Rayuwar Raihana Part 3 By Sumayya Abdulkadir Takori .pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   9 / 9

24K to 25K   out of 25K words

your hand?”
Da sauri kuma a razane ta ce,
“Wa?”
“Yaya Khalipha!”.

Wuta ta daukewa Rayhanah, ta rasa abin da za ta ce masa. Ba ta san sanda ta ce,
“Kai ka taba rike hannun Aunty Nabilah? Saboda kai ne ba ta so na!!!”.
Very shocked Ibrahim ya zama, ya dauke wuta dif! Ashe da wayonta take yin abu irin na yara,
gidadawa. Kuma ashe har tayi masa farin sanin da har ta fahimci akwai wani abu tun tana
karama tsakanin sa da Nabilah Abdulqadir. Yayi ta maza Ya ce,
“Ai ni namiji ne mijin mace hudu ne, ko na rike hannunta bani da laifi, tunda zan iya karawa
da ita. Ke kuwa tare kuka balaga da Khalipha gida daya, ga soyayya da kusanci mai nisa a
tsakaninku, INA KIIISHIIII Rayhanah.......!!! Has he ever did it???”
Duk da amsarsa ta farko ta bugi kirjinta, amma yadda ya yi sentence din karshe ya
gigitata...... tana kokarin kashe wayar ya fadi da karfi.
“Kada ki kuskura ki kashe min waya Rayhanah..... zamu yi mummunar sabawa. Na ce
Khalipha ya taba rike hannunki ko wani abu makamancin haka?”
Cikin rawar murya ta ce,
“Eh”.

“Sau nawa?”
“Sau daya ne Allah”.
“A ina?’
“A kafar benen gida”.
“Sai kuma me?”
“Wallahi Allah shi kenan”.
Sai ta fara kuka tun karfinta. Bata taba ganin irin wannan mutumin ba mai neman kada a
zauna lafiya da titsiye no rhym no reason (babu gara babu dalili). Sai kawai ta ji ya kashe wayar.
Ba a jima ba ta ji shigowar mota harabar gidan, wayarta ta yi kara, shi din ne. Ta sake
dagawa hannunta da jikinta duk suna rawa.

“Zo ki bude min kofa, bazan danna‘doorbell’ ba, kada in tada Inna”.
Ba karamin razana ta yi ba, da ta mike tsaye don cika umarninsa ji ta yi hajijiya na dibar
ta. A haka ta bi bango ta fita daga dakin ta ratsa ta falo ta bude mishi kofar.
Kayan barci ne farare sol a jikinsa masu dan kauri. Ta ba shi hanya ya wuce cikin falon,
amma ita ba ta matsa daga inda take ba, ta rabe a jikin kofar.
Ibraheem zama ya yi cikin tausasan kujerun falon ya nutsa hannuwansa cikin tarin sumar
kansa, ya sunkuyar da kai ya yi shiru. Shudewar mintina goma a hakan sannan ya dago
idanunsa jajir ya dube ta.
Tana rabe a jikin kofar kamar mai jiran ya gama abin da zai yi ya fita ta rufe kofarta. A zafafe
ya ce,
“Ki daina yi min wannan kauyancin da gidadancin da kike mini, a Turai na ganki kina rayuwa
cikin Singaporeans, har shigarsu kin iya, ba a Takai na dauko ki ba. Am not here for what you
think, o.k?”
Ta sadda kai kasa. Hannunshi na dama ya mika mata......
“Zo mu yi hira!”
Jikinta na makyarkyata ta ce,
“Ni barci nake ji”.
“Tunda na kasa kema ba za ki iya ba”.
“Ya Himu don Allah ka zo ka tafi, Inna na fitowa alwalar asubahi, don Allah ka rufa min asiri,
cewa za ta yi ni na kirawo ka.....”
Halin da yake ciki bai hana shi yin dariya ba, gaba daya ta gama firgicewa kamar mai
fargabar kada mijinta ya kamata da kwarto.
A tausashe ya ce,
“Zan tafi, but on one condition....”
Ido ta zazzaro masa tana jiran jin condition din. Hannu ya kara miko mata.
“I only want to kiss you again! Rayhaanah don Allah.....!! Zan miki addu’a Allah ya saki a
aljanna!!!”.

Ba ta motsa daga inda take ba, sai shi din ne ya taso ya tako a hankali ya tadda ita har inda
take. Irin rikon da ya yi mata da amsar da yayiwa bakin nata, ya tabbatar mata he will go far
beyond abinda ya roka din, za ta gayawa aya zakinta idan ta sake ta bashi dama.

A lokacin ne Inna ta fito don yin alwala, ta kuwa yi kyakkyawan gani, sai ta juya a hankali da
baya da baya har ta buge keyarta da kofa.
Sai karfe shida Ibrahim ya bar gidan. Jikinta babu sauran kuzari ta zauna a kujerar falon tana
nemo consciousness din ta da diminishing gigicewarta. Sai da Inna ta tabbatar ya tafi sannan ta
fito ta yi alwalarta ta wuce daki ko uffan bata ce mata ba.
A ranta addu’a take musu tana kuma roqon Allah da ya bawa Rahane soyayyar Ibrahim cikin
sauki. Ba kamar yadda suke tararrabi ba itada Baba Dacta. Yasa abinda ta ganewa idonta
yanzun haka yake har zuciyar Ibrahim!!!

Littafi Na 4 na dauke da karashen labarin kuma tare suke da Dan uwansa. Taku har abada;
Sumayyah Abdulqadir
( TAKORI).

9 / 9