ZAKI BOOK HAUSA NOVELS BY MAMAN TEDDY.pdf

Author :  Aisha Maman Teddy Category :  Taskar Novels

Chapter   3 / 17

6K to 9K   out of 49.8K words

barin Wurin ransa yayi ƙarshen ɓaci ,musamman data fara yunƙurin tado masa da Famin sa na
tsawon shekaru .

*Ƙauran kuregu*

Ganin irin cin mutuncin da Baba Ilu yake mawa Mama Abu yasa ka A'ee cike da Damuwa saurin dakatar da
mahaifin nata ta hanyar cewa “ A'a Baba Bafa da gangar Mama ta yarda ba .
Zaki ci ubanki ne! Ni kike maidawa magana? Wato kina ƙare ta kenan? Zaki ga Abin da zan miki, Tun da na
haife ki ban ga Abu daya da kika taɓa yi na kullamun ba a Duniya . Don haka aikatau zan nema miki a birni
ki nemo mana kudi ai kin kai minxalin da mu ya kamata ne mu huta”. Yana faɗin haka ya juya fuuuuu yana
barin Wannan gona , yayin da Mama Abu jiki na rawa ta kalli ɗiyar nata tana cewa “ A'a A'ieee ,sam kar ki
damu da maganar sa , muna nan tare , babu abin da zai raba mu sai Auren ki . Babu inda zakije kinnji?

Jiki a sanyaye A'iee ta cigaba da Aikin girbin amma a zuciyar ta duk yayi sanyi bisa Abubuwan da suka faru
tare da kalaman Mahaifin nata. A jikin ta take jin Abubuwa marasa dadi tare da Sanin waye mahaifin nata
Ilu da idan ya faɗi abu cika sa abu ne mai sauƙi A gare sa musamman akan ta . Da yake sauƙe duk wani
tarin tsiyar sa da Masifar sa , Tun da suke a kaf ƙauyen nan basu taɓa haɗuwa da tijararren mutum irin
Baba ilu ba . Komai ya tara akan sa . Ga shaye shaye ga Rashin kirki ga kuma caca, komai yin sa yake yi .
Tsofai tsofai dashi don ya manyanta amma wani abin da yake yaro ƙarami ba zai yi ba .

Mama!

A'iee ce ta kira sunan mahaifiyar nata a sanyaye cikin taushin murya ,wanda kamin Mama Abu tace wani
Abu ta tsinkayi Muryar A'iee tana cewa “ Mama Anya Kuwa Baba shine Ya haife Ni? ”.

Wani irin bugawa ƙirjin Mama Abu yayi da ƙarfi bisa ga jin kalaman A'iee da suke fitowa daga bakin ta , Da
sauri da sauri ƙirjinta ke bugawa bakin ta na Rawa haka jikin ta . In...inj....inji wa ya faɗa Miki hakan A'isha?
Ko kaɗan kar Na sake jin wannan daga bakin ki waye zai haife ki a duniyar nan idan ba Ilu ba ?”. Kiyi Haƙuri
Mama bana faɗa Miki don ɗaga hankalin ki bane ba .
Girgiza kai Mama Abu tayi tare da Sauke ajiyar zuciya tana mai cewa “ A'a Kar na sake jin wannan zancen
daga bakin ki kina kina ko?”. Maza mu ƙwashe wanda muka cira gobe in Allah ya kai mu sai mu cigaba”.

Gyaɗa kai A'iee tayi tana fara tattarawa yayin da har a lokacin Mama Abu zuciyar ta bata da sukuni wani
irin buga mata yake yi ga gumin dake sauko mata ”.
**
Shigowar motoci Masu nishi asalin manyan motoci wanda ya girmi ƙaramin mai ƙuɗi ixuwa cikin gidan
Alhaji Bukar Macciɗo ya saka Fahad dake Ɗakin sa saurin fitowa a tunanin sa Masu har kar siyasan
mahaifin sa ne , Wanda suke so tsayawa wasu muƙaman wanda sai da hannun Mahaifin nasa , Sanin
Ƙaramin ƙyautar da suke samu daga gare su shine million Biyar goma yasaka Fahad fitowa don ya samu
rabon sa . A daga saman benen Ya tsaya yana saka hannun sa tare da mamakin ganin me fitowa daga Ɗaya
daga cikin motocin da suka cika gidan baki ɗaya .

Ƙurrrr yayi ma Fuskarsa wanda yafi kama masa dana Turawa har hasken sa , Wuyan sa ya kalla inda ya
hango Cross tare da kallon gyefen kunnen sa da ya sanya ɗan kunne . A'a Wannan ba Musulmi ba ne
baya furta yana mai mamakin me ya kawo sa cikin gidan ? A har kar siyasan Daddy har da arna kenan?
To shi kuma wannan saurayin me yake da buƙata? .
Alexander kuwa tsayawa yayi yana ƙare ma gidan kallo , ba tare da ya sauke baƙar gilashin idon sa ba . A
haka idanun sa suka sauka akan Fahad da ya tsaya sororo yana kallan su . Hannun sa ya ɗaga yana kallon
Fahad inda tamkar wanda yayi ma kiranye Fahad ya fara saukowa daga Up stairs din yana takowa zuwa
inda Alex da mutanen sa suke!�tirƙashi
Anya Alex babu Tsafi a lamarin sa kuwa?

Duk rashin kunyar fahad yayi biyayya lallai da drama a cikin wannan tafiyar miƙaƙaƙƙa . Kedai kada ki
bari a baki labari.

**

Da Sanyin safiya A'ieee ce take sharar tsakar gida yayin da Mama Abu ke Aikin hada wutar icen Ƙara don
dama masu kunun gyero .

Bayan Ai'ee ta kammala sharar ne ta iso inda Mama Abu ke sharce gumin saman gashin ta , tana Firfita
karan da shima yaƙi kamawa saboda yasha dukan ruwa ”. Mama kawo na Firfita Miki!

A hankali Mama Abu ta dubi A'iee tare da cewa “ Har kin gama sharan,sannu da Aiki”. Ba tare da A'ieee
tace komai ba ta saki murmushi tana kai hannun ta tare da Amsan Abin da mama ke firfita dashi tana
farawa . Cikin ikon Allah ba tare da ta dauki tsawon lokaci ba icen karan ya kama , Wannan yasa ka su duka
numfasawa fuskar su na fidda Annuri .
Mama idan nayi Kuɗi ba zan Bari ki cigaba da Amfani da itace ko kara ba wurin yi mana girki . Irin Abin nan
da Salmatun Mai shanu take dashi zan siya miki ”.

Kai A'iee yana da tsada sosai , sunan shi Risho naji suna cewa , da kalanzir ake amfani dashi. Duk kuɗin
sa Mama Zan siya Miki idan na ƙara girma ”.

ALLAH sarki! Mama Abu ta furta tana girgiza kai ƙwallah na ciko ƙwarmin idon ta ”. Kamin tayi magana ne
Motsin shigowar Baba ilu ya sa su duka ɗagowa suna zuba idanun su gare shi ”. Mamaki ne ya kama
Mama Abu Ganin Malam Ilu da Wasu mata su biyu Alamu ba A wannan ƙauyen suke ba ”. Don ba suyi
kama da ƴan ƙauye ba sam ”. Zaf zaf zaf ya iso inda Ai'ee take yana kama hannun ta tare da Ingizata ga
Wannan matan yana cewa “ Gata nan ku tafi da ita ”.

Innalillahi wai'innah....Kafin Mama ta ƙarike ne tuni Baba ya riƙa yana cewa su tafi da Ai'eee. Kuka Ai'ee ta
saka tana kiran sunan Mama yayin da Mama Abu itama kuka take yi tana kiran sunan Ai'eeeee duk kokarin
ƙwace kan ta da Ai'ee keyi amma ina wannan matan sunfi ƙarfin ta , tuni suka fice da ita daga gidan , suna
jefa ta cikin moton su tare da ja da ƙarfi suna mai kokarin barin ƙauyen .
Wayyo Ilu ka cuce Ni ka rabani da ƴa ta ɗaya tilo...cikin doka Tsawa Ilu yake faɗin ke sakarya aikatau zata yi
a birni kin san kudin da zata samo mana ne? Yanzu kin san nawa Duka bani dubu ɗari da hamsin to inaga ta
fara yi masu Aikin kuma????? #babban magana .

To ku mu haɗu a page 5 don jin ya zata kaya ...littafin zaki a page 6 free page zai ƙare maxa hanzarta don ki
samu ayi tafiyar dake. Regular group ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299
Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932.
[5/21, 7:24 PM] Abu~ammar: *ZAKI*
_*The story of courage in hero's journey with secret desire*_



Free page 5

*A page na gaba free page zai ƙare . Ga masu buƙatar shiga grp na wannan littafi Regular group₦500 Vip
group₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta
Wannan number 08081202932*

_________________________

Ilu.....!

Mama Abu ta kira sunan sa cike da Wani irin mamaki tare da mutuwar jiki , hawaye masu ɗumi da zafi na
bin kuncinta . Ilu Yanzu A'ieee ce ka kai Aikatau? An mana halarci an mana Abun Arziƙi da Wannan yarinyar
Marainiyar Allah an bamu , ashe Ni nasan darajarta kai a banza wofi kake kallon ta . Saboda baka san zafin
ta ba shine ka miƙa ta Aikatau ? , Ilu ka daɗe kana cutar da Rayuwar mu Amma Wannan yafi na kullum .
Babu ko nadama bare dana sani yake bin Mama Abu da Wani ƙasƙantaccen kallo ,hakan ya ƙara tunzira
zuciyar mama Abu . Tabbas yanda ka bar Da A'iee cikin gidan nan nima yau zan bar maka gidan ka , kuma
ka shirya ma ganin komai na hukunci daga gareni .

Cike da Muryar sa ta yan karta ya furta “ Tafi mana , Daga An tura yarinya Aikatau nan na faɗa Miki dubu
ɗari da hamsin suka fara badawa ,me makon mu haɗu a rufa ma juna Asiri ,ashe ke ba matar rufin Asiri
bane . Haba malam Ilu! Rufin Asiri na nawa ? Har wani rufin Asiri kake buƙata bayan wanda muke haduwa
muyi maka da Wannan yarinya . Kuka ta fashe dashi tana nufar Ɗakinta tana mai cewa “ Ƙwana ɗaya na
baka kaje ka dawo mun da A'ieee ban yarda a daukin mun yarinya a kai ta Aikatau ba. Tana gama faɗin
haka ta shige Ɗakin ta yayin da Malam Ilu a zuciyar sa ya furta ke da ganin ta sai bayan shekara guda,don
haka suka ce . Ni bari naje Wurin Ado mai balongo ma na fara cin daɗi da kuɗina ”.

**
Ina Tsohon ka?”.

Alexander ya furta yana duban Fahad wanda jiki a mace ya furta yana ciki . Kamin Alexander yayi magana
ne Wani Na hannun daman sa Wato mickel ya furta “ Muje kayi mana iso.! Babu musu ya fara yin gaba
suna bin sa a baya ixuwa Falon Hajiya Turai, A sanin su babu wani bare dake isowa har cikin wannan falo
amma yau ga Fahad tafe dasu Alexander da tawagarsa.
Diyana ce dake saukowa daga Stairs ta tsaya sororo tana bin Fahad da Kallon wato rashin jin nasa har ya kai
ya shigo falon Mami da Tawagarsa ?” . Ganin bai tsaya nan ba ya wuce dasu under ground ɗakin sirrin
Alhaji Bukar Macciɗo dake ƙasa yasa ka Diyana Saurin juyawa tana nufar Inda Hajiya Turai take don ta
cimma ta ”.
Mami...! Mami....!! Ta hau ƙwaɗa kiranta har sau biyu wannan yasa Hajiya Turai dake kishingiɗe tana Waya
saurin datsewa tare da juyawa tana kallon hanyar Da Diyana ke shigowa .

Mami Yanzu abun na Fahad har ya kai haka ? Ya wuto ko ina na cikin gidan nan ya tsallake babban falon ki
har ya wuce under ground na Daddy da Wasu mutane kuma da ganin su ba musulmai bane don a fuskar su
babu Alamar Tsoron Allah . Goshin su kuwa har kyalli yake yi . A takaice shi babban nasu ma Cross a wuyan
shi �What? Cross fa kika ce? Saurin gyaɗa kai Diyana tayi tare da cewa “ Ƙwarai kuwa ” .
**

Ita dai A'ieee ganin ta ci kukan tayi tayi babu mai Rarrashin ta a wannan matan yasa ta share hawayen ta
tana jan Ajiyar zuciya kana tace “ Don Allah ina zaku kai Ni?”. Jiyowa Hanny tayi tana cigaba da Taunar
chewing gum kana tace “ Aikatau mana! Shi mahaifin naki bai faɗa Miki ba?”. Kai A'a Hanny Aikatau ai
wannan ta wuce ma aikatau mu fara kaita wurin Hajiya me gado . Haba ki kalli mace a tsaye ai kudin da
za'a samu da ita yafi na Aikatau kiyi tunani ”. Shiru Hanny tayi tana tunanin maganan Juwairy kana tace “
tabbas haka ne kuma , to mu wuce gidan Hajiya mai gadon yanzu kawai mana a Bamu kudin mu mu miƙa
ta ”.

To maganar dawo da itan kuma fa? Idan sun gama abun da zasuyi da ita ,ta nemi hanyar da kan ta ta koma
.

Duka babu zancen su ɗaya da A'ieee ta fahimta wannan yasa ta lumshe ido hawaye na cigaba da kwaranya
mata ”.

**

A hankali Alhaji Bukar Macciɗo ke bin Fahad da su Alex da kallo . Yayin da shugaba Alexander ne kaɗai ya
zauna a kujeran dake fuskantar na Alhaji Macciɗo . Cike da mamaki Alhaji Macciɗo ya furta “ Fahad su
waye wa'yannan ka shigo mun dasu har nan?”.

Cike da Arrogant voice ɗin shi ya furta “ Ok maka gane mu ba kenan . Mickel! Ya kira sunan mickel cikin
sarautar nan nasa da izza. Da Sauri mickel ya amsa da King Alex ”. Kayi masa Fashin baƙi....oh bar shi ma
bari nayi masa yanda zai fi shiga jikin sa .

Gyara zama Alex yayi yana kallon fuskar Alhaji Macciɗo ta baƙar tabarau din idanun sa . Shawara nake
baka da ka fita Hanyar King Alexander! Idan ba haka ba zaka sa iyalan ka cikin kuka da ƙunci. Daga yau duk
ranar da na sake ganin ka a mafarki na To lahira zata yi baƙo”. Dammmmm.....ƙirjin Fahad ya buga da ƙarfi
, King Alex? Dama wannan shine Alexander ɗin da nake jin sunan sa ? Tabbas haɗuwa dashi ma ko ƴan
uwan sa ne matsafa gudu suke yi , don kuwa ƙwarjinin sa da kuɗin sa ba na ALLAH bane . Cewan Fahad a
zuciyar sa . Thanks ɗan saurayi . Muryar Alexander cikin gurɓatacciyar hausan sa ya katse Fahad inda suka
juya suna ficewa daga Wurin . Alhaji Bukar Macciɗo kuwa ya kasa magana don mamakin waye wannan
yaron? .

A falo kuwa kiciɓusss suka yi da Hajiya Turai da ta fito a zafafe tana shirin cin masu mutunci amma tana ido
biyu da Alex sai jikin ta ya hau rawa . Baki na karwa ta furta sannun ku da fitowa ”. Sakin baki Diyana tayi
cike da mamaki tana kallon ta yayin da su Alexander kallon ta basu yi ba suka fice daga falon.

**
Tun da suka isa gidan A'iee take bin komai na gidan da kallo . Ko a mafarki bata taɓa yi da irin wannan gida
ba . Don a ƙauyen su suka ga wannan gida to babu shakka zasu ce ba a duniyar suke ba .

A wani falo ne taga ƙatuwar mata zaune ƙiban ta ta cike one seater tana zaune da matan da suke
kasuwancin matan su .

Zubewa har ƙasa Hanny suka yi suna kwarara mata gaisuwa, yayin da ko amsa su bata yi ba idanun ta na
kan A'ieee wacce ko ina na jikin ta rawa yake yi , don sam bata ji ta yarda dasu ba .

Cikin Muryar ta mai kaman na maza a tsaye ta furta “ Shekarunta nawa?” . Da sauri Hanny ta furta “ Sha
biyar ”. Girgiza kai Hajiya mai gado tayi kana ta kalli sakatariyar ta tana cewa “ Sakatariya sallame su .

Nufo inda suke Tayi tana kai hannu tare da ɗago A'ieeee . Ku cire mata kayan jikin ta muga komai yanda
zamu ga darajarta . Zare ido A'ieee tayi ƙwallah na ci ko idanun ta . Wayyo Mama , Don Allah kar ku
taɓa Ni Wallh Ni ba ƴar iska bace aikatau nazo.................!



*Hummmm yanzu za'a fara kar ki bari a baki labari a next page free page zai ƙare maxa hanzarta don
kiyi payment naki... regular group ₦500 VIP group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299
Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932*

*SUFY'S PRINT GRAPHIC DESIGN*

Your fevourite Graphic designer for any kind of Designs such as:
✒️LOGO DESIGN
✒️FLYER DESIGN
✒️3D LOGO DESIGN
✒️LOGO PACKAGE

✒️BIRTHDAY DESIGN
✒️WEDDING INVITATION
✒️DIGITAL INVITATION
✒️ADVERT VEDIO
✒️POSTER DESIGN
✒️STICKERS
✒️AND LOTS OF GRAPHICS DESIGN SERVICES

You can visit us at our Instagram Handle at:(Sufys_print_graphics)

...DM us for your Designs now at:
Whatsapp:07045125150
[5/21, 7:24 PM] Abu~ammar: *ZAKI*
_*The story of courage in hero's journey with secret desire*_


Last free page
6

*A page din free page ya ƙare . Ga masu buƙatar shiga grp na wannan littafi Regular group₦500 Vip
group₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta
Wannan number 08081202932*

_________________________

Idanun A'ieee ne suka fito waje Tana daɗa watso su Waje tsoro da firgici duka sun bayyana shimfiɗe a
fuskar ta . Yayin da Azuciyar ta ke cewa “ Wannan Wani irin Aikatau ne da mutum ba zai fara ba sai yayi
tsirara haihuwar uwar sa uban sa , Yayi zindir sannan za'a ɗauke shi .

Kai A'a Ni ba zan cire kaya na ba , Aikatau fa nazo! Ta furta da sauri tana yin baya . Shan gaban ta Hanny
tayi tana Ɗaga hannun ta tare da Sauke su tasssssss da mari akan kuncinta ”. Ni zaki lalata ma ciniki?
Shegiya bagidajiyar Yarinya! To ki sani ba matsayin yar aiki kike ba tamkar wacce aka ɗiyar dake haka
matsayin ki yake a yanzu”. Hanny ke maganar cikin tada jijiyoyin wuya wanda jin kalamanta ya ƙara furgita
A'ieee matuƙa ”. Nan take hawaye suka fara ƙwaranya a kan fuskarta . Innalillahi wai'innah ilaihir raj'iun.
Wayyo Mama na ki zo ki taimake Ni Baba ya sayar dani”. “Ƙayya!” Hajiya me gado ta furta tana gyara
zaman ta tare da ƙara yin wani ragwab da nononta wanda suka yi mata yawa , ko kuwa tsaban Karuwanci
ne a baya da a yanzu ta koma me safarar yara Yasa Suka zube allahu masani ”. Hanny bana Son hayaniya ,
ki sani na sayi yarinyar

3 / 17