Author : Aisha Maman Teddy Category : Taskar Novels
kuma imani”. Uhmmm
Kema dai kyama dai kya faɗa ”. Cewan Hajiya Rahima ,wanda jin hakan yasa Fahad yin shiru bai kuma ce
masu ta tafasa ba ”.
Tun da ya fara magar hawaye ke bin kuncin Mom juliana, Tsawon lokaci tana riƙe da hannun Yaron nata
,wanda take jin ƙaunar sa da Tausayin sa a zuciya . Mom zan tafi ina so ki kula mun da matata da abin da
zata haifa, Ina Son matarsa ina son Aysha . Miƙewa taga yayi yana nufin tafiya sannan yasa Mom juliana sa
hannu tana sharce Hawayen fuskar ta ,kana tace “ Aliyu! Damnnnnnnnn.......!!!” yaji ƙirjin sa ya buga da
ƙarfi , amma sai bai dakata da tafiyar ba ,a tunanin sa ba dashi take ba ,don bai taɓa jin wani ya kiransa da
makamancin Wannan suna ba ”. Da kai nake yi.....Ta furta tana Saurin takawa zuwa inda ALEXANDER yake .
Mom Wani suna naji kin kirani dashi na daban wanda nikam ban taɓa jin sa ba , sunana Alexander tun taso
wata da wannan suna nake . Girgiza kai tayi tana sharɓan wasu zafafan hawaye , a hankali ta furta “ Ba
SUNAN ka bane Wannan suna ce da ta biyo bayan sunan da mahaifin ka ya sanya maka . Sunan ka Aliyu
Haidar,kuma Ni a musulunci na haife ka ....ina mamakin baka taba tambaya na mahaifin ka ba Haidar . I'm
sorry mom Ban taɓa wannan maganar ba ko tambayar ba saboda nasan ke mahaifiya ce ta ƙwarai ba zaki
taɓa kawo Ni duniya da wata tabo ba . Ta hanya me kyau kika haife Ni , yo koda ta gurɓatacciyar hanya ce
to Mom sai dai ƙaddara,amma ba'a son ranki ba , Maganar mahaifina a yanzu lokaci ya ƙure, Na bar ki
lapiya ”. Rungume Mom Juliana na yan sakanni yana jin wannan shine rabuwar tasu ta ƙarshe wanda ba zai
sake ganin ba , Bare har suyi magana haka. Janye jikin sa yayi yana Ɗaga mata hannu alamun banƙwana
kana ya fice ,Wani irin kuka ne yazo mata nan take ta zube a ƙasa tana Wani irin kuka mai gurnani tamkar
zata haɗiye ran ta ta mutu ..... ALLAH ga Ɗana nan ,Allah kai taimake mun Aliyu ,Allah ka tsallakar mun da
ZAKI na daga dukkan Wani sharri da duk wani abu da zai cutar dashi da Rayuwar sa .
*
Egypt
Filin saukar jirgin ne duk da ya rage tawagarsa amma kuma kai daga Ni kasan babba ne ya shigo matashin
mai firgita manya , ALEXANDER sarki kuma zaki . Kallon sa A'ieeee keyi wacce take Gyefen sa yana riƙe da
hannun ta raaam suna mai nufar jirgin da zai iso dasu gida Nigeria . Kallon sa A'ieeee tayi tare da cewa “
Yanzu Kana nufin ka amsa musulunci kamar yanda na gani kuma naji da kunnni na? . Gyaɗa mata kai yayi
yana dan matsa yatsun ta a hankali . Amma banji sunan da ka sauya ba , don bana iya faɗan sunan ka ban
iya ba sam . Kallon ta yayi yana ɗan murmushi kana yace “ Aliyu Haidar . Yayi Miki dadi, idan kika haifa
mun ɗan cikin ki , ki sanar masa da Sunan baban sa Aliyu ”. Shiru tayi don har yanzu Hausar nasa a
gwarance take jin shi ,wannan yasa ta cewa “ Yanxu gida zaka mai dani? . Inshallah! Saurin kallon sa tayi jin
furucin inshallah da yayi , murmushi ya kuma yi mata yana cewa “ Hau step din a hankali ”. A hankali ta
saka ƙafarsa tana shigewa cikin jirgin yana biyo bayan ta . Wanda ko mintuna biyar basu dauka ba jirgin su
ta ɗaga zuwa gida Nigeria .
*
Tun da jirgin ya fara alamar sauka , ya tsaya yana kallon A'ieeee tare da kafe ta da wani irin mayataccen
kallo . Ina zamu rayu tare , da kin fahimci wani irin so nake Miki , ina jin ki a zuciya ta , ki kula sosai bana
son duk abin da zai cutar dake . Wannan kudi ne a ciki , duk abin da kika ga ya faru dani kar ki tsaya ki
gudu, kar kibi mutane na , ki nufi hanyar da zata sada ki da garin ku . Ki ba iyayen ki Haƙuri bisa abin dana
aikata Miki . Amma ki masu albishir da kin haɗu da mijin da ke mutuwar sonki,akan ki ya sadaukar da
komai nasa harta rayuwar sa ”.
Mu tafi . Taji Muryar sa ya katse ta kamin tayi masa wata magana a hankali suka fara sauka daga jirgin ,
ganin baƙar fata da tayi ta ko ina yasa Ai'eee tabbatar ba yaudara Alex yayi mata ba , Murmushi ta saki
tana furta “ Babu wanda ya taɓa mun alƙawari ya cika a rayuwata kamar ka , Kana da halarci tabbas
musulunci.......... Ɗauke Wuta tayi sakamakon ɗagowa da tayi tana ganin jami'ai Da sojoji sun zagaye Alex
sunyi attack din sa da Bindigogi suna daura bisa kansa . Ki gudu! Ya furta yana saurin matsawa daga gareta
Tare Da yin tamkar ba'a tare suke ba . Kasa motsawa tayi tana kallon sa , Idanun ta duka sunyo waje , mene
yayi maku? Ta tambaya kan ta tsaye ba tare da tsoro ko fargaba ba . Tare kuke! Wani soja ya daka mata
tsawa , Kamin A'ieeee ta basa amsa ne Alex yayi saurin cewa “ Ba tare muke ba , mene zai haɗa Ni da
Wannan wacce ba addini na ɗaya da itaba ,A taƙaice bahaushiya ce ban san ta ba .
Baka sanni ba ? Ta furta cike da mamaki ,wanda kamin ta kara wata magana Ahlaan ta iso da tawagar ta
,tana tafiya cike da izzah . A gaban Alex ta tsaya tana Sauke Baƙar Gilashin ta ,kana tace “ Wlcm to Nigeria
King Alexander, Fatan ka gane Ni da ƙyau? . Yesssss! Ya furta yana kafe ta da manyan idanun sa wanda suke
dauke da kwarjini . Kotu muka nufa kai tsaye yanzu kuma . Alright Ina Miki fatan nasara! Ya furta yana fara
takawa tare da shige moton jami'an . Baiwar Allah mene yayi maku? A'ieeee ta furta jikin ta na Rawa .
Kallon ta Ahlaaan tayi tana kai hannun ta tare da dafa Ai'eee kana tace “ Kema kina ɗaya daga cikin wanda
yake safarar ku ,don haka zamu je kotu dake ki bada hujja don a yau za'a yanke masa hukumcin kisa shi
nake tunani . Fizge jikin ta A'iee tayi, tana mai cewa “ Baki da hankali! Ni yar kauye ce ,bani da ilimi
ammma kuma kin san matsayina a wurin sa...................??? Tooohhhhh makaranta muje zuwa
*️ZAKI️*
Na
*Aunty Ayshatou Mamanteddy*
Book 3
61-62
_________________________
The Writer of :
1)Ƙwarton manya
2)the Sexy Boss
3)Gidan ƙwarata
4) Walijaam
5)ƙwarton manya
6)siyasata
7)my Lady boss
8)Ƴar tsakar gida
9)fyade
10)Ƴar aikina
11)ƴar waye
12)dijama yar Fulani
13)Bintoto
14) zuma da maɗaci
15)the virgin maid
16)Rainon soja
17)Duniyar shahara
18)Sadaka yallah
19)Gidan zaurawa
20)Ƙwayar sama
21) Bafullatanan Ruga
22)Taɓarah
23)x world duniyar shahara.
*And now ZAKI......*
_________________________
Littafin na kuɗi ne Regular payment ₦500 Vip payment ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299
Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932
Dakatawa Ahlaan tayi tana yin turusssss tare da kallon A'ieeee wanda take maganar ita kanta bata san mai
yasa Taji Tausayin Alex ya kamata a lokaci ɗaya ba . To wacece ke? A iya sanina bai hada jiɓi da Musulmai
ba ,bare kuma a musulman ma wai yarinya kamar ki bagidajiya . Jan numfashi A'ieeee tayi tana Furta “
Haka ne ,amma a wannan karon zakiyi mamaki idan nace Miki Ni matar sa ce ”. What??? Ahlaan ta furta
zancen tana fiddo da idanun ta waje,kana ta sheƙe da Dariya tana cewa “ kai Lallai Alex shaiɗani ne ,mu zai
saka ma fatsa da Ƴar ƙauye? Faɗa mana menene shirin ku?”. Sanin Shirin sa baya da amfani a gare ki a
halin yanzu , mafi amfanin shi ne ALEXANDER kuma sannan kun kama shi , Don haka indai kin san abin da
kike yi babu buƙatar duka wannan zancen a ganina kenan suka jiyo murya daga bayan su wanda cikin sauri
a tare suka juya don ganin mai faɗin wannan maganar ”.
Mom juliana ce tsaye wanda sam A'iee bata san lokacin da itama ta sauka anan ba . Wasu irin zafafan
ƙwallah ne ya fara biyo kuncin A'ieeee ba tare da tasan mene zata faɗi ba tace “ sun Tafi dashi Hajiya,
kuma bai aikata masu komai ba ”. Takowa Mom juliana tayi cike da dakewa kana tace “ Ki ƙwantar da
hankalin ki A'ieeesha , Mu saka ALLAH a gaba a bisa al'amuran mu , gyaɗa kai Tayi tana cigaba da kuka
Mom juliana ta kamata suna barin wurin tare da barin Ahlaaan anan tsaye ”.
*
Saukowa yayi cike da rawar jiki kamar bashi ba magana yake jikin sa har Rawa yake yi baya ko kallon gaban
sa ya furta “ Kina ina ne yanzu , kina ina ??? Gannn....gani nan zuwa . Ya furta yana ƙoƙarin ficewa daga
falon Hajiya Rahima wanda sam bai lura da yaran ta da suke zaune ba suna sauraren tashar labarai inda
ake gabatar da shari'ar da aka yanke mawa Sarkin matasan Nigeria wato king Alexander . Alhaji dakata
mana kaji wannan shari'ar ɗan .....ya isa da ALLAH ya furta yana saurin ficewa ko waiwaye babu .
Turus duka suka yi , kamin Mufidah ta furta “ Mom kaman Daddy baya farin ciki fa? Ko dai da wata matsala
ce .? Shiru duka suka yi don babu mai amsar tambayar ta . Nan take suka Cigaba da sauraren irin hukuncin
da aka yanke masa ,amma abin mamaki da Tashar take fadi al'umma da dama na mamakin Yanda bai ja da
Shari'a ba , kuma Duk da yana da ƙarfin dukiyar da zai iya dakatar da duk wata Shari'a da za'a yanke a
kansa amma kuma baiyi hakan ba ”. Wannan shike ɗaure ma al'umma da dama kai ,da kuma mamaki.
*
Zumbur Ai'eee tayi tana miƙa tare da ɗaura hannu aka tana fashewa da ihu tare da cewa “ Wayyo Hajiya
Hukuncin ɗaurin shekaru Ashirin da biyar a gidan kaso???????
*️ZAKI️*
Na
*Aunty Ayshatou Mamanteddy*
Book 3
63-64
_________________________
The Writer of :
1)Ƙwarton manya
2)the Sexy Boss
3)Gidan ƙwarata
4) Walijaam
5)ƙwarton manya
6)siyasata
7)my Lady boss
8)Ƴar tsakar gida
9)fyade
10)Ƴar aikina
11)ƴar waye
12)dijama yar Fulani
13)Bintoto
14) zuma da maɗaci
15)the virgin maid
16)Rainon soja
17)Duniyar shahara
18)Sadaka yallah
19)Gidan zaurawa
20)Ƙwayar sama
21) Bafullatanan Ruga
22)Taɓarah
23)x world duniyar shahara.
*And now ZAKI......*
_________________________
Littafin na kuɗi ne Regular payment ₦500 Vip payment ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299
Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932
Hawaye ne suka ciko idanun Mom juliana, wanda kamin tayi mawa A'ieeee wata magana , Sallamar sa ya
katse su . Tamkar wanda aka dinke bakunan su aka rufe duka suka tsaya suna kallon junan su ,su ukun
Wato Alhaji Abubakar Macciɗo, Mom juliana da kuma A'ieeee da Wannan shine karo na farko data fara
ganin baƙuwar fuskar Alhaji Bukar Macciɗo . Hajiya maryam! Maryamu baiwar Allah kece nake gani yau da
idanuna, kece dai Maryamu matata wanda na dauki tsawon shekaru ashirin da biyar ban saka a ido ba ”.
Ƙwallah ne suka ciko idanun Mom juliana tana kai hannun ta tare da gogewa tana sakin murmushi a
saman laɓɓanta ”.
Juyawa tayi ba tare da ta baima Alhaji Bukar Macciɗo amsoshin sa ba ta kalli A'ieeee tana cewa “ Wannan
shine mahaifin ALEXANDER wato Aliyu Haidar ”. Daaamnnn ƙirjin A'ieeee ya buga cikin sauri ta juya tana
kallon Alhaji Bukar Macciɗo mutum mai cike da kamala , Wannan shine mahaifin ALEXANDER? Mene ya
faru ya tsinci kansa a wannan rayuwar dana same shi? Tambayar da A'ieeee keyi ma kan ta kenan , kana
daga bisa Ni ta tsinci Muryar Mom juliana tana cewa “ Nice maryam wacce ka sani, Ka mance da komai na
Rabuwar mu , Sannan mu dauki hakan a matsayin ƙaddara ”.
Magana ta gaba bana kira ka ne don komai ba Sai don na roƙi taimako guda , ba wai dan wanda zaka
taimaka ya gaza ba ,a'a bana so ya ida rayuwar sa bai zauna tare da kai ba.
Hummmm jan numfashi tayi tana furta “ Na gaza Bama Yaron ka tarbiyya a matsayina ta uwa , ka yafe mun
Bukar ”.
Muryar Alhaji Bukar ne ya dauki rawa“ Hajiya Maryam kina nufin Yaro na Haidar yana nan a raye ? Yana ina
ina Ɗa na yake???? . Kallon sa tayi a tsayen da take ba tare da ta zauna ba , cikin dannewa ta furta “
Wannan matashin da aka yanke masa hukuncin shekaru Ashirin da biyar a gidan yari wato ALEXANDER the
young billionaire ba kowa bane fache yaron ka ɗan ka na cikin ka Aliyu Haidar.................!
Jiri ne ya fara ɗiban Alhaji Bukar wanda cikin ganin duhuwa ya lalibi kujeran dake gyefen sa yana zama ba
tare da ɗago ba , Wani irin juwa yake ji na ɗibar sa ,a hankali ya fara tunano haɗuwar sa da Alex na da
furucin sa garesa “ idan kai matsafi ne Ni babban ka ne! Ina yawan ganin ka a mafarki na tun ba yau ba ,to
ka sani ALEXANDER ya fi ƙarfin ka.......Huhhhhmmmmmm Wani irin Dogon numfashi ya sauke ,kana ya
furta “ Innalillahi wai'innah ilaihir raj'iun......!
Kuyi haƙuri Please page din bai yi tsawo ba
*️ZAKI️*
Na
*Aunty Ayshatou Mamanteddy*
Book 3
65-66
_________________________
The Writer of :
1)Ƙwarton manya
2)the Sexy Boss
3)Gidan ƙwarata
4) Walijaam
5)ƙwarton manya
6)siyasata
7)my Lady boss
8)Ƴar tsakar gida
9)fyade
10)Ƴar aikina
11)ƴar waye
12)dijama yar Fulani
13)Bintoto
14) zuma da maɗaci
15)the virgin maid
16)Rainon soja
17)Duniyar shahara
18)Sadaka yallah
19)Gidan zaurawa
20)Ƙwayar sama
21) Bafullatanan Ruga
22)Taɓarah
23)x world duniyar shahara.
*And now ZAKI......*
_________________________
Littafin na kuɗi ne Regular payment ₦500 Vip payment ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299
Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932
Ganin yanda Alhaji Bukar Macciɗo ya zauna hankalin sa tashe yasa Mom juliana itama zama a kujeran dake
fuskantar wanda yake zaune . A hankali ta fara kora masa bayanin Alex da kuma yanda Mom Silvaline wato
yayar ta ta raine sa , Daga karshe ta gangaro masa har Haɗuwar sa da A'iee da Aurenta da yaje Church aka
daura masa , Wanda a yanzu juna biyu ne da ita ”. Hummmmnnnn Jan Numfashi Daddy yayi mai karfi yana
saukewa kana yace “ Aisha kiyi Haƙuri da duk abin da ya faru ki yafe mawa yaro na bisa ga cutarwar da yayi
Miki ,tabbas ko wani Ɗan adam yana tafiya ne a bisa zanen ƙaddarar sa ,Wannan ƙaddara ce ta Alex
wanda ga makomarta duka ba zai mana dadi ba. A yau zan mai daki ma iyayen ki muje domin ayi masu
bayani mu kuma basu haƙiuri ”.
Kallon Alhaji Bukar Macciɗo A'iee tayi kana tace “ eh na san da Wannan amma kuma ban ji kayi maganar
fito da Aliyu ba, Shima burin sa kenan har muka shigo nan garin ,duka a tunanin sa zai je ga iyaye na ya
basu Haƙuri sai wannan Abin ya faru , zan fi jin dadin ace dashi a Wannan tafiyar zuwa gidan mu kaman
yanda shima yaso hakan .
Shiru su duka sukayi suna jin bayanin A'ieeee , Kana Alhaji Bukar ya girgiza kai tare da cewa “ Hajiya
Maryam zaki iya biyoni don muje ga Hajiyata sannan inaso na tara duka family na don nayi masu
bayani....ina mai baki haƙuri Maryam domin kuwa Ahlaan ƙanwar Aliyu itace wacce ta fallasa duk wani
Ayyukan sa ma ƙasa har aka kai ga Wannan matakin ”. Saurin ɗagowa Mom juliana tayi tana kallon Alhaji
Bukar kana tace “ ALLAH mai iko , ba komai bane ai , Sanadin Wani abu zaka ga Allah yayi sanadiyar
Haɗuwar babban Abu . Gashi zata ji labarin ɗan uwan ta ne , sannan kuma nima zan ga Ƴa ta wacce na
barta tun bata fi shekara ɗaya ba a duniya .
Girgiza kai Daddy yayi yana jajanta wa yayin da A'ieeee sam bata ma jin su , don data rufe idanun ta a
yanzu fuskar Alex kawai take gani yana sakar mata Wannan murmushin nasa Wanda ita kaɗai take ganin
irin sa daga gare sa. Ina Sonki matata! Wannan furucin nasa ta tuna wanda yasa ta zuba wasu irin zafafan
ƙwallah”.
*
4:00pm.
Shiru duka falon aka ɗauka tsawon mintuna goma daga masu kuka sai masu haɗawa dogon tunani. A'ieeee
ce na hango zaune kusa da Wata ƴar tsohuwa wato mahaifiyar Alhaji Bukar Macciɗo Hajiya Turai.
Allahu Akbar! Allahu Akbar!!! Tabbas ƙwarai Maryamu kinga Rayuwa , Kin kuma cika ƴar halak da kika kasa
sakin addinin Musulunci. Don haka inshallah wannan kin dawo cikin zuri'ar nan tamu kenan dawowa ta har
abada. Juyawa tayi ga Alhaji Bukar Macciɗo tana share hawaye kana cike da girma tace “ Tabbas kayi
kuskure daka raba ƴa da uwar ta , Ita Hajiya Rahima ba zata iya karɓar ƙaddara ba , data haifi yaro ya mutu
sai Maryamu zaka rarrasa ka amshi ƴar ta Ahlaaan da suka haifa a rana ɗaya ka bata? Shima Wannan
kuskure ne babba . Ƙwarai Ahlaan ki yafe mana duk da ban san Ni lokacin da aka yi wannan aiki ba ,amma
Tabbas Mahaifiyar ki kin yi sa'ar uwa ta gari mai sadaukar da farin cikin ta don