". Aminan tane
da Yan Uwa sukayo bayan ta,don Tabbas a yau sun San An debo mata Abun da ta
mantashi,tayo hakuri ta kuma Dangana". Duk damuwar da Maryam ke ciki,awannan karon
nufan Hajiya Latifah tayi don Rarrashin ta". Duk da taasan itama Nata damuwar duk akan
wannan Yarinyar ce B'ul-b'ul.
"Maryam yana kejin kaman muryanki na cikin wata damuwa"?.Hmm Laylah kenan,aini dama
Kullum indai damuwa ne a cikin ta nake". Wlh har nagaji da itah,Amma Yaya xanyi tunda
Damuwar ta xama jinin jikina,dole sai Hakuri". Hajiya Layla dake kishin Gide ana yarfa mata
Lallaen Zane ne,ta mike daga Zaune,tana Fadin" Hmmm ban gane ba??. Meke faruwa ne,badai
har Yanxu Safwan Ranshi da koman shi na kan wannan Shegiyar yarinyar ba?". Daya bangaren
ne Maryam tace" Layla kenan,tom ya zanyi,na Auri wanda yake mawa tsohuwar matarsa
Kaunar daukar rai,Sakaci nane tun baya Dana Bari So da Kaunar Safwan suka taru sukayi mun
yawa". Har takai ma na Amince duk da baya sona!!!, na Aure shi. amma Sam bansan Yaya
Allah zaiyi Dani ba,tabbas nasan ina hakuri,kuma ina kokarin cinye Jarabtar da Allah yayimun".
Tab". Ikon Allah!!!. Layla ne mai fadin wannan maganar tana,Kara jajanta mawa Maatan Abokin
mijin Nata". Hmmm duk naji Abun da kkce,Amma ki sani ki ajiye wannan Hakurin naki a
gyefe,domun ko Hakuri shi ya kashe Jaki!!. Kya macace mai bukatan ana nunawa so da
Tattali....Don ki ajiye maganar matacciya a gyefe,don a yanxu matar Safwan,ko nace matar da
akayi masu baiko ta mutu,kyece dai matar,kuma dole ki rage Son Safwan ki Fara Nina masa
kyema din Macace kamar kowa....ko yanuna maki so,ko kuma ya jingine Son Wannan Yarinya
watake....? Bull...waye oho dao". Hmmm nisawa Maryam tayi don duka maganar Layla taji babu
na Dauka". Tom Layla Zan yi tunanin akan maganan ki!. Kwarai kam...gsky kiyi tunani,Ya
kwanan Bby na?!. Dariya Maryam tayi tana shafa Litsetsen Cikin ta da ya turo sannan tace"
Bby ki na lfy....? Yaushe ne Zaki Bamu naki Bbyn???.
Hmmm kye Maryam rabani!!. Inahh,gsky ban shirya Haihuwa yanxu ba". Shuru Maryam tayi,kan
tace" Hmmm amma kinsan Omar na Da Son yara ko??. Kuma ai ma yy maki hakuri shekara 5
fah Yabarki yana biye maki??.
Tom Maryam,ba dole ya kyaleni ba". Ai yasan bashi kye nakudar ba!. Hmmm Amma bakya
tunanin ya gaji da Wannan Jan ajin naki??. Gajiya tom me kke nufi kenan??? At any time Omar
zai iyah yi maki Kishiya,yana bala'in son yara,tun kan kuyi Aure kksan da Haka!!. Tom don
nasan da hakan sai mene?? Ina fada maki wlh wargi wuri ya samu. Omar bazai tabs gigun Aure
ba,shi baya ma da Irin wannan kalle²n ko son Hakan.don No baba Damuwa Wai don naji Omar
na Waya da mace,babu mai iya jure masa saini,Omar tamkar gogawa ne,mai turkanan sa idan
ya daga,sai wanda yasan Gabansa da Bayansa!!. Hmmm Maryam ba wani magana ba,nice dai
Matar Omar Amarya kuma Uwar gida". Babu mahalin wani ko Wata a cikin zuciyar miji na, sai
dai ni dai Layla!.
Dariya Maryam tasaka,tana cewa" Wow gsky K'awata kinyi dace". Inama nine kye??. Hmmm
kyema ai kinyi dacen...don Safwan miji ne,wannan Yarinyan itace tayi maki Katanga da
Soyayyar mijin ki,sai kiyi ta Neman hirji da itah". A haka dai sukayi sallama. Kan Hajiya Layla ta
kalli Asabe cike da Masifah tace" kehhh Wata kalon Dabba Ce??. Sau nawa ne zanyi ta maki
mgn akan Abu daya. Jiki na Rawa Asabe tafara cewa" Tuba nake Hjy.Don Allah kiyi hakuri".
Dogon tsaki Tajah Kan ta kauda kai.....tana cigaba da Danna tafkeken Wayar ta".
"Yau a cikin gidannan babu inda Zakuje,Wlh na gaji da Zubar mun da mutuncin da kkyi na
Wannan Maulan!. Baba Jume ne mai wannan maganan yana yi yana daga makoshi". Lalubar
sandar ta Oumma tayi tana lalube da cewa" Haba Malam,idan bamuje Maulah munyi bara
anbamu ba,da yunwa ne zamu zauna?? Kaifa ba nemo wa kk ka bamu ba".
Banyarda ba wlh....ko kye xaki je sai dai kye daya,ba da y'ata ba. Na fada maki. Yana fadin
haka ya juya hadi da ficewa daga kuntacaccen gidan yana Dada sababi har waje". Idon
Safiyyatu ne ya ciko da Kwalah,zaunar da Makauniyar Mahaifiyar Nata tayi,tana aikin rarrashin
ta kaman kullum,don Allah Oumma kiyi hakuri,ki kyale Baba". Tom Safiyyatu yaya zamuyi yau?.
Gashi bama da Abincin da zamu ci?!. Oumma kar ki damu da Akwai Naira Hamsun,sai yanxu
nayi Sauri naje shagon niga na sayo Gari da siga".
Nisawa Oumma tayi cike da hamdllah da gode maww Allah tace" Yowa maza tashi kije ki
sayo......kamin ya dawo,shuma yace zaisha shi!. Tom Oumma.
Fitan Safiyyatu ke da wuya ne tafita layin su hadi da Tsallaka titi,bayan ta sayo garirogon ne,Ta
nufo titin ta Zumar ta Tsallako....Wanda sabd yunwa bata ko kallon gabanta". Karar birki taji
anjah shi da karfin gaske....Wanda nan take jikin ta ya hau rawar kyarma". Jikakke
kuuuuuu.....Tayar tana gogar Kwaltah.........
Share to another grps
Mmn teddy
[7/18, 6:13 AM] Maman Teddy: *Loading.....*
*YAR MAULAH*
_Written by: Mmn teddy_
*SADAUKARWA*
°°°°°°°Wannan littafin sadaukar wane ga Teddyna. Allah yayi ma Rayuwar ki Albarka,d'iyar
Mmn tah".
*TUKWICI*
Tukwici ne gareku mutan kungiya ta, Wato Alheri Writers association,baxan manta daku ba,har
ilah yau inai maku son so fisabillah!!!.
*ABIN ALFAHARI*
Mahaifiyata Abin Alfahiri na,ina kara godiya a bisa ga tarbiyar, da kulawar da kk bani,Allah ya
karemun ke daga Sharrin mai sharri...Allah kuma yaka wanxar maki da xamar lafy,kwanciyar
hankali mai Dorewa Ameen".
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*ALHERI WRITER ASSO.️*
*A.W.A*
©©©©©©©©©©©©©©©©©©©©©
_____________________________________
```Kungiya daya tamkar da dubu,masu rubutu don fadakarwa,da nishadantar da
Al'ummah,Alheri sai d'an Alheri```
https://www.facebook.com/100186388252056/posts/100188104918551/
••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
Da Sunan Allah mai Rahma mai jinkai!!.( In the name of Allah...)
Plz don Allah Hjy indai kinsan baxaki rinka sharhi ( Comment) ba,karki karantamun labari final".
Masu comment ina matukar godiya,Allah yabar kauna...❤️
7-8
Kaman zata kwalah ihu don Tashin hankali,amma a haka ta dake, tsoro yasakata sakin garin
rogon da sugar,tuni ya ledar ta fashe saman Kwalta.....hawaye ne yafara bin kuncinta". Wanda
bata Ankara ba taji Muryan Mutum a saman kanta". Omar kenan". Kehhh Wata kalan
Dabbace???. Bakya gani ne?, ko kye malauniya Ce??. Ya fadi maganan a hasalah,Shiru ta
masa,wanda ta kasa Ce masa komai". Kawai sai ta duka tana Tattara Garin ta tana kwashewa
tana kuka". Bai bi ta kanta ba ya cigaba da mata cim mutuncin shi.
Wanda kamin ta ankare yajah motonshi da matsiyacin gudu ya figeta". Sai a sannan Safiyyatu
ta sami damar Kare mawa shimfidediyar lafiyayyan moton kallo". A haka tana Kuka ta tattara
garirogon,hadi da nufan gida". Da isanta gida ne ta Zauna A turbayan tsakar gidan,tana cigaba
da kukan ta kasa² Gudun kar Oum n ta tajiyo ta".
Shikam Baba jume da fitansa,ne ya dawo cike da Farin ciki yana aikin Kwada kirar Sunan
Safiyyah".
"Safiyyah" Safiyyatu". Sam bai Lura da itah a tsakar gidan ba,sai da yaji amsawan ta tana fadin
na'am Baba". Saurin kallon Gyefen sa yayi ya ganta rakube tana Hawaye". Saka taffan ta tayi
tana gogewa". Cike dajin Tausayin su,don a tunanin sa Kukan da takeyi saboda hanata maulan
ne shine yasa".
Samun Wuri yayi ya zauna a wurin,wanda cike da Taushi da Rarrashin murya ya me cewa"
Safiyyatu kuka kkyi,don na hanaku Xuwa Barar Maulah. Nasan tunanin ki abincin da xakuci
ne,nikuma ba nemowa nake na Baku ba". Kuyi hakuri nasan bana kyauta maku". Amma Ba ina
hanaku Maulah bane sabd Wai tsanar ku danayi,A'a saboda son danake maku ne". Safiyyatu
ina tsoron kar Ki kuma haduwa da Irin Wa'annan miyagun mutanen da suka nemi Halakar da
Rayuwar ki a shekarun baya ne". Safiyyatu babu abun da xan yi na taimakon ki,face shine na
kareki daga duk wani mai son cutar dake".
Kinga fitana Ne amini na Malam Audu,Yake sanar mun cewa" Da Akwai wani ma'aikata suna
bukatar ma'aikaciyar da xata ringayi masu goge kaman Mutane Biyar. Shine da fadamun nayi
hanxarin xuwa na fadeki,kinga da allah ya taimaka kin samu,shikenan sai ki ajiye Maular a
gyefe".
Cike da Farin ciki ta saka Hannu ta Amshi takardar Hannun Baban Nata". Tana Dan murmushi
da cewa" Tom Baba,ai bari yanxu na je Inna samu tom,in an samu ba,dama Allah ya rubuta
hakan!!". Yowa Safiyyatu Allah yayi mawa Rayuwar ki Albarka". Ina matukar gdy ga Allah da
yabani kye kadai a matsayin y'a,Wanda take Yarda da kaddarar ta mai kyau ko Mara kyau".
Murmushi tayi kurum hadi da nufan cikin madafin su. Ta fiddo wasu tsofaffin Kodaddun Robobi
guda Biyu". Tana xuba garirogon da yayi kasa hadi da xuba ruwa tafara rege kasar cikinta". Bin
da kallo Baba yayi,kana yace" Mai yasamu Garin Safiyyatu".?
Sai a lokacin ta kwashe komai da yafaru har xagin da Wannan mutumin ya Yi mata ta fadi
mawa baba jume,sannan a sannan ya fahimci Kukan da takeyi,ta karke fada masa tana kuma
goge guntun Hawwaye".
Hakuri yayi ta bata,kan ta kammala hadawa,ta nufi dakin Oumman ta tana mika mata da cewa"
Oumma Bari na zo!!. Tom Safiyyatu". Oumman tace tana saka Hannu hadi da lalubar Robar ta
dauka hadi da Fara cin garin,tana kuma godiya mawa,Allah da ya axirtasu da Kamilliyar yarinya
Wato Safiyyatu,don da Dabata bakaramun Wahala suka sha ba".
A tsakar gida ma Baban Nata ta mika mawa". Wanda anan shima dayake zuciya ya mutu,yayi
ta washe baki. Yana saka mata Albarka". Itakam da Sauri ta xara Kodaddan Hijab din ta,tana
fadin Baba Bari naje na dawo!!". Ina kuma zakije Safiyyatu?".
Murmushi tayi tana cewa" Zanje wannan ma'aikatan ne". Kasan Baba Fara Abu da Wuri
yafi,musamman gamu yayan da ba kowa ba".Kwarai kuwa Safiyyatu haka yake,Alllah ya bada
sa'a. Yayi kiyaye". Ameen tace hadi da ficewa gidan".
Da fitan tane tajiyo muryan Kananun yara wanda a shekaru bazasu Haura Share biyu sha uku
ba,suna mata wake,kaman yanda suka Saba,don Layin na su babu tarbiya sam. Don wani iro
Ne yasaka su,su ronka mata hakan,yana basu Alawa". "Safiyyatu Yar makauniya....Safiyyatu
Yarinyar makauniya....Uba ba zuciya....Uwa Babu Idon da daza ta nema!!!.
Kwallah ne ya ciko idon Safiyyah,amma sai ta dake hango Iro xaune yana Aikin Dariyan mugun
Abun da ya saka su yi mata".
Wuce su tayi bata Ce komai,saiga Malam Audu,aiko nan yabi yaran Hadi da cire ta kalmin kafan
sa yabisu dashi". Allah kam yabashi sa'ar Kama Babban daga ciki,Wanda shi yake jagorantar
su". Yasha lafta yana Dukan yaron,wanda nan take yaron yafara kuka yana bashi Hakuri".
Shikam Iro nan take Malam Audu