Sabon Salon Gidan Uncle Compelet By Oum Hairan.doc

Author :  Oum Hairan Category :  Taskar Novels

Chapter   12 / 13

33K to 36K   out of 38.4K words

tace  nagaji Saddam
bazan iya shiga kitchen ba bayana ciwo yakeyi shafa bayanta yayi yace  hqr zakiyi
ki shiga ki sama mana ko tea ne ni nan da kika ganni ko ruwan zafi ban iya dafawa
ba"
Janyewa tayi ta nufi qofar dakin tana hawaye zuciyarta tanayi ma tuntuntunin baya
lkcn da suke sha'aninsu da Uncle shattima har mantawa tayi da yanda ake girki da
safe kafin ta tashi ya hada musu komai da rana ya siyo ya kawo Mata da dare su fita
yawonsu sai sun qoshi su dawo, da wadannan tunane tunanen da Kuma kewar abinda
zuciya keso ta dafa tea din ta dora indomie ta soya qwai ta jere musu a dinning, ta
koma tana gyara parlourn bataji fitowarsa ba sai ji tayi yana cewa  aa kune da
safennan sannunku ku iso" dagowa tayi gabanta na faduwa suka kalleta sukayi dariya
daya cikinsu tace  yaya me ka samu a jikin wannan iskantacciyar yarinyar don
Allah?" Kallon me maganar yayi da sauri ya kalli Hudah da ta zuba musu ido jikinta
na rawa yace  Banson hauka Abidah ki tsaya iyakar matsayinki babu ruwanku da abinda
ya shafi sirrin dake tsakanina da matata"
Ta danji dadin amsar daya Basu ya nemi guri ya zauna suka tabe baki Suma suka zauna
a dinning din sukaja flat ya dago ya dubesu sukayi dariya tare da cewa ai dama mun
fada maka indai kayi aure mun daina girki abincin safenmu anan na rana anan na dare
anan" sunkuyar dakai yayi yaci gaba da cin abincinsa itama Hudah tana gamawa ta
shige daki saboda ta fahimci rashin mutunci suka qunso tana tankawa zasuci
mutuncinta, kwanciyarta tayi bata fito ba har suka gama suka tafi shima ya shigo ya
kwanta tanajinsa yana goga mata yar qaramar dick dinsa tayi banza dashi saboda
tayar Mata da kwadayi kawai yayi bai zunguro Mata inda ya kamata ba.......
# *UMMUH HAIRAN*
[9/24, 8:28 PM] OPEN AYES MULTIMEDIA: *_Pls paid before read, account Fauziyya
Tasi'u 0255526235 GTB ko hoton card MTN ta wagga number 09013718241 or VTU for
this number 09031307566 regular 200 VIP 500_*


*FTROGU23* Sosai yaso ta biye masa itakuma taqi ko kallonsa saima sake juya baya da
tayi hakan yasa shima ya qyaleta sukayi baccin a haka babu wata tarairaya bata
tashi ba sai wajen daya da rabi ta shiga ta watsa ruwa ta dauro alwala tayi sallar
azahar ta fito parlourn tsayawa tayi turus batasan sanda wasu zafafan hawaye suka
zubo Mata ba ta rinqa bin parlourn da kallo flat din glass din da sukaci abinci
dasu duk an farfasa su a qasa duka ukun sannan anyi Mata watse da shayi da taliyar
yan yara duka akan center carpet dinta ta tsugunnawa tayi ta fara gyara gurin tana
hawaye ta goge ta gyara ko Ina tsaf sannan ta nufi kitchen ta dora abinci yunwa
na qwaqularta kasancewar ko breakfast batayi ba.
Jallop din cous-cous ta hada lemo ta zauna tanaci suka shigo dukkansu su ukun babu
ko sallama ta dago ta dubesu ta kawar dakai taci gaba dacin abincinta hankalinta
kwance daya cikinsu tace  yar hutu ashe kintashi har kinyi girkin dama yunwa
nakeji" zama sukayi a dinning din suka faracin abincinsu Abidah tace  babu laifi
akwai zaqin hannu" itadai batace musu suci kansu ba tana gamawa ta dauke nata
kwanukan takai kitchen ta dawo ta kwanta, tana danna wayarta sai lkcn ya fito yana
hamma ya dubesu suma shi suke kallo ya zauna a kusa da ita yace  yunwa mijinki
yakeji amarya" kifa wayar tayi a cikinta tace  inajin akwai abinci a dinning"




Miqewa yayi ya nufi dinning din ya zauna ya bude food flast din yaga wayam ya
kallesu Suma suka kalleshi suna miqewa sukace  to yaya saimunzo cin na dare" juyawa

yayi ya kalli Hudah yace  Ki tashi ki dafamin wani abincin wannan dai babu" miqewa
tayi da sauri tace  babu?" Daga Mata Kai yayi tayi murmushi tace  tabdi aikuwa
saidai ka fita ka nemo abinci wlh na gaji ba iya yin wani girkin zanyi ba"
Baice Mata komai ba ya miqe ya sanya kayansa ya fice tabisa da kallo tare da tabe
baki ta miqe tayi komawarta daki sai dare ya shigo tayi masa sannu da zuwa ya amsa
Mata babu yabo babu fallasa ya ajiye kayan daya shigo dasu ya nufi bedroom yayi
wanka ya dawo ya zauna tayi sallar Isha tayi shirin kwanciya tazo zata dauki
wayarta ya janyota jikinsa ya kwantar da ita yace  kamar akwai abinda yake damunki
ko?"




Girgiza masa Kai tayi yace  ok don Allah kada ki tankawa su Abidah duk abinda
zasuyi Miki kiyi hqr mama batason bacin ransu sannan ki rinqayin girki dasu harma
maman ana Kai mata bakiga fadan da tayimin ba dazu dana shiga wai anyi mawa yayanta
wulaqanci akan abinci harma kinyi musu gori kince kayan abincin a daga gdanku
kikazo dashi" janye jikinta tayi tace  kuma kai ka yarda nayi musu?" Sake janyota
yayi yace  ya zaayi na tabbatar tunda bana gurin nidai nasan matata ta gaji arziki
batada halin matsiyata" daga haka bai sake bata damar cewa qalaba ya hade bakinsa
da nata ya fara tsotseta da sarrafata sunyi nisa sosai sukaji an banko qofar suka
miqe da sauri tana gyara rigarta Mama tayi tsaki tace  aikin banza qiba a muqamuqi
wahalalle sallamamme daga shigowarka harta fara lalubeka wannan bazata barka kayi
qibaba, kika wani tsareni da idanunki na karuwai ki tashi ki dafamin ruwan zafi
kisamin a flast dinnan zanyi wanka dashi"
Saurin dagowa yayi yace  amma mama duk yayanki ki rasa me dafa miki ruwan wanka
saikin tsallako titi kin taho nan?" Karkacewa tayi tace  yanzu dai tuhumata kakeyi
kenan ko saboda nasa matarka aiki ko?" Miqewa Hudah tayi tana maqale qirjinta ta
dauki hijjab ta sanya ta nufi kitchen ta dora ruwan zafin zuciyarta na suya tana
tunanin wanne irin dangin miji Allah ya hadata dasu a haka ta tafasa ruwan ta zuba
a flast din ta dauka takai Mata ta karba tace  kin taimaki kanki Kuma idan naje
naji bai tafasa ba komai dare saina dawo"
Hudah kam taga tasku tana fita ya rufe qofar da key ya janye matarsa suka shige
daki yanata rarrashinta saida komai ya kammala shidai yana samun gamsuwa 100%
itakam tsokanota kawai yakeyi yau mararta har ciwo tayi ganin hakanne yasashi dole
ya rinqa amfani da yan dabaru ya samu yaga ta samu gamsuwa sannan ta tashi tayi
wanka shidai baiyi ba da janabarsa ya kwanta abinda bata taba gani ba gurin
Shattima iyakar jarabarsa indai ya kwanta da mace sai yayi wanka yake bacci.




Washegari su Aunty Ubaidah sukazo da Amba ta yini tana murna duk da bata samu zama
ba saboda hidimar gurkin da taketayi ranar Amba taga ikon Allah qannan mijin yarta
kamar zasu takata sukazo suka dauki abinci suka tafi bayan fitarsu ne ta zauna suka
taba hira nan suke sanar da ita ashe tun ranar da aka kawota Shattima yana kwance
baisan waye akanta ba tausayinsa ya cikata tayi qasa da kanta tana share qwallah
magunguna Amba tabata sukayi sallama suka tafi suna fita ta dasa gurbin kuka
tananan zaune tanata yi Musaddam ya shigo ganinta haka yasashi qarasowa da sauri
yace  lfy waye ya mutu?" Cikin zaquwa tace masa  Uncle" gabansa ne ya fadi yace  to
me Kuma yayi?" Dagowa tayi tace  don Allah kakaini na dubashi bashida lfy baisan ma
waye ke akansa ba" ga mamakinta sai taji yayi tsaki yace  yanzu akan wannan zaki
dagamin hankali to bazaki ba" yana fadin haka ya shige daki tabisa da sauri tana
kuka tana  don Allah Saddam badan ni ba hankalina bazai kwantabs idan banje
nagansa ba" cikin masifar kishi yace  idan an rataya ajalinsa a rashin zuwanki to
yau ya mutu wlh indai Dr Musaddam ne yake amsa sunan mijinki bazaki duba wannan dan
iskan kawun nakiba bakisan dama ciki nake dashi ba akansa zan iya cimiki mutunci
fiye da tunaninki sakara kawai da batasan haqqin aure ba daga zuwanki kwana biyu
har danginki sun fara gorantawa qannena suna cewa su talakawane kalmar da wannan

shashashan qanin babar taki ya dade yana fadamin  me nasama yaci balle yaba na qasa
harta fara zagaya dangina to kisani inma zaki cireshi aranki ki cire na rabs duk
wata alaqa dake tsakaninku har abada idan kalma daya ta shiga tsakaninki dashi ko
bana guri ban yafe ba"
# *UMMUH HAIRAN*
[9/26, 7:35 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: *FTROGU24* Kallonsa takeyi cike da mamaki
saidai ta kasa cewa dashi komai ta juya zata fita ya riqota yace  bazan rinqa binki
dakinki kamar wani yaronki ba ki dawo ki kwanta anan" hakanan ta kwanta babu yanda
ta iya tanata jan zuciya shikuma yana danne dannensa a system har batasan lkcn da
bacci ya dauketa ba saida ya gama abinda zaiyi sannan ya hauro gadon ya kwanta.
Hakanan ta daukarwa kanta kullum zasuyi waya zata tambayi jikinsa amma bata taba
kiransa ba har zuwa lkcn da suka fita Cairo aka dorasa akan magani ya dan samu
sauqi ya dawo.
Rayuwarta a gidan mijin nata babu wani Abu na dadi da zata dorar kullum qannensa
cikin yimata rashin kunya suke idan tayi mgn shikuma yace batada hqr idan ta sanar
da mahaifiyarsa sai tahau sababi tana fadin zata raba Mata kan yaya, duk ba wannan
yafi damun Hudah ba aa rashin son ibadar Saddam shine abinda ya fara gallabar
rayuwarta zata iya qirga adadin lkcn daya tashi yayi sallah da asuba, Koda tama
matsa masa da tashin kashedi yayi mata me nauyi akan cewa kadata qara tashinsa.




Dole ta qyaleshi idan Kuma garin ya waye saidai taga ya shirya ya fice lamarin da
yafara sanya Mata kokwanto, lkcn da tayi watanni hudu ta kasa jurewa saboda daren
jiya tayi masa mgn akan ibada har cewa yayi da ita shifa zai iya sakinta akan
wannan takurar da takeyi masa, ta kasa jurewa hakan yasa ta kira Nusaiba tana kuka
take zayyane Mata komai Nusaiba tayi salati tace.
 Au shikuma haka yake? Aa bafa zai yuwu ba addini shine gabada komai ki fadawa
uwarsa tayu masa nasiha idan yaga dama saiya gyara idan Kuma bai gyaraba ba ke ki
fadawa iyayenki su sai su nema Miki mafita" hakan kuwa akayi washegari tashirya
taje gidan momy tasameta da mgnr budar bakinta tace  yo ai ba kabarinku daya ba ina
ruwanki da rayuwarsa ko dole sai yayi abinda kikeso"
Hakanan ta taso jiki babu qwari ta taho gida ranar tayi kuka dz nadamar abubuwa da
yawa ga Saddam ya qaro wulaqanci sai yakai 1:00am awaje sannan yake shigowa gidan
idan tayi masa mgn yace aikine ya riqeshi,




A cikin wannan yanayin Allah ya azurtasu da samun qaruwar juna biyu sosai takeshan
wahala ciwon ciki da Kuma kasala ga rashin son warin komai hakanan dai take daurewa
tayi abinda ya zama dole sauran ta qyale, da farko tana qoqarin girka abinci badon
kanta ba saidon mijinta da yan'uwansa Amma lkcn da cikin ya fara qwari sai ta ke
kasa hassala komai saidai bacci, nanne fah baba binta ta sakota gaba kullum da
tsirfar da zata tsiro da ita yau tace sakwara takeso gobe tace dambu,
Koda tace bazatayi ba bazata iyaba saboda batajin zata iya yima uwar mijinta
gardama, yau tun dare ta tambayesa zataje gda takuwa yi saa yabarta ta tashi tayi
duk abinda zatayi ta shirya bazata iya tuqiba hakan yasa yace tazo ya sauketa, lfyr
Allah yakaita gida yanata Mata Hira ita Kuma abinda ke damunta daban yau dai tayi
niyyar fadawa Abba gskyr abinda ke akwai saboda takasa hqr Kuma tasan zamansu bai
dace ba indai bazai gyara ba"
Yana sauketa ya juya a cewarsa sauri yakeyi ita Kuma taja qafarta ta shiga gdan da
sallamarta Adnan da Jiddah sukayo kanta a guje suna  ga aunty Hudah ga aunty
Hudah" wannan ihunne yasa Shattima dake kwance ya tashi zaune gabansa na faduwa ya
zuba mata ido ta kawar da nata dake cikin nasa ta zauna tana tambayar yaran Ammi,

Saukowa Ammi tayi tace  gani amarya wannan mijinaki da kullen masifa yake cikin
wata takwas wannan shine zuwa na biyu tabe baki Fatah yayi ya koma ya kwanta,
batare da yace Mata qala ba to itama kashedin Saddam yasa taqi tanka masa Ammi tana
latsata tace  meye ya ramar dake haka Hud?" Murmushi tayi cike da kunya tace
 bsnida lfy ne Ammi ga aiki don Allah ki samamin me aiki take Dan kamamin aikin
gidan ya fara yimin yawa musamman yanzu da nake fama da ciwon ciki"
Jinjina kai tayi tace  bayan nan akwai wani Abu Hudah kada ki boyemin" satar kallon
Shattima tayi idanunta ya ciko da qwallah ta miqe da sauri ta shige dakin Ammi,
itama miqewa Ammi tayi tabita ta isheta tanata kukanta ta zauna kusa da ita tace
 ni nasan da damuwa Hudah meye kuma" bata boyewa Ammi komai na abinda yafi damunta
a zaman aurenta ba sosai ammi ta Jinjina lamarin tace  aikuwa wannan ba qaramar
matsala bace bari na Kira Abba yana sama yayi baqo" fita tayi bata jima ba ta dawo
tace taso muje saiku gaisa da Alh Ibrahim dinma" miqewa tayi suka fita yanzu
Shattima bai parlour suka nufi saman




Mutumin da suke tare da Abba kawai ta zubawa ido tana kallonsa gabanta na faduwa
shima abinda takeji yakeji aransa tadai samu ta zauna suka gaisa Abba yace  Hudah
ga Alh Ibrahim nasan bakisanshi ba rabonki dashi tun kina wata bakwai" sake
gaisheshi tayi ya amsa da fara'arsa yana binta da kallo waiwaye na hasko masa
shekaru ashirin baya kawai sai yake hasko fuskar Ummuh matarsa data rasu da cikinsa
a jikinta akan fuskar Hudah tsoro ya kamasa yanajin wani yanayin qauna me tsuma
zuciya yana zagaya zuciyarsa game da Hudah.
Abba ne yace  kafin Mahaifiyarta ta rasu ta sanar da Khadija cewa ita yar Adamawa
ce Maybalwa sannan ta ambaci sunan wani mutum waishi Moddibo Almud...." Dagowa yayi
da sauri yace  Moddibo Almud?" Kallonsa sukayi dukka jikinsa yana rawa yace  me
waye yane sunanta?"




Shiru Abba yayi yana tunani can ya dago yace  ummuh Salma" wata kabbara Alh Ibrahim
yayi yace  ya akayi haka ta faru ko zan iya ganin hoton wani abu wlh Hudah ko
kokwanto banayi yatace ta cikina rungume Hudah Alh Ibrahim yayi yana kuka me taba
zuciya yana shafa kanta yana cewa ashe dama qaunar jini nakeyi Miki Hudah tunda
nabar qasarnan zuciyata taqi hutawa da tunaninki"
Sun jima a haka kafin daga bisani komai ya daidaita Alh Ibrahim yayi musu sallama
ya tafi nan Ammi ta zayyane masa komai Abba yayi shiru yana nazari ya dago ya
dubeta yace  ki shirya kawunki yakaiki gida zan nemi musaddam din zamuyi mgn"
Shattima dake shigowa ya tsaya yana kallonta yace  driver yakaita mana Abba ni
inada abinyi" daquwa Abba ya watsa masa yace  kai nace kakaita ba driver ba"
kallonta yayi yace  kuje Hudah duk yanda mukayi dashi zakiji" miqewa tayi ta fita
har ya shiga motar ta bude gabanta na faduwa ta shiga yaja a fusace ya fice ta
rinqa yimasa kwatance har suka isa bakin get din ta bude ta fita ta shiga gidan
yabi bayanta da kallo yana furzar da iska yace  Allah ya isana wlh duk ya qararmin
da Mata kawai don qaddara tasa tashiga gdansa"




_Kuyi hqr na jina Shiru da kukayi jiya nayi fama da ciwon Kai har yanzun ma ba
sauqi yayi ba_
# *UMMUH HAIRAN*
[9/27, 6:28 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: *_Pls paid before read, account Fauziyya
Tasi'u 0255526235 GTB ko hoton card MTN ta wagga number 09013718241 or VTU for
this number 09031307566 regular 200 VIP 500_*

*FTROGU25* Juyawa yayi da kan motarsa daidai lkcn da ta shiga gdan ta bude ta shige
ciki ta nufi dakinta domin zafi takeji sosai, ruwa ta watsa ta fito parlourn ta
zauna tanashan iska daidai lkcn da Saddamya shigo kamar an jefoshi batayi aune ba
taji ya dauketa da mari ta miqe da sauri tana Shirin yin mgn ya sake dauketa da
mari yace  ubanwa ya baki izinin kula wannan dan iskan dama ashe munafurta ta
kikayi kikace min zakije gda ashe gurinsa kikaje?"
Tsuma jikinta yakeyi sosai tana hawaye tace  zargina kakeyi Saddam?" Nunata yayi da
yatsa yace  an zargeki din ai dama ke abar zargi ce a gurina komai ma zaki iya wato
dokar dana sanya Miki ita kika karya ko to ki koma inda kika fito na sakeki saki
daya...."




Dafe kanta tayi da sauri tace  Innanillahi wa innah ilaihirraji'un Saddam akan dan
wannan abin" juyawa yayi ya shige ciki shima kuma sai jikinsa yayi sanyi wanka yayi
ya sauko da sauri lkcn tagama hada komai nata tana Shirin fita yace  kada ki fita
wlh bansan na furta ba ki dawo muci gaba da rayuwarmu Hud kishinki ne yasa har nayi
wannan subutar bakin"
Janyewa tayi zata fita yayi saurin datse qofar ya fusgota ta fada jikinsa ya
matseta yana sunsunarta yace  ki daina karyamin doka Hud inasonki bana fatan rasaki
don Allah" duk yanda take kuka Saddam Bai kulata ba saida ya gamsu ya qyaleta ta
miqe daqyar ta shiga dakinta tayi wanka ta kwanta tanajin zazzabinta na qaruwa da
haka bacci ya dauketa,
Washegari kam kulleta yayi a ciki saboda tsoron kada ta fita ya fita bai jima ba ya
dawo ya shigo dakinta ya isheta a galabaice yayi Mata sannu ya fita, wasa? saida ta
kwana uku tana jinya ko gdansu bata fada ba Nusaiba kawai ta fadawa ita taketa
taimakonta da ayyukan gdan tana tausayawa qawar tata halin da take ciki.



Kwanaki sun danja tafiyar ba wani dadi takeyi ba babu wata kyakkyawar jituwa
tsakanin ma'auratan ga Kuma dangi miji a gefe da basa uzuri duk da halin da matar
yayan nasu take ciki qa'ida ne sai tayi musu abinda ta saba tanayi musu idan batayi
ba kuma matsala ta haifi, yaudin ma kamar ko yaushe tana kwance cikinta na damunta
da ciwo sai juyi takeyi babu wani mataimaki sai Allah taji an banko qofar an shigo.
Daqyar ta daga idanunta ta dubi me shigowar Mama Binta ce da yayanta biyu ta
yunqura a hankali ta miqe zaune tace  sannu da zuwa mama" daga mata hannu tayi tace
 sannunki rama take sani nazo jin ba'asin dalilin da yasa kika daina yimana girki
ne" qasa tayi da kanta idanunta ya ciko da qwalla tace  banida lfy ne mama kwana
uku komai bana iyawa saidai qawata tazo ta taimaka min...." Daga Mata hannu ta
sakeyi tace  ko asibitin murtala ce ke dole tunda kike auren dana kayimin abinda
nakeso idan ba hakaba Kuma a dauki hanya a koma aci gaba da abinda aka saba sannan
yanzu maza ki tashi ki kirbamin sakwara da miyar ganda"




Girgiza kai tayi cikin kuka tace  wlh Mama bazan iyaba kiyi hqr idan naji dama zuwa
gobe sai nayi miki ..." Dauketa tayi da mari kafin tayi tunanin wani abu sun rufeta
da duka ta ko Ina ta rinqa ihun neman taimako qarshe dai bata tashi farkawa ba sai
ganinta tayi a gadon asibiti tana waiwayawa taga Ammi da Abba suka matso gabanta
sunayi Mata sannu bata iya amsawa ba sai hawaye da takeyi daidai lkcn da Shattima
ya shigo ya dubeta

12 / 13